Showing 18001 words to 21000 words out of 113608 words
dan kuwa ganin yanayi irinna sarki ya tabbatar mata ya gane me tayi, bayan sarki ya mim'e ya gayarda mahaifiyar sa dama tsarin fadar akwai wurin zaman manyan iyaye irinsu wanda yake agefen sarki idan maganar dole ta kama sesunzo to anan suke zama, Bahar sarauni bata zauna ba dukda tayin zaman da akayi mata ta kalli d'aukacin 'yan fadar tace
"Waye yazo da maganar yarinyar da ake cewa Hammude kurma yayiwa fyad'e?" Tsit fada ta d'auki shiru tamkar ba kowa agun" Gyaran tsayuwarta tayi
"Bazan k'ara maimaita tambaya naba, amsa nake jira" Me martaba ne yace
"Ammu Bahar, D'annGaladima ne da idan fada suka ganshi suka tabbatar da hakan" cikin takaici tace
"Suka ganshi k'irik'iri akan 'yar mutane yana mata fyad'e? Da sauri kowa ya kalleta
"Ba haka bane Ran Bahar ya dad'e" Sarki ya fad'a yana k'ara k'ask'antar da kansa cikeda ladabi
"Inajinka gayamun da bakinka yanda komai ya faru" Seda sarki ya kalli mutanen wurin sannan yace yana gyaran zaman rawanin sa
"Ku bamu wuri" D'aga murya tayi
"Zan La'anci duk la'anannen daya fita daga fadar nan, tare daku aka k'ulla agabanku za'a warware komai, Kai Tahir maza ka aika kiran Hammude da gaggawa" Cikin girmamawa ta bada umarnin kiram kurma, sannan ya fuskance ta sosai ya kwashe komai ya sanar da ita, seda yakai aya sannan tace
"Su waye shaidun kace"
"D'an galadima ne da kuma idan fada"
"Su waye idan fada, munafukan fada zakace, kai Tahir ashe bakada hankali? me irin tunaninka samshi ba sarki bane, ban tab'a ganin sarki mara adalci irinkaba, katab'a gani ko a hikayar marasa hankali mutum yayiwa yarinya fyad'e daga waje ya kawota gidansu to tamasa me? tukunna ma ka saurari nashi b'angarin dalilin kawota gidan? Cikin sanyin Jiki yace
"A'a Ammu, naga zahiri shisa ban nemi jin mezaice" Dage gira d'aya tayi ta k'ank'ance ido
"Zahiri kake k'ara gayamun ka gani, Tahir anya sanda malamin islamiyyar ku ke zuwa kana saurarar sa kuwa? bakasan musulunci baya karb'ar shaidun zinaba harse mutane hud'u sun shaida sunga mazinatan turmi da tab'arya, kai jini kawai shine shaidarka, tukunna ma wai ka shirya gayawa Allah ka sauya nashi shaidun zuwa naka dankai sarkine? cikin rawar murya yace
"Subhanallahi, Ammu ba haka nake nufi ha wlh" Suna haka segashinan ya shigo yauma kamar kullum da gudun sa, a gabanta ya tsaya ko haki gudun be cika sakashiba sabida ya zame masa d'abi'a, dafa kafad'arsa Bahar tayi tace
"Harse yaushe zaka dena wannan guje gujen Hammude? Murmushi ya sakar mata abinda yake fin wata beyiba sannan ya mata alama da hannu akan ze dena" Tana murmishi tace
"Nasanka da saurin rubutu, maza mazq rubutamun duk abinda ka sani akan yarinyar da ake zargin ka mata fyad'e" Jinjina kansa yayi lokaci d'aya annurin fuskarsa ya kau, ya zaro jotter da pen a aljihunsa, cikin lokacin dabe gaza 10mns ba ya fayyace labarin iyakar abinda ya sani!!!!!
Barra ce ta karance tsaf a tsanake kowa yayi tsit yana sauraren ta harseda ta kammala.Nisawa Bahar Sarauni tayi yanxu kam ta fahimci duk abinda ya faru, tana jinjina kanta tace
"A matsayinmu na masu hankali be dace sabida munga jini acikin yarinya muce fyad'e aka mata ba, musamman shi jinin kawar da budurci baya zuba bare harya d'iga, kai Galadima baka tab'a kawar da budurci bane, kainkuma D'an galadima kaima matanka biyu ko dukkansu ba sabon takinka bane ba, Sarkin yak'i kana me akayi wannan shirmen ina matanka hud'u harda k'wark'wara? so kake kacemun bakasan jinin kawar da budurci ba, kaikuma sarkin baka, inace matanka uku, dukkanin ku anan kunada mace sama da d'aya cikin hadda sarkin ku? idan har kun d'auka yawan jikin daya zuba haryana d'iga ajikin yarinyar jinin kawar da budurci ne to kuwa dukkanin ku anan an rigaku takin takalminku, in hakane har sarki sena saukeshi a kujerar mulkin sa? kokunsan a k'a'idar mulkin k'asarnan idan ka taki takalmin sauri a matsayin auren fari baka mulki? Kame kame kowa ya hauyi, atake ta tsawatar akayi tsit ta waigo ta kalli D'an galadima ido cikin ido tace
"La'anannen nan dukshi ya shirya komai, soyakeyi tarihi ya maimaita kansa, ba'a rufin asiri nina rufa maka, idan tunanin ka zanje kabari da sirrin ka tokama janye, d'anka yana naj ajiye, kuma kafin aurenka kayiwa baiwar ciki niwa na gayawa? na tilastaka aurenka ne ? abinda kake gudu nan gaba kad'an asirinka ya tonu mulki ya tashi a hannunka, hak'uri zakayi rashin kamun kanka ya b'ata komai, magaji kuma kurma ne, koda kuke cewa kurma ne kunyi kuskure, kurma shine wanda bayaji, Amma Hammude yanajin magana tsaf, lalurarsa a harshensa take bawai a kunnen saba, kuma inshaa Allahu ze mulkeku koda bakwa so, ina abun yin Allah ne bana la'anannun Allah bane irin ku" Kowa yayi tsit taci gaba
"Da D'an galadima da idan fada, suje su yad'a cewar Bahar tayi bincike ta gano cewar yarinya jinin hailarta ne ya zuba a k'asa bana kawar da budurciba, Kurma taimakonta yayi kamar yanda kukaji bayani yanzu a kuma tabbatar cewar lallai munafukai sunyi nasarar da kowa ze wanke kurma daga zargi" Amsa mata akayi cikeda ladabi ta waiga suka fuskanci juna da kurma tace cikin nutsuwa
"Acikin yaran guda biyu da akeso a aura maka waccece kake so,waye kuma bakaso, idan duka kana sonsu zansa a aura maka dukkansu, idan kuma duka baka sonsu zan tsinewa wanda yayi gigin koda tashin maganar ne in la'ancesa har k'arshen rayuwarsa" A hankali Kurma yake kallon ta ya gama karantar iyakar gaskiyarta kenan, sauke idansa yayi zuwaga mahaifin sa cikeda kulawa danyasan akan sa aka tozartar da mahaifin nasa agaban bayinsa da mukaraban sa, bashida zab'in daya wuce zube idanshi a wurin da ake kallon sa, gaba d'aya jikinsa yana bashi Uncle Jay yana kallonsa, jira yake yaji mexaice, kallon juna suka tsayayi na wuccin gadi, ga Uncle Jay acikin manyan fada a jere dan kuwa shine wakili a wannan masarautar amma ba bakin magana, seda ya gama karantar zuciyar uncle Jay sannan ya mayarda dubanshi zuwaga Bahar Sarauni......
******************
*To nima dai gani na kasa kunnen sauraren wacce kurma xe zab'a, shin anya ze zab'a kuwa, befasan koda fuskar khairiyta ba, gashi ya tsani Yar shara.....*
*Mom Nu'aiym.*
*TSINTAR AYA* FREE BOOK
*BILLY GALADANCHI*
*JOIN OUR TELEGRAM PAGE THROU THE LINK BELOW*
https://t.me/joinchat/FgfKMiS_mYc-DIjC.
*Assalamu Alaikum, Readers hak'uri zamuyi da juna, kui hak'uri zakuyi inkeyin post yau gobe bazan yiba, kunga ina sab'a alk'awari gwanda na daina, dan Allah kumun wannan alfarmar, Nagode.*
*SHAFI NA BAKWAI*
Jotter sa ya mik'a hannu ya karb'a a hannun Barra sannan ya rubuta
"Bahar i will marry them both, but please not now, se bayan shekara d'aya, and lastly i want to leave the country kafin lokacin auren, i really need some fresh air, this place is like a hell, bazasu tab'a bari in samu nutsuwaba" Barra ya mik'awa seda ta karance sannan seta sauya maganganun daga yanda yayisu, tace tana kallon Bahar
"Ammu Bahar, yace ze auri yaran duka amma yana neman alfarmar abari senan da shekara d'aya, kuma dan Allah a rok'a masa izinin sarki yanaso yabar k'asar kafin zuwan lokacin sabida akwai wasu ayyuka dazeyi k'asar dazeje" Nisawa Bahar tayi dajin hukuncin daya yanke tace a nuste tana kallon sa
"Kada tsoron wasu la'anannu ya sanya ka amsa abinda bashine bane aranka, ka tabbatar haka kakeso? A hankali ya gyad'a mata kai, yayinda me martaba ya sauke wata nannauyan ajiyan zuciya, ta waiga ta kalli Me martaba tace
"Hammude ya zab'i barin k'asar, yakuma ce aure zeyi dasu duka amma se bayan shekara d'aya sabida haka yanda yakeso haka za'a masa, a k'ara masa da miliyan goma sabida yanayin tafiya, a bashi bayi maza da mata ko wanne b'arin k'waya goma sannan kuma kamar ko yaushe a karrama tafiyarsa" Badan sarki yaso hukun cinba ya amsa komai da "to"
"Yarinyar da ake magana akanta a mayarmun ita b'angarena kafin musamu iyayenta,kuma kafin ta samu lafiya" Nanma To aka amsa mata dashi ba musu ta kuma cewa
"Tafiyar sa Nanda sati biyu nakeso a shirya komai" Cikin girmamawa Sarki yace
"Amma ya dace yaje yaga ita Khairiyya d'in, tunda yake ba sanin juna sukayi ba Ammu, kinga daganan ma sesu fahimci juna kafin yabar k'asar kuma" Jinjina kanta tayi alamun gamsuwa sannan tace
"Zeje ya ganta" Iyakar abinda tace kenan ta juya, Barra da sauri tabi bayan ta cikin sassarfa, gogan ko motsawa beyi ba daga inda yake har ammu dabar fadar, Me martaba yayi fushi sosai da faruwar wannan tozarcin, Takowa yayi har zuwa gaban hammood ya tsoma idansa ana sa, shikuwa yana nan tsaye tamkar wani statue, ganin idan Me martaba ya masa k'warjini ya sanyashi sauke nasa idan a k'asa acikin zuciyar yace "Abi am so sorry" A sarari kuwa idan nan yayi jajir, cikin murya kamar meyin rad'a Me martaba yace
"You broke ur promise Hammood, haka mukayi dakai? da dare ka sameni a taska" Lumshe idansa yayi yana tunano alk'warin dayayiwa mahaifin nasa amma ya zeyi, Abi d'insa ya sauya masa, Abi ya soma bin maganar mazuga, Abi yabi layin masu yi masa caaa a kullum, Abi yana d'aukan komai dayaji da zafi akan sa koda bekai abun zafi ba ya zeyi? D'aga masa kansa kawai yayi alamar to ya kauce daga wurinsa ya juya, yau beyi guduba a hankali ya taka har gaban D'an galadima daketa muzurai cikin tashin hankali, kallon juna sukayi na seconds haka, sannan se Mood ya soma wani shu'umin murmushi a hankali har Murmushin sa ya koma dariya mara sauti, ilahirin k'irjinsa da kafad'unsa sesuka soma cirawa alamar dariyar daga k'irjin sa take, seda yayi me isarsa sannan ya dafa kafad'ar sa yana bubbuga, ya masa tumb's up sannan da yare irin nasu na kurame ya soma demonstration da hannu, duk wanda yasan abinda yake nufi ya gano cewa D'an galadima yake
"Kayi kok'ari sosai da tsaya akan kalamanka na cewa seka rigani haihuwar magajin ka bayan ka zama sarki! Yana kaiwa ya shiga aikin gudun daya saba yabar cikin fadar kowa yayi sororo ido ya koma akan D'an Galadima.
******************
Shigowar message da code d'inda kairiyya ta baiwa Bilal ne ya bata daman saving number sa, wanda dama ka'idane idan batayi saving number mutum ba yayi kad'an ya sameta a waya, bayan kamar 30mns da shigowar Text message d'in sega kiransa ya shigo seda ya kusan katsewa sannan ta d'auka amma batace komai ba shine yace
"Your Royal Highness, barka da wannan lokacin" Murmushi tayi, kafin tace
"Bilal" Lumshe idansa yayi jinta kira sunan sa da wata zazzak'ar murya sannan yace
"Your Majesty" Murmushi taketa zubawa kafin tace
"Ya akayi?
"Nakira ne kawai in gaisheki ur highness, dafatar kin tashi lafiya" Nisawa tayi tayi wani juyi akan k'aton gadon ta sannan tace
"Na tashi mana amma na gagara tashi daga kan gado, Anna na batazo ta tasheni ba, fushi takeyi dani"
"Eyyah me kika mata haka" Tabare fuska tayi wane zatayi kuka tamkar yana ganin ta
"Toba kawai dannace zanje wurin Momyna ba, its being long na ganta fa almost 2yrs, they are making things hard for me i really wanna see my mother" ta k'arashe maganar cikin kuka med'an sauti, Bilal a take ya rud'e dama ba laifi Bilal akwai tausayi
"Nooo please do not cry, kuka dai da kanki ur highness kiyi hak'uri, zaki ganta kuma Anna zata dena miki fushi, amma me kikawa Annah?
"Granny wai? ka rabu da ita just because i refuses to eat, shikenan fa, kuma tasan bazan iya hak'ura take fushi dani ba"
"Eyyah, kinga nima zan miki fushi akan zama da yunwa, kawai tashi zakiyi kije ki gaidata sekici abinci agabanta, shikenan fad'a ya k'are and issue na ganin mommyn ki, zamuyi magana daga baya inshaa Allah zanzo da idea yanda zakije gareta" Mirginawa tayi jin maganar sa ta k'arshe
"Bazasu barni bafa, ga kuma yaa Bilal baya nan" Yana murmushi tamkar tana gabansa yace
"But am here, am here for you, waye Yaa Bilal?"
"My only Brother yana U.S idanda yana nan zakaga koda kowa be yadda ba, ze sace ni mu gudu gunta, tafiyan awa nawane dududu"
"Ayya, thank God another yaa Bilal is here.... Dariya me sauti tayi
"Alright then bye bye" Yana murmushi yace
"Ok bye" suka ajiye wayoyin kowa yaji dad'in maganar sa da d'an uwansa, Bilal kansa ya soma juyawa akan khairiyya, zuciyarsa tanaso koda fyad'ene yayiwa khairiyya amma cen k'ark'ashin zuciyar sa so yake ya k'aryata hakan, dukda haka yayi k'udirin abinda duk yayi niyya akan khairiyya baze fasa ba.
*******************
Kallon sosai Dr Sunita kewa Momy, harga Allah tausayin k'awarta takeji, cikin rashin kuzari tace tana kallon ta
"Bintu banaji kinawa kanki adalci akan lafiyarki, hawan jini ba cuta bace ta wasa Binta, ni ina gaya miki gaskia ne ba'a matsayin likitaba ina gaya miki gaskiya ne a matsayina na k'awarki, abu seya hauhawa yake kaman farashi, me kika nema a rayuwa kika rasa da zaki cutar da kanki har haka? Dafe kai Momy tayi
"Sunita akwai wani abu dake damuna ne dana kasa ciresa a raina nakuma kasa denawa dukda nasan girman zunubin danake kwasa, ina kuma kyautatawa kaina rayuwa mara kyau a rana gobe k'iyama" Da sauri sunita ta ajiye biro dake hannun ta
"Subhanallah Bintu, wannan wace irin magana sekace wacce tayi kisan kai? Nisawa tayi
"Sunita yau zan bayyana miki labarin koni wacece kamar yanda kika dad'e kina son sanin ainahin ni wacece, tattare nutsuwa sunita tayi tana hanko tashin hankali sosai a fuskarta client d'in nata kuma friend d'inta.....
Fatima Bintu zuhrah wad'annn sune sunayen da ake kiran bintu dasu, mahaifin Bintu, sananne ne kuma me kud'i ne sosai d'an boko ne kuma d'an kasuwa sunansa Alhaj Mamman me Tabarau. Bintu ita kad'ai k'wallin k'wal Allah ya azurta Mamman me tabatau da ita shi da matarsa Khadeeja wacce itama ta kasance 'yar boko sedai asalinta ba 'yar Nigeria bace 'yar mutan sudan ce a wata ziyara dayakai k'asar ta aiki suka had'u soyayya me tsanani tashiga tsakanin su, a haka ya daddage seda yaga an aura masa khadeeja sannan hankalin sa ya kwanta, ya kwasota gaba d'aya suka dawo Nigeria inda mutane ukune kawai suka rakota. Soyayya lafiyayya aka k'ulla tsakanin Mamman da khadeeja agidan aurensu, amma me seda suka shuka shekaru goma cur kafin Allah ya baiwa khadeejah ciki ta haifi Fatima Bintu, bayan haihuwar Fatima Bintu da shekaru uku khadeeja ta samu ciki wanda agarin haihuwar sa da 'yar da uwar duk suka koma ga Allah, wannan mutuwar ta girgiza Mamman kasancewar shifa bashida wasu 'yan uwa a birni duk suna k'auye kuma baze tab'a barin Bintu ta koma sudan gun dangin mahaifiyar taba, wannan dalilin ya sanya yaje ya sanar abokin sa, sarkin Baihatul mulk,inda atake rik'on Bintu ya koma wannan masarautar, sedai akan dole suka barta tayi karatun boko me zurfi harta zama Banker! a wannan yanayin ne sarki Abduljabar ya dan tsohon sarkin baiha ya ganta yace yanaso, ba musu aka aura masa ita mahaifinta se murna yake, dama dangin babarta sunso sanin inda take yaki gayamusu gudun kada su karb'e 'yarsu se lokacin aurenta aikuwa sukace bazasu zoba sunbar masa 'yar ala dole ya shafa musu lafiya.
Auren khadeeja da Abduljabar beyi shekaru biyar ba alokacin ta haifi yaranta duka biyu Bilal me shakru hud'u da kuma Khairiyya 'yar wata shida me martab'a na wancen lokaci ya rasu, hakan ya tilastawa Abdullajabr zama sarkin baihatul Mulk meci yanzu, a wannan gab'ar Abduljabar yace Lallai se khadeeja ta ajiye aikinta dan kuwa matar sarki babu ita babu zuwa aiki ita kuwa ta kafe akan tana jin dad'in aikinta babu wanda ya isa ya hanata, mahaifinta ma yace ta hak'ura amma ta kafe, a haka shekara bata zago ba mahaifin nata ma yace ga garinku. Abduljabbar ba yanda beso khadeeja ta hak'ura ba amma tak'i daga k'arshe tace lallai seya saketa, mahaifiyar Abduljabbar Anna mulk tayi tayi akan ta hakura ta kafe taki, haka suka k'yaleta taci gaba da zuwa aikin bankin datakeyi.
Cikin shekaru biyar datake aiki abubuwa da dama marasa dadi da kananun maganganu sun faru akan matar saraki tana yawo amma haka ya toshe kune, katsam sega transfer anmata zuwa wani garin inda Daulatul Dinar suke mulka, yayi yayi akan ta share maganar tafiyar ze nema abarta anan amma taki akan dan tana auren sarki bazata zama koma baya ba, duk abinda yazo naci gaba seta karbeshi a wannan lokacin bak'in ciki ya sanya Sarki ya saketa saki d'aya akan inta tafi babushi babu ita babu yaranta. Haka cikin fushi tabar gidan ta tafi ta kama hayar gida taci gaba da zuwa aikin ta. Bintu ko bayan auren saraki da aikinta ta gaji dukiya me tarin yawa daga wurin mahaifinta dakuma mahaifiyarta, ganin ta kafu a wannan daular seta fad'a sana'a itace hadda siyan share's a wasu manyan kamfunna dakuma siye da siyarda kayan suturu datake d'akkowa daga waje duk sanda ta dauki hutu!!! Abu na farko daya fara ragargazar rayuwar Bintu itace Sha'awa! dama Bintu yarinyace me tsananin sha'awa dason kasamcewa tare da Namiji, lokacin dataga tafi k'arfin haya seta saka kud'i ta k'ea gida acikin wata shida tun a shekarun baya, ganin gidan ya mata girma ita kad'ai seta ebi 'yan aiki susu biyu takuma d'auki me gadi wani buzu wanda yake da mata me suna Baba Lami, a wannan lokacin sunada yaro namiji me shekaru sha biyar, se kanwarsa datake jinjira.......
Momy tana cikin kewar gida da kuma tsananin son ganin yaranta amma batada halin zuwa, fada gidansu ne,tun tana 'yar shekaru uku take hannun Annah, tare suka taso da Abdullajabbar dukda ya girmeta sosai, taga gata da gatantawa awurin su, yanda ake yiwa kowanne dan sarki haka ake mata, tun bata zama matar sarki ba ita d'in dama 'yar sarki ce princess Deejah, kowa yasan Gimbiya Deejah kafin ta dawo Sarauniya khadeejah, amma duk ta watsar akan aikin banza, bata fito dan karta koma ba, tayi zaton ko sati bazatayiba Abdullajabr ze biyota se gashi shekaru sun tunzura baya waiwayarta, tana son mijinta tana tsananin matse k'afa akan sha'awarsa amma babu inda zata d'aura kanta, bazata komaba ta wulakanta rayuwar ta awurin su! katsam wata rana 'yan aikinta sukace zasuje bikin mauludi gida tunda sun shekara 2 basujeba, hakan ya sanya ala tilas ta