Showing 78001 words to 81000 words out of 133328 words
kanwata ce, kuma matar da zan aura, akwai wata Amal tana makaranta, wacan kuma Momy mahaifiyarmu, muna da masu aiki biyu Mairo da Zulai idan kina bukatar wani abu ki fada musu za su miki. Wannan kuma Kabir, shine likitan da zai rika dubaki shi ma kuma kanena ne”
Talba na ajewa Kabir ya tari numfashinsa.
“No no no Malam shekara biyu ka bani ba, sai wani ji kake da kanka wai kanenka kar ta dauka da gaske”
Talba be ce komai ba, daman ba komai yake saka shi dariya ko magana ba, sai ya kalli Momy.
“Momy ina son zamu yi magana”
Momy ta dauke kai daga kallon Aminatu ta kalli Talba tana jin wani irin zafi a zuciyarta.
“Har a bada dan wani br taba zama nawa ba, nawa kuma be taba zama dan kowa ba”
Kusan wannan ne karo na biyu da wata kalmar ta fito daga bakin Momy da bata masa dadi ba, bayan wacan karo da shigarwa Leila.
“Momy yarinyar nan marainiya ce, ba uwa ba uba, kuma ban daukota na kawo ta nan ba sai dan nasan zamu iya kula da ita, kuma kin san muhimmanci rikon maraya, and ko dan ni ya kamata ki daga mata kafa...”
“Saboda gaka Ubana? Ko kuma saboda mu muka fi kowa son lada? Waya sani ko karya ta tsara maka? Idan ma da gaske ne mu muka kashe iyayenta ne da responsible din ta zai dawo kanmu?”
Da mugun mamaki Talba yake kallonta jin irin kalaman dake fitowa daga bakinta, sai dai be ce mata komai ya kalli Aminatu ya dauke kai ya kalli Kabir da yanayinsa ke nuna be jidadin kalaman Momy ba.
“Kabir kira Mairo”
Momy ta ja tsaki ta nufi upstairs ta bar Leila tsaye tana kallon ikon Allah.
“Mairo...”
Kabir ya kwala mata kira, ya san daga muryar ne ba zai iya ba shiyasa ya saka shi kiranta ba wai dan yana nufin ya tafi yaje ya kirata ba. Da gudu Mairon ta fito daga kitchen hannunta da kumfa.
“Gani ranka ya dade”
“A wanke mata baki, a bata abun karyawa, sannan a gyara mata dakin kasa, ki taimaka mata tai wanka sai dai kafarta na ciwo sai kin yi a hankali”
“To ranka ya dade”
Ta amsa da sauri, shi kuma ya juya ya fice daga falon ya bar Aminatu sai Kabir da Leila.
“Let me help you with brush and toothpaste”
Kabir ya fada sannan ya juya ya nufi upstairs. Leila ta bishi da kallo sai da ya haye gaba daya sannan ta kalli Mairo tana yamutsa fuska.
“Idan kika mata wanka, sai Momy ta ci ubanki”
Mairo ta kalleta da duba na rashin jindadi.
“Haba Leila kina ganina kin san na yi kanwa ta uku da ke, be kamata ki ce min haka ba, ko da kuwa kin san Hajiya zata yi fada ne, amman be dace ki zage ni ba”
“Okay miya dace na fada miki? Ki zo aiki gidanmu sannan ki yi tunanin zan girmamaki? Koya min magana zaki yi ko mai”
Yanayin yadda Leila ta rufe Mairo da masifa ne ya saka jikin Aminatu rawa, sai ta fashe da kuka.
“Mtssss munafuskar banza”
Leila ta fada tana hararar Aminatu, sannan ta nufi kofar baya ta falon tana danna waya.
21
Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
BATURIYA POV.
Sai da Ramlee ta shiga da ita har cikin falon sannan ta fita ta barta. Baturiya ta dade a falon sannan ta ji tsayarwar Mota harabar gidan, sai ta leka ta window ta hangoshi ya fito daga motar rike da wata karamar jaka, dayan hannunsa kuma rike da Makalle da waya a kunne. Babban mutum ne a haife ya haife ta kuma ya haifi yayunta, irin mazan nan ne da ake kira da sugar daddy.
Wani irin faduwa ta ji gabanta yayi, sai hakan be hanata daidaita natsuwarta, Ta gyara zamanta sannan ta kunna wayarta ta saka ta silent, gabanta ya tsanata bugawa ne a lokacin daya turo kofar falon ya shigo, abun ka da wanda be saba ba sai ta mike tsaye tana kallonsa, shi kuma ya kare mata kallon tun daga sama har kasa sannan yai mata alama data zauna, sai ta koma ta zauna tana kirkiro murmushi, a kujera dake kusa da kofar ya aje jakar hannunsa sannan ya karasa kusa da ita yana murmushi ya zauna. Ita ma murmushin ta sakar masa, sai ya kai hannu ya shafa fuskarta ya nuna mata fuskarsa alamar tai masa kiss, ba musu ta mika bakinta ta sumbanci gafen fuskarsa sai ya rumgumeta yana shafa bayanta.
“Yanzu dai Hajiya ki bari idan na dawo gida hankali kwance sai mu yi maganar, kisan Muhammad baya jin maganar kowa a yanzu so dole lallabashi za ku yi, idan yaji yana son ta ya amince daman abun da muke nema ne tun da yar'uwarsa ce, idan kuma yace sai wacan sai mu masa addu'a”
Ya fada yana gangarowa da hannunsa ya cire mata zip din atamfar ya fara murza fatarta ta baya dake cike da taushi da fari.
“Yanzu muna da meeting, idan mun gama kuma zan je na ga gwana saboda maganar kudin kwangilar nan, ba zan dawo da wuri ba sai dare”
Baturiya ta yi shiru tana sauraren yadda hannunsa ke ta yawo a jikinta, Sai wani abu take ji na rashin jindadi, ta saba mu'amala da Faruq balle tace ko dan bata saba bane, wata kila kuma saboda wannan sabo ne tsabanin wacan da take samu lada.
“Eh ya same ni da maganar ai, shiyasa muka taho tare sai kuma na buge wani mai acha, sun tafi da shi su kai shi asibiti, idan ya dawo nace ya same ni a gida mu yi maganar, so zamu zauna gani ga ki gashi sai mu yi maganar, sai anjima”
Ya kashe wayar gaba daya yana kallon Baturiya.
“Yan mata ya kike?”
“Lafiya kalau ya aikin?”
Ta amsa cikin rashin sakewa, shi kam sai murmushi yake abun nema ya samu.
“Alhamdulillah”
Ya fada yana kokarin cire mata dankwalin kanta gaba daya, ya fara shafa gashin kanta, sannan ya kamo hannunta ya saka a kirjinsa.
“Ba za a taya ni cire tufafin ba agajiye nake fa”
Sai da ta hade yawun bakinta sannan ta rika babbar rigarsa ta cire masa, da haka wasan ya canja salo, sai dai duk inda ya taba a jikinta sai ta ji wani iri musamman ma daya raba ta da rigar jikinta yana shafa kirjinta.
“Taso mu watsa ruwa yadda zamu jidadin bachi”
Ta dan yi murmushi ta mike tsaye, sai ya rika hannunta suka bathroom dinsa, a tare sukai wankan, yana ta labarta mata karamar haukar data same shi a lokacin da Ramlee take nuja masa honta a wayarta. Bayan sun gama suka fito sai kallon tsiraicin yake yana yabawa, tare da kai hannu ya taba inda yake jin ya masa. Kusan duk abun da Ramlee ta karantar da ita sai da ta aikata masa har abun da bata taba yi ma Faruq ba da sunan ya samu gamsuwa sai da tai ma Alhaji Haroon, sannan ta biyewa son zuciyarta ta budewa kanta babban file daga cikin manyan manyan files din zunubai. Ba shi ba ita kanta kanta ta samu gamsu irin wanda bata taba samu ba, sakamakon kayan matan da Ramlee ta bata ta sha, balle kuma shi da yai kamar zai haukace.
Nan da nan bachi yai gaba da shi, ita kuma ta tashi zaune ta daura tawul ta fito falo inda ta bar wayarta ta dauka tana dubawa sai ta samu miss calls biyu daga Fahat, jiki na rawa ta mayar masa da kiran daman can yana cikin ranta tun da ta shigo gidan take jiran kiransa. Ringing daya yai picking
“Na yi fushi yau duk ban ji muryarki ba kuma na kira wayarki na ji ta a kashe, na sake kira baki daga ba”
“Bana kusa da wayar ne, kasan idan ina kusa da wayar babu abun da zai hana ni dagawa, ni ma ai tun dazun nake ta jiran kiranka”
“Miyasa baki kira ni ba? Anyway yanzu dai bari na miki wani albishir na yi magana da Daddy, na fada masa cewar na samu mata”
Hannu ta saka ta dafe kirjinta, farinciki da faduwar gaba suka zo mata a lokaci daya.
“Da gaske? Amman me ya ce maka?”
“Me zai ce min kuwa, daman ai sun dade suna jiran ranar da zan fada musu na samu wanda nake so, even though akwai yan'uwa da ake son hada ni da su, amman ni bana son auren zumunci gaskiya”
“Allah yasa ya amince dai”
“Zai amince ma, fatar ba zan samu matsala daga bangarenki ba”
“Aa babu wata matsala Inshallahu”
“Haka nake son ji, ya kike?”
“Lafiya kalau, kai fa?”
“Ni ma kalau nake”
Sama sama take amsa masa duk wata magana da yake mata saboda bata son Alhaji Haroon ya ji tana waya da wani, ko da be nuna mata baya so ba ta san be dace tan a guest house dinta tai haka ba, domin maza suna da kishi no matter how old and young they are.
Bayan sun yi sallama ta kashe wayar ta koma cikin dakin ta hau gadon ta kwanta, ba jimawa bachi yai gaba da ita. Sai da aka yi sallah azabar suka farka kowanensu ya gabatar da wanka sannan suka yi sallah.
“Baby Fee'at me zaki ci na aika yarona ya siyo mana?”
“Shimkafa jalof”
“An gama gimbiyar mata”
Ya fada har wani kashe ido yake, ita kuma tai murmushi, tana sauraren wayar daya dauka ya kira yaronsa fada masa abun da suke bukata. Yana aje wayar ya mika mata hannunsa.
“Ta so zo nan”
Babu kunya balle tsoron Allah haka ta sake zuwa ta biye masa suka sake tarawa kansu wani babban zunubin, suna gamawa yaronsa ya kira wayarsa ya fada masa ya siyo.
“Ka aje a falo”
Ya fada masa sannan ya aje wayar ya tashi ya fita, ko da ya fito yaron ya aje abinci yayi ficewarsa, daukowa kawai yai ya shigo da shi ciki.
Jalof kawai ta bukata amman ya hado mata da farfesun kayan ciki da naman kai, ga kuma lemu mai sanyi da soyayyen naman kaza, zaunawa tai ta ci ta koshi nas, sannan ta tashi tana jindadi, rabon da ta ci abincin hotel har ta manta.
Bandaki ta shiga ta sake yin wanka ta fito, sai ya kalleta da mamaki.
“Wanka kika yi? Ai bamu gama ba, ni fa wuni ake min ba zaki koma gida ba sai dare, Ramlee bata fada miki ba”
“Aa bata fada min ba, amman tun kai ka fada min ai ya wadatar”
Murmushi yai ya bude nasa abinci ya fara ci yana yaba yadda ya sake me, da kuma irin gamsuwar daya samuna jikinta, ba karamin dadi ta ji ba domin Faruq ba mutum ne mai yaba mata ba idan ma ta gyara masa shimfidar, baya daga cikin mazan nan dake nuna jindadinsu a gurin matansu, ba dan komai ba sai dai be dauki yabon a bakin komai ba.
Kamar yadda ya bukata haka ta biyewa sharholiyarsa suka wuni suna raya sabo, sai bayan sallah Magariba ya rabu da ita tai wanka ta shirya cikin tufafinta, tana kokarin daura dankwalinta ta dauko jakarsa ya bude ya kirga dubu dari hudu ya aje mata.
“Ga wannan, sai kuma yaushe?”
Juyowa tai ta kalli kudin, a take gabanta yai mugun faduwa, sai dai bata yarda ta nuna matsa yawan kudin sun tsoratata ba sai tai murmushi.
“Sai kuma ranar daka tashi Alhajina”
“Ni kullum ai ban ki mun hadu ba, idan son samu ne ma tafiyar nan da zan yi China naje dake, kin taba zuwa china?”
“Aa Wallahi”
“To ki shirya dake zamu je”
Ta yi murmushi tana jin wani kalar dadi ya sakota gaba, duk kuwa da bata da tabbacin zata amince ta bishi din ko kuma aa, saboda aure da kuma Fahat.
Wayarsa ya mika mata..
“Saka min number ki a nan, ya kamata ace muna da number juna, ba dole sai mun biyo ta bangaren Ramlee ba”
Ta karbi wayar ta saka masa number, sannan ta dauki kudin ta saka a jakarta ta fito falo ta dauki wayarta ta saka mayafinta tai masa sallama ta fice tana mamakin yawan kudin daya bata, wannan karom bata yi shakkar saka gyaren ba saboda dare ne kuma a yanzu bata da kwaliya kamar dazun.
FARUQ POV.
Sai da ya fara biyawa gurin Mama ya gaisheta suka dan taba hira sannan ya kama hanyar zuwa shagonsa. Ba su karasa ba wani mai mota ya bugu babur din da yake kai, shi da mai achaban suka fadi gefen titi. A take mutane suka yo kansu da gudu mutumen daya buge su ma faka motarsa yai gefe ya fito yana dubasu. Kana ganinsa ka san babban mutum ne, domin shaddar jikinsa ma kadai abun kallo ce balle kuma bakar motar data buge su, a tare da shi a akwai direba sai kuma wata jar mota dake bayan tasa da alama take masa baya take ko kuma a tare suke. Daga mai achaban har Faruq daya ji ciwo a kafa zaune sukai mutane na musu sannu.
“Akwai asibiti nan kusa?”
Mutumen ya fada yana kallon direbansa, sai saurayin dake tsaye kusa da shi ya amsa masa.
“No Abba ba kace kana uzuri ba, ka tafi kawai ni ni zan kai su”
“Okay Muhammad idan an dubasu ka samu abun aka basu, idan mun hadu gida anjima zamu yi magana, yanzu jirana ake”
“Okay”
Dan nasa ya amsa sannan ya rika Faruq da yafi jin ciwo ya mikar da shi tsaye.
“Muje ga motana can”
Ya nuna masa jar motar da take bayan ta mahaifinsa, kamin su karasa gurin motar har mahaifinsa ya shiga tashi motar direban yaja motar sun kama hanya. A front seat ya zaunar da Faruq sannan ya bude back seat din ya ce da mai achaban ya shiga.
“Aa kaje ka kai shi, ni ban ji ciwo ba”
“Ka tabbata?”
“Inshallah”
Sai ya rufe motar ya rufe inda Faruq yake zaune, ya zagaya mazaunin direba ya kirga dubu biyar ya mikawa mai achaban, sai ya karba yana godiya daman haka tafi masa dadi. Ya hau achabansa ya kama hanya shi kuma ya shiga motar yaja Faruq suka isa asibiti.
“Sannu ko kana da asibitin da kake zuwa?”
“Aa”
“Okay bari muje ta nan kusa, ai zaka iya jurewa ko?”
“Haba sai kace ba namiji ba”
Faruq ya fada yana murmushi, shi ma murmushin yai ya cigaba da tukin har suka isa asibitin, aka duba kafar aka bashi magani suka rufe ciwon. Sannan ya sake daukoshi a motarsa suka suka nufo unguwarsu, suna tafe suka hira kamar daman can sun saba, be yarda ya bar Faruq a bakin titin ba duk kuwa da kasancewar mota bata shiga har kofar gidansu, sai ya fito ya taka masa har kofar gidan yana masa wasa wai kar madan tace sun buge mata miji, Faruq murmushi kawai yai ya kai hannu ya taba gidan sai ya ji shi a rufe, key dinsa ya dauko ya bude ya shiga ciki.
“Ina jin bata nan, daman tace min tana da biki zata je”
Fada a kokarinsa na kare matarsa duk da kasancewar mutumen be san Rafi'a balle har ya munana mata zato.
“To a gaishe ta, kuma a bata hakuri ga kuma wannan ayi cefane”
Ya fada yana mikawa Faruq dubu goma.
“Aa haba ai abu ne da Allah ya kawo...”
Kamin Faruq ya karasa Mutumen ya saka rantsuwa.
“Wallahi sai ka karba, kai shedan kadai ke maida kyauta”
Murmushi Faruq yai a karo na barkatai ya karbi kudin yana masa godiya.
“Na manta ban tambayi sunanka ba”
“Faruq”
“Ni kuma Muhammad Fahat na gode sosai Allah ya tsare gaba”
“Ameen”
Daga haka Faruq ya karaso cikin gidan shi kuma ya juya ya kama hanyarsa. A falo Faruq ya zauna yana kiran Baturiya a waya domin jin inda take, sai dai bata dauka ba daga baya ma sai yaji wayar a kashe, hakan kuma ba karamin bata masa rai yai ba, ba yau ta saba fita ba tare da izininsa ba sai dai ya fi jin zafin fitarta fiye da koyaushe. Cikin karfin hali ya shiga uwar daka ya tube tufafin jikinsa yai wanka ya canja wasu kayan sannan ya kwanta, nan da nan bachi yai gaba da shi. Kiran Allah azahar ne ya tashe shi, ya tashi yai alwala ya fita masallaci a can ya hadu da dansa da yabi yaran makotansu suka tafi masallacin a tare. Kusan kowa da ya gaisa da shi sai ya masa sannu da fatar Allah ya tsare gaba, shi kuma ya amsa da Ameen bayan ya labarta musu abun da ya faru.
Sultan na ganin mahaifinsa ya rike shi suka dawo gida tare. Abun ka yaro yana shigowa ya fara tambayar Faruq ina mamansa.
“Dady Momy bata dawo ba?”
“Ina ta tafi?”
“Bata fada min ba, amman na ji tana ta waya da yawa tana ta waya har ta ce ummouy”
Ya nuna yadda tai kiss din da bakinsa. Faruq ya hade yawu yana jin wani bakinciki na taso masa. Haka ya wuni a gidan daga shi sai dansa girkin rana ma shi ya girka duk da kasancewar akwai ciwo a kafarsa, tun yana tunanin zata dawo da la'asar bata dawo gidan ba sai bayan magariba ana daf da kiran sallah isha'i wani gurin ma har an fara kiran. Sannan ta shigo da dan faduwar gaba, ganin cewar Faruq ya rigata dawowa, ta shigo falon da sallama, ya amsa mata ya mike ya fice ya bar mata falon, sai ta bishi da kallo kamin ta kalli danta.
“Sultan yaushe Dadynka ya dawo?”
“Tun da rana har ma ya ji ciwo a kafarsa”
Bata sake cewa komai ba ta nufi dakinta ta aje