Showing 27001 words to 30000 words out of 133328 words

Chapter 10 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

456

Middle Ads

ko da kwakkwaran motsi. Wani irin sanyi ne marar misaltuwa ya taso mata ya baibaye ilahirin jikinta, sai ta soma jin abu na mata yawo a cikin kai kamar hatsi.

“Baba...”

Ta furta daker tana kallon yadda suka rabe masa kai biyu a cikin dakin mahaifiyarta da suka harbe bayan sun kashe Ya Isah.

“Tashi ki saka tufafinki”

Dayan ya fada, sai ta kalleshi, duk da kasancewar hasken fitilar ba ya iya bari ya ta ga fuskokinsu, ba kuma dan ta fahimci abun da yake fada mata ba, sai dan hasketa da yai da fitila da yai, kana kallon kwayar idonta ka san bata cikin hayyacinta. Dayan ya kai mata mugun shuri a cinyarta.

“Saka tufafinki dan ubanki”

Maimakon ta saka tufafin sai ta juyarda fuskarta ta kalli inda ya shuri ta, ta kai hannu ta taba.

“Baba....”

Ta furta domin har yanzu tana jin sautin kalmar shahadar da yake a kunnenta, dayan ya fisgota sai ta mike tsaye sam ta manta a sirara take, yau ga ranar da bata kunyar siraicinta, ranar da dimauta da bakinciki suka saka ta manta babu sutura a jikinki.

“Wuce mu tafi”

Ta kalli inda mai maganar yake tana jin kamar ta taba jin kalmar. Tasss ya wanke mata fuska da wani irin mari mai zafi, sai ta rikice ta fara kuka.

“Inna.... Baba.... Wayyo Baba.... ”

“Saka tufafinki”

Ras ta ji abun da ya fada, kuma ta fahimce shi, hakan yasa tai saurin nufar inda tufafin suke ta dauka, sai dai a maimakon ta saka sai ta rike tufafin tana ganin komai kamar a mafarki. Dayan cikinsu ne ya fisgota ya turo keyarta waje, sai ta samu kanta da bin bayan wadanda suke gabanta, abun da bata sani ba ashe a sauran gidajen nan ma sun fito da sauran matan da suka rage, tafiya kawai take tana jin kamar ba kasa take takawa ba, hade ta sukai da sauran matan dake ta rawar jikin tsoro, domin sun kasu kashi kashi ne, suna shiga gidaje. Kamar wandanda suka fito yakin duniya, haka kowa ganinsu, karyar mutun yace ga iyakarsu sai dai ya kiyasta a kiyasinsa ya fadi iya abun da idonsa ya gane masa, babura ne ko wane da goyon mutum uku dauke da makamai, wasu kuma mutum biyu ne a kai, wasu kuma a kafa sun saka manyan samarin maza a gaba dauke da hatsin da suka kwasa.
Ba Aminatu ce kadai mace da suka tafi da ita ba, sai dai Aminatu ita kadai ce tsirara a cikin matan da suka kora zuwa daji, kamar sun kora dabbobi haka suka saka matan a gaba, wasu kuma suna daga gefe duk wanda yai kokarin guduwa daga cikin matan sai a halbeshi. Wasu mazan kuma suna bayan su Aminatu dauke da hatsin da suka dora musu, suna tafe suna dukan mazan a baya. Tafiya suke ta yi Aminatu na rumgume da tufafinta, bakinta kuma be daina furta Baba ba, da muryar da ita kadai zata iya ji, tana jin ta taka abu har ya huda fatarta ya shiga cikin kafarta, sai dai ko kadan tashin hankali be barta ta ji zafi ba, ko da ma ta ji bata isa ya tsaya cirewa ba, a cikin matan da suka tura gaba har da masu goyo, da kananan yan mata da matan auren, babu mai waiwaye balle ya taimaki wani, a cikin masu goyon wandanda yayansu suka fi takura musu da kuka sai su fige yaran su jefar, tsofafin da suka fara gazawa kuma sai su halbe su, masu sauran jini a jika kuma suna tafe suna dukansu. Zalincin da mutanen nan suke sai ka rantse da Allah ba zuciyar dan'adam ce a jikinsu ba. Ba su san wani abu tausayi ba, ba su ragowa ba, ba su san rai yana da muhimmancin ba, ba su wani abu imani ba, ba su san ragowa ba. Tun cikin dare suke tafiya a kafa suna ratsa wani irin jeji da Aminatu bata taba mafarkin gani ba, ba su isa inda za su je ba sai da hasken asuba ya fara ketowa.
Ba ita kadai ba mata da yawa idan ka duba kafafuwansa zaka tarar sun kumbura, saboda babu mai talkami a kafarsa, kuma da yawa sun taka kaya wasu kuma ice ya shiga kafar amman ba damar cirewa, sai dai kai ta taka kafar a haka.

Wani irin jeji ne da baka iya ganin iyakarsa, sai dai da alama mutanen kowa ne da dabarsa dabam, domin an raba matan ne wasu suka kora wasu zuwa yamma wasu kuma suka arewa, a cikin matan da aka kora arewa har da Aminatu dake rike da tufafinta.
  Har ga Allah ba zata iya fadar inda take ba, har yanzu bata yarda ba rayuwarta ba mafarki bace, har yanzu kisan da akai Baba da Inna gani take kamar ba gaske ba ne. A wani kebantaccen guri aka tsayar da su, sannan wadanda suke manyansu suka taso da manyan fitilu suka haska matan, kamin su kalli mazan da su ma sun gama galabaita.

“Wadanda ku kashe su kawai”

Aminatu ta juya a hankali ta kalli mazan da bata iya tantance fuskar kowa a cikinsu saboda tana cikin nata tashin hankali. Kamar umarni suke jira a take suka budewa mazan wuta suka musu mugun halbi, wadanda bindiga bata kamawa kuma suka takasu da babur. Faduwa Aminatu tai durkushe ta fashe da kuka, domin a yanzu ta tabbatar ya baro duniyarta, ta shigo wata duniyar ta azzaluman mutanen da babu digon tausayi a zuciyarsu. Kukan da tai ne ya saka dayan sake haskata.

“Wai iyakar matan kenan?”

“Aa an raba dai, Daba... Ba ruwana ba zan fadi suna ba🤐, sun dauki rabi, kai duk mun watse garin nan fa yau babu wanda muka bari, Wallahi yau mun aiki”

Dayan ya fada cikin mutanen da suka zo da su Aminatu, idan suka ce suna nufin gundu, domin akwai Babbar daba akwai karama, kuma daba kala kala ce, kowa da tashi, suna maganar yaron wata na kuka sai dayan ya ce.

“Kai wacan ya dame mu da kuka”

Wanda ke kusa da ita ya fisge yaron, sai ta rike masa kafafuwa tana kuka.

“Dan Allah kai hakuri yaro ne be san komai ba”

Ba su saurareta ba, sai suka aje yaron gefe suka halbeshi, da sauri uwar ta saka hannunta ta rufe bakinta saboda kar kukanta ya fito ita ma su halbeta.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Aminatu ta furta tana jin hawayen ya tsaya mata cak. Sai dayan ya haskata daga masa zuwa kasa.

“Ku daure wadanda”

Kamar dabbobi haka aka turasu zuwa wani gurin da babu wanda zai iya tantance shi, suka fara dauresu da sarka. Wasu kuma da igiya irin yadda ake yi ma dabbobi, idan an daure sai a saka igiyar a turke. Sauran da aka baro a garin suna da suke kan babura ba su iso ba sai kusan 6:30am daman can haka ake, idan za a saka mata to wadanda za su kura matan su zasu fara tafiya da su a gaba, su kuma sauran su biyo bayan idan sun gama na su aikin. Sai da haske safiya ya baibaye ko'ina sannan Aminatu ta tabbatar da ba ita kadai take ba, domin a gabansu wasu mazan ne aka daure masu yawan gaske, gafensu kuma akwai mata, gana ganin su kasan sun dade a gurin domin sun galabaita tufafin jikinsu sun yi datti sosai, mazan kuma wasu har gemu ya tarar musu, wasu gashin kai yayi musu yawa, a cikin wadanda suke daure akwai marasa lafiya. Sai dai wayewar gari zuwa karfe takwas an kashe mutun biyu a gaban idonta saboda sun cika tari, wai suna gudun kar su saka musu cuta, da zarar ka fara tari yayi yawa sai su ce a kashe ka kar ka saka musu cuta. A lokacin ne Aminatu ta samu kuzari da karfin zuciyar daura zanen dake hannunta ta suturta jikinta.
A wani kebantaccen guri aka fito da abinci, aka fara bin wadanda suka dade a gurin ana zuba musu 3 Spoon na shimkafa fara babu mai babu gishiri babu komai a ciki, kowa aka zubawa jiki na rawa yake cinyewa yana hadeye yawu, ba a baka abinci wadataccen, kuma baka isa ka yi magana ba. Bayan an gama da su aka biyo gurin su Aminatu aka zuba musu a hannu, ita kam rike nata tai a hannu tana ta kallon abinci kamar wanda bata san abun da ake kira da shimkafa ba. Suna zaune a gurin har rana ta fara dukansu, daga ita sai ireirenta ne suke ta murkususun zafin ranar da ya tsanata, sauran wadanda suka tarar a gurin kam da alama sun sab da zafin rana domin ko motsi basa yi. Wadansu mutanen ne dabam suka nufo inda Aminatu take suka kwance ta tare da wasu matan suka zaga da su zuwa bayan wata zana da aka kafa aka kare ta kamar katanga.

“Kwanta nan”

Ya nuna mata wani karamin duhu dake shimfide a gurin. Sai ta kwanta kamar daman can an halittota ne kawai dan ta bi umarninsa, da kansa ya kama zanenta ya cire, ya bude kafafuwanta, sannan ya kwance wando ya kwanto samanta ya ratsa cinyoyinta yana kokarin ratsa jikinta, runtse ido tai, ta ja wani dogon numfashi kamar zata shude, sannan ta fashe da kuka.
  Har cikin kwakwalwar kanta take jin yadda yake ratsa cinyoyinta yana kokarin shigarta da karfi, zabar da ta ji ne yasa ta fasa ihu, sai ya rika kanta ya buga da kasa, a take ta ji kan ya sara mata.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Take ta maimaitawa tana tuna nasihar da Inna tai mata. Bayan ya gama abun da zai yi ya tashi, sai wani ya shigo ya saka zanenta ya shafe gabanta, sannan shi ma ya kwanta jikinta ya aikata irin abun da mutumen farko ya aikata, bayan ya gama wani ya shigo, suka suka bi layi, tun tana iya ambaton Allah tana kuka har ta kai bata iya yin komai, Wallahi sun keta haddi Aminatu tun tana cikin hayyacinta har sai da hankalinta ya bace gaba daya, babu komai a tsakanin cinyoyinta sai jini da fatar gabanta data zazzago tana rawa, bayan sun gama suka janyota kamar shara suka fito da ita suka kawo ta a inda sauran matan suke suka barta nan kwance galala sai zanenta da suka rufa mata a jikin.
  Ba Aminatu kawai sukai ma ba, kusan duk macen da suka dauko sai sun mata haka, suna yi ma mata fyade har sai sun fita hayyacinsu, ba matan kadai ba har da mazan suna keta musu haddi, sai dai ba kowa ce Daba ce suke haikewa mace kamar Dabar da aka kai su Aminatu ba, ta haka ne mazan da aka kama suke gane an ketawa mace haddi, ko kuma namiji, domin idan sun gama suna barin mutun a wulakance.


LEILA POV.

“So kike ki tonawa kanki asiri ne?”

Momy ta tambaya tana kallon Leila, sai Leila ta girgiza kai tana share hawayenta.

“To na ce ki yi shiru ya isa, babu abun da zai faru, amman wannan kukan da kike zai saka Talba ko Daddynku ya zargi wani abu, bana son tashin hankali kin sani”

Kai ta daga mata, sannan ta kai hannunta ta dauki tissue ta goge hancinta, a daidai lokacin da Momy ta faka motar a harabar gidan. Kusan a tare Talba da Amal suka fito har ma da Kabir da ya shigo bangaren ba da dadewa ba.
  Amal da Kabir suka karasa gurin Motar ban da Talba da ya tsaya jikin kofar yana kallon Momy da Leila da ta kasa hada ido da shi. Abun da Momy ta fadawa Talba shi ta fadawa Kabir, sannan ta nufo inda kofar falonta take wato inda Talba yake tsaye yana jiran karasowarsu.

“Sannu da zuwa Momy”

“Yauwa”

Ta amsa masa sannan ta ratsa gefensa ta wuce cikin falon. Yana tsaye a gurin har Leila ta iso, idonta yayi ja sosai kana ganinta ka san ta ci kuka ba kadan ba, uffan Talba be ce mata ba, bayan kallonta da yake har ta shige cikin Falon.

“Me Leila take yi ma kuka?”

Ba Kabir daya tambaya ba, har Amal dake tare da Kabir din sai da ta Kalleshi, sai dai bata ce komai ba ta wuce cikin falon. Kabir ya saka hannayensa biyu aljihu yana kallon Talba da mamaki.

“Really? Ina ce matar da zaka aura ce, miyasa ba zaka same ta da kanka ka tambaye ta damuwarta ba?”

Talba ya dan daga kansa sama ya sauke.

“Kabir Leila tana da matsala you know it”

“Tana da matsala ko kana da matsala? Simple tambaya ba zaka iya ba”

“No baka gane ba ne, ina son na san idan tana kuka ne saboda abun da ya faru da Baaba or not, saboda ban gansu da abun da Momy ta fada ba”

“So Momy ta yi karya kenan?”

Kabir ta tambaya yana masa wani kallo. Shiru Talba yai domin be san me zai sake ce masa ba. Ganin hakan yasa Kabir kai hannunsa ya tura kofar falon ya shiga ciki, Talba kuma ya sauke ajiyar zuciya sannan ya nufi bangarensa.

“Momy miyasa za ku dage sai Talba ya auri Leila ne? Ba ku tunanin kamar za ku takura masa ne?”

Momy dake kokarin yaye mayafinta ta juyo ta kalli Kabir dake tsaye bayanta.

“Ya maka wata maganar ne?”

“No kawai ina ganin kamar Talba ba sonta yake ba”

“Idan ba sonta yake ba wa yake so? Tun da kake a gidan nan ka taba jin ya yi maganar wata yarinya? Be taba yin maganar aure ba, sai da Engineer ya gabatar masa da Leila, kuma ya amsa yace yana son ta, idan kuma har baya son ta ai ba zai ce yana so ba”

Kabir ya kwanto jikin kujerar yana fadin.

“Ina ganin kamar ya amince ne saboda kar ya bawa Daddy kunya... ”

Momy ta daga masa hannu.

“Yana sonta baya sonta, saboda Engineer ya amince what so ever, ba damuwar mu bace, tun da ita Leila tana sonsa, daman shi ai be san so ba”

“Amman tsakani da Allah fa zai cutu nan gaba, kuma ita ma....”

“Kabir....!!!”

Momy ta daka masa tsawa, tare da mikewa tsaye.

“Ka daina yin abu kamar ciki daya kuka fito, kai yana tausayinka ne ko ya raga maka? Ba zaka gane hakan ba sai nan gaba, kullum maganar Talba kake baka duba yar'uwarka, baka tunanin idan aka fasa aure ita Leila zata iya shiga damuwa?”

“Kara ta shiga damuwa a yanzu, da wanda zata shiga nan gaba... Domin abu ne mai wahala Talba ya canja rayuwarsa, imagine yanzu fa ni yake tambaya miyasa Leila take kuka ba zai iya tunkararta ya tambaye ta ba”

“Zai canja, domin dole ya canja, dole ne mu gyara masa zama, idan ba haka ba zai wahala ne”

“Ko kuma ita ta wahala ba..”

Momy ta kalleshi da kyau.

“Wai Kabir ko so kake mu bar Talba ya dauko mana wata bare can daban? Bayan ga yar'uwarsa a gida?”

Ya dan tabe baki yana kallon Momy, domin ya san a yanzu ba zata fahimce ba. Daukar mayafinta tai da jakarta ta nufi upstairs rai a bace. Har zata shige dakinta sai kuma ta nufi dakin Leila ta murda kofar a hankali ta tura, sai ta same ta zauna tsakiyar gado hawaye shabe shabe a fuskarta wayarta makalle a kunne, da alama magana take da wani.

“Da wa kike waya?”

Momy ta tambaya with serious face. Sai da ta sauke wayar sannan ta kalli Momy.

“Madina”

Momy ta karasa shigowa cikin dakin gaba daya, tare da maida kofar ta rufe.

“Leila wannan sirrinki ne, duk amintar da kike da Madina karki fada mata sirrinki”

“Toh Momy”

Ta amsa tana share hawayenta.

“Ki dauka kuskure ne kowa ai yana kuskure, idan kina yawan kuka sai ki saka mutane su zargi wani abu”

Saukowa tai da kafafuwanta a kasa, tana kara share hawayenta. Momy har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleta.

“And for the very last time, zan sake tambayarki kina son Talba?”

Leila ta daga kai.

“Wallahi ina son sa sosai Momy, ina son shi, miyasa kika tambaye ni?”

“Ba komai, ki kwantar da hankalinki”

Leila ta daga kai alamar gamsuwa, sannan Momy ta juya ta fice daga dakin zuwa dakinta. A hankali ta tura kofar dakinta ta shiga kai tsaye ta nufi gadonta ta sauke jakarta da mayafinta akai sannan ta zauna tana sauke dogon numfashi.

“Allah ka yafe mana...”

Ya furta tana lumshe ido, sai kuma ta busar da iskar bakinta.




FARUQ POV.

“Ina son anjima zan tafi kasuwa”

Ya juyo ya kalleta yana kokarin saka agogon hannunsa.

“Gurin me?”

“Tufafi zan siyo, kuma zan siyawa Sultan ma”

“Karki je ko'ina, kuma karki siyawa dana komai da kudin da ban san inda suka fito ba”

Yana gama fadar hakan ya saka talkaminsa ya fice daga gidan gaba daya. Wani dogon tsaki ta ja ta murguda masa baki.

“Wallahi sai na je, wato bayan talauci har da hassada tana damun talaka”

Ta fadi zaune saman kujera rike da wayarta tana tabe baki, Data ta kunna ta shiga facebook, sai da ta fara duba notifications dinta, ta shiga comments tana duba yadda maza ke yaba surarta kowa da yadda yake yaba sabon hoton da ta dora, murmushi take tana ta bin comments dinsu da like har cikin zuciyarta take jindadin yadda suke yabonta. Bata da fargabar komai domin ta yi blocking din Faruq da duk wani dan'uwanta na kusa da ta san zai iya ce mata ta gyara ko ta daina, daga familyn Faruq har nata yan'uwan. Bayan ta gama karanta comments din ta leka inbox dinta, sakonni ta tarar da yawa cikin har da bakin fuskar da basu saba mata magana ba, kamin ta yi ma mutun reply sai ta duba profile dinsa ta duba abokansa aikinsa hotunansa da kuma inda yake zaune, da zarar ta ga alamar mai rufin asiri ne sai ta sake masa idan kuma ta ga sabanin haka sai ta yi blocking dinsa a take.

“Ibrahim”

Ta furta sunan dake profile dinsa sai kuma ta shiga duba hotunansa, da inda yake aiki kana ganinsa kasan mai abun hannun ne. Komawa tai inbox din ta amsa masa da thanks akan yaba kyauta da yai. Kasancewar yana online a take ya maido mata da amsa.

“Babu godiya a tsakaninmu, wani ma yai rawa balle dan makadi”

“Uhmm haka kace”

“Haka ma yake, wani ya bawa mana matarmu balle kuma ni”

Ba shiri ta zaro ido gabanta ya fadi.

“Ya san ni kenan,

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login