Showing 129001 words to 132000 words out of 133328 words

Chapter 44 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

481

Middle Ads

kamar mai tsoronsa.

“Kana da wanda zaka aura, Yallabai ka rufa min asiri bana son na sake shiga wata matsalar idan ma Kaka tana fushi da kai ne saboda ka ce ba zaka aure ni ba, na fahimta”

Yayi Murmushi ya kalli wani gefen sannan ya sake kallonta.

“Yan mata, idan ma kin yi karya zuciya bata iya karya ba, na riga na karance ki kina kokarin hana zuciyarki abun da take so ne, a miyasa kika rika tambayar yaushe zan dawo a lokacin da zan tafi?”

“Saboda na sabu da kai ne kawai na kwana biyu”

“Miyasa a lokacin dana tafi kika kwanta ciwo sai a yanzu dana dawo kika samu lafiya?”

Ta yi shiru.

“Kin san saboda me?”

Ta girgiza kai.

“Saboda na tafi da zuciyarki, a yanzu kuma da na dawo na dawo miki da ita, karki yarda zuciyarki ta raya miki banbanci tsakaninki da wata ko wani, karki yarda ki sake nisa da mutanen da suke da muhimmanci a rayuwarki, domin zuciyarki ba zata iya daukar wani ciwon ba”

Har lokacin kanta a kasa yake tana hawaye, shi kuma yana kallonta yana jin kamar ace yana da permission din rumgumarta ya rarrasheta. Kamar daga sama suka ji muryar kaka tana jan tsaki.

“Maye ne kai da ka tafi da zuciyata, ka ji wata maganar banza idan son ta kake da gaske ai aurenta zaka yi”

Runtse ido Talba yai ya bude ya kalli Kaka da be san tana cikin bandakin ba har sai da ta fito.

“Kaka labe kike mana ne?”

“Ina ce dai Dakina ne? Kuma ina jinka dazun kana min karya wai na hana ka Auta, ai ban mutu ba da rai na”

“Dakinki ne, amman ni ma ina da hakki da shi ko? Kuma ai ban fadi karya ba na fada miki a waya zan zo kika ce ba zaki ba ni ba, kin dauka wasa nake? Wallahi Kaka ba zan bar garin nan ba sai na auri Aminatu”

A take Kaka ta washe hakora, gaban Aminatu kuma yai dukan uku uku.

“Aa dan Allah dan Annabi Aa”

Aminatu ta fada cikin kuka, sai Kaka ta watsa mata harara.

“Ke Wallahi baki isa ba ke ma, idan ba haka ba ni da ke ne, wannan abun farinciki da jindadi haka zaki ce wani aa, Mu'azu da gaske kake yi?”

“Wallahi da gaske nake yi kaka, amman dan Allah karki cilasta mata ki barni zan yi magana da ita”

“Mu can da aka mana aure, zabi aka bamu ne? Ko mazan ma ba mu sani ba sai da aka daura auren, karka biye shashancinta yarinya ce karama bata da wayo”

Talba yayi murmushi yana kallon Aminatu dake hawaye. Kamin ya kalli kofar shigowa dakin Kaka na amsa sallamar Aminu baki har kunnen.

“Aminu”

“Na'am Tsohuwa ya jikin?”

“Aa ni ai na warke, abun farinciki ya samu kuma ai”

Har Aminu yayi kamar ya tambaya minene domin ya lura Kaka tana son labarta masa sai kuma wata zuciyar ta hana shi, sai ya karasa gaban Talba ya aje masa kular abinci da ledar lemu ya mika masa canji.

“No ka rike carjin”

“To na gode Allah ya kara sutura”

Aminu na fita Kaka ta bi bayansa domin labarta masa, abun da ya kasa boyuwa a ruhinta. Sai da suka fice sannan Talba ya kai hannu ya bude cooler kamshin ferfesun kayan ciki ya daki hancin Aminatu.

“Sauko ki ci”

“Aa”

Ta fada da muryar kuka, domin kukan ne ya zo mata da gasken gaske. Kallonta yai.

“Shalele? Kar dai ki ce min baki son auren nan?”

Ta daga masa kai.

“No please, kar mu yi haka da ke, ba wai zan aureki saboda Kaka ne kawai ba, zan aureki ne saboda na faranta miki rai, ina tunanin zaki so abun da zai faranta min rai kuma ya shirya tsakanina da yan'uwana, idan har ban aureki ba ina cikin matsala ba yar karama ba...”

From a to z ya zayyana mata komai ciki har da kudirinsa na boye auren na su na wani lokaci. A nan ne hankalinta ya kara tashi.

“Ina jin tsoron abun da rayuwa zata samar min a gaba, komai nawa ya banbanta dana kowa, rayuwata ta zama ba tawa ba, duhu ne ya fara bayyana a ciki, sai iska ya mamaye komai, kamin na ankara taurarin ciki sun tarwatse! Hakan ne silar rushewar duniyata... Talba ba ni da gata, ni fa yar gudun hijira ce kawai...! Ina jin tsoro abun da zai faru”

Ta share hawayenta. Yayi saurin kama hannayenta, a cikin yanayin da ke nuna tsantsan tausayinta, fararen idanuwansa masu kamar madara suka rine da ja tsabar bacin rai da bakinciki.

“Ashe ba ina kusa da ke ba? Ki daina tunani wannan tunanin Shalele da yarda Allah sai na mai da ke yar lele”

“Taya? Kana da wanda zaka aura, kana da rayuwarka da mafarkinka, miyasa zaka rusa komai? Baka tsoron halin da zan shiga? Abun da iyaye basa so akwai hadari a yinsa”

“Ki daina damuwa da iyayena ko Leila, ni mijin mace hudu ne, ba san ba zaki yarda alakar dake tsakanina da Kaka ta lalace ba akan abun da zaka iya yi min, zan sama miki wata rayuwar mai kyau mai inganci, zamu gina wata duniyar mai ciki da daula da jindadi mai cike da zuri'a”

Ta fisge hannayenta hawaye na ta zirya a fuskarta, mikewa tai tsaye tana masa kallon tsoro.

“Ta ya kake tunanin rayuwa zata zama mai sauki a gareni? Ya kake tunanin Leila zata ji idan ta san ka aure ni? Miyasa kake tunanin samun wasu Family a gareni mai sauki ne? Bayan na rasa kowa? Taya mace irina wanda ta rasa komai na kima da mutuncin mace farinciki zai rabeta, ta ya Yallabai...!”

Mikewa yai tsaye yana kallon cikin idonta.

“Kar bakinki ya sake furta irin kalamin nan, ina gargade ki a kan furucin... Ina son na roki ki wannan alfarmar Aminatu, dan Allah ki yarda ki aureni ba dan saboda kanki ba ko Kaka, saboda ni”

Ta runtse ido hawaye na sauko mata, a take ta ji zazzabin ya dawo mata sabo.

“Na san akwai wahala amman ki daure dan Allah”

Ta bude idon ta kalleshi sai kuma ta sake rufewa sakamakon jirin data ji yana dibanta.

“Ina son zan kwanta”

Ta fara lalaben gadon tana kokarin kwantawa idonta a rufe.

“Wannan maganar zata zama a tsakaninmu, bana son Kaka ta san cewa a boye zamu yi wannan aure”

Nan ma bata ce masa komai ba har ta zauna.

“Ki ci abinci sannan ki kwanta”

“Bana jin yunwa”

“Ba zan cilastaki ba, bana son na saka ki a cikin abun da zai haifar miki da damuwa, zan yi magana da Kaka”

Bata ce masa komai ba har ya fice daga dakin. Ta inda yake jiyo muryar Kaka ya nufi sai ya tsaya daga bakin kofar dakin yana sallama.

“Shigo Mana Mu'azu”

Kaka ta fada da far'arta, sai ya cire talkamin kafarsa ya shiga dakin ya zauna kusa da Kaka yana kallon matar kawon nasa dake da far'ar da alama ita ma abun ya mata dadi.

“Mu'azu yanzu nake jin abun alheri Allah ya tabbatar ya sanya alheri”

“Amin na gode”

Kaka ta kalleshi tana fadin.

“Salamatu ce ta zo da wata magana wai idan Alhaji ya ji zai iya hanawa, ko kuma ya cilasta sai ka sake ta”

“Kaka kar wannan na dame ki, da saninsa na zo nan, kawai dai yace babu ruwansa saboda na dage sai na yi auren, shiyasa nake son kamin ya canja shawara a daura mana aure da ita inya so idan tarewa ne sai a barshi har sai komai ya kamalla”

“Amman Mu'azu hakan ba zai haifar muku da matsala ba? Baka ganin hakan zai iya sakawa su can su tsane ta?”

Cewar Salamatu tana kallonsa.

“Idan ma sun tsane ta, ni dai ina son ta kuma ba zan tana yarda a cutar da ita ba ko kuma ni da kaina na cutar da ita, a kokarin sama mata wasu iyalin na kawo ta nan, a can ma abubuwa da yawa marasa dadi sun faru saboda ni da ita, ina tunanin ko da a mafarki aka ce muku zan cutar da ita ko kuma na yarda a cutar da ita ba zaku yarda”

“Wallahi ko kadan, ban kawowa raina Cewar zaka cutar da ita ba, ai babu wanda ya dace ta aura sama da kai, kai da kasan komai nata kuma kake tausayinta, kawai dai ina ji maka tsoron abun da zai faru ne a gaba, kasan za su iya fushi da kai”

Salamatu ta sake fada tana kallon Kaka dake jinjina kai.

“Wannan kuma ai mai sauki ne, komai zai wuce Inshallahu, ni dai yanzu ina son ku amince min ayi komai tsakanin yau zuwa gobe amman da idan har ta amince domin bana son na cilastata”

Kaka ta dafa shi.

“Karka damu ita fa bata san so ba, kuma ta sabawa kanta da kuka tun da ka tafi kullum kuka take sai ciwo, bata da wayo amman an mata auren zata yi hankali”

Yayi shiru ya sauke kansa kasa can kuma yaja numfashi a hankali ya sauke.

“Na yi magana da Kawo Hasan kuma ya nuna min cewar ba wata matsala, amman duk da haka ina son yi sake yin magana da shi, sai a yanka min sadaki kuma idan son samu ne a daura auren nan yau ko gobe kamin Daddy ya canja shawara”.

“Ka yi gaskiya saboda bakar matar nan ma zata iya kitsa masa wani yace ya canja shawara ba zaka aureta ba, kuma dan be saka hannunsa ba, sai me ai mu masu yi maka komai ne, ba mu hana ka auri yarsa ba karawa kawai aka ce kai amman sai taya yarsa kishi yake, wannan abun da kai ni ka yi wa Allah ya maka albarka”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu.

“Idan kun yi magana da su, sai ki sanar min domin ina son komawa yau, idan kuma hakan be samu ba, zan jira har sai zuwa gobe idan an daura auren”

“To bari na nemo shi yanzu”

Kaka ta fada sai ya sa kai ya fice ya bar Kaka da Salamatu kadai a dakin. Salamtu ta kalli sarakuwarta cikin yanayi na damuwa ta ce.

“Inna baki ganin hakan zai iya haifa da matsala? Allah ya ma ba aurenta zai yi ya tafi ya barta ba sai an gansa”

“Aiko da sun ci ubansu, daga shi har uban nasa, be ma isa ba, idan zai tafi kafarta kafarsa haka zai tafi da ita, idan ma wayonsa kenan ba zan yarda ya barta ba”

“Toh sai dai haka nan, kam idan ba haka ba zai iya mana wani wayon kin san halin yaran nn na zamani, amman kam da ta yi miji yaro barakalla da shi gwanin kyau”

Kaka ta tashi zuwa neman danta Hassan. A lokacin da Talba ya fita daga dakin Salamatu sai ya koma dakin Kaka, daga bakin kofa ya tsaya yana kallon Aminatu dake kwance rairai idonta a rufe, sai dai jin kamshin turarensa yasa ta shakar kamshi bada ta san yan tsaye bakin kofar ba, idan yaja numfashin da karfi sai ta sauke a hankali.

“Kina son turarena amman baki son kusanci da ni”

Ta bude idon ta sauri ta juyo ta kalli gurin kofar sai ta ganshi a tsaye, wani irin kwarjini da haifa ya kara a idonta. Idan har tace bata son Talba to ta yaudari kanta kuma ta yi karya, amman tana sonsa? Anya akwai son sa a zuciyar dake cike da damuwa da bakinciki? Anya ma ta gama karantar minene son? Ko kuwa dai sabo ne irin wanda ta ji a wacan lokacin da tafi ya barta, a yanzu ma idan bata amince ba zata sake ganinsa ko kuwa zai tafi ne har a bada ba zai dawo ba?

“Tashi ki ci abinci idan ba haka ba zan kira wannan mutun ya zo yai miki allura”

Daga inda yake tsaye ya fada, sai ta tashi zaune tana turo baki tana masa wani kallo dake nuna alamar kiris ya rage ta fashe masa da kuka. Sai yai murmushi ya saka kafarsa cikin dakin ba tare da ya cire talkaminsa ba.

“Idan kika aminta kika zauna da ni, zamu rika ganin juna kullum, amman idan kika ki ni wata kila ba zaki sake ganina ba Aminatu, amman na san ba zaki bawa Kaka kunya ba ko?”

Ta yi shiru sai kuma ta fashe masa da kukan da bata san na minene ba. Cooler ya dauka ya sake budewa ya saka hannunsa ya rika dauko farfesun ya kai mata a baki.

“Bude baki”

Ta bude bakin daker tana ta kukan shagwaba. Sai ya kai mata a bakin yana kallon kyakkyawan lips dinta.

“Pretty girl”

Ya furta yana hade yawu, even though be taba kissing lips din wata mace ba, he like her pink lips, dan karamin bakinta nan ya dauki hankalinsa sosai da yadda take tauna abinci a hankali kamar ya mata dole. Da hannunsa yake bata har sai da wayarsa tai ringing sannan ya saka hannunsa na hagu ya karba kiran kawo Hassan sannan ya mike tsaye yana fadin.

“Okay gani zuwa”

Be ce mata komai ba ya fice daga dakin, a harabar gidan ya kunna bohore ya wanke hannunsa sannan ya nufi dakin wajen, ba Kawo Hassan Kawai ya samu a gurin ba har da wane kanen Hassan din wanda shi na kawo ne a gareshi da kuma Kaka, kusan abun da suka tattauna a dakin Salamatu shine suka sake tattauna da Uncles din nasa, sai da ya tabbatar musu da babu wata matsala sannan suka amince akan gobe idan an sauke Sallah azahar za a daura masa aure da Aminatu a Masallacin kofar gidan. Kawu Hassan sai nuna bacin ransa yake akan abun da Daddy yai yana ganin kamar ya wulakanta kuma ya nuna shi kadai yake da iko da Talba, be jidadin da za a yi komai ba tare da shi ba, amman be tsammaci haka daga gareshi ba, sai dai dukansu sun raja'ah ne aka ce maganar Kaka cewar saboda ya maida su talakawa ne shi kuma yan ganin shi mai arziki ne.
A garin Talba ya wuni har dare, sai guraren tara da rabi Daddy ya kirashi Saboda Momy ta fada masa Talba baya gidan, sai da ya fita waje can nesa da gidan sannan ya amsa kiran Daddy, ya fada masa cewar yana gurin Kaka.

“Amman kasan yanayin kasar nan ki? Musamman kauye idan sun ga bakuwar fuska har hada kai ake azo a dauke mutum, sannan taya zaka yi tafiya baka fada min ba?”

“Saboda zaka iya hanani da wannan hujojin naka daka zayyano a yanzu, ni kuma ina bukatar zuwa saboda na yi magana da Kaka ka san tana cikin fushin a yanzu”

“Na ji ka dawo da wuri, Allah ya tsare, kuma ka yi addu'a sosai Wallahi ina tsoron garin nan”

“Inshallahu Daddy babu abun da zai faru”

“Toh Allah dai ya tsare, amman ka daina wasa da rayuwarka irin haka”

“Inshallahu”

Daga haka sukai sallama sannan ya kira Momy ita ma ya sanar mata inda yake ya kuma fada mata ba zai samu dawowa ba sai gobe.

“Allah yasa dai ba gurin yarinyar nan ka tafi ba”

Momy ta fada cike da gadara.

“Momy kina manta cewar akwai zumunci a tsakanina da ita a yanzu, ko bayan ita kuma Kaka ta tana nan kuma tana raye dole ne na rika zuwa”

“Hmmm Talba kenan, a hannuna ka tashi karka ce zaka min wayo, ni dai n gargadeka, kuma na ja maka kunne ka fita sabgar yarinyar nan tun wuri indai har ka dauke ni uwa, ina tunanin zaka ji magana ta”

Ya sauke ajiyar zuciya ba tare da yace komai ba, Momy ma bata sake cewa komai ba ta kashe wayar, sai ya koma cikin gidan ya ari wayar Kaka da sunan zai duba wata number yai blocking din number Daddy a wayar Kaka sannan ya goge number gaba daya, gudun kar Kaka tai karabanin cewa zata kira shi.
Bayan ya gama abun da zai yi ya mika mata wayarta ya fita, Kawu Hassan ya shigo dakin Kaka ya saka Aminatu a gaba yana tambayar idan tana son Talba, sai dai Kaka bata bata damar amsawa da eh ko aa ba, duk inda Kawu Hassan yai sai a tare, tana cewa wai Aminatu bata da wayo bata san ciwon kanta ba, kuma ba san minene so ba. Ita kanta Aminatu da za a bata dama da bata san wace kalar amsa zata bawa Kawu Hassan ba, domin kanta a yanzu a duhu yake.
Daga ita har Talba bachinsu kadan ne, misalin biyu da rabi ta tashi ta shiga bandakin Kaka tai alwala ta fara raya daren na Laraba tana kaiwa Allah kukanta da neman zaba mata abun da zai zame mata alheri da kuma rokin daukinsa a dukan al'amurranta, ta bangaren Talba ma sallah nafila ya kwana yi, a da can sai dai yai raka'a biyu yai karatu da addua ta kwanta sai dai wannan karon har asuba yana zaune a saman carpet din da yai sallah yana karatun qur'ane, bayan ya kamalla ya fadawa Allah bukatarsa da neman daukinsa a abun da yake kokarin aikatawa.
Washe gari abun kari na musamman Kaka ta saka aka shirya masa, aka kawo masa har dakinsa, ruwan tea kawai ya sha ya kasa cin komai, sai abubuwan da suka faru a jiya suka rika dawo masa, ya sani akwai kalubale mai yawa a gabansa, sai dai yayi ma kansa alkawarin duk rintsi duk tsanana ba zai taba yarda ya cutar da Aminatu da saninsa ba.
Misalin Tara da yan mintuna Kawu Hassan ya same shi da maganar Sadakin da kuma wanda zai masa walicci domin shi zai dauki bangaren Aminatu ne.

“Na saka dubu ashiri Hajiya tace yayi kadan zai dai a saka arba'in”

“Ba matsala Kawu zan bada 100k, Inshallahu”

Kawu yayi murmushi yana mamaki.

“100k fa kace Mu'azu, aa yayi yawa”

“No be yi yawa ba, ita kanta Aminatun ina son ta ji cewar na dauke ta da kima”

“Duk da haka dai dubu dari yayi yawa”

“Be yi yawa ba Kawu, Allah dai ya tabbatar mana da alheri”

“To amin”

Talba ba mutum ne mai yawo da kudi mai yawa ba, haka ya saka dole sai da ya je POS ya cire wasu kudin sadakin ya bawa Kawu da kuma kudin da za a siye komai na al'ada na daurin auren. Bayan ya dawo ne ya kira Ali

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login