Showing 75001 words to 78000 words out of 133328 words
ba?”
“Kai ya taba ka kenan?”
“Yeah, duk wani mai imani ne dole ne labarin yarinyar nan ya taba shi”
“Kar tausayinta ya saka ka manta da yadda kake da Leila, tsakani da Allah yarinyar nan tana sonka kuma tana azabtuwa da irin abun da kake mata”
“We can talk later”
Yana fadar haka ya kashe wayar ya jefa saman gado, sannan ya shiga dan karamin dakin da aka tanada domin ajiyar tufafi ya saka riga da wando na suit blue sannan ya fito ya dawo gaban madubi yana duba kansa. Komawa yai ya dauki turare ya murza a hannunsa na fesawa kuma ya fesa a jikinsa. Sannan ya dauki abun da ya kamata ya dauka ya fice daga dakin yana kokari saka wayarsa aljihu.
Ya fito bangarensa ya nufi bangaren Momy sai dai turarensa ya riga shi isa bangaren Momy saboda karfin kamshinsa, yau kam a bude ya samu kofar falon Zulai nata aikin mopping tana ganinsa tai saurin risinawa ta gaishe shi, sai dai be ma kalleta ba balle har ya amsa mata. Motsin da yaji a kitchen ne yasa ya nufi kitchen din, sai dai be karasa ciki ba saboda ya hango Leila a tsaye kusa da Momy da alama yau kamar a tare suke hada abun karyawan.
“Momy ina kwana?”
Momy ta juyo ta kalleshi, sai ta amsa fuska ba yabo ba fallasa.
“Lafiya Kalau an tashi lafiya?”
“Alhamdulillah”
Ya amsa sannan ya juya da zimmar ficewa, sai Momy tai masa tayin abun kadyawan.
“Ba zaka tsaya ka karya ba?”
Kamar zai ce a a sai kuma ya juyo.
“Idan an gama a saka min a kula zan tafi da shi”
“Okay”
Momy ta amsa sannan ta dauki abu ta shiga zuba masa dukan abubuwan da suka hada, yana ganin haka ya fice daga kitchen din, ko da ya fito Zulai ta gama mopping din sai ta bude masa kofa da sauri, ya fice yana addu'ar fita daga gida, sannan ya nufi inda Motarsa take fake, tun kamin ya karasa ya danna remote din hannunsa motar tai kara ta bude kanta daga lock. Hannunsa ya mika ya bude motar ya shiga ya zauna yana warming dinta, yana kokarin yin reverse da Motar, Mairo da fito da gudunta rike da kwadon abinci ta nufo inda yake, after yayi reverse din ta bude gidan baya ta saka masa sannan ta rufe motar tana masa addu'ar Allah ya tsare.
Kamin ya isa gate ya daga wayarsa ya kira Daddy, domin ba al'adarsa ba ce ficewa ba tare da ya gaisa da Daddy ba, sai idan Daddy na bachi ko kuma baya garin, ko kuma wani ne, shi kadai ne ke saka shi fita ba tare da yayi ido biyu da Daddy ba. Har ya hau babban titi Daddy be dauki wayar ba, as usual idan ya kira sau daya ba a dauka ba zai sake kira ba.
Sai kawai ya aje wayar ya cigaba da tukinsa, a gogon hannunsa ya duba a daidai lokacin daya faka motarsa harabar asibitin, sannan ya bude motar ya fito ya bude baya ya dauki abinci ya nufi ciki, akwai jama'a sosai a asibitin ba kamar jiya da shekaran jiya ba da suke ranakun hutu, yau kam Monday mutane sai hada hada suke, kamar bako haka ya tura kofar dakin ya shiga. Zaune ya same ta tana ta kallon kofar kamar mai jiran shigowar wani, hawaye suna mata zuba, sai da ya maida kofar ya rufe sannan ya karasa kusa da ita ya aje abinci.
“Ya jikinki?”
Sai ta juyo ta kalleshi, ta kasa amsawa.
“Ya sunanki?”
Ya tambaya yana cigaba da kallonta.
Nan ma bata ce komai ba, sai ya matsa kusa da inda aka aje file dinta ya bude yana dubawa Ramlat Ibrahim ya ga an rubuta.
“Ramlat...?”
“Aminatu...”
Ta amsa tana kallon wani wajen tare da kai hannu ta share hawayenta.
“Mamana, ba ki gajiya da kuka?”
Sai ta sake kallonsa a karo na biyu tana murmushin da ya fi kuka ciwo.
“Baka san yadda nake ji ba, yanzu ba ni da mai damuwa da ni, babu wanda ya rasa kamar yadda na rasa komai a lokaci daya, yanzu bara zan koma a titi, ina zan kwana? Me zan ci ko na ci babu ruwan kowa, ni kadai na rage.... ”
Kamar fada take maganar tana kuka mai karfi, sai kuma ta saka hannayenta ta rike kanta tana lumshe ido. Kallonta kawai Talba yake har ta fara yunkura sauka saman gadon.
“Zauna karki sauka”
Dagowa tai ta kalleshi, sai ta zauna din kamar yadda ya bukata ta rumgume kanta tana hadiyar yawun bakinta da ya bushe. Dukawa yai ya fara bude abincin yana dorawa a saman gadon da take sannan ya duba fruits din daya kawo mata jiya, domin tun jiya da ya kawo mata fruit din ya fita be sake dawowa ba.
“Baki ci komai ba?”
Ya tambaya yana kallonta. Sai ta daga masa kai.
“Ina jin yunwa amman bana iya cin komai, kuma hannuna baya kaiwa”
Be sake ce mata Uffan ba, ya bude mata abinci.
“Zaki iya cin wannan?”
Ta kalli abinci sai ta girgiza masa kai, alamar aa domin komai na duniyar baya burgerta. Zai sake yin magana likitan daya karbeta ya shigo dakin rike da takardu da wata Nurse a bayansa.
“Yauwa, daman ina son magana da kai”
Likitan ya fada sannan ya mika masa hannu suka gaisa. Sai kuma ya shiga duba Aminatu.
“Kina jin wani ciwo ne?”
“Kirjina yana ciwo sosai ksmar zai cire, kuma idanuwana ma suna ciwo suna kai kayi”
“Ki daure ki rage tunani, da yawan kuka damuwace ke saka haka, ita kuma damuwa bata da magani kamar a gusar da abun da yake rai”
Ya fada yana rika hannunta ya saka mata abun hauna bp ya aunata, bayan ya gama ya kalli Talba dake tsaye ya ce
“Tsakani da Allah yarinyar nan na bukatar kulawa, akwai maganin daya kamata ace ana shafa mata a kafa kuma ana bata lokaci zuwa lokaci, and tana yawan kuka wanda hakan yana kara mata damuwa, kamata yayi ace akwai wani abu da zai dauke mata hankali, ka ga ko shiga bandaki ya kamata ace akwai mai rikata domin jiya ma a nan tai fisari sai da aka gyara gurin, sannan tana zaman kadaici ne kawai babu kowa a tare da ita a nan”
Talba ya kalleta cike da tausayi, shi kansa ya san tana bukatar mai kula da ita, domin tufafin jikinta ma sun yi datti duk da kasancewar Ali ya saka an canja mata wasu tufafin tun a lokacin da take asibitinsa.
“And jiya ma ance bata yi bachi ba sai magana take ta yi da kanta tana kuka, be kama ace kullum sai an mata allurar bachi sannan zata iya bachi ba, domin ita kanta allurar yawan yinta yana haifar da wata cutar ta dabam”
“Ba ni da wanda zai kula da ita a yanzu gaskiya”
“Ko da a gida?”
Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai fada.
Aminatu ta kalleshi da idanuwanta da suka sha kuka har suka canja kala.
“A yanzu ba mu da gida, idan kun gaji da ni, to ku kai ni gurin da yan gudun hijira suke zama, ko kuma gidan marayu ko gidan nakasassu, ba ni da kowa...”
Talba ya risina kusa da gadonta yana kallonta cike da tausayi.
“Ba nasasa kika yi ba, ciwo kika ji, kuma zaki warke soon ko Likita?”
Sai likitan ya daga mata kai yana murmushi.
“Bata da kowa ne?”
“I can take care of her zan kai ta gida...”
Talba ya fada, sannan ya mike tsaye.
“Okay, idan zaka kaita gida, za ta fi samun kulawa gaskiya, domin a yanzu damuwarci kawai ciwonta sai kuma kafafuwan. Amman a shawarce zai fi kyau ka samu likitan da zai rika zuwa yana dubata, ko kuma ka rika kawota time to time asibiti ana duba kafar”
Talba ya daga masa kai alamar gamsuwa, Likitan ya kai hannunsa ya rika kan Aminatu ya bude idonta.
[3/7, 11:34 AM] Zatuuu🦋: “Ki daina yawan kuka kina daga idonki sama saboda kar glass din idonki ya samu matsala”
Ita dai bata sake ce masa komai ba har yai abun da zai yi ya fice. Sai da ya fice sannan Talba ya zauna a saman kujerar dake facing din gadon yana kallonta.
“Ki zama mai jajircewa da hakuri, komai da kika gani na rayuwar duniya baya zuwa da sauki, kuma kowa da kalar jarabawarsa, and ina tunanin Allah ya hada ni da ke saboda na taimakeki, wata kila da dace da wani kika hadu shi ba ni ba, da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, so ki dauki haduwa ta dake a matsayin kaddara, akwai wani karon magana da ake cewar when life gave you hundreds reasons to cry, show life you have thousand reasons to smile, ina da tabbacin zaki zama jaruma, ki hade komai ki rayu ko dan iyayenki”
“Kuka ya zame min dole baka san yadda nake ji ba, rashin iyaye yan'uwa abu ne mai matukar ciwo, lokaci daya na rasa komai”
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta, hawaye nata wanke mata fuska kamar ba gobe.
“Na san yadda kike ji, ni ma maraya ne kamar ke ba uwa ba uba, banbancina da ke shine, ni ban taba kukan maraici ba, ban taba neman wani abu na rasa ba, ke ma kuma za ki samu kulawa Daga yanzu har karshen rayuwarki, kamin ki gane danginki, zan sama miki wasu dangin da zaki zauna tare da su, su rika debe miki kewa, na san ba za a rasa wani daga familynki da yake raye ba, From now on babu abun da zaki nema ki rasa Inshallah, babu abun da ya dace da ke a yanzu sai farinciki!”
Ta yi kasa da kanta tana hawaye.
“Da gaske na rasa kowa kenan! Da gaske ni kadai zan rayu? Taya farinciki zai zama a tare da ruhin da bakinciki ya zagaye, kuka da damuwa suka masa masauki? Har yanzu na kasa yarda a duniya na ke, an raba ni da kowa”
Ta fashe da sabon kuka tana jin wani irin bakinciki mai taba zuciya yana ratsata.
“Faranta ran mutane na daga cikin abun da yake saka ni farinciki, musamman irinki, ta ya mutum mai imani zai same ki a irin wannan halin kuma ya kasa taimakonki? Ki saka a ranki daman can haka Allah ya rubuta kuma akwai irinki da yawa”
Haka ya dage yana ta kokarin kwantar mata da hankali kamar na shi ba. So yake ta ji cewar ba ita kadai bace a cikin halin damuwa, so that ta kwantar da hankalinta, gudun kar abun yai mata yawa.
“Ki ci abinci yanzu sai na yi ma likitan magana, ya ba ku takardar sallama”
Wannan karon har dan guntun murmushi a fuskarsa.
“Bakina akwai datti da yawa”
Ya dan wara ido yana jin haka yasa mai tsabta ce.
“Okay bari muje gida gaba daya sai ki wanke bakinki a can ki karya”
Ta yi shiru bata ce masa komai ba, sai ya rufe abinci ya mike tsaye ya fice daga dakin. Be dade ba ya dawo rike da wata takardar sai wasu nurse biyu bayansa, su suka dauke ta suka saka ta a Wheelchair. Shi kuma ya dauki abincin kadai ba tare da ledar fruit din daya kawo ba sai kuma magani. Nurse din ce ta turo ta, shi kuma yana gaba har suka isa gurin motarsa, back seat ya bude musu suka saka ta sannan ya bude bayan motar suka saka masa wheelchair din, after ya rufe ya nufi driver seat ya bude ya shiga ya zauna.
“Yanzu zaki ga sabon gidanku da kuma yan'uwanki”
Ya fada ba tare da ya juyo ya kalleta.
“Na gode Yallabai”
Ta fada da muryar kuka, domin a yanzu ko kalma yan'uwa ta ji sai ta tuna da nata.
“Talba sunana, daga yanzu ni yayanki ne, kin zama kanwata gashi kina da sunan Momy kin zama Shalele”
Bata ce komai ba, har ya fara tukin motar ya fice daga asibitin, yana hawa babban titi ya fara gudu kamar yadda ya saba, sai jikinta ya fara rawa ta fara tsorata, abun da ya faru ya taba mata zuciya kuma ya shiga kwakwalwarta ya zauna, abu kadan sai hankalinta ya tashi.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Ta furta da karfi tana runtse idonta. Hakan yasa shi juyowa ya kalleta sai ya rage gudun da yake, sai dai be ce mata komai ba, ita kuma bata yarda ta bude idon ba har suka isa gidan da bata san yadda yanayinsa da tsarinsa ba. Harabar gidan ya faka ya motarsa sannan ya fito ya dauko Wheelchair ya aje ya bude back seat din yai ma daya daga cikin mai aikinsu hannu, sai gashi ya zo da gudunsa.
“Ka dora Wheelchair din nan a kofar falo, sai ka saka yarinyar nan ciki, ka dauko abinci yana ciki Motar”
Ya fada yana kallon motar Daddy dake fake, hakan ke tabbatar da Daddy be fita ba kenan. Wayarsa ya ciro daga aljihu da zimmar kiransa sai ya hangoshi ya fito direbansa na rike da jakarsa, da sauri ya nufi inda yake Daddy na hango shi sai ya tsaya jikin motar yana jiran karasowarsa.
“Daddy good morning”
“Morning Mu'az har na fita?”
“Yeah muna da meeting a office, amman ka rasawa na dawo na fada maka wani abu”
Daddy ya masa irin kallon nan dake nuna ina saurarenka. Tun daga biri har wutsiya ya fedewa Daddy komai, ba karamin tausayin yarinyar Daddy ya ji ba.
“Yarinyar tana ina?”
“Gata acan na zo da ita, ina neman amincewarka, idan kuma hakan be maka ba, zamu iya duba wani gurin sa zamu iya ajeta, saboda gida marayunmu yawanci kanana ne ba su kai kamar ta ba, idan ma na aje ta a can zata sake shiga kadaicin ne”
Daddy yayi murmushi jindadi ya kai hannunsa ya dafa kafadar Talba.
“Ina alfaharin da kai Mu'az ka ci sunana kuma baka rago komai daga halina ba, mu gidan nan ai kullum muna marhabun da baki ne, kuma ni uban marayu ne karka manta da wannan, ko da ace tana da kowa nata a raye ta so zama da mu zan dauke ta kamar ya balle ma tana marainiya, ka yi tunani mai kyau ka ga yanzu kun zama ku biyar, Allah ya muku albarka”
Talba yayi murmushi.
“Thank you Daddy, amman Momy ba lallai ta yarda ba”
Daddy yai masa wani kallo.
“Momy ke da gida ko ni?”
“For now ita ke da gidanta...”
“Really to bari mu ga idan kai aure kai ne da gida ko matarka”
Talba yayi murmushi.
“Wannanai dabam, ni Talba ne kai kuma Daddy ne”
Daddy ya girgiza kai yana murmushi tare da zolayarsa.
“Za'a min izinin ganin yarinyar?”
Ban da dariya babu abun da Talba yake, ya wuce gaba Daddy ya biyo bayansa, sai dai hakan be hana su isa kofar falon a tare ba.
[3/7, 11:34 AM] Zatuuu🦋: Talba ya danna door bell ba dadewa aka bude masa sai ya matsa Daddy ya fara wuce sannan shi ma ya shiga. A tsakiyar falon ya hango Aminatu zaune a wheelchair ta sanda kanta kasa hawaye na sauko mata, Kabir na tsaye gabanta. Momy kuma na zaune a kujera daya ita da Leila suna kallon ikon Allah.
“Ita wannan bata magana ne?”
Kabir ya tambaya yana kallon Talba.
“Ka dame ta da surutun ne ko?”
Cewar Daddy. Sai Kabir ya ce.
“Sunanta kawai na tambaya, sai ta rufe ido ta fara min kuka”
Daddy ya karasa kusa da ita yana kallonta cike da tausayawa.
“Sannu Allah ya baki lafiya”
Bata bude idon ba har sai da ta ji kamshin turaren Talba, sannan ta bude ido ta kalli inda take jin kamshin na fitowa, ido biyu suka yi sai dai nata idon cike suke da hawaye.
“Ya sunanta?”
“Sunan Momy”
Talba ya fada, sai Daddy yai murmushi ya kalleta.
“Yar gata ce kenan, sunan matata kuma uwar yayana kin ga babu wanda zai taba ki a gidan nan! Ki kwantar da hankalinki ki dauki kowa kamar dan'uwanki ni kuma na miki alkawarin zama mahaifinki da yarda Allah, duk abun da zan iya yi ma yayana zan miki Inshallah”
Talba yayi murmushi, sai Kabir ya wara ido.
“Ji wannan daga zuwanki zaki karbe mana fada, bari fitinanniyar ta zo zata zalzaleki”
Daddy ya girgiza kai yana dariya.
“Aa yanzu ita ce auta, daga gani Amal zata girme ta ai”
Ya fada sannan ya dago ya kalli Momy.
“Hajiya karaso ki ga yar da muka samu kyauta daga Allah”
Momy ta taso daga inda take zaune tare da Leila suka karaso inda Aminatu, sai da Momy ta kare mata kallo sannan ta ce.
“Ya kamata a nemi izini na kamin a kawo ta, amman sai ganin musaka nai a falona, saboda ban isa da gidan ba”
“Na fara magana da Daddy ne, kamin na yi magana da ke, ni ma ban yi zaton hakan zai faru ba sai da likitan ya fada min sai na ga kamar hakan ya dace”
“To be dace ba, be kamata ka dauko min wata bare can ka kawo min a gida ba, yarinyar da ban san daga inda ta fito ba”
A hankali Aminatu ta dago ta kalleta sai ta maida kanta kasa.
“Momy karki tsorata mana, ba nan ya kamata ku yi wannan maganar ba”
Kabir ya fada. Sai Momy ta watsa masa harara.
“Idan na tsoratata sai ka saka zane ka goya ta ai”
Daddy ya hade rai yana kallon Momy cikin rashin jindadi.
“Bana son maganar nan, Danki zai fada miki komai”
Sannan ya kalli Aminatu dake hawaye.
“Aminatu ki kwantar da hankalinki kin ji, mu iyayenki ne”
Ta kasa dagowa ta kalleshi ma balle ta ce masa komai, har sai da Talba ya kirata da sunan da Inna take kiranta da shi.
“Auta...”
Sai ta kalleshi da sauri tana jin wani tsam a jikinta.
“Ki cewa Daddy kin gode”
Ya fada yana mata murmushi kadan kamar na dole. Sai ta kalli Daddy da idanuwanta da ke zubar da hawaye.
“Na gode...!”
“Oh Really.. Zai ka mata umarni zata yi magana kenan”
Kabir ya fada yana kallon Talba, murmushi kawai Daddy yai ya nufi kofar fita.
“Zan tafi kar na yi latti, sai a gyara mana daya daga cikin dakunan da suke kasa nan”
“Da a BQ na so ta zauna”
Talba ya fada.
“Why BQ ga dakuna a cikin gida? A bar ta nan BQ ai na amsu aiki ne, sai na dawo”
A karon farko Momy ta kasa ce masa Allah ya tsare balle har tai masa rakiya. Bayan Daddy ya fice Talba ya risina gabanta ya nuna mata Leila.
“Sunan wannan Leila