Showing 6001 words to 9000 words out of 133328 words
bata iya kalaman soyayya ba, bata san ta kira ni ta gaishe ni ba ko ta turon sakon soyayya, kai ni bana jin ma akwai ranar da Leila ta taba kallona tace kana da kyau simple word bata taba fada min ba, sai ni zan fada mata? Ba yi wannan macen da zan zauna ina bude mata sirrin zuciyata ba har ina rarrashinta”
“Wannan ji da kan babu inda zai kaika Talba, idan ka sake mata ka nuna mata kauna dole ita ma zata sauko fa”
“Malam na ce ka fitar min a mota...!”
Yanayin yadda yai maganar ya isa ya sanar masa ba da wasa yake ba, kuma ya san halin abokinsa idan ransa ya bace baya jin rarrashin sai dai hakan ba zai hana anjima ya kira shi yace yana son wani abu ba ko kuma su gadu a guri kaza. Salun alum ya bude motar ya fita yana murmushi da mamakin irin halin Talba.
“Ina fada maka matsalata kana wani kokarin ba ni laifi, an fada maka mata haka ake musu ne!”
Magana yake da kansa yana tukin cikin bacin rai, domin be san inda zai je ba a yanzu kasancewar yau weekend kuma gashi safiya ce be ma karya ba.
@12:44pm
Leila na zaune tool din mirror Momy tana zana mata abun da ya faru.
“Kawai sakonsa na gani a wayata wai na fito waje yana son magana da ni, Momy babu ko irin shaukin nan Wai Ke fito waje ina son magana da ke, haka dai na daure na fita, na same shi a balcony ya kusan 30 be ce min komai ba, sannan wai ki yi fixing date na auren mu, Imaging babu ko dan shauki sai wani ji da kai”
“Ke kuma kika ce masa me?”
Momy ta tambaya tana harararta.
“Na ce nasa ba zan yi ba, ni ban tashi aure yanzu ba”
“Ki ba shi hakuri”
Ta kalli Momy kamar tai magana sai dai ganin babu wasa a fuskar Momy yasa ta mike tsaye ba tare da tace komai ba ta fice daga dakin cike da bacin rai. Dakinta ta shiga ta dauki key din motarta da jakarta da wayarta, ta fito babu mayafi ta sauko kasa kamar zata tashi sama, daman ta saba fita babu mayafi abu ne mai wahala ka ganta da mayafi a jiki komai kankantarsa.
Tana fitowa ta nufi gurin da motarta take ta bude ta shiga tai yi warming dinta sannan ta danna horn da karfi mai gadin na ganin hakan yai saurin bude mata gate. Kamar wata mai gasar tsere haka ta fito daga cikin gidan da mugun gudu ta hau titi tana jin kamar ta fasa ihu. Sai da tai nisa sannan ta dauki wayarta ta kira Adam.
“Besty kana ina?”
“Ina gida ya akai? Kamar kina cikin damuwa”
“Ina ciki besty mun yi fada da Talba?”
“Mtssss wai me ke damun Talba ne?”
“Ina na sani, ban san abun da yake takama da shi ba, indai kudi ne ni ma ina da su, ilmin ina da shi kyau ba za a min gori ba, amman sai wani nuna isa da ji da kai”
“Wallahi kam yan kalaman soyayya ma ace ba zaka iya yi ma mace ba, idan an yi auren ya kenan?”
“Shine abun da nake magana a kai, ni kuma sai na nuna masa ina da tsada ni ba kamar sauran mata ba ne, dole na ja masa aji, yadda yake jin ba zai iya min kalaman soyayya ba ko ya dauke ni mu fita ko ba ni hakuri haka ni ma ba zan taba yi masa ba”
“Hakan shi ne daidai, kara ya san darajarki a dole ya sauko idan yana sonki”
“Shine ai, shi kawai abunda ya dauki mace ya mata umarni ta bi ya juyata yadda yake so, ni kuma sai na nuna masa na fi karfin haka Wallahi”
“Yanzu dai kwantar da hankalinki ki samu ruwa ki sha, ki fita waje ki sha iska zan zo na dauke ki mu fita”
“Har na ma fito gida amman bari na koma”
“Okay but ki yi murmushi pls”
Ta yi murmushin mai sauti kamar yadda ya bukata, sannan ta aje wayar, ta juya ta koma inda ta fito. Kamar yadda ta fito haka ta koma gidan da gudunta ba da damuwa da titi ko sauran motoci burinta dai ta aikawatar da abun da take so. Horn biyu tai kamin tai na uku Mai gadin ya bude mata gate ta shiga cikin gidan da mugun gudu ta faka motar a inda ranta ya so ta fito ta nufi kofar falon, door bell ta danna da karfi kamar zata balla shi sannan taja ta tsaya tana tsaki, shiru ba a bude ba har sai da ta sake danna door bell din sau biyu ta hada da knocking. Sannan Baaba ta bude mata.
“Wallahi tallahi kika sake barina a tsaye a waje ina knocking, abincin ki ya kare a gidan nan Baaba”
“Wanke wanke nake yi Leila shiyasa”
“Na dai fada miki”
Ta fada cikin tsawa, ba dan Baaba ta yi saurin kaucewa ba da Leila tureta zata yi ta wuce. Baaba ta maida kofar ta rufe sannan ta juyo cikin falon cikin rashin jindadi zata koma Kitchen din sai ta ji muryar Momy dake tsaye stairs.
“Baaba a rika kula mun dauke ku aiki ne kawai saboda mu huta, a daina batawa yarana rai”
Baaba ta daga kai ta kalli Momy sannan ta daga mata kai cikin da ladabi.
“To Hajiya Inshallahu za a kiyaye”
Sannan ta sadda kanta kasa ta nufi kitchen din cikin rashin kuzari.
FARUQ POV.
Kallonta ya tsaya yi da dayan biyu kamin ya amsa gaisuwar da tai masa, domin ba kasafai take gaishe shi da safe ba sai idan tana son wani abun ko kuma ta lura aljihunsa da dan nauyi.
“Lafiya Kalau an tashi lafiya?”
“Alhamdulillah, sai yunwa da nake ta ji tun jiya”
“Toh Allah ya buda mana kofafin samu”
“Amin...”
Ta amsa tana kallon Sultan dake motsawa alamar zai farka daga bachin da yake.
“Na ce wai ba zaka kira abokin nan naka ba, ka roki shi dan wani abu?”
Ya girgiza mata alamar aa.
“Ba zan dauna kullum ina bin abokai ina rokonsu ba, bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abun da zai ci ba, kuma ni ma na yi karatun idan mu kai hakuri komai zai wuce”
“Matsalar kenan Faruk girman kai, kana da girman kai, yanzu haka zamu zauna mu wuni da yunwa gashi idan ka fita baka dawowa sai dare? Ga ni da ciki ga Sultan?”
Yayi shiru yana jin yadda kansa yake sara masa saboda maganganun da Baturiya ta fara masa.
“Shiyasa na ce zubar da cikin nan zan yi na huta, kai ma ka huta domin na san ko ragon suna da wahala a samu a yanka masa wannan bakin talaucin da muke fama da shi”
Ta fada cikin kukanta na munafurci. Sai ya kalleta a raunane.
“Zubar da ciki ba zai kawo mana Mafita ba Rafi'a miyasa ba ki da tunani ne wai?”
“To ni dai gaskiya yunwa nake ji, tun jiya fa ban ci komai ba, kuma anjima na nan ga Sultan ma”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya mike tsaye ya fice daga dakin cike da damuwa. Binsa tai da harara.
“Ni dai Wallahi na gaji da wannan bakar rayuwa, Allah kadai ya san yadda masu kudi suke ji, su kwanta a mai kyau a ci abun da ake so, ni ko na kare a nan duk kyau na”
Ta fada tana mikewa tsaye tare da bin bayansa, sai da ta tabbatar ya fita sannan ta dawo ta dauki wayarta ta shiga contact list dinta ta kamo number da tai saving jiya. Maryam Dahiru Sokoto ta aika mata kira, ringing tai har ta tsinke ba a daga ba ta sake kira nan ma ba a daga ba.
“Ka ji yan gayu sai ayi ta kira basa dagawa...”
Whatsapp dinta ta bude ta shiga gurin numbers ta kamo number wanda ke dauki da hoton wani matashin da ba zai wuce sa'an mijinta hakimce cikin mota. Sai da ta gama kallon hoton sannan ta shiga aika masa sako.
‘Assalamu Alaikum, ranka ya dade fatar an tashi lafiya, ya aiki ya Madam da yara. Ranka ya dade sunana Fee'ah matar Faruq abokinka, na kira baka daga ba shiyasa na yanke shawarar turo maka sako. Wallahi muna ciki matsala, yau kusan kwana nan mu hudu ba mu girka komai ba, shi ma idan ya fita haka yake dawowa saboda shagon da aka bude sabon gurin ne cikin wata sabuwar unguwa ba kowa yake ta aski ba, yanzu haka Sultan kuka yake, ni kaina dauriya kawai nai saboda da na, Dan Allah ka taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ka, na duba na ga a cikin abokan Faruk babu mai tausayinsa da son taimaka masa irinka, na so Faruq yai maka magana da kansa amman yace nauyi yake ji, yanzu haka be san na dauki number ka ba, domin idan ya sani ina ciki matsala. Ka huta lafiya Allah kara rufa asiri’
A rarrabe ta tura sakon har tana gadawa da emoji din rokon da kuka. Sannan ta duba last seen dinsa tun jiya da dare, tana jin motsin turo kofar gidan tai saurin aje wayar ta kwanta kasa. Faruq ne ya shigo dakin rike da bakar leda har biyu a hannunsa. Ya aje mata dayar a gabanta ganin hakan yasa ta tashi zaune tana kallon 200 dari biyun da ya mika mata.
“Ina ka samo?”
“Ke dai ka bar”
“Dan girman Allah Faruq ka daina mana cin bashi kana kara mana kanskanci a unguwa kamar kan mu farau talauci”
“Ba bashi na ci ba wayata na bashi jingina”
Bata ce komai ba ta karbi dari biyu kana ta bude ledar tana duba taliya da makaroni dake ciki sai maggi da mangyada.
“To wannan ledar fa?”
“Mama zan kaiwa”
Yana fadar hakan ya juya ya kalli dansa dake sharar bachi sannan ya fice ba dan ranta ya so ba.
“Mu ba mu wadatu ba amman sai dauka ka kaiwa wasu, mtchhhh”
Ta karasa tana jan tsaki.
“Kuma Wallahi sai na zubar da cikin nan haka kawai zan zauna ga talauci ga wahala da kurciyata da kyauna”
Ta fada tana mikewa tsaye ta dauki ledar taliyar ta fito waje domin sarrafawa. Kallo daya zaka masa ka karanci damuwarsa abubuwan duniya sun taru sun masa turr kamar ya zagi arziki kamar komai yake juye masa, gashi yayi degree amman aiki ya gagara duk inda yai applying shiru ba wani motsi. Da tunani kala kala mai achaba ya sauke shi unguwar Dallatu wato gidan mahaifiyarsa, sai ta ciro naira dari a mika masa sannan ya ratsa cikin gidanje har ya isa kofar gidan ya tura ya shiga da sallamarsa. Kanensu biyu mata da suke tsakar gidan suka amsa masa suna masa sannu da zuwa, bayan ya amsa musu ya nufi dakin Mahaifiyarsa ba karamin faduwa gabansa yai ba ganinta a kwance domin ba al'adarta bace yawan kwanciya musamman a irin wannan lokacin.
“Mama lafiya dai? Ko jikin ne?”
“Da sauki ai Alhamdulillah”
Ta amsa masa tana murmushin karfin hali.
“Wani irin da sauki ga ki kwance? Kai Innalillahi Wa'inna illahirraji'un”
Jin furuncinsa yasa ta yunkura ta tashi zaune tana kallonsa.
“Ina Sultan?”
Kasa amsawa yai sai kallon mahaifiyarsa yake, yana jin kamar ace yana arzikin da zai iya kaita Asibiti, domin ba yau ciwon ya fara ba.
“Mama ko dai maganar auren Aisha da akai ne jiya ya tada miki hankali? Idan ma fasa aurenta zai yi ai ba wani abu ba ne zata samu wani”
“Har aure nawa za'ayi ta fashi ne Faruq? Haka zamu ta zama ana fashin aure saboda talauci? Kuma yaran nan sai girma suke, sai gulma ake mana a unguwa”
Ta tambaya idonta tab da hawaye, Faruq yayi saurin kawarda nasa idon yana sauke ajiyar zuciya, domin kukan mahaifiyarsa na daga cikin abun da ya fi tsana a rayuwarsa.
________
Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.
Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
https://www.wattpad.com/story/283871769?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=reading&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZCqcO2wXIv6pkkxIr3do4ng1%2BTHhzoVPTPFtpfDcb1ftHOVsldMflpG2lAwd5aYtrehJ12WEeerjWSVNDZunKAH9QpxhI0A%2BzJsYI6RrshbTOZsoLUXljeZDCPaDNtKr
*💔 BAKAR WASIKA 💔*
By Khadeeja Candy
Page -3️⃣
Shigowar Daddy ne yasa Momy ta cire farin gilashin idonta tana murmushi.
“Ranka ya dade an fito?”
Kusa da Amal ya zauna yana murmushi.
“Allah ya yarda”
Ya fada yana karewa katon falon kallo ganin Momy ce kawai sai Khadija da kuma Kabir, abun da ba kasafai yake gani ba, ya saba every weekend yana zuwa falon Momy ya zauna tare da ita da kuma yaransa, kowa ya fadi bukatarsa ayi hira a bawa juna shawara, ayi nishadi. Sometimes kuma shi zai kira su a bangarensa a tare a can.
“Daddy barka da wuni”
“Yauwa, Son”
Ya amsawa yana yi ma kowa kallon tsanaki, ciki har da yar autarsa Amal da ta wani hade rai.
“Hajiya ya ga falon ku kadai? Ina sauran yarana suke?”
Momy ta kalli Kabir dake kallonta sannan ta kalli Amal kamin tace komai Kabir ya tari numfashinta.
“Daddy yaranka biyu fushi suke da juna, kasan Angry Birds ne”
Daddy ya kalli Momy.
“Since when?”
Kabir zai sake magana Daddy ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu, wanda hakan ke nuna kai tsaye Momy yake son ta amsa masa tambayarsa. Momy ta sauke ajiyar zuciya.
“Ni ma dazun nan na sani...”
A tsanake ta labarta masa abun da ya faru ciki har da fadan da tai ma Leila.
“Amman baki fada min ba? Taya zaki bar Mu'az ya fita ba tare da yayi breakfast ba? And baki dama ki san a wane hali yake ba?”
Momy ta lumshe ido ta bude tana murmushi.
“Wani lokacin kana maida Talba kamar wani karamin yaro, ya san yadda zai kula da kansa Alhaji”
“Ko da Mu'az zai shekara dari matukar ina raye to shi yaro ne a gurina, a shirya mana abincin rana tare”
“An gama ranka ya dade”
Ya mike tsaye sai Amal ta kalleshi.
“Daddy ni ma fa kaga ina fushin nan amman baka ce komai ba”
Sai a lokacin Daddy ya tuna da tana gefensa sai ya kalleta yana murmushi.
“Amal sorry wata taba ki?”
Ta nuna Kabir sai Kabir yai saurin daga hannayensa sama ya mike tsaye.
“Na ma bar muku falon”
Kamin Daddy yace komai ya nufi kofar fita daga falon da saurinsa yana murmushi.
“Mu yi masa uzuri amman yau kawai next idan ya sake tsokanarki zamu raba gari da shi”
Daddy ya fada yana kallon kyakkyawar yarsa. Sai ta sakar masa murmushi.
“Toh Daddy”
“Good”
Cewar Daddy yana ciro wayarsa ya kira Talba, ringing daya yai picking kamar daman can kiran yake jira.
“Hello Daddy”
“Mu'az kana Ina?”
Ya kalli katon office din da yake ciki kamar mai son tantance inda yake.
“Office Daddy”
“Me kake a office? Yau Weekend?”
“I don't know...Getting some fresh air”
“Baka fada min kana da damuwa ba, mu da kai ba abokai ba ne? Ba ma boyewa juna abu?”
Wani irin kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, ya mike tsaye daga inda yake zaune ya nufi windows.
“Daddy ba irin wannan ba you know dan crisis ne kadan”
Daddy ya tabe baki yana juya fuska kamar Talba na gabansa.
“Uhm.. Ka dawo gida yanzu zamu yi lunch tare”
“Okay Daddy Allah kara maka lafiya, i love you”
Daddy yayi murmushi ba tare da yace komai ba ya sauke wayar, sannan ya nufi wata kofa a dayan bangaren falon wanda zata sadashi da bangarensa.
“Ita Leila ba ya bace kenan? Da ba zaka kirata ka tambayi inda take ba?”
Daf da zai wuce Momy ta yi wannan maganar sai ya juyo ya kalleta, sannan ya dauke kai ya bude kofar ya fice.
Sai da ya rufe kofar sannan Momy ta tabe baki ta kai hannunta ta dauki wayarta ta kira Leila, sai da wayar ta kusa yankewa sannan Leila ta daga.
“Leila kina ina?”
“Gidansu Madina”
Ta amsa murya can ciki.
“Ki dawo da wuri, and make sure kin ci abinci”
“To Momy”
Momy ta sauke wayar sannan ta mike tsaye ta nufi kitchen.
Misalin 2:30pm Talba ya daka motarsa harabar Daddy, ya fito ya nufi bangarensa kai tsaye hannayensa duka biyu zube a alhaji, tafiya yake kamar wanda baya son shiga bangaren, haka yake idan yana fushi be cika son ya rabi mutane ba ko kuma mutane su rabe shi, a tunaninsa tare da kowa zasu ci abinci, domin Daddy ya saba zuwa bangaren Momy ya zauna a ci abinci rana tare ko na dare wani lokacin har da na safe, sai dai yana yin haka ne kawai ranar kun Assabar da Lahadi. Domin ranar weekend ba ya fita ko'ina sai idan fitar mai dalili ce kamar daurin aure ko wani abun, wannan al'adar ba shi kadai ba har yaransa sun saba da ita, every weekend zaka samu kowa a gida sai mai dalilin fita yake fita.
Ya samu kusan dakika 40 zuwa 50 sannan ya danna door bell din kofar falon Daddy, babu bata lokaci Amal ta bude masa kofar.
“Ya Talba”
“Lil Sis... Waye da waye a ciki?”
“Just me and Daddy”
Ya sakar mata murmushi sannan ta shiga cikin falon, tun da ya hango dinning din babu komai a kai ya tabbatar daga shi sai Daddy za su ci abincin. Kai tsaye ya wuce karamin Falon Daddy inda ya saba zama. Yana shiga ya samu Daddy zaune saman kujera yana amsa waya, sai ya zauna a inda aka jera manyan kuloli ya dauki plate biyu ya zubawa Daddy shimkafa, ya zubawa kansa a dayan plate din sannan ya bude miyar dake ta kamshin naman kaji ya zuba ma kansa kadan domin ba ya son miya tai yawa a abinci ya zubawa Daddy ta jera kofuna biyu ta zuba musu lemu ya hada komai sannan ya dauki na Daddy ya dora masa a dan karamin center table dake gefen kujera da Daddy yake kai. Sannan ya koma ya dauko na shi ya dawo kusa da Daddy ya