Showing 6001 words to 9000 words out of 113608 words

Chapter 3 - TSINTAR_AYA

Start ads

09 Aug 2025

686

Middle Ads

had'u da kowa ba se mutanen dayake da tabbacin idansu biyu wato munafukan fada, ya tabbatar munafukan fada idansu yanzu yake bude ma, be wani damuba ya haura samansa da ita.

Yafi minti 30 yana tunanin abinda zeyi da yarinyar har lokacin idanshi be kaishi akan tafukan k'afarta, daga bisani sai ya mik'e ya debo ruwan sanyi ya soma kokarin dawo sa ita hayyacin ta ta farka amma ga alama she's unconcious dafe kanshi yayi ya kalli lokaci k'arfe hud'u saura yan mintuna, yaya zeyi? Family Dr. nasu yawa message akan by 6 ya kasance a b'angaren sa akwai patient daze duba masa sannan ya koma yaci gaba da aikin kallon ta har zuwa sanda yaji ana kiran sallan asubah wannan ne ya tilasta masa mik'ewa ya d'auro alwala ya fita masallaci!

Bayan idar da sallan yajima sosai yana lazimi bayan yayi azkhar d'insa da komai sannan ya mik'e tsaye yana duba message d'in likitan dake tabbatar masa da cewar baya k'asar gaba d'aya, k'aramin tsaki yaja ya fito sekuma yayi karo da Muhseen dake jiransa a k'ofar masallacin dakuwa ko ba'a gaya masa ba ya tabbatar cewar yana masallacin a irin wannan lokacin musabaha sukayi sannan yabi bayanshi zuwa ciki danya tabbatar baze samu amsar komai ba se'a rubuce. Turus Suka tsaya suka kalli jama'ar dake wurin motar Mood ciki kuwa hadda me martaba, k'arasawa yayi shida Muhseen atake muhseen ya zube ya gayar da Me martaba, shikuwa yayi tsaye tamkar an dasashi a wurin ya kafe Me martaba da ido yana jira yaji mezaice wanne kalan labari zezo dashi yau kuma da sanyin safiyar nan, shid'inma shi yake kallo cikeda takaici

"Munaso musan wannan jinin daya fito daga motarka daga ina yake? menene asalin abinda ya faru? munyi tsammanin cewar ai rauni kaji sekaga fess dakai, amma wannan layin jinin dayayita d'iga har zuwa k'ofar d'akinka yake tun daga mota, gashi ana iya hangowa daga motar daka hau jiya aciki akwai jini a sit d'in baya dukda bame yawa bane ba, meke faruwa?" Har wannan lokacin be motsa ba ya daddage ya kafeshi da ido bayako k'iftawa, Muhseen ne ya rik'o hannunsa suka kalli juna yamai magana irinta kurame ma'ana sighn Language yace dashi

"Bro mana meke faruwa? karka bari wani mugun abu ya faru dakai a wannan safiyar, bannason kafiyar nan kakuma sani please talk" Nan d'inma kallon Muhseen kawai yake seda ya gama k'arewa Muhseen kallo sannan yayi amfani da sighn language(Yaren kurame) yace dashi

"Duk Munafukai ne fa! bakaga suna kallona ba, sunsai komai kome zanyi konace bazan wanke kaina ba sun gama shirya komai tsaf so i will not say a word" Dafe kai Muhseen yayi, Me martaba yace da Muhseen

"Ni banna gane wannan yaren na kurame kai Muhseen meyace maka? Wasu yawun takaici ya had'iya sannan yace

"Ni d'inma be bani amsa ba" Gyaran tsayuwa Me martaba yayi sannan yace

"Idon Masarauta sun tabbatar mana da cewar da mace ya shigo rai a hannun Allah tana d'akin sa, mukasan wacece? yau bazan lamuntaba wlh, muje d'akin nasa" Matse hannunsa Muhseen yayi amma seya warce hannun ransa a tsananin b'ace ya juya zuwa d'akin duk suka rufa masa baya ciki kuwa hadda sarki....... Tun a parlor k'asa ya tarar ma'aikata sunyi cirko cirko suna tsegumin jiya ya shigo da mace a hannu kuma maybe rauni taji jini duk a k'asan tile basuma goge wurinba tsabar sonjin mezaije yazo, ganin me martaba ya tilasta musu zubewa a k'asa dukkansu suna kwasar gaisuwa shikuwa cikeda sassarfa ya haura saman inda duk jama'ar suka rufa masa baya. Be b'ata lokaci ba wuri bud'e k'ofar d'akin dayake mallakin sa, duk kuwa suka rutsa aciki ciki kuwa hadda Muhseen dake fatan abunda suke son gani karsu gani d'in sedai kuma turus suka tsaya kallon 'Yarsha dake zube akan gadon zaninta a yafe kawai rigarta ata gaba a yage sumar kanta a hautsine sannan yanayin fuskarta kad'ai ya isa bayyanar maka cewar bata cikin hayyacinta, Me martaba cikin k'araji yace

"Hamood!!! meka aikatawa 'yar mutane wai? wacece wannan kwance a haka, Hammod neman matan naka haryakai kawa 'yar mutane fyad'e ka kawota cikin fada!" Babu alamun tsoro ko fargaba a tattare da Hammod girarsa ta sama ta had'e tas data k'asa fuskarsa babu annuri, beko motsaba amma ya tabbatar wannan shirine, baze tab'a iya kare kansa ba anyi amfani da tsananin tausayin dayake dashi akan al'umma an had'a kai da yarinyar dabe saniba an cutar dashi, anyi destroying rayuwar sa acikin sa'o'i dabasufi 12 biyu, da wanne bakin ze kare kansa koda yanadashi tunda wanda suka aikata masa sun shirya abunsu tunkafin yasani, ya afka acikin muguwar ramin su, ya tsunduma sosai acikin bak'in kogin da aka k'irk'ira domin sa kawai!! Muryar yarinyar ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin dayaje na wuccin gadi!

"Karka k'onamun k'afata, ban maka komai ba, kayi hak'uri, dan Allah kaikuma karka mun fyad'e, karka zo kusa dani, ku rabu dani karku ketamun haddi na, niba 'yar iska bace dan Allah kayi hak'uri" Wani uban ihu ta saka sekuma ta farka a zabure, ganin mutane a kanta kuma duk maza ya sanya tayi azamar soma rufe k'irjinta dake a bayyane, sannan ta soma gyaran zaninta tana kuka sosai! kalaman datake furtawa sune suka tabbatar da zargin dake zuciyar Hammood akan cewar had'a baki akayi da ita ake shirin cutar dashi, sannan tsawon dare yana tare da ita amma bata farkaba seda suka shigo wannan duk shiri ne. Salati wurin ya d'auka Manyan Fada suka dinga tsinewa Hamood, seda surutu ya lafa sannan Me martaba ya taka har wurin da yarinyar take yace yana kallon ta

"Ki kwantar da hankalinki yarinya, nan wurin kina wurin dazamu k'watar miki hakk'inki da tsare mutuncinki, kina hannun iyayen wanda basuda iyaye" Cikin kuka tace

"Hijabina zaku bani intafi dan Allah" Idan D'an Galadima ne ya sauka a kan tafukan k'afanta yahau salati

"Me martaba kalli k'afafun yarinyar nan, wai anya akwai imani akan Mood kuwa, haba mana se maganar karya k'ona mata k'afa takeyi" Ita dai se kuka take su kuwa mutane se lek'en tafukan k'afarta suke suna k'arawa da salati, sallamar kowa me Martaba yayi ya tura akan akira masa Jakadiya, yarage a d'akin iya shine dakuma Hammod se kuwa 'Yar Shara, kallon sosai Me martaba yayi masa sannan yace

"Ka sauk'ak'a abubuwa sosai agareni Hammood, nagode daka bari mukazo wannan lokacin acikin sauk'i kajiko" Har lokacin kallon sa yake bayako k'iftawa idan nan ya kad'a yayi jajir jijiyoyin dasuke a murd'e se walk'iya suke gaba d'aya sun k'ara fitowa sunyi rud'u rud'u, zuwa wannan lokacin zuciyarsa tafarfasa takeyi k'irjinsa se ciccira yake alamun abubuwan na shirin taso masa, suna haka Jakadiya ta iso, janye fuska me martaba yayi daga ta Hamood koda wane lokaci karonsu baya kwashewa lafiya besan dalili ba shikam

"Jakadiya a suturta yarinyar nan fyad'e aka mata, a duba idan akwai rauni a jikinta, a k'asan k'afarta duka biyu akwai rauni me alamun k'una ce, zan tura akawo likita kokuma akaiku asibiti, na baki izinin ajiye duk abinda kike ki kula da ita sosai dan kuwa Matar da Hammood ze aura ce, daga yanzu zuwa lokacin dazata samu sauk'i" Zubewa k'asa tayi tana me.jadda da masa bin umarnin sa shikuwa Hammod siririya dariya yayi yanzukam wacce harta bayyanar da sautin muryarsa da babu wanda ya tab'ajinsa a duk fad'in duniya! shi kanshi bazece ga amon sautin dariyar saba sabida bayi yake ba, Aransa yace here we are @ last! Dama nasan da manufa akayi dukkan wannan shirin, girar sa d'aya kawai ya d'age har lokacin murmushi bebar fuskar saba, Me martaba yace yana kallon Jakadiya

"D'akin dake kusa da nasa zaki gyara mata, ai b'arnar sace, idan mun gama gyarata sesu tare" Har lokacin bece komai ba se murmushi haka me martab'a ya fice yabarshi a tsaye, Jakadiya ta hau gyaran 'Yar shara da har lokacin kuka takeyi, tanayi tana mata sannu sabida yanayin tausayin datake bata a ranta tanata tsinewa Hammood akan b'akar halayyarsa mara kyau.....Yajima sosai tsaye yana k'arewa 'yar shara kallo, tunda yake tsanar mutane be tab'a tsanar wata halitta sama da wannan halittar daya zata abar tausayi bace ada, dajin sautin kukan nan nata gwanda jiyo sautin kukan mutuwar sa, ya tsani munafuki, bayason munafuki konan dacen, meya mata wacece ita? zata d'and'ani kud'arta a hannunsa tabbas! Muhseen ne yazo yaja hannunsa suka bar d'akin kai tsaye ma gidan yajashi suka bari sukaje gidansu muhseen d'in, atake ya rubuce masa tun farkon ganinsa da ita dakuma abinda ayake zargi zuwa yanzu, nisawa Muhseen yayi sannan ya fara magana a hankali

"Ban saniba ko abinda kake tunani hakanne amma banaso ka yankewa yarinyar hukuncin abinda bashikenan ba, wannan zargi kawai kake amma bamuda tabbacin cewar had'in baki ne, abu d'aya na sani, acikin biyu kodai hakan take had'in bakine kamar yanda kace kokuma inaga an sarane akan gab'a" Cikin fusata ya soma magana irin ta kurame ransa a b'ace

"Muhseen niba yaro bane ba, nasan sarai me suke nufi dani, tayaya wannan yarinyar duk inda nabi acen itama takebi? mesa ze zamana seni kad'ai, sunyi amfani da halina da suka sani na tausayi suka cutar dani, kaima kayi tunani mana ina iyayen yarinyar? daga faruwar abu se zancen aure? kaji sun tambayeta danginta ne? kokuma kaji sun tambayeta wani abu daya faru a tsakanina da ita, they used me suka kuma cutar dani, gayamun idan kaji sunyi wata magana dake nuni da cewar basusan komai akanta ba, ka dubafa ka gani muhseen awurin dana sameta ita kad'ai ba kowa, jinin dake fita ajikinta is not real, they planned everything they set me up" Ya k'arashe alamar maganar da hawaye a idanshi" Jinjina kai Muhseen yayi

"Yanzu na hango abinda kake hangowa tun d'azu mood, yanzu na harbo jirgin tabbas shirine, amma ya zamu b'ullowa lamarin? Da hannayensa yaci gaba da amfani da sign language wurin yi masa magana

"Sun rigada sunje sun gayawa Mami nssani, bansan mezance mata ba yanzu, she will not listen to me, please muhseen help me out" Rungumesa D'an uwan nasa yayi yana patting bayansa a hankali

"Calm down mana Mood, komai zezo ya wuce ne kamar yanda na baya suka wuce kaji" Shiru dukkabsu sukayi se sauke ajiyar zuciya da Mood keyi cikin jin zafin zuciyar sa.

**********

Gabaki d'aya kan Hafsat ya d'aure, bazata manta meya faruba itada wad'an nan gayun, lokacin da take k'ok'arin tserewa se k'afafunta suka gaza, k'unar dake k'afarta ya tsananta azaba, hakan ne ya tilasta mata tsayawa tana mayarda numfarfashi har suka cimmata, a lokacin ne ogansu ya musu umarni akan su b'are masa ita haka suka dinga jan kayan jikinta har sukayi nasarar rabata da zaninta da hijabinta suka kuma yaga mata rigarta, tayi iya k'ok'arinta taga cewar ta k'waci kanta amma haka suka daddage seda suka rabata da har pant d'inta, sesukayi rashin sa'a tana period, bayaga haka kuma ya b'alle mata tamkar ruwa sabida tsananin firgicin datake ciki, ogansu dayaji haushin haka seyace shiba k'azami bane bazeyi ba amma gudun data sakashi su lakad'a mata shegen duka, wannan ne abinda ya k'ara haukatar da ita dan kuwa tasha duka sanda sukaga bata iya koda iya d'aga k'afarta sannan suka tsere suka barta agun tsirara! To meyasa wad'an nan mutane masu magana daban suke cewa wani ya mata fyad'e ita babu wanda ya mata fyad'e, hasalima a fuskar wanda suke alak'antawa da fyad'en bata tab'a ganin saba, dan harga Allah sanda yaje gunta bataga fuskar saba batamasan me take ba, shin meke faruwa da itane a rayuwa? su waye anan kuma waya kawota nan d'in?.......

***************

Lokacin da Hammod da Muhseen sukazo wurin Mami sun jima a zaune kafin ta fito, bayan sun gayar da ita ta amsa sekuma sukayi shiru, sedaga bisani Muhseen ya gyara zamansa ya kwashe komai ya gaya mata yanda ya faru da yanda abubuwa suka juye, kallon nutsuwa tayi masa sannan dayake matsalar ta iri d'ayace da Hammood sunaji amma basa magana seta shiga mayar masa da sighn language cikin fad'a

"Shishi kad'ai yafi kowa yawan mak'iya a masarautar nan, idan bashi bane yayi meye nakaita d'akinsa, idan taimako yakeso ya kawota guna mana, koya kaita wurin daya dace, yakaita a sibiti mana ko ya kira en sanda, yanada iko isa da matsayin daba wanda ze tunkareshi akan yayi karya idan ya aikata d'aya daga cikin wad'an nan, ina goyon bayan me martaba, hukuncin sa daidaine tabbas seya aureta" Tana k'arashe maganar ta mik'e zuwa ciki ranta a b'ace. Mik'ewa Mood yayi ya lumshe idansa, banda mahaifiyar sa, baze tab'a jurar fushinta akan saba har abada, Muhseen da azama ya mik'e ya rik'eshi amma seya zame hannun sa ya soma aikin daya saba wato gudu yana zuwa b'angarensa gaba d'aya yayi umarni akan a sallami hadiman sa baya buk'atar aikin aransa yana nazarin yanda zeyi sa wannan wawiyar yarinyar seta yabawa aya zak'inta seya wulak'anta asalinta indai sunan sa Hammood!!

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA* FREE BOOK


*BILLY GALADANCHI*


*SHAFI NA HUD'U*


kai tsaye d'akin da aka tanada dominta ya shiga yana me banke k'ofar da iyakacin k'arfin sa, idanuwansu suka tsark'e dana juna atake jikinta ya soma b'ari tana zaune asaman gado ta takure wuri d'aya se rarraba ido takeyi! Yafi mintuna goma a tsaye yana kallonta bece komai ba, seda dan kanshi ya gama tunanin dayake sannan ya juya da zummar barin d'akin abinda yajiyo je daga waje ya dakatar dashi ad'an lobin dake tsakanin waje dacikin d'akin

"Bari bari bari prince mood anji haushi, ai yanzu ance ko sarki yaji komai, jakadiya ta tabbatar wa sarki wannan yarinyar 'yar hannu ce cikine sukaje su zubar yazo da gaddama, ance tutsiye yarinyar akayi ta fad'i gaskia akan dama saurayintane dasukaje azubar da cikin daya mata shine fa aka samu matsala seya d'akkota ya kawo ta nan besan asirinsa ze tonu ba" Dariya d'ayar tayi

"Daba sunce aure zasu masa da itaba? to yanzu naji ance sarki yace a koreta tunda abun hakane, yazata hakk'inta yaci daze d'aura aurensu yanzu kuwa korace" Tafawa sukayi

"Bakiji yanda na tsani yarinyar ba wlh, da akace ze aureta nace su kurma an iya zab'e wannan yarinyar kyau kamar aljana shegiya se gashi,yanzu danaji labarin za'a koreta se wani sanyi ya mamayeni, dankuwa ni wlh inasan sa haka" Duka d'ayar ta d'aka mata a cinya

"Banza yafi k'arfin ma'aikata da bayi ki kama kanki" Be jira sun k'ara wata maganar ba ya fito daga d'akin,yauma kamar kullum beko kallesu ba ya shiga d'akinsa jikinsa a matuk'ar mace wai meke faruwa ne? menene gaskiyar maganar mutanen nan su kuma manyan munafukai ba? yaya yakejin maganar tana juyawa up side down?..... Mik'ewa yayi yanzun ma da sassarfa ya sakko k'asa ya nufi motar sa, beko nemi Muhseen ba dankuwa yaga motarsa a sukwane ya nufi gidan *UNCLE JAY*.......

Tunda Anty Barra taji tsayuwar motar da gudun tasan D'an kurma ne agidan yau kamar yanda take kiranshi, dan hakanda azama ta juya daga parlor zuwa ciki

"Uncle Jay bazan iya da rigimar Kurma ba, naji tsayuwar motarsa nakumaji gudunsa dan Allah ka tashi kaje" D'ago kai yayi ya kalleta yana murmushi

"Dama nasan zezo ban tsammanin zezo yanzu bane ba" Murmushin ta mayar masa "amma lafiya dai?"

"Ba lau ba dai, Mood ne bashida wayau ko kad'an, duk abinda zeyi seya saka rashin wayau se uban zurfin ciki da miskilancin tsiya" Tana kallon sa harya kai aya, nisawa tayi tace

"Ka saurareshi yanzu, tunda yazo mayi maganar daga baya" Mik'ewa yayi

"Noo wife agabanki zamuyi maganar muje kawai, its good kina wurin with those ur boosting idea's i belive abubuwan zasuje mana da sauk'i" Ba musu suka fita atare hannayensu sak'ale ana juna, a parlor suka sameshi harya shigo yana zaune akan sopa ya sunkuyar da kanshi hannayensa duka cure acikin sumar kansa. Gaisawa sukayi dashi da yarensa sannan ya mik'awa Uncle Jay duk abubuwan da suka faru a rubuce a takarda har gulman dayaji ma'aikatan dayace a kora sunayi, ga alama be isa yace ayi ba ayi a yanzu! Tare da Barra Jay ya zauna suka karance takardar tatas kallon sa yayi sannan yace

"Naje gidan da safe gun Maminka tamun bayanin farko akan yanda ka shigo da ita, dakuma ya da maganar ta k'ara juyewa akan na ciki, sedai sarki be yarda da maganar jakadiya ba akamar yanda kaji ana tsegumi, hasalima ya kashe wannan maganar, abu d'ayane ya dai ya kafe akan seka auri yarinyar ranar juma'a" Da sauri ya d'ago ya kallesa,cikin yare irin nasu kurame da tsananin b'acin rai ya soma magana da hannayensa wannan karon har kansa da wuya mosti yake yana yi tamkar ze tashi sama. Seda ya lafa sannan Uncle Jay ya kalli Barra

"Barra me kike hasashe, da gaske kema abinda muke zargi akan had'in bakine da yarinyar haka kema kike zargi" D'an shiru tayi na wani lokaci kafin ta nisa tace

"kaso saba'in harda biyar acikin d'ari yana nuni kai tsaye da cewar had'in bakine musamman idan akayi duba da yanayin yanda al'amura suke tafiya acikin fada tsakanin Mood da sauran 'yan uwansa kai harma da mahaifin sa daya haifeshi da cikinsa,na biyu kuma ita yarinyar bata musa akan dikkanin abubuwan da ake cewa ba alhali ya tabbatar mana cewar ta ganshi sanda yaje d'aukan ta har tashi tayi se kuma ta kasa, kaga anan ya dace ta kareshi idan har taimakon daya mata yakai mata matsayin taimako bawai sharri ake k'ulla masa da ita ba. Abu na biyu kuma shine kaso 25 acikin d'ari suna nuni da cewar faruwar komai co-incidence ne kawai aka samu, duba da irin wowtar dashi yayi, mesa sanda ya d'aukota bezo nan gidan ba, besa beje wurin Muhseen ba, shin mema ya hanashi zuwa gun Mami koya sanar da ita a waya, wannan zargine dabaze goguba musamman da idon Fada suka tabbatar k'arfe biyu ta wuce sanda ya shigo da ita, CCTV ma ya shaida hakan, bayaga haka ga jini kuma, bansan yaya ze faruba su k'ulla sharri irin wannan hadd fake jini, kaina yana k'ullewa sosai" Ta k'arashe maganar taname jingina bayanta da bayan kujerar. Gyaran zama Jay yayi

"Melon think mana, say something please" Nisawa tayi

"I need an

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login