Showing 111001 words to 114000 words out of 133328 words

Chapter 38 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

485

Middle Ads

Ali, ba laifi ta samu sakewar zuciya ba kamar dazun da take a cikin damuwa ba. Da kansa ya bude mata mota ta shiga front seat ta zauna sai Madina ta dubeshi tana murmushi.

“Yayi kyau Aminin ango, lallai kasan ta kan amaryar nan ta ku, nan da nan har ka mantar da ita damuwarta”

Leila ta kalli Ali tana murmushi, shi ma murmushin yake yai yana ganin kamar da biyu Madina ta fada masa maganar nan.

“Dole ne na yi abun da zan iya na tare abokina kar ya fadi”

“Yayi kyau, ai ka fi abokinka sanin darajar mata shiyasa kake damuwa da kukansu, matarka da huta Ali, Wallahi da ni na aureka da more miji”

A zahiri da kanta take, sai dai a kasan zuciyarta tana ingiza mai kan tururuwa ne, saboda Leila ta soma dasa wani abu a zuciyarsa akan Ali.

“Kina da son zolaya Madina, yanzu dai kuje gida ku huta”

“Thank Youu Ali”

Leile ta fada sai ya gyada mata kai ya rufe mata motar, Madina ta tashi motar tana fadin.

“Angonki fa ya kira ni yana tambayar ina kike?”

“Ai ina ganin kiransa na share shi”

“Aa Leila be kamata ki yi haka ba ai sai ransa ya bace, kuma tun da har ya kira ai ya nuna miki kulawa”

Madina na rufe baki sakon Talba ya shigo wayar Leila, tsaki tai bayan ta karanta sannan ta nunawa Madina, Madina kam dariya tai ta rike wayar da hannu daya tana rubutawa Talba amsar da take ganin ta dace da shi, sai da ta tura sannan ta mikawa Leila wayar.

“Duba ki ga amsar da na bashi, ta nan zamu fara wana shi kuma mu gane irin son da yake miki”

Leila ta tabe baki.

“Ni yanzu ma ban sani ba, ina sonsa ko tsanarsa nake, bayan duk abubuwan da yake min, yanzu wannan abun da yai ya saka na fara jin tsanarsa a raina”

Madina ta yi saurin kallonta tana tukin motar.

“Da gaske? Wai kin bincika inda ya aje yarinyar nan kuwa?”

“Yace be san inda ya kaita ba, ki kai ni gurin Momy can zan kwana”

“Okay”

Daga haka bata sake cewa komai ba, sai dai a zuciyarta murmushin jindadi take, domin Leila ce kawai zata zame mata matsala a tarayyarta da Talba, idan kuma har Leila ta juyawa Talba baya burinta zai samu ciki, a tunaninta Talba zai iya neman maye gurbin Leila da ita ko dan ya batawa Leila rai, a iya tunaninta Aminatu ba matsala bace a gurinta, domin ta san waye Talba kuma ya dade tana karantar rayuwarsa fiye da Leila da suka taso a gida daya.



FARUQ POV.

Yana tsaye a tsakar gidan rike da yar karamar traveling bag, yana sanye da kananan kaya kansa a kasa yana furta

“Ameen”

Idonsa yar rine yayi ja sosai kamar wanda ya wuni ya kwana yana kuka.

“Allah ya baka abun da ka je nema Faruk, Allah ya shige maka gaba”

Mama ta fada tana fashewa da kuka, ji take kamar idan Faruq ya tafi gurin ginar zinari nan ba zai dawo ba, shi kansa yana jin wani yanayi na rashin jindadi wata kila saboda be saba tafiya mai hadari da nisa kamar wannan ba ne. Dukawa yai ya kama hannun dansa yana kallon fuskarsa sai ya ji kamar kar ya tafi ya bar Sultan.

“Dady yaushe zaka dawo?”

“Ba zan dade ba, kuma zan kira a waya na gaisa da kai ka ji”

“Momy fa yaushe zata dawo?”

Faruk yai shiru kamar mai tunanin abun da zai fada masa, ya san shi kansa dauriya kawai yake balle kuma Sultan da yake karami, an raba shi da uwarsa yanzu kuma zai tafi ya bar shi hannun Mama.

“Ita ma zata kira ka a waya ku gaisa, kuma idan zan dawo zan dawo tare da ita”

Sai kawai ya fashe da kuka, daman tun da ya bude ido ya ga Dadynsa na shirin tafiya yake ta son yin kukan, Faruk ya kama shi ya rumgume zuciyarsa tana sosuwa da kukan dansa.

“Dady zan bika, ka tafi da ni”

“Ba a zuwa da yara, amman kai ta ma Dady Addu'a, idan ya samu kudi zan siya maka komai kake so kuma zai dawo lafiya”

A take Sultan ya kara fashewa da kuka, sai Aisha ta zo ta kama hannunsa ta dauke shi ita ma hawayen ne kwance a idonta.

“Kyale Dady zamu je mu siyo minti mu sha ba zamu je da shi ba ka ji?”

“Dady zan bika zan bika Dady zan bika”

Shi ne abun da Sultan yake ta maimaitawa har Aisha ta fice da shi. Sannan Faruk ya mike tsaye yana duba agogon hannunsa, hudu da yan mintuna gashi kuma abokin tafiyarsa ya fada masa da biyar za su kama hanya. Karasawa yai gaban mahaifiyarsa ya risina gabanta yana rokon gafararta.

“Mama dan Allah ki yafe min duk abun da na yi miki na bacin rai wanda na sani da wanda ban sani ba, kuma yi min addu'a, Inshallahu da zarar na isa zan kira ku, ga Sultan nn na bari a hannunki kuma a karkashin kulawarki, ko da Allah be kaddara min dawowa ba, Mama dan Allah karki bari Rafi'a ta dauke shi, kara yai ta zama a nan tare da ku da talauchi da ya koma karkashin kulawarta, ban zan iya abun da zata aikata nan gaba ba, kuma zan rika yi miki aike ke da ita saboda cikin dake jikinta Inshallahu”

Ya karasa hawaye ya sauko masa, sannan ya mike tsaye Mama ta bishi da kallo tana hawaye kamar wanda aka cewa idan ya tafi mutuwa zai yi ba zai dawo ba, har ya fara tafiya bata ce masa komai ba sai da saka kafarsa daya a waje zai fita.

“Allah ya maka albarka Faruk, Alhamdulillah ko Allah be ba ni arziki ba ya ba ni ɗa mai tarbiya, ni da kai ba a san gawar fari ba”

Juyowa yai ya kalleta ita ma ta kalleshi sannan ya juya ya fice ba tare da yace mata komai ba.
30

Ko kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


BATURIYA POV.

“Amman kina ganin idan n zubar da cikin ba wata matsala?”

“Wane irin matsala? Yau aka saba zubar da ciki ne ki rika yi ma kanki fata na gari mana”

“Tsorona nake ji Wallahi kin san abun da baka saba ba”

“Ba wata matsala kawai shawarar da zan baki karki yarda ki zubar da cikin yanzu, sai kin yi tafiyar nan da Alhaji kin dawo”

“Ni fa bana son zuwa ko'ina Ramlee, iya abun da zamu a nan ya ishemu, ba sai mun tsallaka mun bar kasar ba, ka shiga jirgi kai sama da sunan zaka je aikata sabo?”

Ramlee ta kalleta tana tabe baki.

“Kar dai ki ce min tsoro kike ji? Ashe a gaishe da masu zuwa saudiya su aikata fiye da abun da kike tsoron aikatawa, ke matan da suka kware suka waye har lesbians suke fa da matan manya wasu kuma ta baya ake yi da su”

Baturiya ta kwalo ido tana kallon Ramlee da mugun mamaki.

“Yanzu Ramlee mutun zai taka jirgi ya tafi maka ka aikata sabo? Wannan kuma ai ya zama ganganci da isgilanci”

“Babu ko daya Allah shi gafurun raheemun ne, ki rika kyautata zato mana, idan ka tara dan abun da ka tara kamin lokaci ya kure maka sai ka tuba ai, duk abun da zaki aikata wani yana can zai aikata fiye da abun da kika aikata na zubinu kuma Allah a cikin rahamarsa sai ya yafe masa ya saka shi aljanna, wani kuma zai aikata aikin lada mai yawa kuma daga karshe ya zama dan wuta”

Baturiya ta sauke ajiyar zuciya.

“Toh ai baka da tabbacin wuta zaka je ko aljanna, ni fa ina tsoron kar zunubin yai min yawa, ga kuma wani ina kokarin aikatawa yanzu cikin nan yanzu cikin wata na hudu yake”

“Masu haihuwa su kashe yayan fa? Balle ke da be ma zo duniya ba? Gaskiya Baturiya kina da matsala ana nuna miki hanyar arziki kina sanyi jiki, ni dai yanzu fada min yaushe za ki samu fita sai na fadawa dan gidanki ya shirya?”

“Fitar ce tawa yanzu zata zama aiki, idan ma cika fita za a fara saka min ido”

“Shiyasa ni ban jidadin da kika kashe aurenki a yanzu ba Wallahi saboda Faruq be da matsala kina fita duk inda kike so weather ya barki ko akasin haka, su kuwa wadannan iyayene abu kadan sai ka fara jin tsinuwa da baki kala kala”

“Wallahi kuwa, kuma kin ga za ayi saurin gane ni ce ba ni da gaskiya, domin ya ki fadawa Yaya abun da ya hada mu, sai cewa yai wai ko minene za su gani, shiyasa kudin ma na kasa kashewa, ina gudun na taba kudi Umma ta fara zargina”

“Baki da wayo ne, ai wata hanyar zaki bijiro da ita ta samu kudi, kamar sana'a ko kuma ki nemi wani aikin ma wanda zai rika baki damar fita ki ga daga nan sai ki samu kafa kina yin yadda kike so hankali kwance”

“Kuma fa da maganar ki, amman wace irin sana'a ce mai kawo kudi haka? Ni fa bana son zargi ko kadan”

“Wannan kuma sai kin yi tunani, ko kuma mu samu hanyar yin aiki zai fi mana sauki ma”

“Ssce ce da ni fa aiki zai samu da ssce? Na ga Faruq ma mai degree yana fama balle ni”

“Ai ke da Faruq akwai banbanci, ke fa mace ce kuma a cikin matan ma mai kyau da daukar hankali, shi kansa da zai bada kasansa ga irin mazan nan da suke neman maza Wallahi na aiki ba har abun da yafi aiki idan yana so sai ya samu, yanzu fa duniyar ta zama yi min na yi maka ne, ba ni girishi na baka manda”

“Ramlee kina da wayo Wallahi, ni kam sam irin wannan tunanin baya zuwa min”

“Ba ki waye ba ne a abun, idan kika gwane ni kaina sai kin fara min wani gani-gani”

“Uhm... Yanzu ki fadawa dan gidanki sai karshen satin nan za mu hadu”


“Ni fa ce min yai ki saka masa ranar da zai rika ganinki, Wallahi Fee'at kina da farinjini da sa'a, kin ga manyan mutanen nan su suke sakawa mutum lokacin da za a gansu amman ke ya yarda ki saka masa ranar da zai rika ganinki”

“Uhmmm yanzu ne zan tabbatar idan ina da sa'a ko akasin haka, sai idan na auri Fahat zan tabbatar da haka, duk kuwa da na san akwai kalubale mai yawa a gaba”

“Kina ji zai aure ki da da? Kuma anya ya san kin taba yin aure kuwa?”

“Be sani ba, kallon budurwa yake min, amman very soon zan fada masa na taba yin auren, sai dai ba zan nuna masa ina da da ba, kuma zan nuna masa cewar auren dole akai min, shi ma kuma saboda na ji yana cewa za ayi bincike gudun kar a binciko a gano wani abu”

“Kina son Fahat din nan sosai Fee'at”

“Uhmm ya hada komai ne da mace take so, kyau kudi, dan mayan mutane ga shi yana so na, jiya har tambayata yake wani kalar gida nake so yanayinsa da yadda zai kasance saboda yana son a fara gina masa gida irin tsarin da nake so”

Baturiya na rufe baki kiran Fahat na shigowa wayarta, a take murmushi ya wanke fuskarta farincika kuma ya cika ruhinta.

“Dan halak ka ƙi ambaton, kin ga shi ya kira”

Ramlee ta yi murmushi kamar yadda Baturiya ma take murmushin tana kara wayarta a kunne.

“I just call to say hi kin san idan ban kira ba hankalina baya kwanciya, bana gajiya da jin muryarki”

“Yanzu kuwa nake zancenka a raina ina ta waken ganinka”

“Da gaskiya ne ai da kin nemo mana hanyar da zamu rika ganin juna, amman sai rowar fuskarki kike min, muryar ma yanzu ba kullum nake ji ba”

“Wallahi Umman mu ce take yawan fada idan ta ga ina waya, shiyasa sai na fakaici idonta nake kiranka ko na amss kiranka, yanzu haka ma ina tare da wata kawata”

“Kin samu fitowa kenan? Amman shi ne baki kirani na zo mun gaisa ba? Ko shi ma Umma ta hana? Domin na lura Umma har yanzu bata san yarta ta girma ba”

Ta yi dariya cike da nishadi.

“Ai ba zata yarda na girma ba sai ranar da ka sace mata ni”

“Ai na dade da sace ki, dauka ce kawai ban yi ba ita ma very soon zan mai da kulawarki karkashina”

Kusan a tare suka saki murmushi ita da shi, kamin ya dora mata da.

“Yanzu kina ina? Ina son na biyo mu gaisa i miss your face and your smile”

“Ina nan bayan government house gidan wata kanwar Babana”

“Okay yanzu zan karbo wani sako a tasha idan na fito zan same ki a can sai mu gaisa, ki min kwaliya mai kyau kamin na zo”

“An gama Dear”

“I love you”

“I love you too”

Ya sauke wayar yana murmushi, a can kasan zuciyarsa yai ma Baturiya muhallin, son ta yake so bana wasa ba, shi kansa yana mamakin yadda ya zurfafa a sonta. Tuki yake da hannu daya, dayan hannunsa kuma wayarsa ce a rike ya saka ajewa, daya daga cikin hotunan data turo masa ne ya saka a wallpaper dinsa idan ya kalli hoton har wani sanyi yake ji a ransa, fuskarsa dauke da murmushi zuciyarsa wasai yau zai gana da masoyiyarsa bayan tsawon lokacin daya dauka be hadu da ita face to face ba.
Sabuwar ta sha ya nufa kamin ya isa ya kira direban ya sanar masa gashi ya kusa karasowa a ina zai karbi sakon.

“Kace gurin Iliyasu Mai gadi ka karba sai ka bashi kudin”

“Okay”

Sai a lokacin ya samu aje wayar ya faka motar gefen titi domin baya son shiga da motar cikin tashar, ya fito ya nufi gate din. Kamin ya shiga ya tambayi wani mai talkami dake kusa da gate din ya nuna masa teburin da Iliyan yake zama, sai yai masa godiya ya nufi gurin da Iliyan yake zaune kamin ya karasa shi da Faruq suka rika kallon juna, yana ta kokarin tuna inda ya taba ganin fuskar Faruq, Faruq kam yana ganinsa ya gane shi, hakan ya saka ya mika masa hannu suka gaisa.

“Kamar na sanka”

Cewar Fahat sai Faruq ya mike tsaye yana murmushi.

“Ni ai ina ganinka na gane ka, ka san ku manya ne ba ku saurin gane mutane, ni ne wanda ka kai asibiti lokacin da Mahaifinka ya kade ni”

“Anyi haka to ya lafiyar jiki”

“Alhamdulillah, gashi har muna shirin barin kasar”

“To kaga kai ne babban kenan kasa”

Kusan a tare suka yi dariya Faruq ya shafa kansa yana fadin.

“Dole ne ai tun da kasar ta zama sai a hankali idan hagu da kiya ba sai mu koma dama ba”

“Haka ne, Allah ya bada abun da aka je nema, koto zaku je ko togo?”

“Nijar zamu leka mu samu rabonmu”

“Nijar dai? Ba ku tsoron tafiya a mota kasar nan ba lafiya”

“To ya za'ayi, dole ne mu fita daman ba asan maza da zama ba, kamin mu samu abun da muka samu mu dawo tun da aikin ya zama sai wane da wane”

“Ka yi karatu?”

“Na yi karatu Wallahi degree na yi, amman aikin ya zama sai a hankali”

Da mamaki Fahat yake kallonsa domin this is the first time da ya taba ganin mai degree zai tafi nema a inda wasu suka ganin ko ba su yi karatu ba ba za su iya ba.

“Da gaske?”

Faruq yayi murmushi mai sauti. Sai Fahat ya ce.

“Na yi mamaki Wallahi ba kasafai masu irin kwalinka suke yarda su yi aikin da zaka je yi ba, indai da har kwalinka yayi kyau ka turo min cv na maka alkawarin aiki inshallahu”

“Da gaske? Allah yasa domin na raba cv gurare da yawa amman shiru ne har yanzu Wallahi”

“Karka damu wani rabon nesa yake, me kake yi yanzu?”

“Ina jiran abokan tafiyata ne”

“Okay bari na karbi sako, sai mu je motana na baka number na da mail ka turo min cv ka, kuma ka kira ni Inshallahu zan sama maka aiki, ko dan sharar gidanmu ne na san sai ba zaka raina ba”

Faruq yayi dariya sosai.

“Ai ba zaka fara ba, nan gaba kadan ma kai zaka fara goge min talkami”

Fahat ya kyalkyale da dariya.

“Aiko zaka ga keta, Allah ya nuna mana lokacin”

“Ameen ya Allah”

“Bari na karbi sako sai mu na baka ko? Iliyasu nake nema mai gadi”

“Gashi nan”

Faruq ya nuna masa shi, ba dan ya masa wani farin sani ba sai dan yawan kiransa da yaji mutane na yi a daman zaman jiran abokan tafiyarsa da yake a gurin. Fahat ya karasa kusa da shi ya gaisa ya ciro kudinsa ya mika masa sannan ya karbi sakon takardun, suka jero tare da Faruq zuwa gurin motarsa, shi ya fara budewa ya shiga ya zauna ya dauki diary ya rubuta masa addireshinsa na email a kasa kuma ya rubuta masa number wayarsa sannan ya kai hannunsa ya bude front seat.

“Bismillahi ban rike sunanka ba”

“Umar Faruq”

Faruq ya fada yana zama, sai ya mika masa takardar sannan ya bude ma'adanar kudi a motar ya ciro kudin da zai kai 20k ya mikawa Faruq.

“Wannan a kara a sha ruwa, mail dina yana jiki sai ka turo min Inshallahu zan yi ma iya kokari”

Faruq ya rasa da wane baki zai gode masa, ga wani uban mamaki daya cika shi na kyautar 20k a take.

“To ai ni ka daure ni gaba daya, Wallahi ban san me zance maka ba”

“Bana bukatar godiya, kawai kai min addu'a Allah ya cika min burina na auren wata yarinya da nake so”

“Idan aurenta alheri

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login