Showing 57001 words to 60000 words out of 133328 words

Chapter 20 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

470

Middle Ads

tana kallon mai aikinta Mairo, sai Mairo ta amsa a ladance.

“Toh Hajiya”

Ta wuce gab Shamsu ya bi bayanta, Momy ta gyara tsayuwarta tana kallon Talba.

“Bangaren Mahaifinku zaku yi lunch”

Ya gyada mata kai yana bin Shamsu da kallo.

“Zulai ta kai komai a can Engineer kai kawai yake jira”

Ta fada tana juya wayarta a hannunta, yanayin yadda tai maganar yana nuna masa son take ya bar mata falon. Ya san ba zai iya nufar falon ta ce akai Shamsu ba, idan ma yaje ba zata bari yai magana da shi ba, idan kuma ya ce zai musa mata zata yi korafi.
Juyawa yai ya fice daga falon gaba daya zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala, a entrance ya tsaya yana kallon harabar gidan, sai kuma ya nufi gate din ya fice daga gidan gaba daya.
Yana fita falon Momy ta rufe kofar da kanta tana sauke ajiyar zuciya. Lumshe ido tai ta bude tana kai hannu ta dafa kirjinta dake mugun bugawa da karfi, sannan ta bar jikin kofar ta nufi karamin falon inda Shamsu yake zaune, yana ganinta sai ya sauka daga kan kujerar ya zauna a kasa abun ka da mutunen kauye akaai girmama mutane.

“Shamsu ya gida ya kowa?”

Ta tambaya bayan ta zauna.

“Lafiya kalau Hajiya”

“Maa Shaa Allah, fatar su Baaba ma suna lafiya?”

“Eh... Ai ita aka ce na zo na duba, kwana biyu an ta kiran wayarta baya shiga”

“Ah ah Subhanallahi, Baaba ai yau kwananta tara ko takwas da tafiya gida”

Shamsu ya kalleta da sauri.

“Gida Hajiya? Wallahi bata je gida ba”

“Subhanallahi Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, lallai tabbas ni ma nayi ta kiran wayarta bayan tafiyarta ban samu ba, amman ban saka ran komai ba saboda na san kauye wani lokacin akwai matsalar network ko nepa, kaga ai shiyasa binciken yake da dadi Allah yasa ba mugun hannu ta fada ba, amman ka bincika aka ce bata je ba?”

“Wallahi bata je ba, ai idan tana can dole zan sani saboda a gidan nake, kuma bata fada miki dalilinta na zuwa ba”

“Eh to gaskiya bata fada min ba, na san dai kamin ta tafi tana dan jin jiki, domin da kaina ma na dauke ta muka je asibiti aka ce zazzabi ne da hawan jini, bayan mun dawo da kwana biyu tace min tana son taje kauye ta ga kowa hankalinta ya koma can a yanzu, ta inda nai kuskure ban tambaye ta me take tunani ba, domin hawan jini baya tasowa haka siddan sai da damuwa ko bakinciki har ma nake cewa ba zata kira ta fada a kauye ba tace bata son ta tashi hankalinsu”

Wani kalar tashin hankali ne ya cika Shamsu, jin cewar Baaba bata gidan ga wayarta ma idan an kira ba a samu, Momy kuma ta fada masa cewar yau kwananta tara da tafiya. A gabansa Momy ta nemo number Baaba ta kira ta saka wayar a speaker, daga ita har Shamsu suka ji cewar wayar a kashe take. Shamsu ya mike tsaye

“Wallahi haka nima suke ce min idan na kira, su ma can haka suka ce wayar a kashe take, amman yanzu zan kira na fada musu halin da ake ciki”

“Gaskiya kam kara a dage da addu'a kuma a saka cigiya, ni ma Inshallah zan bada sanarwa gidan radio ko Allah zai saka a dace”

“Zan tafi Hajiya”

“To Shamsu bari na baka number na duk yadda kake ciki sai ka kirani”

Ta fada tana karanto masa number ya saka sannan ita ma ta mike tsaye.

“Bari na kawo maka wani abu ka hau mota”

Tsaye a falon cikin tashin hankalin kamin Momy ta kawo masa 5k din har ya matsu domin hankalinsa gaba daya ya koma gurin inda yake tunanin Baaba zata iya zuwa. Ya karbi dubu biyar din data bashi yana godiya ya fice da saurinsa kana ganinsa kasan bayan cikin natsuwa. Har bakin kofar babban falon Momy ta raka shi tana ta masa addu'ar Allah yasa a gane ta ya amsa da Ameen sannan ya fice ta maida kofar ta rufe. Sannan ta hau sama da sauri ta nufi dakin Leila, Momy na turo kofar Leila ta zabura ta mike tsaye da sauri tana hawaye jikinta har rawa yake.

“Miye haka? So kike idan ya gani ya fara zargin wani abu”

Leila ta kama hannayen Momy ta rike tana kuka.

“Momy tsoro nake ji”

“Ki daina jin tsoro, babu abun da zai faru, idan kina nuna irin wannan hallayar sai ki tonawa kanki asiri, amman idan kika cire komai a ranki sai ki samu kwanciyar hankali”

“Momy har yanzu ina mafarkinta Wallahi, kuma ina jin kamar asirina zai tonu”

“Idan ma asirin ki ya tonu sai mu zuba miki ido akaiki gidan yare? Ko ayi miki wani hukunci? Noooo babu abun da zai same ki, je ki kwanke fuskarki ki shafa hoda ki same ni a bangaren Daddynku”

Ta gyada kai wasu hawayen na sauko mata.

“Momy akwai CCTV a gidan nan, Talba zai iya bincikawa, kuma idan ya gane zai iya cewa ba zai aure ni ba”

“No kul bakinki ya daina furta wadannan kalaman, Talba ba shi da mata sai ke, ki kwantarta hankalinki zan saka a cire CCTV cameras din, je ki wanke fuskarki”

Ta saki hannayen Momy ta nufi bathroom dinta Momy kuma ta fice daga dakin, tana saukowa ta nufi kofar da zata sadata da part din Daddy.

Kamar zai tashi sama haka Shamsu ya nufi gate yana ciro karamar wayarsa ya ciro karamar wayarsa domin kiran yan'uwansa ya sanar musu halin da ake ciki, police din dake gadin gate din ya bude masa ya fita hankali a tashe. Talba dake tsaye wajen gate din ya kalleshi yana karantar irin tashin hankalin da yake ciki.

“Ka fito”

“Eh ranka ya dade, zan je can gida na fada musu halin da ake ciki”

Talba ya masa kamar ya san abun da yake magana akai.

“Oh ba su sani ba”

“Eh Wallahi shiyasa suka ce na zo na bincika ai, ita ma Hajiya tace tana ta kiran wayar sai ta jita a kashe, Allah yasa dai ba mugun hannu ta fada ba”

“Ameen”

“Yanzu zanje can na fada musu, Hajiya ma tace yau kwananta tara da tace mata zata je ganin gida, ka ga ita bata san bata isa ba, mu kuma ba su san da zuwanta ba”

“Haka ne, Allah ya bayyanata”

Shine abun da Talba ya fada zuciyarsa na bugawa kamar zata fasa kirjinsa ta fito saboda bacin rai, zuciyarsa na ta dawo masa da abun da Ali ya fada masa akan halin da aka samu Aminatu.
Bayan Shamsu ya amsa da Ameen Talba ya kwankwasa karamar kofar gate din suka bude masa, ya doshi cikin gidan, Momy na shiga bangaren Daddy Talba ya danna door bell din, Mairo ta zo da gudunta ta bude masa, kana ganin yanayinsa kasan ransa a bace yake, kai tsaye ya nufi stairs sai dai kamin ya karasa hawa Leila ta fito fuskarta cike da ruwa ko hodar da Momy ta ce ta shafa bata shafa ba, tana ganin Talba ta hade yawu da karfi ta dauke numfashi na tsawon dakika uku.

“Yanzu zan iya sanin abun da kika yi ma Baaba?”

A karo na biyu ta sake hade yawu da karfi a tana kallonsa kamar wanda bata fahimci abun da yake magana a kai ba. Ya kara matsowa kusa da ita cikin wani irin bacin rai sai ta koma baya da sauri tana kallon kofar da Momy ta fito.

“Lafiya na shiga can ban ganku ba, Daddynku yana jira zamu ci abinci”

“Answer me...!!!”

Talba ya fada a tsawace yana Kallon Leila. Cikin karfin hali tace.

“Ni ban gane abun da kake magana a kai ba”

“Miya faru?”

Momy ta tambaya daga downstairs din da take tsaye. Sai Leila ta amsa mata.

“Tambaya yai wai zan iya sanin abun da ya faru da Baaba”

“What? Me kake kokarin cewa Talba?”

Talba be kula Momy ba ya kara yin sama ya matsa kusa da Leila.

“I hope ba ke kika shakari yarinyar can ba, kike kokarin kasheta, saboda zafin zai zame miki biyu wahalar zata miki yawa...”

Hawaye ne ya fara saukowa Leila.

“Talba wace irin magana ce wannan? Me kake son fada?”

Juyowa yai ya kalli Momy.

“Momy kin san me nake magana a kai, I'm not a fool na fahimci komai, and i do hope Leila bata da hannu a kokarin kashe yarinyar nan...!”

Yana kawai nan ya sauka a fusace ya fice daga falon gaba daya, Momy ta bishi da kallo, Leila kam ban da hawaye babu abun da take.

“Wace yarinya yake magana akai?”

Zubewa Leila tai a gurin ta fashe da kuka.

“Momy....”

Sai kuma ta kasa karasa, Momy ta hau saman da sauri ta rika Leila suka nufi dakinta.

TALBA POV.

bangarensa ya nufa wayarsa makalle a kunnensa yana ta kiran Ali, sai dai har wayar ta gaji da ringing ta katse Ali be daga ba, zaunawa yai saman kujera ya sake kiran wayar, wannan karon ma Ali be daga ba. Hakan yasa ya dauki keys dinsa ya fito ya shiga motarsa ya fito ya ja motar da karfi, suna ganin ya kunna motar suka bude masa gate. Cikin saurin ya fice daga gidan, yana driving zuciyarsa na raya masa Leila zata iya yin yunkurin kashe yarinyar saboda ta tambayi Ali akan ta, wata kila zata iya zargin wani abu ne a tsakaninsu idan ma bata yi da kanta ba zata iya saka wani yai.
Yana isa asibitin ya faka motarsa ya fito ya mufi hanyar da zata sada shi da office din Ali, kamin ya karasa Office din Ali ya fito daga ward din, yayi mamakin ganin Talba sai dai kamin yace komai Talba ya ce.

“Ali ya yarinyar take?”

“Ba dadi, but she's still alive”

Wani deep breath Talba yai sannan ya bude office din suka shiga.

“Ya akai abun ya faru?”

Ali ya rufe kofar yana fadin.

“Nurse Karima dai ta fada min cewar tana shiga dakin ta same ta a sume, robar a zagaye da wuyanta kuma an fisge robar hannunta jini ya zuba, yanzu haka sai da muka saka mata robar jini, daman jinin be isheta ba”

Talba ya zauna saman kujera yana dan tunani kaminnya kalli Ali daya kai hannu ya dauki wayarsa yana dubawa.

“Ali lokacin da Leila take tambayarka akan yarinyar nan ta tambaye inda take?”

“Tace dai wace yarinya ce na fada mata tana asibitin mu”

“Ka fada mata number dakin?”

Alinya dago ya kalleshi.

“No miya faru?”

“Ali Leila can do this yarinyar nan bata da zuciya mai kyau....”

“Noooooooooooooooo”

Ali yayi saurin dakatar da shi yana daga masa hannu, domin maganar ta masa nauyi sosai har sai da ya runtse ido ya bude ya kalleshi.

“Look Talba yanzu na fahimci baka son Leila, and it fine, ka ji baka son mutum normal ne amman kokarin dora mata sheri ba zai amfana maka komai ba”

“Na san dalilin daya saka na fad....”

Talba be kasara Ali ya daka masa tsawa.

“Baka da wani dalili, and karka manta Leila yar'uwarka ce ko da babu alakar kauna a tsakaninku be kamata ka jefe ta da wannan ba”

“Ali ba zaka gane ba ne, Leila can do this”

Talba ya sake maimaitawa with full confidence, abun da ya kara fusata Ali.

“Enough Talba, enough. Leila tana da damar da zata yi kishi, ta nuna bakincikinta ko bacin rai akan ka damu da wata, amman for now ka bar Leila ta ji da damuwarka karka kara mata wata”

Ali ya fada cikin tsawa jijiyar wuyansa har tashi take. Talba ya mike tsaye yana kallon Ali cikin wani irin zafin nama.

“So you're shouting at me...?”

“Yes me ke damunka Talba? Why Leila? What if ita tai kokarin kashe kanta? What if kila ta akan wani abu dabam ake kokarin kasheta?”

Talba ya matsa kusa da shi yana kallon idonsa.

“Don't fool me, haka nan kawai zata yi kokarin kashe kanta saboda bata son kanta? Bayan ta samu ta fito daga daji? And you already told me babu wanda ya taba zuwa ganinta how could someone know tana a nan? Ali Let me tell you this, zan bincike yarinyar nan and if i find out Leila ta aikata abun nan, sai na bata mamaki”

“And before you do this let me show you something, daga yau ba zan sake kula yarinyar nan ba, and i swear sai ta bar asibitin nan yau, ba zan zuba maka ido ka bata alakarka da matar da zaka aura ba kuma yar'uwarka saboda wata bare ba, kuma a dalilina ka san yarinyar nan and now na fahimci halin da Leila take ciki akanka”

Talba yayi murmushi irin murmushin na bacin rai da mamaki a lokaci daya.

“And remember you said yarinyar bata da kowa”

“I don't care, idan ma mutuwa zata yi tai mutu, she's not my responsibility...”

“And for now on she's my responsibility har sai ta dawo hayyacinta ta fada min komai... And believe me with or without you yarinyar nan zata rayu Doctor Aliyu Muhammad Bukar...”

Talba na fadar hakan ya juya ya nufi kofa a mugun fusace, da mugun karfi yake taka kasar kamar zai fasata tsabar bacin rai, rabon da ya samu kansa cikin irin wannan bacin rai har ya manta. Har ya fito daga ward din sai kuma ya juya ya koma ciki, kai tsaye ya nufi gurin da sauran nurses din suke, mostly sun sanshi domin yana yawan zuwa asibitin gurin Ali kuma gashi sanannen mutum kuma dan babban mutum wato Alhaji Mu'azu Shimkafi, sai dai ba zai iya shadar sunansu duka ba musamman a yau da yake weekend ne ba faces din daya sani ba ne a gurin.

“Who's Karima a nan?”

“Ni ce”

Ta amsa tana kallonsa.

“Ali ya ce ki dauko yarinyar ki saka a motana zan canja mata asibiti”

“Okay”

Ta mike tsaye ta kira mutun biyu da za su rika mata ita, a gurin ya tsaya har aka fito da ita suka turota a kujera idonta a rufe. Yana gaba suna Karima na biye da shi wata mai aikin shara da dauko files tana rike da file din Aminatu, suna isa gurin Motar Talba ya bude gidan bayan Nurse din da matar suka rikata suka sakata ciki sannan suka rufe motar. Shi kuma ya karbi file din ya bude side dinsa ya shiga ya aje file din a front seat, hakan kawai ya samu kansa da juyawa ya kalli fuskarta, sai tausayinta ya kara kama shi, abun da Ali ya fada masa akanta ya dawo masa, ga kuma wanda yake tunanin Leila na kokarin kara mata.

“Leila...”

Ya furta bayan a dauke kansa daga barin kallon Aminatu, yana jin tsanar Leila na kokarin dasuwa a ransa. Key yai ma motar yai reverse, ya kama hanyar ficewa daga asibitin.
Wata expensive private hospital ya nufa da ita, yana shiga ya nufi emergency, duk da kasancewar yau weekend ne ya samu ma'aikata da yawa a asibitin saboda private hospital ce da suka san aikinsu, sai dai ba kowa yake iya kai kansa ko wani nasa a can ba, sai ya tsaya da kafafuwansa.
Sun karbi Aminatu da gaggauwa da kuma kulawa suka shiga da ita ciki domin bata taimakon da take bukata.
Shi kuma ya tsaya daga waje ya ciro wayarsa dake aljihunsa tana ringing, ganin number Daddy yasa shi saurin picking.

“Hello Daddy”

“Mu'az kana ina? Mun ci abincin rana ba tare da kai ba?”

Ya daga jikin motarsa yana kallon harabar asibitin.

“Daddy ina asibiti”

Sometimes idan yana gurin Ali a asibitin ya kan cewa Daddy yana asibiti, hakan yasa Daddy yai zaton ko yana tare da Ali ne?

“An bata maka rai ne? Could we talk?”

“No Daddy ina wata magana ne mai muhimmanci, bata shafe ka tsakanina ne da Ali”

“Okay”

Daddy ya fada sannan ya kashe wayar, Talba ya cikawa bakinsa iska ya busar a hankali yana kallon Nurse din data doso inda yake.

“Dan Allah kai ne mijin yarinyar nan? Ko dan'uwanta?”

Tsaye Talba yai kamar an dasa shi ya kasa amsa mata.

“Tana bukatar jini da gaggauwa”

“A ina zamu samu?”

“Lab amman for now za mu bincika mu ga ko za'a samu jinin da zai dace da nata”

Ya gyada mata kai a hankali cike da natsuwa, sannan ya bi bayanta suka nufi cikin ward din, ita ta nuna masa dakin da suka saka Aminatu. Ita ta fara shiga shi kuma ya bi bayanta ya tsaya jikin kofar yana kallon fuskar Aminatu dake ta bachi kana gani kasan bata san inda take ba. Nurse din ta yi abun da zata yi ta fita Talba yana tsaye jikin kofar idonta akan Aminatu, takawa yai a hankali ya karasa kusa da gadonta still ya kasa kauda idonsa akanta.

“You need to survive”

Ya furta yana jin kamar ya tashe ta ya tambaye ta waya mata haka, kuma ayi sa'a ta amsa masa cewar Leila ce. Yana tsaye akanta har na kusan mintuna talati, sai ga nurse din ta dawo tare da likitan daya karbi Aminatu a dazun.
Sake dubawa yai sannan ya kalli Talba.

“Ba mu da kalar jininta a yanzu, sai kaje babbar asibiti ko kuma ka samu wani daga familynta idan zai iya bada jinin”

Uffan Talba be ce ba har sai da Likitan ya nufi kofar fita.

“Ko zaka iya gwada nawa? O ne”

Likitan ya juyo ya kalleshi.

“Yes why not amman zamu fara maka test mu tabbatar baka dauke da kowace irin cuta gudun samun matsala”

Ya daga masa kai kamar an masa dole, sannan ya bi bayan Nurse din dake nuna masa kofa.

“Bismillah Malam”



LEILA POV.

Wani irin kuka take wanda ita kanta ba zata iya fadar dalinlinta na yin kukan a yanzu ba, na zargin da Talba yake mata ne ko kuma na laifin ne da yake kokarin dora mata? Taya zai zarge da da abun da bata san wanzuwarsa ba? Miyasa ma zai yi maganar wata yarinyar a gabanta? Ko kuma dai tana kukan ne saboda zuwan Shamsu? For now she can't tell, all what she know is dukansu is painful, daga zargin har zuwan Shamsu har zancen yarinyar da Talba yake.

“Tun dazun kike ta kukan nan? Haka zaki yi ta yi a gaban mutane ki daure kanki?”

Momy ta fada cike da tausayin yarta.

“Wai wace yarinya ce ma yake magana akai?”

A take ta amsawa Momy hawaye ma sauko matan

“Wata ce, wata yar gudun hijira ce”

“Yar gudun hijira kuma? Shine har zai zarge ki da kashe ta? Ke kin santa ne?”

Ta daga kai tana

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login