Showing 54001 words to 57000 words out of 113608 words

Chapter 19 - TSINTAR_AYA

Start ads

09 Aug 2025

706

Middle Ads

tsaraban 4msd cols" Daria Cylia tayi

"Ku gaba d'aya bakuda right ba kuda freedom, just text back an tell him directly that you are at the coffee shop" Seda tayi nazarin cylia sannan ta aika masa reply

"At a coffee shop with my friend's, akwai wani damuwa ne?" Mik'ewa yayi tsaye da mamakinta d'auke a Fuskar sa sanda ya karanta sak'on nata, aranshi yace "Ni takewa magana haka, lallai yarinyar nan kinji gishiri, jikinsa yana rawa ya kara aika mata sak'on

"Which area" Nunawa Cylia tayi sukayi dariya Cylia tace

"Brother d'in kin nan yanada abun daria, ur no more a kid fa" Dariya sukayi tayi mass texting address d'in sukaci gaba da hirar su, Bilal dama duk bayan kwana biyu yakanzo domin karb'ar balance asan me ake buk'ata a shop d'in, Dan haka yauma yana zuwa sukayi karo dasu Hafsat, kai tsaye wurin datake yaje ya zaune yana dariya ita d'inma dariyar tayi ganin sa yace

"'Yar k'asarmu, Kingston coffee namu da yawa fa, duk nazo sena ganki anan" Murmushi tayi sannan tace

"Kaima ai coffee d'ance take kawo mana kai anan, toni danazo meye naka aciki? Yana Murmushi yace

"Wannan shop d'inane fa, kuma ni ina ruwan karb'ar balance ne kawai, kinsan ni inason kasuwanci Lamar me, banaso Nike dogara da kud'in mahaifina ko something like that, Kuma kinsan agarin nan basa rena Sana'a koma meye zaka kass to kuwa zasu siye, shisa kikaga inata k'arewa wurin nan girma, bayan coffee kinga akwai snacks da irin dishes nasu" Murmushi tayi

"Zanso nima na iya kasuwancin nan, amma yanzu karatu nake sena kammala tukunna" Jinjina kansa yayi

"Allah ya taimaka, d'an jirani ina zuwa please" Ya k'arashe maganar yana barin wurin, be komaba ya dawo koda yazo harsun mik'e tsaye shi d'inma bin bayansu yayi yaketa ayiwa hafsat hiran zezo gidan su da dare, k'awayenta sula hau bus ita kuwa ta jeru dashi suna magana cikin sakin fuska, dama sosai takeson sabawa dashi. Mood ganin message nata kuwa be tsaya komai ba ya kamo hanyar zuwa inda take, sedai abinda ya bata mamaki ganin ta tsaye tare da Bilal suna hira cikin raha da sakin fuska "Yarinyar nan tana hauka ne wai? Yaya za'ayi ace tana mingling da Maza tamkar batasan matsayin ta na auren as dazatayi ba, meye haka Bilal yake shirin koyawa Hafsat d'in? Yana nan mota a zaune yaga Bilal ya bud'e mata mota ya wangale k'ofar ta zauna a mazaunin me zaman banza shikuwa ya zagaya yashiga ya tashi motar suka bar wurin, kasa hak'uri yayi ya rubuta mata message

"Where do you think you are going with that man? Batako zaro wayarta daga hakaba jin vibration alamun shigowar sak'o, Bilal yana Murmushi rik'o hannunta kallon Data wurga mai ne ya tilasta masa sakin ta yace

"Am sorry na saba ne da mutanen wannan k'asar mantawa nake karkiyi zargin wani abu daban" Murmushi tayi

"Ba komai ka kiyaye kawai" Yanajin dad'i yace

"Hafsat kina burgeni sosai, ur very straight forward, bakida kwana kwana, ina son mutum me irin halinki na gaskia, zanso ace in auri made nagartacciya kamar ke" Murmushi tayi Kafin tace

"Aure kakeso kayi? Kallonta shima yake

"Auren bawai ya sameni bane, kawai ganin ki ne ya bijiro dason auren" Murmushi tayi

"Yanaga bakabi hangar zuwa gida? Yana Murmushi yace

"Akwai abinda nakeso in nuna miki ne" Jinjina kai kawai tayi sukayi shiru na wasu mintuna, har suka isa wani katafaren wuri babba me kyau, Murmushi yayi mata sannan yace yana kallon ta

"Wannan kamfanina babba na sarrafa sanyaye zuwa ganyen shayi, Bilal Tea dazaki gani a duk fad'in k'asar nan tokuwa nawa ne, na bud'e coffee shops a kusan state bakwai dake garin nan inayi ne matsayin marketing kinsan 'yan k'asar nan basason musulmai, yanzu yanzu sesu manna maka hauka, yanzu haka ina gina irinsu a Nigeria da Kuma k'asar Cairo suma suna shan shayi sosai, saudia ne next target d'ina, duk abinda na mallaka a duniya yana k'ark'ashin harkar nan, harkar Tea kuwa Harna tafarnuwa inayi yanzu, kuma ban tsaya anan ba nikam shiga tafarnuwa daga Nigeria dakuma citta da kanunfari duk sunaso amma basuda shi sosai ina samun alkhairi sosai, ina miki wannan bayanin ne ina Kuma nuna miki dukiyata sabida akwai rai akwai Kuma mutuwa, na nunawa Khairiyya da mijinta kwanaki yanzu ke Kuma na nuna miki" Murmushi tayi arayuwa tanajin dad'i sosai mutum ya nuna mata muhimmancin ta arayuwar sa, tana kallon sa tace

"Your a very hard working man, Kuma dama haka akeson Namiji a jajirce, me tsayawa tsaye k'yan akan neman na kansa na maka murna sosai, Allah ya Sanya alkhairi da albarka acikin duk wata Sana'a dazaka Sanya agaba" Yanajin dad'i yace "Ameen My rose" Murmushi tayi ta langwab'ar dakai

"Sunan yayi dad'i sosai fa" Hannu ya zira a aljihu

"Muje ciki kiga office d'ina" Agogon hannunta ta kalla tace dashi

"Ka Mayer dani gida, Wataran idan muka fito zanzo nagani" Shagwab'e fuskar sa yayi abun tausayi "Haba mana Rose why not now? Langwab'ar dakai itama tayi

"Yaa mood zemun fad'a sosai, Hasan time damuka tashi a school" Jinjina kansa yayi sannan yace

"Amma gaskia sena saya miki chicken wurin wani d'an Nigeria daya k'ware sosai a harkar gashin kaza anan garin" Murmushi tayi

"Ba damuwa muje" Suka k'ara jiyowa suna jere suna hira tamkar sun shekara da sanin juna, kallon skirt d'in Hafsat Mood yayi na uniform daga nesa bak'in cikine ya taso masa tamkar zeyi ihu, haka yaja motar da yabar wurin zuwa gida aranshi yace "Nigeria zata koma, zaman me zatayi anan tana yawo da wannan mugun skirt d'in fake bayyana tsiraici, ace duk rad'in garin uniform nasu haka yake a d'age, ina sam baze iyaba wannan ai iskanci ne, Kuma meye na yawo da Bilal, yaran nan bajin magana yake ba akan me zataje fita yawo bayan an tashi a school? Su kuwa seda sula sayi ice cream, kaza, chocolate sannan suka wuce gida gaba d'aya,a gate ta sauka da kaya nik'i Nik'I ta Nufi cikin gidan, gaba d'aya hankalin Hammood a tashe yake, shida kansa yasan cewar bashida nutsuwar zuciya, a k'ofa ta had'u dashi fuskar nan tsabar b'acin rai yayi ja sosai, idan nan ma yayi jajir hankalin sa kana kallon sa kasan atashe yake, wanda Kuma duk yasan yanda Hammood ke fitina daya ganshi ze tsere dan kuwa iya wuya yake, amma Hafsat dayake akwaita da kafiya akan abu seta d'auke kanta gefe garda sanya wak'ar jirginso a bakin ta, sanda tazo daf dashi d'an sunkuyawa yayi a hankali ya bayar dashi beko kalleta ba harta shige ciki dan kuwa ze iya shak'eta har lahira. Da sallama ta shiga kai tsaye Kuma d'akinta ta wuce ta tub'e uniform nata ga fad'a ban d'aki dana period take, seda ta gyara ajikinta sannan ta dawo d'akin tiger dress ta zura kawai ta Zare ribbon dake kanta sumar manta ya tarwatse taja wanda ke rufe mata fuska zuwa bayan kunnenta taja gajeran tsaki a hankali

"Kitso nakeso nayi wlh, bansan ta ina zan fara neman me kitso agarin nan ba, San tambayi kuyangin nan waye aciki ta iya kawai tamun, ban Mason wahalar da sumar nan ke bani, aske rabinta ma zanyi bazan iya ba" Tana nan tanacin kazar tana lumshe idanta akan banko k'ofar d'akin ganin Hammood ne ya Sanya ta mik'e a tsaye tana Zare ido

"Yaa Mood sannu da zuwa" Ta furta muryan ta yana rawa, abincin yabi da kallo kafin ya k'are mata kallo itama, sumar kanta data baje ya taka a hankali har inda take ya damk'oshi tamkar ze tube gashin ihu ta k'walla abinda ya janyo hankalin khairiyya zuwa d'akin kenan tace

"Ayyah wai nikam baka hak'ura ba? Nace maka Kayi hak'uri tunda Bilal ne zan masa magana ya dena d'aukan ta suna yawo, ita Kuma ka mata maganar kwad'ayi kullum haka take dawowa daga makaranta dan baka nan ne, dan yanzu kaga bamuda tabbacin cewar iya Bilal d'in kawai take bi, gaskia Hafsat baki kyautawa kanki ba, bin Maza kina yar gidan girma ina dad'i, shidai gaskiya Bilal namasa waya yace coffee shop ya had'u dasu kawai ya zaga da itane taga gari Kuma yaune farkon fitarsu a tare" k'ara matse sumar kan nata yayi ya Sanya idansa anata, seda ta tsorata da ganin yanayin sa amma gaba d'aya seta kasa koda motsi, kantane yake tsananin sara mata, a hankali ta soma ganin jiri gashi ya rik'o gashin kan nata da iya k'arfin sa,hannunta takai ta d'aura Akan nasa hawaye ya gangaro daga idanta, bece komai ba Kuma be saketa d'inba, so take ya daketa akan wannan yawon zuciyar ta hanashi sukuni, bean mesa yake kasa aiwatar da hukuncinakan Hafsat ba shi sam bayason take yawo, tsoron maza yakeyi har gobe yana tunawa da Maryam, budurwar sa ta farko data fita yawo da friend d'inta yayi mata fyad'e harta rasa ranta, dukda maryam ita ke haukanta akansa amma besan yanason maryam ba seda ta mutu, tunawa da yanda Bilal keda mugun son matan tsiya ya Sanya shi k'ara matse sumar kanta, yauji yake kamar baze iya danne maganar datakeso yayi ba, cikin murya cen k'asa tace

"Yaa Mood Kayi hak'uri, ka sakeni kaji, ban tan's zuwa yawo ba wlh, yauma yaa Bilal ne yace na rakasa" Jin sunan Bilal data ambata ya Sanya ya k'ara sanya iya k'arfin sa ya matse suma, bata iya k'ara koda motsi bane, hannunta dake kan nasa kawai ya tafi luuuu ita d'inma gaba d'aya seta saki nauyinta akan sumar daya rik'e idanta ya rufe ruf, da sauri ya taro ta, ya sake sumar kan nata yana Jinjjigata, khairii dale fatan Allah yasa Hafsat mutuwa tayi tace

"Honey la gani ko, kasanfa Bahar tace mana ba lafiya ta ishi Hafsat ba akanta, lallab'ata kawai zakayi bawai dukaba, kuma rik'on sumar kai irin haka akwai azaba" cak yayi sama da ita zuwa kan gadon ta, ya bud'e k'aramin fridge dake wurin ya d'akko ruwan sanyi ya b'alle murfin robar ya kwarara mata amma ko gezau! Hankalin sa ne ya tashi sosai, ya kwasheta driver kawai ya kira suka bar gidan, bayan motar ya sakata ya zaune shima a abaya ya d'aura kanta a saman cinyar sa, banda kallonta babu abinda yake, lana ganin yanayin ta kasan cewar she's in deep pain, to meyayi zafi haka? Se danna k'irjinta yake amma ba numfashi, da k'yar yaga sun isa asibitin, aka karb'eta zuwa Emergency. Iyashi da driver suka zo Kuma ko wayarsa bezo da iya ba, kusan 2hours tana jiran gawon shanu Kafin likita yazo kiransa.

A Office likitan ya kalle sa da kyau yace

"Na duba file na patient d'inka, lokacin da akace ku dawo a mata surgery baku dawo ba, Kuma yanzu gashi wani abu ya k'ara dukan kanta kome jinin kan nata ya k'ara yawa, jijiyar dake kula da d'abi'un d'an adam na kanta wani jinin ya Kuma harbawa aciki, na rasa dalilin dayasanya bakwa kulawa da lafiyar yarinyar nan, anya kuwa iyayenta suna tare da ita? Kofa damuwa bamaso tana shiga kaga yanzu da k'yar muka shawo kanta, Zata tashi lafiya lau amma tabbas bazata iyayin komai da babba keyi ba, zakuyita hak'urin behavious nata zuwa wata uku masu zuwa, semuyi aiki mu cire jinin duka, Zara samu lafiya bayan nan, yanzu idan muka tab'a kanta komai ze iya faruwa" Nisawa yayi, mekenan yayi? Kawai sabida zuciyar sa ta rufe seya hauta da zalinci, kallon Dr d'in yayi

"Nagode dr, zuwa yaushe zamuke zuwa check up Kuma yaushe zaku sallame mu?

"Se zuwa gobe gaskia koma jibi, se munga jinin dake fita a hancinta ya dena zuba gaba d'aya" Jinjina kansa yayi sannan yayiw likitan godiya ya karb'i takardar maganin yafita, driver ya tura yaje ya d'akko masa kuyangi biyu inda yafita sayen maganin.

Lokacin da yake magana da nurse d'in akan zancen maganin daya saya,lokacin ne Amina da Barira suka shigo asibitin barre dayasan dasu ba, atare suka kalli juna sannan da sauri suka koma da baya suka lab'e, Amina jikinta had rawa yake sanda ya zaro wayarta da aka Tanada aka bata aka turo mata wani ya kawo mata layi takanas sabida irin wannan aiki, Message ta turawa wata lamba da cewa

"Bayan was biyu ka kirani, akwai labari meban al'ajabi" Seda sula kimtso kansu suna ganin ya nufo kofar barin wurin suka fito, atare sula gaishesa be amsaba ya kaisu d'akin Hafsat suka duba ta, sannan yabarsu anan ya tafi.

*Jiya taro ya tab'an keyboard d'ina gaba d'aya na gagara typing, da k'yar ko yanzu nayi wannan ya sayan keyboard bana gane kansa, zuwa dare zan Baku post d'inku na dare, nisha Allah, koma yamma*

Mom Nu'aiym.

*Mutan wattpad sam bakwa kyautawa, Rowan comment, ga rowan votes, da gaske zan dena posting muku.*

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

   *NA:BILLY GALADANCHI*

*Masu tambaya akan yanayin ciwon hafsat, tabbas ana samu, anyi a unguwar su antyna, nasan yarinyar kuma har yanzu datayi aure ta haihu befi idan abun ya tashi mata ba tayi wasan k'asa, idan fatan kun gamsu.*


*SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI*
17.
Seda suka zauna sannan suka kalli juna, gano yanayin cewar Hafsat bata cikin hayyacinta ya sanya Amina tace

"Kinji abinda naji kuwa? Kinga abinda na gani Barira? Kamar fa Prince Mood nagani tsage tsage yana magana da waccen nurse d'in ko" Ita kanda Barara mamaki bawai ya barta bane ba ta kalleta cikin jimami tace

"Amma ke Amina banace ki rabu da shiga shirgin Idan fad'a ba? Banace ki rabu da d'aukar muhimman maganganu kina gaya musu ba, ke yanzu 'yar wannan gulmar damuke a tsakanin mu bata ishemu ba sekin d'auki magana kinkai wa idan fada, kuma kina sane da cewar k'yas kawai suke jira kisa ma zasu iya yi" Turo baki gaba tayi

"Haba Barira ke sam bakya tab'a dubawa ci gabanmu koda wane lokaci ci bayanmu kawai kike kallo, a bauta zamu mutu? Iyaye da kakanninmu haka suka k'are suka auri bayi suka tabbata a bayin su, yanzu mu banbancinmu dasu d'aya shine munsamu mund'anyi makarantar bokon nan, a duk cikin fad'in fada gayamun idan ba idan fada ba wayake ta tamu? Magana idan kikaga sun mana toko tabbas aiki zasu sakamu, da gaske tona masa asiri zanyi kowa ya huta" Rik'o hannunta Barira tayi

"Kada kiyi haka Amina, nifa ina ganin ma kamar bawai magana yake mata ba, koke kinji sautin muryar sa, akan wane dalili ze dawwama da harshe me motsi yana dak'ushe tasirin sa, wane d'an adam ze tabbata kurma har'a wurin matar sa alhali yana magana, nida ina tunanin kawai motsi yake da bakinsa tunda kinga har hannun sama yana motsi, ta yiyu matar batajin yaren kurmanci, kinga dole yayi yanda zata fahimta" Shiru Amina tayi tana kallon yanayin Barira tare da tunanin kumafa hakane? Barira ganin Amina ta d'auki maganar datake gaya mata yasanya tace

"Idan fada ko jininsu basu ragawa ba bare mu, ya dace mu tabbatar dakoma meye kafin mu sanar dasu, bayaga haka yanada kyau sosai mu iya kame bakunan mu mu dena shiga sha'ani irin wannan daya shafi rayuwa da mutuwa, kiyi komai amma ki kiyayi d'aukan hakk'i wannan shine iyakar abinda zan iya gaya miki, idan kunne yaji gangar jiki ya tsira" Nisawa tayi

"Toni dana rigada nakira Baba babba yanzu inya kirawoni mezan gaya masa" shiru Barira tayi kafin tace

"Kice dashi kina tsammanin ciki ajikin amaryar prince" Jinjina kanta tayi alamun gamsuwa "Dama kuma kinsan suna tsammanin baze nemi mace ba"

****************
  Barra dai jiki yak'i dad'i, daga asibiti an kuma dawowa da ita gida, wannan karon da kanta take addu'ar neman mafita daga wurin Allah, tasani wannan wata ayace, watak'il sabida yanda take neman haihuwa ne ido a rufe Allah ya jarabe ta a yanzu kam gwanda mata lafiyar ta akan wannan bak'ar wahalar ga zullumin ganin kamar zata mutu. Sun dawo asibiti da kwana biyu lolacin cikinta yacika wata biyar ta haihu, haihuwar d'an tayi ba'ako gama halittar saba amma kana kallon jinjirin zaka gano cewar mace ce, shida kanshi yasha wahala ainun, kuma anan se jini yak'i d'aukewa baya dai b'ulala kaman da amma tas yak'i ya d'auke se wasa yake mata da hankali, hankalin uwarta ya tashi tashiga damuwa me tsanani akan rayuwar da Barra  take ciki, anan aka duk'ufa wurin karb'o mata magunguna da addu'o'i irin gargajiya tunda asibiti yaki yi.

    Tunda aka sallamo Hafsat asibiti abubuwan datake sunfi k'arfin tunani, gabaki d'aya be wuce ta zauna tayita gwab'e abinci a wuri ba kokuma, tayita surutai irin na yara, ko irin tabi'un yara, kuka ba komai bane akan tanason abu idan ba'ayi mata ba, ga Mood se b'oye b'oye yakewa Bahar bayaso tasan halin da ake ciki, kusan sati hudu kenan yana fama da Hafsat ga tsananin tausayin datake bashi, bahar naso tayi waya da Hafsat amma wayar hafsat d'inma tana hannunsa ya kashe ko school ta dena zuwa sabida yanayin ta. Yauma kamar ko yaushe yana zaune yana aiki a laptop dake gabansa, wani kamfani suka bashi aikin zanen tiles yake so ya kammala yaje yanzu takai musu yanada presentation ba, zama tazo tayi kusa dashi shiru kamar me nazarin wani abu,se cen kuma ta sanya rigarta abakinta tana tsotsawa, kallonta yayi rigar ma gaba d'aya be dace ta sanya shiba, ya gayawa Barira kuma take kula da ita tadena barinta tana sanya gajerun kaya tunda ba hankali bane akanta, yanzu ta yane rigar zuwa bakinta duk ga pant d'inta nan afili, kawar da kanshi yayi sannan ya mik'e daga wurin zuwa d'akin sa batare daya d'auki komai na aikin saba,ganin ya tashi a wurin ya sanya ta saka hannunta tayita dandanna lambobi gaba d'aya seda tayi erasing aikin dayasha wahalar yi wuni d'aya, koda ya dawo da sauri wurinta yazo ya karb'i laptop d'insa yana duba, a zuciyar sa ya soma ambaton Allah sannan ya juyo ya wanka mata mari, so yake ya taushi zuciyar sa akan karya ci gaba da dukanta amma seda ya shureta, da gudu ta nufi d'akin ta tanata zuba kuka me k'ara sekace ta goye, haka yabar gidan ransa a b'ace a dole ya lalubo zanen farko daya gama yace be masa ba ya nuna musu, ga mamakin sa se murna suke suka karb'a hadda k'arin kud'in aiki, yayi godiya sosai sannan ya wuce presentation shima na zane nez sedai wannan bedding company ne

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login