Showing 114001 words to 117000 words out of 133328 words

Chapter 39 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

488

Middle Ads

ne a gareka, kuma ita din matar ka ce Allah ya shige maka gaba ka aureta”

Fahat yayi dariya.

“Mutun ya taba auren matar da ba tasa ba”

“Sosai, zaka auri mace kai ta wahala da ita amman bata gani, kuma ku yi ta samu matsala ku kasa samun kwanciyar hankali saboda ba matar data dace da kai ba ce, kasan ance mata ta gari rabin jindadin duniya ce, I'm talking from experience, ko da yake kai kana da rufin asiri wata kila ba zaka samu irin matsalar da na samu ba”

“Ta gujeka saboda talauci kenan ko kuma tana azabtar da kai”

“Ba ma tare da juna yanzu, amman mace idan ba ta gari ba ce kuma ba alheri bace a gurinka kin aurenta shi yafi, duk da yake wani lokacin ba zamu san alheri ko sherin ba wani abu ba har sai mun kusancesu ko sun kusance mu”

“Haka ne, ni ma zan yi ta addu'a kamar yadda Hajiyata take ce min, kuma kai ma wata rana zata dawo gareka tana neman yafiyarka idan ta gane kuskurenta Inshallah hope dai ba ku haihu da ita ba?”

“Da daya, sai cikin dake jikinta yanzu”

Faruq na maganar idonsa har ya sauya kala yayi ja alamar bacin rai.

“Komai zai wuce, karki watsar da hakkin da yake kanka, ka yi kokarin ganin ka sauke duka nauyin dake kanka ba tare da ka zalince ba ko yaran, inshallahu Allah zai taimake ka, da kai yi zalinci kara azalince ka”

“Haka ne na gode sosai, Inshallahu zan yi kokarin yin haka, Allah ya saka da alheri ya biya bukata”

“Ameen nima na gode, Allah ya kaiku lafiya”

Fahat ya mika masa hannu sukai sallama.

“Ameen”

Faruq ya amsa sannan ya fita motar ya rufe, key Fahat yai mata ya hau titi jikinsa a sanyaye, maganar da Faruq ya fada masa ta saka ya tuna da yawan nanata masa da Hajiyar take cewa ya rika addu'a idan alheri, sai dai shi yana kallon kamar tana fada masa haka ne saboda bata son ya auri wata sai wanda ta zaba masa. Wayarsa ya dauka ya kalli hoton Baturiya dake shimfide gaban wayar.

“Ina fatar yadda kike da kyau nan, haka zuciyarki take, ko ma zuciyarki ta fi wannan kyau”

Ya fada da murmushi a fuskarsa sannan ya kai wayar a bakinsa ya sumbace ta, kana ya cire key din ya kira Baturiya ta fada masa daidai inda gidan yake, yana driving din yana waya da ita har ya isa kofar gidan.

“Gani kofar gidan”

“Gani fitowa Dear”

“I love you, sai kin fito”

“I Love you too”

Ya yi murmushi ya sauke wayar zuciyarsa cike da kaunarta.


TALBA POV.

A falon ya zauna kan karamin stairs din da kai ka sakiyar falon, domin ayi falon ne a kasa bedrooms da kitchen kuma a sama sai dai ba sama irin na gidan sama ba, wani tsari ne akai mai kyau. Yana zaune a gurin yana ta kallon falon da ba a saka komai a ciki ba sai farin fenti da kuma na'urar sanyaya daki, ya dauki enough time din da yake ganin ya kamata ace ta gama sallah sannan ya mike tsaye ya juyo da zimmar shiga bedroom din sai ya ganta zaune a bakin bedroom din tana kallonsa.

“Kin gama?”

Ta daga masa kai.

“Kin ci abinci?”

Ya sake tambaya yana karasawa kusa da ita.

“Aa”

“Ta so ki ci abinci sai ki kwanta”

“Ni kadai?”

“No nan zan kwana”

“Toh”

Ta mike tsaye tana dafa ginin ta koma ciki sai ya bi bayanta, a kasa ta zauna inda ledar abincin take shi kuma ya zauna kan gadon, da kanta ta bude ledar ta dauko takeaway din ta bude sai ta kalleshi.

“Bismillah”

“Ni na koshi, ci abincinki ki koshi”

Ta maida kanta kasa ta fara cin abincin a hankali, shi kuma sai ya ciro wayarsa ya shiga dannawa, sai ga kiran Ali ya shigo wayarsa, yana kallon kiran har ya katse be daga ba, sai da wani ya sake shigowa sannan yai picking.

“Ya akai?”

“Ka kirani wayar na silent ban sani ba, I'm sorry”

“Daman wata matsalar ce kuma yanzu ta wuce”

“Gani kofar gidanka”

Kai tsaye ya san a cikin gidansa yake nufi domin idan family house dinsu ne zai ce gashi a cikin gidansu, ba kamar yanzu da ya banbanta ta shi da gidansa ba.

“Bana ciki”

“Haba Malam ba halinka ba ne, ga motarka ka waje”

“Toh bana son ka shigo”

“Akwai maganar da nake son mu yi da kai”

Talba ya mike tsaye ya kashe wayar ta kalli Aminatu.

“Bari na budewa wani gate okay?”

Kallonsa kawai tai ba tace masa komai ba har ya nufi kofar fita.

“Karka ka dade tsoro nake ji”

Ya juyo ya kalleta sannan ya daga mata kai alamar okay. Ya fice cikin izza da isa yake tafiya har ya isa bakin gate din ya bude karamar kofar ya kalli motar Ali. Ali na ganinsa sai ya bude ya fito ya rufe ya nufo inda yake yana murmushi, a can abu ne mai wahala su yi kwana daya ba su ga juna ba, idan dayan yana da wata matsala zai kira dayan ya sanar masa amman ya lura da Talba ya canja gaba daya ko irin sakewar nan ya daina masa.

“Ya akai?”

Talba ya tambaya sound so serious domin idan babu abun da ya kawo shi zai koma ciki ne ba zai tsaya saurarensa ba.

“Ba zaka min tayin shiga ciki ba”

Talba ya sakar masa kofar, ya juyo ya dawo cikin gidan, sai da Ali yai murmushi sannan ya shigo yana ta kallon gidan, Talba ya rigashi isa gurin kofar falon dan haka ya rigashi ganin Aminatu dake tsaye bakin kofar rana tana jiran karasowarsa. Be bukatar ya tambayi dalilinta na fitowa bayan ya san ya baro ta tana cin abinci, idan ma ya tambaye ta ya san amsar ta ba zai wuce tana jin tsoro ba. Da hannu yai mata alama da ta shiga ciki sai ta juya ta koma sai dai bata yarda ta koma bedroom din ba sai ta tsaya a falon har ya shigo, Ali ma ya shigo. Kallonta yai sannan ya kalli Talba.

“What this?”

Uffan Talba be ce masa ba, kallonsa kawai yake.

“To be frank wannan abun be dace da kai ba sam, not because ina side din Leila but because I'm your friend, be kamata na ga abun da zai kai ka ga halaka ba ko ya taba mutuncin ka kuma ina gani na bari ka aikata, this is wrong very very wrong, kana tunanin idan Daddy ya gani ko Momy ko Leila da kanta za su jidadi? Haba Talba”

“Kana da wata magana mai muhimmanci ne? Bachi nake son yi”

“A nan zaka kwana kenan?”

“Ina kake tsammanin zan kwana?”

“Bana zarginka ko kadan Talba, amman sheidan mugun ne”

Talba ya nufi kofa ya bude masa alamar ya fita, wani mugun mamaki ne ya kama Ali, ya san Talba yana da zuciya sosai amman be saba masa abun da yake masa a yau ba.

“Okay”

Ali ya fada yana jinjina kansa, kamin ya juya ya kalli Aminatu data rakube guri daya tana masa kallon tsoro. Sai kuma ya juya ya fice.

“Kin ci abinci?”

Talba ya tambaya sai ta daga masa kai,

“Kin koshi?”

Nan ma kan ta daga masa.

“Shiga ki kwanta zan shigo da motata ciki”

A nan bata samu damar daga masa kan ba, balle har ta amsa masa da to ko ta shiga dakin kamar yadda ya bukata. Be kula ta ba ya shiga dakin ya dauko keys dinsa ya fito tana tsaye ya fice daga falon, sai ta sake dawowa bakin kofar falon kamar dazun ta tsaya tana kallonsa har ya bude gate din ya shigo da motar ya rufe motar ya nufo kofar falon. Sannan ta kauce masa ya shigo sai ya wuce dakin kai tsaye, ganin ya dade be fito ba yasa ta bi bayansa. Sai ta same shi zaune kan dankwalin da tai sallah tana ta taba wayarsa, bata bukatar yace mata ta hau ta kwanta daman tun dazun bachi ke kawo mata hari bayan wanda tai. Sai kawai ta nufi gadon ta hau ta kwanta ta juyo da fuskarta ta inda zata rika ganinsa. Ko da wasa be kalli inda take ba har bachi ya dauke ta, sai da ya tabbatar bachin nata ya nina ta hanyar numfashi dake ta fita da karfi yana bada sauti, sannan ya tashi ya nufo inda yake aje bedsheet ya dauki daya kana ya doshi inda switch din wutar yake ya kashe, gudun kar ta farka yasa be rufe kofar ba ya fito falon ya shimfida bedsheet din ya cire jallabiyarsa yar vest din dake jikinsa ma sai da ya cireta, domin abu ne mai matukar wahala ya kwana da riga, no matter how hot or sanyin sa ake a gari ko a waje, baya sakewa idan ya kwana da riga, sai da ya rage hasken falon sannan ya kwanta a kasa, can kuma ya tashi yai addu'a ya sake kwantawa ya rufe ido ba dan yana jin bachi ba, kuma ba dan yana tsammanin bachin zai bashi hadin kai ba, sai dai be bude idon ba har kusan daya na dare.
Yana jin motsin lokacin da Aminatu ta fito daga dakin ta tsaya bakin kofa, can kuma ta kwanta nesa da shi ba sosai ba tana facing dinsa, kamar dazun yanzu ma be bude idon ba sai da ya tabbatar da bachinta ya nina sannan ya bude idon ya tashi zaune. Fitilar wayarsa ya kunna ya haske fuskarta, sai ya hangeta tana bachi hankali kwance ta saka hannunta daya a cikin baki kamar mai tsutsar hannu.
He spend more than thirty minutes yana kallo kyakkyawar hallitar Allah, an tsara mata komai cikin kwarewa da hikima irin ta Ubangiji, hancinta ya tsayu, kana gani kasan gwanin baiwa da rahama ne yai halinci komai na fuskarta, a kasan hancin an yanka mata wani karamin baki gwanin sha'awa da burgewa, idanuwanta dake rufe suka kara bayyanar da gashin idonta daya cika kamar ta aro.
Fuskarta na ta sheki kana ganin fentin fatarta kasan ba dai mutum ba sai dai Allah, babu digon fari ko kadan a jikinta, sai dai hakan be rage ta da komai ba a kyau, sai ma kara bayyanar da godiyarta ga Allah na tsaya a yadda Allah ya yi ta.

“Unique”

Ya fada yana jin kamar a yau ya fara ganin bakar fatar da ta dara fararen mata kyau da aiba irin ta hallintar Allah Subhanahu Wata'ala. A yau ya tabbatar da akwai hikimar Allah na yin fararen mata da bakake, sai dai bakin mutum ya banbanta da kowa, domin ba a siyen baki.
Daukar rigarsa yai ya saka sannan ya dauki bedsheet din da ya shimfida ya karasa inda take ya lulluba mata, ya tsakala ta ya shiga dakin ya dauko matashin kai ya daga kanta ya saka mata, kana ya hanye mata hannun data saka a baki, sai ta turo bakin kamar mai shirin fashewa da kuka, sai dai ba kukan zata yi ba domin bachi take.



31

Ko kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Komawa yai cikin dakin yai alwala ya shimfida dankwalinta yai sallah nafila akai sannan ya cire rigarsa ya hau saman gadon ya kwanta. Misalin uku da wani abu ta farka, tana bude ido ta hango inda yake kwance babu kowa sai tai saurin tashi tana waige waige. Har ta yi kamar ta fara kuka sai ta hangoshi saman gadon hasken gulob din waje na hasko shi, tashi tai da sauri ta koma can kusa da gadon ta kwanta kasa ta takure kanta sosai kamar zata shige karkashin gadon. Bachi da bata farka ba kenan har sai da yai sallah asuba ya tashe ta. Sai ta farka a firgice duk da kasancewar a hankali yake tashinta.

“Tashi ki yi sallah”

Ta fara murza ido, sannan yunkura ta tashi ta nufi bandaki tana takawa a hankali kamar yadda take har ta shiga, bata sha wahala gurin kunna fanfo ba domin ta kula da yadda ya kunna mata fanfon jiya. Bayan ta gama alwala ta fito sai ta same shi zaune gefen gado yana karantu a alqur'ane da wayarsa, inda tai sallah jiya a gurin ta sake yin sallah asuba. Bayan ta gama ta daga hannunta ya yabi Allah ta miyar godiyarta a gareshi sannan ta yi salati fa Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wassalam, kana ta bijiro da bukatarta na naman gafara ga iyayenta, sannan tai ma maka na neman mafita da madafa, sai kuma ta rufe tana yi ma al'ummar Musulmi, ta dora da salati. Jinginawa tai jikin gado tana ta sauraren karatun da yake da muryarsa mai dadi saurare, sai ta lumshe ido kamar mai bachi alhalin ba bachin take ba. Sai da ya kai karshen suratul Ibrahim sannan yai addu'a ya aje wayar ya kalli inda take jingine jikin gadon idonta a rufe. Hakan nan kawai ya ji yana bukatar gyara mata kwanciyar kanta jikin gadon domin bata aje shi yadda ya kamata ba, wuyanta zai iya ciwo. Tashi yai ya karasa gefen gadon a haka ya kai kyakkyawan hannunsa ya kama fuskarta da zimmar kwantar da ita sai ta bude. Idanuwanta da na shi suka sarkafewa juna, ko wanensu ya kasa yin kawaicin dauke nasa, a zahirin kyaun idanuwanta yake kallo, a yayinda fuskarsa da idanuwansa suke mata kwarjini.

“Ina kwana... ”   “Ina kwana... ”

Suka furta a tare muryarsa ta muryarta sukai tarayya a lokaci daya, kamar yadda numfashinsu sukai auratayya da junansu, ta hanyar shiga da ita a tare. Ta kowace kusurwa a hancinta na shigar mata da kanshin turarensa, ya samu guri can kasan ruhinta ya kwanata. A yayin da shi shiga da fitar numfashin yake shiga tare da bugun zuciya mai tsanani. Ita ta fara dauke idanuwanta tana murmushi kadan, sai kuma murmushi ya cika bakinsa har ya kawata fuskarsa, mikewa yai tsaye yana kallon kofa.

“Kar mu yi latti, ki shirya sai mu tafi waje mu karya, sai mu kama hanyar”

“Toh Yallabai”

Ta amsa tana kokarin mikewa tsaye, sai ya nufi kofar dake kallon yana jin sunan wani iri wai Yallabai, sound so funny. A falon ya dawo ya zauna har sai da ta fito sannan ya juyo ya kalleta he thought ko zata yi wanka ne ta canja tufafin jikinta.

“Baki yi wanka ba?”

“Baka ce na yi ba”

Ya wara ido.

“Komai sai na ce ki yi? Come on ba ki bukatar komai sai na fada miki fa”

Juyawa tai ta koma ciki bathroom din ta shiga bata ga soso sai sabulu da shower gel kusan kala uku. Bata san abun da ake da shower gel din ba hakan yasa ba tai karanbanin tabawa ba, sai kawai tai amfanin da sabulun tai wanka, bata yarda ta fito ba sai da ta leko ta ga baya cikin dakin sannan ta nufi inda akwatinta yake da saurinta kamar ba mai ciwon kafa ba, ta bude akwatin ta dauko doguwar riga ta saka tana kokarin daura dankwalin ya shigo sai tai saurin juyawa ta bashi baya, shi kuma sai ya fice yana jin wani iri.
Be sake dawawo dakin ba har sai da ta saka hijabinta ta fito falon.

“Na gama”

Juyowa tai ya kalleta ita ma kallonsa take kamin ta kalli jikinta ganin yadda ya kura mata ido. Sai ya mike tsaye ya shiga bedroom din ya hada tufafinta har Wadanda ta cire a cikin akwatin sannan ya janyo akwatin ya fito da shi, yana gaba tana binsa a hankali har suka fita falon, cikin karfin hali ta karasa gurin daya faka motarsa shi ya fara bude mata kasancewar ya rigata isa gurin motar sai ta shiga gidan gaba ta zauna, bayan ya saka akwatin a mota ya koma ya rufe kofar falon sannan ya nufi gate ya bude ya dawo cikin motar yai mata key.

“Zan fara biya gida na yi wanka n canja tufafi sannan na tafi”

“Toh Yallabai”

“Talba, idan ba zaki iya ba ki kira ainahin sunana Mu'az”

Ya fada yana reverse sannan ya fita da motar gaba daya, ya dawo ya rufe gate din sannan ya sake komawa cikin motar ya ja suka dauki hanyar Shimkafi road.
  A lokacin daya isa kofar gidan sai ya faka motarsa daga waje, sannan ya fita ya nufi gate din yai knocking aka bude masa, ya shiga ciki suna ta mamakin ganin motarsa a waje kuma a jiya be kwana gida ba. Be shiga bangarensa ba sai da ya fara shiga part din Daddy ya gaishe shi sannan ya fito ya nufi part dinsa, a gaggauce yai wanka ya fito be tsaya shafa komai ba sai turaren daya zame masa jiki sannan ya dauki abubuwna bukatarsa ya saka aljihun shaddarsa ya saka agogon hannunsa sannan ya fito yana ta sauri kar Daddy ya riga shi fitowa ya ga Aminatu a motarsa, gashi yayi sa'a Daddy ya manta be masa maganar tafiyarsa kauye ba kamar yadda ya sanar masa a jiya, wata kila Daddy ya dauka ko sai da rana zai tafi ko kuma ya fasa ne, yana ta sake sake ya mai gadin ya bude masa gate ya fita. Sai ya hango motar Leila kusa da tasa motar rage tafiyar da yake yai yana nazarin a gidan ta kwana ko kuma yau ta dawo? Ta dade a gurin.

“Miyasa kike zargina da abun da ba ni na aikatawa kaina ba? Ke kin fi karfin Allah ya jarabeki ne?”

Aminatu ta tambaya cikin wani irin kuka marar misaltuwa.

“Me ke faruwa”

Talba ya tambaya a lokacin daya karasa kusa da su, Leila da ta baro motarta ta zo gurin Aminatu ta tsaya ta kalleshi.

“Babu, kawai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login