Showing 90001 words to 93000 words out of 133328 words

Chapter 31 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

484

Middle Ads

ita falon, kanta a kasa tana tsoron kallon mutane, shi ma kuma kofar fita daga falon kawai yake kallo. Momy da Leila har ma da Kabir na tsaye ban kallonsa babu abun da suke har ya fita da ita.

“Aikin banza mtsssss”

Leila ta fada tana jan tsaki. Sai da Madina ta leka windows ta hango ya tashi motar yana kokarin yin ribas sannan ta kalli Momy ta ce.

“Momy zan tafi da yarinyar nan saboda anan zata haifar da fitana ne kawai, kuma idan tana tare da ni zata nisanta da shi ba kamar yanzu ba”

Momy ta kalli Leila sannan ta kalli Madina.

“Ke iyayenki za su yarda ta zauna ne?”

“Eh zan musu bayani kuma ai kin ga ba dadewa za ta yi ba, na dan lokaci ne”

“Shi zai yarda ki tafi da ita?”

“Eh na masa magana, amman yace min na fara zuwa na yi magana da iyeyena”

“Okay ba matsala”

Momy ta amsa ta tana kallon yanayinta, sai ta yi ma Leila sallama tana fadin sai sun yi waya. Momy ta bita da kallo har sai da ta fice sannan ta kalli Leila ta ce.

“Ki yi hankali da yarinyar nan, hankalina be kwanta da ita ba, idan b munafurci ba ta ya za ayi fada akan yarinya kuma ke ki ce zaki dauketa ki kaita gidanku?”

“Momy da sani na tai, sai da tai shawara da ni, plan ne muke hadawa, Madina bata da matsala, ba yau na santa ba fa Momy”

“Ki dai yi hankali, kuma ki san irin sirrin da kike fada mata”

Kabir ya mike tsaye yana kallon Leila.

“I hope plan din da kike hadawa ba cutar da yarinyar nan zaki yi ba, ba na goyi bayanki ba ne saboda ki samu damar wulakantata, no na yi hakan ne saboda na san kina jin kishin abun da Talba yake yi ma yarinyar nan”

“Ba wanda za a cutar kawai zan nisanta ta da shi ne”

“Dauketa za ki yi?”

“Haba Kabir? Idan ma na dauke ta zan yi ai shi ya ja mata...”

Uffan Kabir be sake ce mata ba ya fice falon. Ita ma tashi tau ta nufi upstairs aka bar Momy zaune tana kallon Leila har ta haye.

TALBA POV.

A entrance din ya bar ta, sai da ya fara isa ya bude motarsa sannan ya dawo ya saka hannunsa ya dauke ta ta saka a motar ya dawo ya dauki wheelchair din ya saka a bayan motar, kana ya zagayo ya rufe side dinta ya shiga driver seat yaja motar suka ce daga gidan.
A hankali yake tuka motar yana kallonta, ita kuma tana ta kallon titi, da motocin dake kai da kawo har suka isa super market din da yake siyen chocolate da sweet da yake kaiwa a gidan marayu, fakawa yai a harabar sannan ya fita ya shiga ciki be dade ba ya fito ya dawo cikin motar, yaja suka dauki hanyar by pass.
Har suka isa aka bude musu gate din ya shiga ciki ya faka motarsa Aminatu bata kalli inda yake ba, sai da ya bude motar ya fito, sannan ya zagayo gefenta ya bude mata.

“Ina kujerar?”

Ta fada tana kallonsa.

“Ya kamata ki fara takawa”

Ta bata fuska tana turo baki gaba kamar zata fashe da kuka.

“Akwai zafi idan na taka”

“Idan baki taka ba, then yaushe zaki taka kafar? Kullum haka zaki yi ta zama fa”

“Ni dai ba zan iya takawa ba”

A dole ya bude ya dauko mata kujera ya aje mata.

“Ta so ki zauna”

Ta kalli kujera ta kalleshi sai ta kara bata fuska.

“Akwai nisa ai sai na yi taku har hudu”

“Idan ba zaki taka ba, zan tafi na bar nan”

“Sai na yi ta zama a nan ina ruwana”

“Ni ma ina ruwana ki yi ta zaman to”

Ya fara takawa kamar gaske, sai ta fashe masa da kuka.

“Ashe kin iya kuka... Ya miki kyau”

Ya fada ba tare daya juyo ba, hakan yasa dole ta fito da kafafuwanta ta taka kadan.

“Wash wash wash...”

Tana fada tana hannunta rike ta ganbun motar har ta karasa gurin kujerar ta zauna.

“To na zauna”

Ta fada cikin kuka. Sai ya juyo ya kalleta yai murmushi.

“Daga yau ba za a sake turaki a keke ba”

“Ni kuma ba zan yi tafiyar ba, ai saboda kasan akwai ciwon a kafata ne, idan kai ne Allah kadai ya san yadda zaka yi kuka”

This time around murmushi yake mai sauti. Ya dawo kusa da ita ya tsaya.

“Wato kukan zan yi, an fada miki ni rago ne kamar ke?”

Ya fada yana kai hannu ya lasa kumatunta, sai ta kara turo bakin gaba. Murmushi yai ya bude back seat din ya dauko abubuwan da suka siyo ya dora mata saman jiki sannan ya koma bayanta ya fara tura keken.

“Yaran da zan nuna miki yanzu, basa da uwa ba uba, ba yan'uwa ba kowa, amman sun zama kamar iyalai a nan, kuma suna farinciki, ba dan yau yana ranar karatu ba, suna makaranta da yanzu sun zo sun zagaye mota suna murna da ganina”

“Waya kawo a nan to?”

“Na yi miki karya?”

“Aa ka fada min gaskiya dai, Babba ba ya karya karya ba kyau”

Yayi murmushi.

“Ni na kawo su a nan”

“Amman da zaka yi karya me zaka ce min?”

“Sai na ce Babana”

“Babanka ba ya rasu ba?”

“Yeah tun ina ciki mahaifina ya rasu, amman Daddy ai shi ne Babana gatan da yai min ko da ace Babana yana da rai ba zai min shi ba”

Ya fada sannan ya turata har gaban ajijiwansu, yaran na ganinsa suka  taso ta gudu suna masa oyoyo.

“Uncle Uncle”

Yayi murmushi ya duka yana tambayar lafiyarsu. Aminatu na kan kujerar tana kallonsu cike da burgewa, irin yadda yake sake musu ya saka suka saba da shi sosai har taba jikinsa suke wasu na tsokanarsa. Mikewa yai tsaye ya dawo kusa da Aminatu ya dauki ledar sweet din ya bude ya mika mata.

“Ki ba su”

Ta kalleshi kamin ta kai hannu ta dauka ta fara mika musu duk wanda ya karba sai ya koma gefe, wasu kuma sai su dawo a kara musu, shi ma ya dauki daya ya fasa ya saka a baki, bayan sweet din ya kare ya bude chocolate ya bata tana dauka tana ba su, sai ga murmushi a fuskarta. Sai da ya kare sannan yai musu sallama suka koma ciki, shi kuma ya turo Aminatu har gurin Motarsa.

“Yanzu ma ke zaki shiga da kanki”

Ta bata fuska.

“Wallahi akwai zafi tafiyar dazun ma daurewa kawai na yi”

“Yanzu ma daurewa kawai zaki yi”

“Yanzu ba zan iya daurewa ba”

Ta fara matsar hawaye sai yai murmushi kadan ya ciro wayarsa dake ring, sai da yai kamar kar ya dauka sai kuma yai picking.

“Ya akai?”

“Talba... Kana ina?”

Ya kalli harabar gurin.

“Ina wani guri”

“I need to see you akwai magana mai muhimmanci daya kamata ka sani”

“Idan na dawo zan kira ka”

Yana fadar hakan ya kashe wayar ya kalli Aminatu dake masa kallon tsoro.

“Momy ce?”

“Momy kike tsoro? Abokina ne”

“Wannan likitan?”

Ya daga mata kai, sannan ya duka ya saka hannunsa ya dauke ta ya saka a front seat ya rufe, ya nade kujerar ya saka ta a bayan motarsa, ya zagayo zai shiga motar wayarsa ta sake yin ringing, sai da ya zauna sannan ya duba wayar sai ya ga bakuwar number. Picking yai ya kara a kunne sai Madina ta yi masa sallama.

“Assalamu Alaikum, Madina ce”

“Ina ji”

“Ka kawota gidanmu Hajiya ta amince”

“Mahaifinku fa?”

“Shi ma ya amince, baya gidan amman na yi magana da shi ta waya”

Be sake cewa komai ba ya kashe wayar. Ya yi ma motar key yai reverse suka fice daga gidan. Be yi wata doguwar tafiya ba, suka iso gidansu Madina, horn daya yai aka bude masa gate din ko kamin ya faka harabar gidan Madina da kanenta biyu mata sun fito da saurinsu suna tarbonsu, ko wanensu fuskarsa a sake alamar suna maraba da zuwanta.

“Ina fatar dai kina ra'ayin zama, bana son na cilasta ki, kuma zan rika zuwa kullum ina dubaki, idan kin ga wani abu na daman ki fada min”

Ta daga masa kai, sannan ya bude motar ya fita kamin ya zagaya ya bude gefen da Aminatu take, har Madina ta ta rumgume Aminatu a gabansa, hakan da tai kuma ba karamin dadi yai masa ba, domin a ganinsa ko ba komai ta nuna mata rashin kyama. Da kansa ya fito da wheelchair din ya aje ta nesa da inda motar take, ita kuma ta riko Aminatu suka ta fito.

“A matso da kujerar”

“Aa ki taka a hankali, ki isa gurin kujerar, ya kamata ki rika takawa”

“Akwai zafi sosai”

Ta fada kamar zata fashe da kuka, Madina ta yi dariya.

“Aiko kara ki saba, domin ni ba zan yarda ki yi ra zama kan kujera ba kullum dole ne ki fara tafiya”

Da wash wash ta karasa gurin kamin ta zauna har ta kagu, Madina ta fara tura kujerar Talba kuma yana dagawa kanenta dake gaishe shi kai, sai kuma yai tsaye sai har sai da suka karasa gurin kofar falon sai ta juyo ta kalleshi ya sakar mata murmushinsa mai kyau, Madina ta ji gabanta yayi mugun faduwa, sai yanzu ta tabbatar Leila ta fita juriya, domin bata jin zata iya jurewa Talba ya rika kula Aminatu a gabanta, saboda shi, yanzu ma ba dan tana neman kusanci da shi ba da ba zata yarda ta karbi Aminatu ba.

“Maraba maraba”

Hajiya ta fada da fuskar dake nuna dole Madina tai mata ba dan tana so ba.

“Ina wuni”

“Lafiya Kalau”

Tana amsawa ta kalli Madina sai kuma ta dan yi murmushi.

“Yanzu bari mu fara cin abinci sannan ki yi wanka, ki huta”

“Ina son zan yi sallah”

“Okay”

Ta turata har zuwa dakinta.

“Nan zamu zauna, nan ne dakina so yanzu mun zama mu biyu”

Aminatu dai bata ce mata komai ba, har gaban gadonta ta kaita ta fita ta debo mata abincin da aka girka shinkafa da miya. Da kanta tai feeding dinta sannan ya kaita bandaki ta hada mata ruwan wanka ta fito ta baro ta a ciki, bayan ta gama ta koma ta turo ta suka fito, wata doguwar rigar ta dauko mata ta taimaka mata ta saka sannan ta nuna mata gabas ta bata hijabi.
Haka tai ta wuni tare da ita a dakin tana kunna mata tv can kuma ta jata da hira.

Da dare ma a tare suka ci abincin dare, sannan ta dauko mata daya daga cikin tufafin na kwana ta bata ta saka. Sannan ta dauko wayarta ta rike.

“Ko na kira miki Talba ki masa sai da safe?”

Aminatu ta yi shiru kamar mai tunani.

“Aa”

Sai Madina ta kai hannu ta dafa ta.

“Ai kara ki saba da gaisawa da shi, ai zai jidadi kuma zai ce kin damu da shi, kamar yadda shi ma ya nuna miki kulawa”

“Toh...”

Sai Madina tai murmushi ta nemi number sa ta kira shi.

“Idan ya dauka ki ce kina son ki ji muryarsa ne kamin ki kwanta”

“Toh”

Wayar ta yi ringing ta katse be daga ba, tasan Talba baya son hayaniya, hakan yasa bata sake kira ba.

“Be daga ba wata kila baya kusa da wayar”

Aminatu ta daga mata kai sannan ta kwanta saman gadon. Tara da yan mintuna Madina ta sake kiran Talba, rejecting call din yai ya kira jiki na rawa ta dauka.

“Hello”

“Madina bana son yawan kira”

“Ka yi hakuri dan Allah, ni ma ban so kiran ba, Amina ce tace tana son na kira mata kai”

Yayi shiru be ce mata komai ba, sai ta saka wayar a hands-free ta mikawa Amina.

“Fada yayi?”

Amina ta tambaya kamin ta karba.

“Ban yi fada ba, Shalele ba ki kwanta ba?”

“Eh”

“Akwai wata matsala ne?”

“Aa kawai ina son na ji muryar ka ne kamin na kwanta”

Yayi murmushi ya.

“Shalele sleep tight”

“Miye haka nan?”

“Ba ki san abun da hakan ke nufi ba?”

“Eh ni bana jin turanci”

“To za a koya miki, ki kwanta yanzu ki yi bachi da kyau”

“Toh sai da safe”

“Sai da safe”

Yanke kiransa yayi daidai ta sauke ajiyar da Madina tai yi, domin har ga Allah bata dauka tana kishin Talba har haka ba sai yanzu. A take yanayinta ya canja, ta kwanta ba tare da tace cewa Amina komai ba.
Washe gari a dakinta ta kawo mata komai a karyawa, sannan ta nufi wayarta dake ringing ta dauka.

“Hello”

“Madina ya kika?”

“Lafiya kalau, kamar Kabir”

“Ni ne baki da number ta, ni ai ina da taki”

“Uhm Ya aikin?”

“Alhamdulillah, Yarinyar nan tana gurinki?”

“Wai Shalele? Eh tana nan”

“Shalele kuma?”

“Eh haka na ji Talba na kiranta, na dauka haka kuke kiranta ne ai saboda tana da sunan Momy”

“Aa zan zo na dubata yanzu”

“Momy ta sauko kenan?”

“No tana da ciwo a kafarta, zan duba ciwon ne, kuma ga maganinta nan kin manta”

“Okay sai ka zo”

Ta sauke wayar tana kallon Aminatu.

“Shalele wai haka Talba ke kiranki ko a gida?”

“Aa”

Aminatu ta amsa mata a takaice cikin rashin sakewa. Tsayawa tai tana kallonta sannan ta fice tana kiran Leila a waya.
Harabar gidan ta fito tana labartawa Leila abun da ya faru.

“Yau fa be ma shigo nan ba, ko Momy ta waya ya gaishe ta, be leko bangaren nan gaba daya, kuma na san duk saboda na ce ba zata zauna a bangaren ba ne”

“Ni abun har mamaki, taya zaka hadu da yarinya a titi kace zaka fifitata sama da yar'uwarka kuma matar da zaka aura”

“Daman kin san bama sha inuwa daya, idan ba ganin yai raina ya bace ba hankalinsa ba zai taba kwanciya ba”

“Jiya fa bata kwanta ba sai da ta ji muryarsa”

“Da gaske?”

“Wallahi kuwa, kin ji yadda yake kiranta Shalele”

“Madina sai na ci uban yarinyar nan, me take nufi?”

“Me yake nufi dai shi, idan bata ga fuska ba ai ba zata soma ba, amman fa karki ce ni na fada miki”

“Ai ba zan fada ba, amman dole na dauki mataki?”

“Matakin me zaki dauka? Har a bada, Talba ba zai taba auren yarinyar nan ba, ko da yana sonta, Wallahi ba zan bari ba, sai dai ina ganin yana yi ne saboda ya musguna miki, shiyasa na baki shawarar ki kulla soyayya da Ali, so that ya ji yadda kike ji, amman ko dan rashin sanin asalinta da kuma fyaden da akai mata ai ba zai aureta ba, besides ita fa ba yar kowa ba ce”

“Na san da wannan, amman ko zai yi dan ya bata min rai be kamata yai da wannan yarinyar ba”

“Zan kira ki anjima”

Ta yi saurin katse kiran hango motar Kabir da tai, tana tsaye har ya iso kusa da ita ya faka motar ya bude.

“Hajiya Madina...?”

“Yau dai sai gaka gidanmu kamar wasa”

Yayi dariya.

“Na zo na goge laifina ne, kin san jiya ba mu kyautawa Talba ba, shiyasa na zo na goge laifina”

“Hakan ya kamata gaskiya, bari na fito da ita”

Ya mika mata maganin ta karba ta shiga ciki ba dadewa ta fito tare da Aminatu ta kawo masa har gurin motar.

“Tashi tsaye”

Ta girgiza kai.

“Ni bana ita tashi yana min ciwo”

Fitowa yai motar ya duka gabanta yana duba kafafuwan, sannan ya koma ciki ya dauko safa ya saka a hannunsa ya fara latsa kafafuwan.

“Akwai zafi fa”

Ta fada a shagwabe. Rikata ya mikar da ita tsaye, sannan ya saka dayan hannunsa ya janye kujerar yana kokarin sakinta.

“Aa aa aa akwai zafi”

“Haka zaki hakura ki tsaya idan baki tafiya ya za'ayi ya warke? Kin yi gudun daya wuce kima ne shiyasa amman kina fara takawa zai warke tun da an saka miki magani”

Ya saketa sai ta fara rawa can kuma ta kasa tsayuwar ta fadi, tsakanin Madina da Kabir aka rasa wanda zai rika ta har ta kai kasa.

“Kar a sake bari tai zauna, ku rika barinta tana tafiya”

“Ton”

Ya koma cikin motar ya dauko takardar yayi rubutu akai ya mikawa Madina.

“A nemo mata wannan maganin duka na shafawa ne”

“Okay”

Ta fada tana karba sannan ya rufe motar ya juya ya fice daga gidan. Sannan Madina ta nufi inda take da keken ta rikata ta zauna.

“Karki takura kanki da tafiya, idan ba zaki iya ba ki yi zamanki a nan kin ji?”

“Toh”

Ta fada idonta tab da kwalla. Suna shiga ciki Madina ta kalleta tace.

“Anjima zan kaiki gurin gyaran kai, kuma zan muje da ke ki zabo tufafin da kike so, amman kamin mu tafi zan kira Talba ki fada masa inda zamu je, sai ki ce masa kina son ya raka mu okay?”

“Toh”

“Good, kuma idan yace zai je aiki ki ce masa kina son zaman a gurin aikinsa kamin na dawo daga nawa aikin, saboda ni ma aiki zanje yanzu”

“Tohm”

Kamar hadin baki Madina na daukar wayar da zimmar kiran Talba sai gashi ya kirata, murmushi ne ya kawata fuskarsa tai picking call din ranta fes.

“Hello”

“Shalele na kusa”

“Eh”

Ta amsa tana hade abu mai daci na kiran Aminatu da yai da Shalele sannan ta mika mata wayar.

“Hello”

“Shalele kin tashi lafiya?”

“Lafiya kalau, yanzu zamu je gurim siyen kayan sakawa da kuma gyaran kai, idan kana nan ina son mu tafi tare”

Ya dan yi jimmm kamar mai sauraren wani gurin, har sai da ta dauke wayar daga kunnenta ta duba sannan ta sake maida wayar.

“Hello”

“Already ina Office, ba zan samu zuwa ba kuje tare da Madina ki zabo duk abun da kike so”

“Ita ma aiki zata je yanzu, ko ta kawo ni a nan idan ta tashi sai ta zo mu tafi tare”

“Miyasa kike son zuwa inda nake ne?”

Tayi shiru sai kuma ta ce.

“Ka yi hakuri”

“No ba zan cen na yi hakuri ba ne, bata wayar”

“Gashi yace a baki wayar”

Ta mikawa Madina.

“Ki kawo ta nan idan zaki je aikin, idan kin dawo sai ki zo ki dauketa kuje siyayyar”

“Wata kila zata fi sakewa idan muka je tare da kai, tun jiya bata da magana sai taka, tun safe take son na kiraka, ni kuma bana son ka ga kamar ina takura maka ne, and you know her situation duk abun da zai sakata farinciki shi ya kamata mu yi”

Tana kawai nan ya yanke wayar, sai tai murmushi.
25

Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login