Showing 123001 words to 126000 words out of 133328 words

Chapter 42 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

471

Middle Ads

ita kuma ta dago zata mika masa nata gaisuwar.

“Ina kwana” “Ina kwana”

Sun fada a tare, shi yana kokarin gaishe da Kaka ita kuma tana mika masa nata gaisuwar, sai suka kalli juna ita da shi murmushi ya biyo baya, wanda ya karawa kowanensu kyau da haiba.

“Lafiya Kalau an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah”

Ta amsa sannan tai kasa da kanta, shi kuma ya juya ya saka gaishe da kaka, kamar dazun yanzun ma bata amsa masa ba sai ta daga masa alamar amsawa. Murmushi yai ya kalli kunun da Aminatu take sha.

“Kaka ni ba za a bani kunun ba? Saboda ni ba dan gida ba ne ko kuma me?”

Kaka ta yi kamar bata ji shi sai jan charbinta take. Aminatu ta mikawa Talba nata.

“Ka sha wannan”

Ya mika hannu ya karba ba dan yana son sha ba, kusan zai iya cewa be taba shan kunu ba a rayuwarsa idan ma ta taba to ya manta, tashinsa Momy ta saba masa da tea ba kunu. Babu kyama ya kai kofin bakinsa ya kurba, sai yai saurin runtse ido, ba dan dadi ko rashin dadin kunun ba, sugar da Aminatu ta zuba ne ya ji shi har cikin kansa, saboda be saba shan suga da yawa ba, wani lokacin ma ya kan iya jika Lipton kawai ya sha ba tare da suga ba, idan ma zai saka sugar baya wuce one or two to three cube.

“Shalele haka kike shan zaki ko Kaka ce take son bata ki?”

“Ni na zuba”

Daukar kunun yai ya kara a cup din ya motsa sai zakin sugar ya ragu, sai dai hakan be hana shi jinsa har cikin kansa ba, haka dai ya daure yana shan kunun idan yayi ludayi daya sai ya mika mata ta sha daya a haka har suka shanye kunun.

“Idan baki koshi ba ki kara ki cika cikinki, sai ki kwanta kamin a kawo dumame”

Kaka ta fada tana janyo kwanon da take ajiyar goro ta bude ta balla kadan ta saka a baki tana taunawa.

“Na koshi”

Aminatu ta fada tana lashe baki.

“Kaka ni ban koshi ba”

Talba ya fada yana kallonta, sai tai masa banza kamar ma bata san da zamansa a gurin ba. Murmushi yai ya tashi ya kuma kusa da ita ya zauna ya kai hannunsa ya dafa ta.

“Haba Uwargida kin taba ganin matar dake son aljanna kuma tana fushi da mijinta”

“Kai Mu'azu babu wani abun da zaka min ka wanke kanka, kar nake kallonka, kuma ka gwada min yan'uwan ubanka sun fi na uwarka, ba zan manta da wannan ba, ka nuna wasu dangin sun fi wasu”

Saurin dauke hannunsa yai yana jin wani irin, har ga Allah ba manufarsa kenan ba, amman kaka ta kasa fahimtarsa. Kallon Aminatu yai.

“Shalele zaki iya zuwa waje? Zamu yi magana da Kaka”

“Toh”

Ta amsa tana kokarin tashi sai Kaka tai karaf ta ce.

“Babu inda zata je, ni ce uwarta ni ce ubanta a yanzu, bata da wasu dangin sai ni, idan zaka yi maganar kai a gabanta ko kuma ka je can gurin naka dangin kai magana ai kai kana da gata”

“Haba Kaka wannan wace irin magana ce kuma?”

Ta furta cikin rashin jindadi, sannan ya mike tsaye ya ciro kudin dake aljihunsa ya aje masa a gabanta.

“Gashi nan a ci goro ni zan kama hanya, kuma zan aiko mota a daukeki saboda ciwon kafafuwan a kai ki asibiti”

“Ai daman idan ka zo garin nan kamar ana tsikararka kake, shiyasa kowa baka sani ba na dangin uwarka, idan ka zo baka san kaje ko'ina ba, idan kuma ka tafi sai an sake ganinka. Ka dauki kudinka sisin kabo bana so naka Mu'azu, ai baka gan ni a wahala ba, komai bana so naka, kuma karka sake takowa garin nan da sunan zuwa ganina na yafe maka har na mutu”

Sai a yanzu ya tabbatar da gaske kaka take, domin babu alamar wasa a fuskarta sai ma fushin dake kara bayyana a maganarta. Kallon Aminatu yai wanda ita ma kallonsa take tana mamakin yadda Kaka take masa magana da fushi, be ce komai ba ya dauke kai ya fice daga dakin cikin rashin jindadi.

“Auta dauki kudin nan ki kai masa”

Kaka ta fada tana nuna mata kudi, kamar marar kuzari haka Aminatu ta isa gurin kudin ta dauka ta fito daga dakin tana jin kamar ta tambayi kaka dalilinta na kin karbar kudin.
Ko da ta fito waje yana zaune cikin motarsa ya bar kofar a bude yana kallon kofar gidan kamar ya san zata fito, tafiya take kamar wata hawainiya har ta isa gurin motar ta ja ta tsaya, ya dade yana kallonta ita kuma ta kasa daga ido ta kalleshi saboda kukan dake son zuwa mata.

“Shalele ya akai?”

Ta mika masa kudin da hannu biyu. Sai yai murmushi.

“Kin ga na kawo ki nan amman kin fini fada, saboda ke Kaka take fushi da ni”

“Ko dai tana jin an dora mata lalura ne?”

Ta tambaya hawaye na cika idonta.

“Aa wani abun ne dabam”

Ta hade yawun bakinta.

“Zan koma Gusau”

Bata ce masa komai ba, kuma ta kasa daga idon ta kalleshi.

“Ba zaki ce min Allah ya tsare ba?”

Ya furta yana kallon yadda yanayinta ya sauya, shi kansa yana jin kamar kar ya tafi ya barta. Sai a lokacin ta kalleshi hawaye a sauko mata.

“Da gaske idan ka tafi sai bayan shekara zaka dawo?”

Ido ya kura mata sannan ya fito cikin motar ya tsaya a gabanta still yana kallonta.

“Ba ki son na tafi?”

Samun kanta tai da daga masa kai.

“Kina son na dawo?”

Nan ma kan ta daga masa.

“Zan dawo”

“Yaushe?”

Ta tambaya cike da shauki da kuma zakuwar ta ji yace mata gobe ko jibi.

“Yaushe?”

Ta sake tambaya.

“Ba da dadewa ba”

“Yaushe?”

Ya shafa kansa zuwa hancinsa.

“Cikin satin nan”

“Ya za'ayi na yarda zaka dawo”

“Saboda nace zan dawo, idan na ce zan yi abu, zan yi”

Ta dauki idonta hawaye na sauko mata sosai, sai take jin kamar shi ma din idan ya tafi ba zai dawo ba. Ya kara matsowa kusa da ita cike da tausayinta.

“Kina son na zauna ne?”

Ta daga masa kai sai ya saka hannunsa ya dago kafadarta.

“Idan kina son na zauna sai idan zaki yarda ki zauna da ni zama na har abada”

Ta masa kallon rashin fahimta, sai dai kuma ta kasa tambayarsa abun da yake nufi da haka. Ganin haka ya saka shi yin murmushi ya dauke hannunsa daga fuskarta ya dan ja baya kadan yana kallon harabar gidan.

“Kina son zama da ni?”

Ta sauke kanta k'asa ta kasa cewa komai. He just ask dan ya gane idan tana son zaman da shi ko akasin haka, domin Kaka tana kokarin hada aurensu ne kawai ba tare da lura da suna son junansu ba ko a'a, hadi ne kawai take son tai musu irin na kauye na zamanin baya.

“To ni ina son zama dake, shiyasa nake son Kaka ta bani ke...”

Sai kuma ya kasa karasawa yana ta kallon reaction dinta.

“Na aureki...”

Dagowa tai da sauri ta kalleshi gabanta ya buga da mugun karfi, zuciyarta tai wani uban zillo kamar zata fito daga kirjinta ta fado kasa. Bata san miyasa take jin kamar kalamansa sun mata nauyi ba, alhalin ba a yau ya fara furta mata wannan kalmar cewar zai aureta ba, wacan karon ya ce saboda kar su sabawa Allah ne, har yace idan ta samu wanda take so ko yan'uwanta zai sake yanzu fa? Bayan gashi tana tare da kaka. Ganin ta yi shiru bata ce komai ba ya saka shi zaunawa cikin motar.

“Zan tafi”

Sai ta sake mika masa kudin a karo na biyu.

“Ki koma ki kai mata, idan bata karba ba ki dauka na baki”

Yaja motar ya rufe yai reverse tana tsaye tana kallonsa hawaye na sauko mata, sai da ya juya motar sannan ya sauke gilashin motar ya leko da kansa ya kalleta ya sakar mata murmushi sannan yaja motar ya kama hanya. Tsaye take tana kallonsa tun tana hangensa har ta daina hangosa, sai ta durkushe a gurin ta fashe da kuka ta saka kanta cikin guiwar hannunta tana kuka sosai. Sai da ta soma jin motsin mutane na wucewa sannan ta tashi ta share hawayenta ta shiga cikin gidan kanta a kasa tana tafiya kamar dazun.
  Ko da ta shiga Kaka bata cikin dakin, sai kawai ta hau gadon data kwana a jiya ta rumgume kudin a kirjinta, can kuma ta juya baya ta fara kuka a hankali tana jin zuciyarta na mata mugun zafi.


TALBA POV.

Be taba rabuwa da wani abu ya ji yana marmarinsa ba so soon kamar Aminatu, baronta da yai a can har ya fara jin kewarta. Murmushi yai tunawa da tambayar da tai masa cewar yaushe zai dawo.
Wayarsa ya dauka ya kira Daddy, ringing daya ya daga.

“Ranka ya dade yanzu nake kokarin kiranka”

“Daddy barka da safiya”

“An tashi lafiya fatar ka kamo hanya”

“Gani a hanya Daddy, fatar Momy ta dawo”

“Kun fara damuna da zancen Momy fa, ni ma zan yi yaji na tafi Abuja na yi zamana”

Talba yayi murmushi cike da kaunar Daddy daman san shi da barkwanci.

“Haba Daddy idan ba Momy ai ba rayuwa, dan Allah kace min ta dawo”

“I think dai yau ko gobe zata dawo”

“Gani tafe, zan rakaka ka dauko ta akwai maganar da nake son yi da ku mai muhimmanci kuma ina fatar zaku fahimta”

“Allah ya kawo ka lafiya”

“Ameen”

Ya katse kiran, sannan ya kira Leila kamar yadda ya tsammata bata daga kiran ba, sai ya kira Amal ya gaisa da ita sannan ya kira Momy.

“Talba”

“Momy barka da safiya”

“An tashi lafiya”

“Lafiya kalau Alhamdulillah”

“Ance ka baka kwana a gida ba, ina kaje?”

“Waya fada miki?”

“Amal”

Yayi murmushi mai sauti.

“Allah ya shirya Amal ba zata daina gulma ba, naje kauye ne”

“Amman kasan hanyoyin nan ba su da kyau Talba”

“Nan ai da sauki abun be kawo ba, kuma gani hanyar dawowa, ina fatar kin dawo Momy”

Ta yi shiru.

“Rashinki ne ya saka muka bar gidan nan, gaba daya gidan baya mana dadi, kuma ina jin babu dadi idan na tuna cewar saboda ni komai ya faru”

“Zan dawo ai, kuma ba laifinka ba ne komai ya wuce”

“Zan zo anjima na daukeki”

“Aa sai next week”

“Momy do this favor for me dan Allah...!!!”

“Shikenan”

Yayi murmushi.

“Thank Youu Momy ashe kina so na”

“Wannan wace irin magana ce Talba? Bana son ka nake zaune tare da kai? Na taba cutar da kai a tsawon zaman da na yi da kai? Ta ya uwa zata zauna da tun yana jariri har ya girma a hannunta kuma ta ce bata taba son dan nan ba, bayan kuma yaron nan be mata komai ba? Engineer ya riga ya dasa maka wani mugun ice na kiyayata a zuciyarka shiyasa har kake min wani kallo na dabam”

“Ko kadan Momy, ban taba kallo wata mace a matsayin uwata ba sai ke, ban san wata uwa ba sai ke, kuma Daddy be shimfida min komai ba a zuciyata sai kaunarki, ke da shi kun kasa fahimtar juna ne kawai, kina ganin kamar ya zurfafa a so na, shi kuma yana ganin kamar baki so ni a yadda ya kamata ki so ni ba, kuma duka na fahimcinku, fatar za a yafe min”

“Baka yi komai ba, Allah ya maka albarka”

“Ameen”

Ya amsa da murmushi sannan ya kashe wayar, ya cigaba da tukinsa yana tunanin yadda zai gabatar da Daddy da Momy maganar Kaka.
Ko da goma tai har yayi wanka ya canja tufafi, be tarar da Daddy a gidan ba haka ma Amal tana makaranta Leila ce kawai a bangare sai Kabir dake karyawa a dinning.
Kallo daya Kabir yai masa ya dauke ido domin a yanzu be da makiyi kamar Talba, Leila kuma ta kura masa ido ta kasa daukewa har ya karaso kusa da ita ya zauna, sai gabanta ya buga da karfi, duk yadda take son hana zuciyarta soyayyar Talba sai ta kasa musamman ma idan yana kusa da ita wani lokacin har jin take kamar ta rumgume shi, sai dai gudun zubar da class dinta ya saka bata nuna masa haka, dauke idonta tai tana ganin wani uban kyau daya kara kamar an shafa masa hoda.

“Ya kike?”

Ta mike tsaye sai ya kalleta.

“Can we talk”

Tsayawa tai sai dai bata juyo ta kalleshi ba, kuma bata ce masa komai ba.

“Zauna mana”

Ta koma ta zauna.

“Akwai abun da kike so ne?”

Ya tambaya feeling some how kamar he's out of words, haka yake a duk lokacin da yake tare da Leila, duk kalmar da zai kama yai magana ta fahimta da ita sai ya ji kamar ba zai iya ba, except ta fada masa baka magana ne ko kuma ta masa wani laifi, on that point kam ya san abun da zai fada mata. Mikewa tai tsaye ta nufi upstairs sai ya bita da kallo yana ta kokarin hada kalmomin da zai yi mata magana ta fahimta amman ya kasa har ta haye sama. Tashi yai ya nufi kofar fita Kabir ya bishi da wani banzan kallo har ya fice, bangarensa ya koma ya dauki keys dinsa ya fito ya shiga motarsa. Ko da ya isa gate har sun bude masa. Yana fita ya fisge motar da karfi ya dauki hanyar da zata kai shi gurin da Daddy yake aiki. A harabar ma'aikatar ya faka motarsa ya fito ya nufi ciki da saurinsa yana kiran Daddy a waya.

“Daddy gani shigowa zan muje mu dauko Momy yanzu”

“Bana gida”

“Yeah na sani office dinka nake nufi”

“Bana office, ina gidan Hajiya Yana, na yi marmarin abincin Doctor ne shi ne na zo na yi breakfast, amman idan na gama zamu dawo gida yanzu”

Talba ya tsaya cak yana mamakin yadda Daddy ya fishi hikima da wayo, wato a can ma ya karya a maimaikon ya jirashi su tafi tare, and yes yayi abun da ya dace, daman shi yana son saka Daddy a gaba ne saboda yana ganin kamar baya son dawowa da Momy ne.

“Fine sai kun iso”

Ya fada sannan ya juyo ya dawo yana murmushi ya nufo motarsa. A ranar be yi maganar da Daddy ba, duk da kasancewar Daddy ya tambaye shi amman sai ya dauko wani zancen, ba dan komai ba sai dan ganin a ranar Momy ta dawo be kamata yai maganar ba, washe gari ma be yi maganar ba, har sai da aka kwana uku da dawowar Momy a gidan. In all these three days yana kiran Kaka a waya idan ta daga ta ji muryarsa sai ta kashe, last kiran da yai mata ma ya bukaci ta bawa Aminatu wayar amman bata ko tsaya saurarensa ba ta kashe wayar.
  Sai da Amal ta tafi makaranta Kabir ma ya fita Leila kuma ta koma dakinta, sannan ya kalli Momy ya ce.

“Momy ina son magana da ke da Daddy,  ko zamu iya zuwa can?”

Momy ta kalleshi daman tun da suka zauna karin kumallon ta lura da babu abun da ya ci sai kofin tea yake ta juyawa.

“Miya faru?”

“Magana ce mai muhimmanci kuma ina son na yi ta ne tare da ke da Daddy”

“Okay gani zuwa”

Sai ya dauki tea din ya mike tsaye ya nufi kofar fita, Ta kofar gaba ya shiga bangaren Daddy a babban falonsa ya zauna yana shan tea a hankali. Sai ga Momy ta shigo ta kofar ciki,

“Baka shiga ciki ba?”

“I think yana karyawa”

“Let me talk to him”

Ta nufi hanyar karanin falon, sannan ta wuce bedroom dinsa. After like thirty minutes Daddy ya fito Momy tana bayansa, a karamin falo ya zauna sai Momy ta kira Talba.

“Talba...”

“Na'am”

Ya amsa sannan ya tashi ya nufi falon, a kasa ya zauna Momy kuma na zaune kusa da Daddy, dukansu sun tattara hankalinsu guri daya suna kallonsa musamman ma Daddy da ya fahimci akwai damuwa a tattare da dansa.

“Kana da wata matsala ne? Na ga ko breakfast ba ka yi ba”

Momy ta fada, sai Daddy ya cire gilashin idonsa.

“Mu'az akwai wata damuwa ne?”

Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya ce.

“Matsala ce kuma ba matsala ba”

“Wani abun ne?”

Momy ta sake tambaya. Sai Talba ya fere musu daga buri har wutsiya akan kudirin Kaka da kuma irin yadda ta dauki fushi da shi. Ba abun da kaka tai ne ya bawa Momy mamaki ba kamar jun cewar Aminatu yar'uwarsa ce, Daddy ya yunkuro yana kallonsa shi ma da mamaki.

“Wato baka rabu da yarinyar nan ba Talba? Har da daukarta ka kaita gurin Hajiya, da ba yar'uwarta ba ce acan zaka aje ta kenan?”

Cewar Momy cikin wani irin bakinciki na jin abun da Talba ya fada, sai Daddy ya daga mata hannu domin shi ba wannan ne damuwarsa ba.

“Taimako ai abu ne mai kyau, babu laifi a abun da Mu'az yai, ki tattara wannan abun ki aje gefe daya, ki bari mu ji da damuwarsa. Kai kana son yarinyar”

Daddy ya karasa yana kallonsa with serious face. Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai ce.

“I don't know yet”

“That's mean baka son ta, and no one can forced you shikenan”

Daddy ya karasa masa domin yasan waye Talba idan yana son abu zai fito kai tsaye ne ya ce yana so, haka ma ida baya so zai fadi cewar baya so.

“Ya ma za'ayi ya so ta? Yarinyar ai bata dace da shi ba, imagine an yi raped dinta kasan iya mutanen da sukai mata wannan aika aikan? And waya sani ko tana dauke da wata cutar, lastly Talba ba mutum ne mai son hayaniya ba bana tunanin zai iya zama da mata biyu”

“Wannan ba matsala ba ce, da ace yana sonta za a iya bincikar lafiyarta kuma i will support him ya aureta, amman tun da baya son ta ba zai aureta ba”

Daddy ya fada, gaba daya sai jikin Talba ya mutu kalaman bakinsa suka kare, domin ya san duk juyin duniyar nan da za'ayi Daddy ba zai yarda ya aureta tun da har be nuna cewar yana sonta ba, and yes shi kansa be san yana sonta ba, all what he know is yana tausayinta.

“Amman... Kaka...”

Talba be karasa ba Daddy ya tari numfashinsa.

“Zan kirata zan yi magana da ita a waya, zan fahimtar da ita, yaushe rabon duniya da ayaraye, ai an daina wannan abu a wannan zamani, ko da ma ana yi ni ba zan bari ayi maka ba”

Daddy na kawai nan ya mike

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login