Showing 102001 words to 105000 words out of 133328 words
din miye hadinka da ita? Kana kokarin bata alakarka da kowa saboda wata yarinyar da baka san asalinta ba? Ka bata hakuri daman ba zai yiyu mutum ya samu abun da yake so dari cikin dari ba, idan tai hakuri da zaman a can sannu sannu sai mafita ta zo mata, idan ta samu lafiya sai ka kaita gurin yan'uwanta, idan kuma ta ki yanzu ka dauke ta ka kaita gurin da yan gudun hijira suke zama ka siya mata abinci da dan wani abu mai dama ka bata”
Talba ya rumgume hannayensa yana kallon Ali.
“Karka zama marar tausayi Mana, abun da ya faru da ita zai iya faruwa da kowa, kuma ina ce kai ka gabatar da min da yarinyar nan saboda kana ganin tana bukatar taimako”
“Amman ni ban yi tunanin zata haifar da matsala tsakaninku da Leila da kuma Momy da Daddy”
“Babu matsalar data haifar, domin bata ce dole a taimake ta ba, kuma ba zuwa tai ta hada su fadan ba, daman na san damuna zaka yi da maganar Leila shiyasa bana son zuwa gurinka yanzu”
Ali yayi murmushin takaici.
“Allah sarki Leila baiwar Allah, yanzu har baka son maganarta? Ni daman shawarar da zan baka kawai ya daure ka sake yi mata maganar auren ka lallabata, idan ta aureka hankalinku zai kwanta zata samu natsuwa kai ma kuma zaka samu?”
“That's the only solution, gidan zan kaita kuma wannan ya zama a tsakaninmu, ni Wallahi kasa ma na kara jin tausayin yarinyar nan, bata da gata ko kadan”
Yana kawai nan ya nufi driver seat. Ali ya bishi da kallo.
“Ya ina maka maganar Leila kana maganar wata yarinyar? Talba lafiyarka kuwa”
“No ban da lafiya zo ka kai ni asibiti”
Ya fada bayan ya shiga motarsa sai da yai mata key sannan ya rufe, yai reverse ya ja motarsa ya bar Ali tsaye bakin kofar gidansa.
Daga gidansu Ali family house dinsu ya nufa, sai da ya faka motarsa harabar gidan sannan ya soma jin wani yanayi na kadaici tunawa da Momy bata ciki. Ya dade cikin motar sannan ya bude ya fito ya nufi bangarensa, kamar wani bako haka ya shiga bedroom din ya zauna kan kujera yana maida numfashi, sai kuma ya dago wayarsa yana kallo kamar mai tunani, yawo ya fara yi da yatsunsa saman wayar har zuwa gurin number Madina sai dai be kira ba, kiran Amal ya shigo wayarsa saurin tashi yai zaune ya amsa kiran.
“Lil Sis”
“Ya ka yi magana da Daddy?”
Ya kai hannunsa ya shafa hancinsa zuwa kasan bakinsa.
“Yeah na yi magana da shi, kuma zai dawo da ita komai zai wuce, amman yana bukatar mu ba shi lokaci domin shi ma yana cikin bacin rai a yanzu”
“Amman dai ai zata dawo ko?”
“Eh dole ma ne Daddy ya dawo mana a ita, Ki kwantar da hankalinki”
“Toh”
Ya yanke kiran, ya mike tsaye ya fice daga idakin, motarsa ya nufa ya shiga tun kamin yai reverse ya danna horn, ko kamin ya isa gate din an bude masa.
Kai tsaye gidansu Madina ya nufa, sai dai wannan karon be shiga ciki ba ya faka bakin gate din, ya kirata a waya ya sanar mata yana waje.
Bayan kamar minti talati aka bude gate din ta fito rike da Aminatu, mai aikinsu kuma na rike da jakar tufafin Aminatu, daga cikin motar yake kallonsu har suka karaso sannan ya bude motar ya fito ya zagaya ya bude mata gidan gaba ta zauna ya rufe. Sannan ya juyo ya kalli Madina.
“Thank Youu, zan so wata rana nima n rama abun da kika yi min na karamci”
Murmushi take tana masa wani irin kallo mai cike da saukin so.
‘Ina ma zan iya buda maka zuciyata ka kalli irin kaunar da nake maka? Taya zan iya fada maka cewar kaunarka ita ce tukuicin abun da na yi maka?’
A ranta take ta wannan tunanin tana binsa da kallon da bata san tana yi ba, har ya bude back seat ya saka jakar tufafin ya rufe ya zagaya bangaren direba ya shiga ya ja motar, sai da yai horn sannan hankalinta ya dawo jikinta har ta zabura sai kuma ta lumshe ido tana maida mumfashi a hankali.
Sai da yai nisa sannan ya kalli Aminatu ya ce.
“Ana miki wani abu ne a gidan?”
“Aa”
“Miyasa baki son zama a can?”
“Ba komai”
Be sake cewa komai ba, sai dai duk bayan lokaci yana kallonta da karantar yanayinta.
“Yanzu zan kai ki gidana ki zauna, a can babu wanda zai takura miki”
“Gurin su Momy?”
Ta tambaya tana kallonsa nan da nan idonta har ya cika da hawaye.
“No gidana ni kadai ne a ciki nima kuma bana zama, yanzu ke kadai zaki fara zama a ciki”
Ta yi shiru bata ce komai ba, sai dai kuma bata gama fahimtarsa, ba mutane kamar ya? Gida ne da zata zauna ita kadai? Ko kuma da matarsa? Amman ai yace mata Leila ce matarsa kuma da alama be aureta ba. Haka tai ta jerowa kanta tambayoyi tana yi tana kallonsa har suka kusa isa gidan, each and every single kallo da take masa sai idanuwanta da na shi sun yi tarayya. Wata sabuwar unguwa ce mai dauke da manyan gidaje na Alfama, a gaban wani katon green gate ya faka, sai ya kalleta.
“Bari na bude gate din”
Bata ce masa komai ba, ya bude motar ya fita tare da keys din hannunsa ya saka ya bude gidan ya shiga ciki ya bude gate din gaba daya sannan ya dawo yaja motar ya shiga da ita ciki, kato gidane mai matukar kyau da tsari, ya fenti ko'ina da golde color, ga manyan itatauwa da ko'ina daga bakin entrance din kuma flowers har harabar gidan. A inda ya faka motarsa guri ne da aka tanada aka kawata domin aje motoci kawai, a kusa da inda ya aje motar akwai mota biyu dake lullube. Sai da ya kashe motar sannan ya bude ya fito, ya isa gurin gate din ya rufe, ya dawonya bude bangarenta ya miko mata hannunsa.
“Fito”
Ta rika hannunsa ta fito, ya rufe motar ya da taimakonsa suka isa entrance din, sai dai a nan be tsaya jiran ta taka da kafarta sai ya sake ta ta isa gurin kofar falon ya bude, sannan ya dawo ya dauke ta cak ya shiga da ita cikin falon, babu komai a ciki sai dai an ware gurin yin komai kama daga dinning har zuwa gurin saka plama. Sai dai ba a saka kujeru ba, ba a masa kwalliyar komai ba. Bedroom din ya nufa da ita shi ma ba yi masa wani gyara ba sai dai an saka gado da standing mirror.
A saman gadon ya sauke ta sai ta fara rabon ido yana karewa dakin kallo, ko'ina yayi datti alamar an dade ba a zauna a gidan ba.
“Bari na kunna miki inji”
Har ya juya sai ta mike tsaye tana jin tsoro.
“Ni kadai zan zauna nan?”
Ya juyo ya kalleta, babu komai a cikin idanuwanta sai tsoro da tashin hankalin da be san inda ya samu asali ba.
“Kina jin tsoro ne?”
Ta daga masa kai idonsa na cika da hawaye.
“Ba zan iya zama a nan ni kadai ba”
“Amman idan ba a nan ba, babu inda zan kai ki, duk inda zan kaiki za a takura miki ne”
“Ni dai ba zan iya zama a nan ba”
Ta fashe da kuka, tunani ya soma dawo mara, tana ganin kamar a nan din ma wani abun zai same ta.
“Dan Allah karka bar ni a nan tsoro nake ji sosai”
Ta fada tana ta kokarin takawa ta isa inda yake.
“Ba zai yiyu na kai ki wani guri ba, kuma ba ni da inda ya fi nan, kuma ba zai yiyu na zauna a nan ba, saboda ni ba muharramin ki ba ne, taba ki ma da nake Allah kadai ya san zunubin da zan samu”
Yana kai Aya saibta fashe masa da kuka sosai jikinta ya fara rawa, ta fara daga masa murya zata masa irin kukan da tai a lokacin da Leila ta mari Mairo. Sauri karasa yai kusa da ita ya rikata, sai ta fada jikinsa, nata jikin yana karkarwa numfashinta har rawa yake.
“Ya isa ya isa ba zan bari ki zauna a nan ke kadai ba”
Ta runtse ido sosai jikinta nata rawa numfashinta ma kamar zai fita ya bar jikinta. Sai da ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ta taka tana a jikinsa ya zauna bakin gadon tare da ita.
“Tsoro nake ji, bana son zama ni kadai”
“Ba zaki zauna ke kadai ba, amman we have to plan, ba zai yiyu mu zauna sheidan ya rijanye mu, be kamata na yi kusanci da ke haka ba...”
Ya fada yana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya dago ta a hankali sai ta kalleshi idonta har ya fada.
“Zan zauna tare da ke, amman sai idan zaki yarda da wani sharadi da zan gindaya miki”
“Minene?”
Ta tambaya bakinta na rawa, jikinta na amsawa wani sanyi ya taso mata. Buaar da iskar bakinsa yai ya mike tsaye yana ganin kamar be dace yai mata wannan maganar ba, ya zata kalleshi? Ya zata dauki abun? Besides shi dai ya san ba sonta yake ba, amman dole yai haka saboda masa wa kansa mafita da kuma ita. Wayarsa ya ciro ya kira line Momy ringing biyu kamin tai na uku ta daga, da sallama.
“Talba”
“Na'am Momy kina lafiya?”
“Lafiya kalau ya kuke?”
“Momy kina ina?”
“Ina gidanmu, ina zan je?”
“Haba Momy ko da ace saki uku Daddy yai miki ai be kamata ki bar gidan nan ba, saboda kin tara mu sai dai shi ya tafi ya barki”
“Uhm... Indai kuna lafiya ai shikenan zan dan yi wani aiki”
Be ce komai ba har ta kashe wayar, sai ya juyo ya kalli Aminatu, sai kuma ya juya ya fita, kamin ya kunna injin din ya dawo har ta kawo bakin kofar falo tana hawaye, da tana dafa gini, har ga Allah tsoro take ji bana wasa ba, yanayin gidan da yadda yake shiru ga shi da girma sai yai mata kamar wacan dajin.
“Har kin kawo nan?”
Ya fada bayan ya bude kofar falon ya shigo, da mamaki ya kalleshi.
“Ba zan zauna a nan ba, dan Allah ka kai ni wani gu....gu... rin...”
Kamin ta karasa tai baya ta fadi duk kokarin da yai na riko be yi nasara ba har ta kai kasa babu numfashi.
28
MG'S COLLECTION.
"Saudatu ki shirya zamu je gaishe da su Baba, kasancewar azumi ya yi nisa ya kamata ace sun samu wani tagomashi daga arziƙin haihuwa"
Ta faɗa tana nufoni da ƙunshin kayan da ta soma zazzagesu. Galala yaro da wayau, haka na saki baki ina kallonta.
"Amma Raulatu baki kyautamin ba, haka zan je gaishe da su hannu na dukan cinya bayan ke kin gama shiryawa?"
"Ban fahimta shiri ba? Kina nufin ki ce min baki da labarin ƙayatacen wajen da suka sahalce mana yin Ramadan package?"
"Ina kenan?"
"MG'S COLLECTION mana. Wajan da ya tanadar mana da sauƙaƙiyar hanyar kyautatawa makusantamu ta hanya me sauƙi. Ingantattun kayansu masu sauƙi da kuma inganci. Ɗangin Turare, Darduma, Jallabiya, Agogo, Jaka da Takalmi. Har ma da Alƙur'ani mai girma"
"Eh lalai ki ce sa'a tafi manyan kaya, da hanau gara manau"
"Tabbas kuwa ba su tsaya iya nan ba, sun saida ingantatun kayan ɗa'a masu maida tsohuwa yarinya shar washar da ita.sannan munada set n gyaranjiki me matukar kyau yasakiyi haske meban shaawa,munasaida daddaya,kuma Akwai frams na ƙawata ɗakin amarya da uwargida"
"Tabbas zan garzaya ƴar uwa domin kashe ƙwarƙwatar idanuna"
"Za kuwa ki godemin, zaki same su a adireshinsu dake
Kunemesu ta WhatsApp number nasu 07046881166, 08062991549
kan waɗanan lambobi. Ga sauƙi ga inganci ga kuma mutuntawa.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Momy ta aje wayar tana murmushin takaici.
“Waya kira?”
Hajiya Yana ta tambaya, sai Momy ta kalleta.
“Talba ne”
“Bawan Allah, bayan duk abun da kike masa har kiranki yake”
“Uhm Hajiya kenan, ke da Alhaji sai dora min laifi kuke”
“Dole a dora miki laifi mana Amina, yaron da zai girma a hannunka be san wata uwa ba bayan ke, amman ya kawo wata ki masa haka saboda kawai ba ke kika haife shi ba”
Cewar Mahaifiyarta Hajiya Yana.
“Hajiya ni fa ba kamar ke bace, ni kam kaza ce mai son yayanta, ba zan iya yi ma yayana abun da kike mana ba, na nuna mana kin fi son yayan yan'uwa fiye da mu, yanzu fa zamani ya canja, Wallahi kowa kansa ya sani”
“Allah ya wadaran wannan canji na zamani Amina, mu kam a da ko dan makoci dan ka ne balle kuma dan dan'uwa na kusa da nesa”
“Hajiya ai ni ban hada jini da Talba ba”
“Ban ga ta inda Talba ya babanta ki da mahaifiyarsa ba, bibiyar da yake miki ko Kabiru da kika haifa be fishi yi miki bibiyaya ba”
“Babu wannan damar ne ai, da ace zai samu hanyar nuna min zai yi, ai ruwa be taba zama jini ba”
Hajiya Yana ta girgiza kai.
“Na yi tunanin sakin nan da Alhaji yai miki zai saka ki natsu ki gane kuskurenki domin yayi abun da ya dace, ya nuna miki jini ba abun wasa ba ne, ke kam dai halinki ya fita dabam dana yan'uwanki, ba ki dauko ni ba kuma baki biyo halin mahaifinki ba, sam wannan ba rayuwa bace”
Mikewa tai tsaye tana dariya.
“Hajiya idan kina min wani abun kamar ba ke kika haife ni ba, ni saki be tashi hankalina ba, amman ya saka na kara nazari da tunani da kuma fahimtar abubuwa, ina mai tabbatar miki sai Engineer yayi nadama sai ya zo da kansa yana neman afuwa yana kuka da hawayensa, abun da be min a kurciya ba yanzu zai min shi da tsufana? Da yaya? Ai duk wanda ya zama silar mutuwar aurenka a gidan mijinka da kake kauna kuma da yayanka manya ba kakana ba, ba masoyinka ba ne Hajiya...Hmmm”
Ta karasa tana kashe ido daya, sannan ta kai hannu ta dauki wayarta tare da plate din data gama cin abincin ta nufi bedroom, Hajiya Yana binta tai da kallo tana mamaki yadda zamani ya lalace har zaka fifita danka akan son zuciya, domin a iya abun da ta fada mata bata hango Talba ko Daddy da wata matsala ba, duk abun da ya faru ita ta janyo komai, ba tun yau ba halin Amina ya fita dabam a cikin yayanta.
“Allah ya kyauta ya shirya ki”
Addu'ar da Hajiya Yana tai kenan ta cigaba da jan carbinta, tana gama tasbihin jikanta Kabir ya turo kofar falon ya shigo, juyows tai ta bishi da kallo har ya zauna, bata ce masa uffan ba domin ta lura yana cikin yanayi na bacin rai, domin ba haka ya saba shigo mata ba. Idan zai shigo ya kan yi sallama kuma ya shigo yana wasa da ita tsabanin yau da ya shigo kamar wanda akai wa dole.
“Hajiya Yana Ina Momy?”
“Bacin ran da ubanku ya saka muku shi ne zaka zo ka sauke a kaina?”
Ya kalleta sai kuma ya hade yawu yana ta kokarin danne bacin ransa.
“Hajiya ki yi hakuri, ina Momy?”
Da hannu tai masa nuna da kofar dakin, har ya mike tsaye sai ta kira shi.
“Kabiru... Zauna”
Bayan ya juyo tai masa umarnin zama, sai ya koma ya zauna.
“Karka dorawa mahaifinka laifi, karka kuskura ka biyewa mahaifiyarka abun da tai da kai da ita Leila duk ba ku kyauta ba, hakan da kuka yi kun nunawa Talba rashin gata ne da galihu, domin na tabbatar idan kai ne Amina ba zata maka haka ba”
“Son da Daddy yake yi ma Talba yayi yawa Hajiya, ni ma sai yanzu na lura da haka, kuma da Talba ya dauki Momy a matsayin uwa ba zai tana yarda ta kawo yanzu a gidan nan ba, duk yadda zai yi ya saka Daddy ya maidata gidanta zai yi, saboda Daddy yana jin maganarsa kuma yana gudun bacin ransa, amman be yi komai ba, saboda ba mahaifiyarsa ba ce”
“Aa Kabiru kar fushi ya rufd maka ido, ka rika ganin daya a matsayin biyu, baka san abun da yake kasa ba, kuma ka san halin Mahaifinka sani murdanden mutum ne, ba lallai ne wani ya iya saka shi abun da be tashi ba, yanzu kuma Amina ta gama waya da Talba”
Kabir ya mike tsaye.
“Ke ma kina goyon bayansa kenan? Akan mahaifiyata bana ganin kowa da gashi Hajiya, ya sha saka ta kuka saboda Silly abu Daddy zai rufeta da fada har sai ta yi kuka ranta ya bace, amman yanzu mai gaba daya Daddy yai, be dubi ni ko Leila ko Amal ba, abun da be yi da kurciya zai aikata da tsufa saboda Talba? Ya duniya zata kallemu da girmanmu ace iyayenmu sun rabu”
Hajiya ta nuna shi da yatsa.
“Kabiru me mahaifiyarka ta fada maka? Ka zurfafa abun nan”
“Babu zancen zurfafawa Hajiya, ina fada miki gaskiya ne, har yanzu Talba ne kira ya min magana ba, kuma be saka kafarsa ya shigo gidan nan ba, that's mean ya jidadin abun da Daddy yai kenan? Yanzu na fahimci dalilinsa na kin nunuwa Leila kulawa wato baya son ta kuma ba zai iya cewa baya son ta ba, ai ya san kulawa tun da gashi nan yana nunawa yarinyar, and now da Leila ta kamu da kaunarsa ta saka a zuciyarta shi ne yake kokarin broken heart dinta and i won't let that happen, i will teach him a lesson”
Yana fadar haka ya nufi dakin da Hajiya Yana ta nuna masa sai wani cika yake fushinsa yana kara hauhawa.
TALBA POV.
Kallonta yake yana ta tunanin ta inda zai fara mata bayanin, zata fahimta? No wait ya ma dace yai haka? Amman idan be yi ba yana da wata mafitar ne? Idan yace zai kaita wani gurin zata zauna? Zata jidadin rayuwa? Idan kuma ya zauna da ita anya zai iya rike ba tare da shiga hurumin da Allah ya haramta masa ba?
Ta dan sakar masa murmushi ganin kallon yayi yawa har ta soma tsarguwa, sai shi ma yai murmushi yana cigaba da kallonta.
“Kin san me?”
Ta girgiza kai alamar aa.
“Ina ganin kamar muna da mafita daya ni da ke? Ita kadai ta rage mana”
Kamar ya san ba zata tambaye shi minene mafitar ba, sai