Showing 99001 words to 102000 words out of 133328 words

Chapter 34 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

492

Middle Ads

zaka taba rasa komai ba, ba zaka taba kukan rashin uwa ko uba ba, musamman uwa”

Talba ya gyada kai wasu hawayen na sauko masa.

“Kamar yadda na ji a yanzu nan Daddy, amman duk da haka Ina rokon Alfarma a yafewa Momy, ita ma ta rike ni kamar danta, na taso ban ta wata uba ba bayan ita, dan Allah Daddy ka dawo da ita”

“Of course zan dawo da ita, do you think I can live without Amina? Zan dawo da ita amman sai ta karbi hukuncinta, ni ma ina fatar za a daga min kafa”

Talba yayi murmushi idonsa na cika da wasu hawayen.

“Ina kaunarka Daddy, Allah kara maka lafiya”

“Amin Allah ya maka albarka”

“Amin”

Ya amsa sannan ya dauki tissue ya gyara idonsa, sannan ya nufi kofar fita.

“Mu'az ina ka kai yarinyar nan?”

“Gidansu Madina”

“Ka dawo da ita gida”

“A can din ma ta fi sakewa, Madina tana sonta”

“Baka da inda yafi gida, kuma be kamata akaita ko'ina ba, bayan ga inda kake da iko”

“Na ji, amman sai ka fara dawowa da Momy”

Daddy yayi murmushi yana daga masa hannu alamar ya tafi, shi ma murmushin yai kadan ya fice yana jin zuciyarsa wani iri, samun kansa yai a motarsa yana ta sauke ajiyar zuciya, be taba jin irin yadda yake ji a yau ba. Sai dai babu wanda ta fado masa a rai sai Aminatu, shi da be taba ganin iyayensa ba, be san su ba amman a yau yaji yana marmarin ganinsu yana kewarsu balle ita data rayu da iyayenta ta girma tare da su ta san dadinsu ace an raba ta da su lokaci daya, kuma a gaban idonta, ya tabbatar abu ne da ba zata taba iya mantawa da shi ba, ba kuma zai gogu a zuciyarta da idanuwanta ba. A masallacin gurin yai sallah azahar sannan ya fito yana ta tukin ba dan ya san inda zai je ba, baya tunanin zuwa gida a yanzu, dan baya jin zaman gidan zai masa dadi, but ina zai je? Office? No baya bukatar komawa can, gurin Ali? Nope zai fara damunsa da maganar Leila, haka yai ta yawo idan ya gaji da tukin sai ya saka motarsa ya zauna a motar, uku da rabi ya nufi gidan marayunsa be fito ba sai hudu da rabi. Kai tsaye ya nufo gidansu Madina domin zuciyarsa ta bukaci ganin Aminatu, be kira Madina ya fada mata gashi zuwa ba, balle ta san da zuwansa, he just want go ba tare daya sanar mata ba, sai da ya isa gate din gidan sai kuma ya ji wani iri, kar mutanen gidan su ce ya cika zuwa, tun da dazun ma ya zo, gashi yanzu baya cikin yanayin na walwala. Amman ya kamata ya koma b tare da ya ga Aminatu ba? Bayan ya kudurtawa kansa son magana da ita? Hannu ya kai ya dannn horn sau biyu mai gadin ya leko ya ganshi sai ya koma ciki ya bude masa gate din. Tun kamin ya karasa harabar gidan ya hango Aminatu zaune a parking lot sanye da daya daga cikin rigar da suka siyo dazun picking color, bakinta ya sha man lebe har wani sheki yake gashin kanta kuma ya sha gyara, an basa mata shi ya sauko har bayanta, sai wata yar karamar farar hula wanda ke bayyana gashin tsakiyar kanta da kasan gashinta, sai a lokacin ya tuna dazun be kaita gurin gyaran gashin ba, and now he think Madina ta kaita ko kuma ta gyara mata. Tana zaune kan kujera kusa da wata mota, sai dan karamin teburi a gabanta mai cike da littafai textbooks hannunta rike da biro. Ana bude gate din ta dago tana kallon motarsa har ya karaso kusa da ita ya faka motar ya sauke gilashin motar yana kallonta. Ita ma kallonsa take har ya bude motar ya fito ya rufe a hankali ya karaso kusa da ita cikin yanayi na damuwa.

“Ina wuni”

“Lafiya kalau, me kike a nan ke kadai?”

“Na gaji da zama ciki ne shi ne Ya Madina ta fito da ni tace wai na sha iska, ta bani abun rubutu”

“Kin iya rubutu ashe?”

“Ajami ba”

Ya kai hannu ya dauki littafin da take rubutu akai.

_Ina samun natsuwa a kalamanka, kamar yadda ganinka ke kwantar min da hankali, rashinka yana nufin mutuwata, samunka kuma farincikina_

Yayi murmushi bayan ya gama karantawa, sannan ya kalleta.

“Ashe kin iya kalaman soyayya”

Sai tai kasa da kanta tana murmushin daya kara bayyana kyauta da hasken bakar fatarta.

“Ina rubutawa wani saurayina shi kuma yana rubuto min, idan zan tafi talla sai ya ba ni ta shi, ni kuma na a shi tawa, duk da ajami muke rubutawa, kamin rayuwarmu ta canja, ni na dawo nan shi kuma ya tafi inda ba a dawowa”

Ta karasa idanuwanta na cika da kwalla. Sai ya risina gabanta yana kallon kyakkyawar fuskarta.

“Kin rasa abubuwa da yawa, kina da juriya na injina miki, yanzu fada min ya kike ji?”

Ta dago ta kalleshi.

“Ba dadi, sabawa da mutanen da baka sani ba, abu ne mai wahala, na kasa manta iyalina”

“Na fahimta”

Ya fada yana kallon wani gurin dabam, hakan ya bata damar kare masa kallo, fari ne fes irin farin nan mai kyau da daukar ido, ga wani dogon hanci da sauko masa gashin kansa ma sai sheki yake, abu ne mai wahala a iya yi masa kallo daya a kawar da ido. Ba kyaunsa ne kadai abun da idanuwanta suke nuna mata ba, har da damuwar dake fuskarsa domin bata taba ganinsa a haka ba.

“Kai ma kana da damuwa...?”

Ta tambaya cikin tsoro da fargabar irin amsar da zai bata, juyowa yai ya kalleta sai tai arba da kyakkyawan Murmushin daya fadada fuskarsa.

“Ya akai kika gane?”

Ta yi shiru tare da sauke idonta kasa.

“Ina ce miki Shalele kin cancanci sunan, saboda kin rayu da iyeyenki kin jin duminsu, kin san muryarsu, kin san farincikin da damuwarsu, a karon farko yau na ji ina kewar mahaifiyata duk da kasancewar ban taba ganinta ba, amman ina jin kamar na kirata ta amsa min, kamar tace Talba be dace kai wannan ba, wannan ya dace kai, ban san maraici ba amman ina jin son ganin mahaifiyata ko da sau daya ne a rayuwata”

Yanayin yadda kalaman suke fitowa daga bakinsa kadai sun isar da kewar dake zuciyarsa.

“To ai Daddy yana raye, ka rika kallon dabi'unsa da kamaninsa kamar na mahaifinka, mahaifiyarka kuma sai ka nemi hotonta ka rika kalla”

Murmushi yake yana kallonta kamar ba shi ba.

“Kina da wayo Shalele, kin fahimci damuwata a take kuma kin sama min mafita duk da karancin shekarunki”

Ya fada yana kai hannu ya taba halshen gashinta. Sai ta kai hannu ta sanye gashin.

“Waya gyara miki?”

“Ya Madina, gata can”

Mikawa tai tsaye daga ita har shi suka koma kallon entrance din da Madina ta fito sanye da dogon Hijab ta nufosu da saurinta.

“Sannu da zuwa”

Ta fada a yayinda ta karaso kusa da su, sai ya daga mata kai alamar ya amsa.

“Ban san ka shigo ba sai yanzu bari na kawo maka ruwa”

“Ka ci abinci dazun ka ce min kana jin yunwa?”

Aminatu ta tambaya, sai ya kalleta ya girgiza mata kai alamar a'a. Sai Madina ta kalleshi.

“Ko na dafa maka wani abu? Zama da yunwa be da kyau”

“Ruwa kawai”

“Okay”

Ta juya da sauri sai ya kira sunanta.

“Madina...”

Ta juyo da saurin gabanta na faduwa a zatonta ko zai ce ya fasa shan ruwan ne.

“Thank Youuuuuuuu”

Suma ne kawai ba tai a gurin ba, amman ta yi mutuwar tsaye har ta kasa yarda da ita yake. Ita fa? Madina yace wa Thank you after celled her name kuma yace mata ya gode, godiya fa yake mata...? Murmushi ta sakar masa duk da kasancewar babu murmushi a tasa fuskarsa ta juya ba tare da tace komai ba ta cigaba da tafiya, tana jin kamar ta zuba ruwa kasa ta sha dan murna da jindadi, yadda ya kira sunanta ma abun alfahari ne a gurinta, sai ta ji kamar ba a taba kiran sunanta da lafazi mai dadi irin na Talba ba, lastly zai sha ruwan hannunta.
27

Ko kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Yana tsaye a gurin kusa da Aminatu har ta fito da glass cup dayan hannunta dauke da gorar ruwa. Tana isowa ta mika masa cup din ya karba sannan ta bude ruwan ta zuba masa, sai ya sha kadan ya mika mata cup din, ya juya ya nufi mota ba tare da yace da ita komai ba, haka ma be yi ma Aminatu sallama ba, daga ita har Madina binshi sukai da kallo har ya shiga motar ya fice daga gidan.
Sannan Madina ta kalli Aminatu.

“Idan kin gama ki min magana zan shiga dake ciki”

“Toh”

Ta juyo tana ta kallon gate din kamar ance mata Talba zai dawo, ta nufi kofar falon cikin wani irin farinciki, ta shigo falo, bata ko kula Hajiya dake falon ba ta nufi kitchen, cup din ta aje ta kara ruwan gorar hannunta sannan ta dauka ta saita bakinta a inda Talba ya sha, tana sha tana murmushi.

“Madina...”

Ta juyo da sauri ta kalli Hajiya hannunta rike da cup din.

“Na'am Hajiya”

“Waya zo yanzu?”

“Talba ne”

“Miyasa be tafi da yarinyar ba? Ba kin ce kwana biyu zata yi ba?”

Ta yi kasa da kanta.

“Hajiya gaskiya ba kwana biyu zata yi ba, kusan zata zauna a nan ne kamin abubuwa su daidaita a can gidan, yanzu haka Momy bata gidan sun samu matsala da Daddy har ya turata gida”

“Saboda yarinyar?”

Ta daga mata kai.

“Eh saboda abun da Momy tai ma Talba a kan yarinyar”

“Amman shi Talba ba yana da yan'uwa uba da uwa ba? Miyasa be kaita can ba sai a nan? Saboda mu ya raina mu ko kuma saboda me? Ke baki tunanin aje a nan zai lalata alakarku da Leila ko mahaifiyarta? Ni kaina sai ki ga abun ya shiga tsakaninmu da Hajiya dan mutuncin da muke ma mu daina”

“Bana fatar hakan Hajiya, kuma ba wai ya dauke ta kai tsaye ya ba ni ba ne, ni na bukata”

Hajiya ta yi mata wani kallo na mamaki.

“Saboda...”

“Saboda na faranta masa rai”

Ta amsa kai tsaye, sai kuma ta aje kofin hannunta ta karasa kusa da mahaifiyarta ta kama hannunta cikin yanayi na damuwa.

“Hajiya ke mahaifyata ce, na san ko ban fada ba kin fahimta, Wallahi ina matukar son Talba na rasa yadda zan yi”

Hajiya ta yi saurin janye hannunta daga rikon da Madina tai mata.

“Kul...!!! Karki yarda son zuciya ya debe ki ya kaiki ya baro karki, Aminiyarki? Kuma mijin da zata aura? Ki ce kina sonsa? To me kike tsammani zai juyo gurinki ya bar zabin iyayensa? Anya kin shirya yin takara da Leila? Hajiya bata has akan yayanta, karki kuskura dinke rigar kanki inda kai ba zai fito ba balle sauran jiki, domin wahala kawai zaki sha ki tashi a tutar babu kuma tutar kunya”

Hawaye ya cika idonta.

“Na yi iya yadda zan yi na yaki abun nan Hajiya, na yi iya yadda zan yi na kawarda idona daga Talba, amman na kasa, na yi ta hangowa kaina matsalolin dake tattare da hakan, amman zuciya na raya min zan iya dauka, na san kawance na da Leila mai zurfi ne, mun taso tare an girma tare mun zama kamar yan'uwa, be kamata na yi hakan ba, amman wata kila wannan ce kaddarata, Wallahi Hajiya ina matukar son Talba fiye da yadda Leila take sonsa”

Maganar take cikin kuka hawaye na sauko mata.

“Ki gaggauta cire shi a zuciyarki, kuma bana son yarinyar nan ta wuce yau, ki fada masa na ce ya zo ya dauke ta, daman ai na lura da take taken ki ba tun yau ba”

Hajiya na kaiwa nan ta juya ta fice, sai Madina ta durkushe a gurin ta fashe da kuka. Kuka tai sosai marar sauti sannan ta mike tsaye ta nufi dakinta tana shiga ta kulle kanta ta fara rusar kuka kamar wanda akai wa mutuwa, can kuma ya dauki wayarta ta shiga gallery wayarta ta kamo hoton Talba ta tisa a gaba tana ta kallo hawaye na yi mata sallama.
Wani irin abu take ji marar misaltuwa, da daske yanzu kam ta tabbatar sonsa take fiye da kima, tun da har sonsa zai saka ta kasa ganin Leila kuma kunnuwanta su toshe daga maganganun da mahaifiyarta tai mata. tashi tai ta shiga bandaki ta wanke fuskarta ta fito falon idonta har ya canja kala, sai da ta zauna sai kuma ta ji zaman baya mata dadi, sai kawai ta mike tsaye ta fice daga falon zuwa parking lot inda Aminatu take zaune. Tun kamin ta karaso Aminatu take kallonta da karantar yadda yanayinta ya canja daga far'a da jindadin da ta shiga da shi dazun, zuwa fitowa da damuwa da kumburarin idanuwa.
Zuwa tai ta tsaya akan Aminatu ba tare da tace mata komai ba. Aminatu ta tsayar da rubutun da take tana sauraren abun da Madina zata ce mata ammam shiru bata ce mata komai ba har na tsawo lokaci. Hakan yasa ta dago kai ta kalleta sai ta ga hawaye na sauko mata.

“Yaya Madina baki da Lafiya ne?”

Madina ta lumshe ido wasu hawayen na sauko mata.

“Ba ni da lafiya Aminatu, kuma ciwo ne da ba zan tana warke shi ba, ciwo ne da Allah ya dora min, kuma kowa ya kasa fahimtata”

“Me ke damunki?”

“Ciwon son, ciwon son wanda be san da wanzuwar son ba”

Aminatu kan kallonta kawai take ba dan ta fahimci inda kalamanta suka dosa ba, sai dai ta fahimci son wani take amman wanenen wanda be san da wanzuwar son ba? Dukawa tai gaban Aminatu kamar mai neman gafara.

“Hajiya tace dole ne na dauke ki daga gidan nan tsakanin yau da gobe, ni kuma bana son ran Talba ya bace, ban san yadda zan yi ba, daman na fada mata cewar zaki zauna na kwana biyu ne, bana son bata ran Talba, kamar yadda bana son tsabawa umarnin mahaifiyarta”

“Shine kike kuka?”

Ta girgiza kai.

“Aa abun da nake yi ma kuka dabam”

“Ki kirashi a waya Sai ki fada masa na ce bana son zama a nan”

“Zai iya zargin wani abu, bana son abun da zai nisanta ni da shi, ko ya saka ya ga kamar ni ce bana son zamanki a kusa da mu”

“Zan fada masa gaskiya ba amin komai ba”

Saaz  ta fada tana Kallon Madina, sai Madina ta hade yawun bakinta ta saka hannunta ta share hawayen da suka zubo mata. Sai da ta kira Talba sannan ta kara wayar a kunne.

“Hello...”

Ta fada bayan ya dauki kiransa jin muryarta sai yai shiru be ce komai ba, bata damu ba ta cigaba da maganar.

“Aminatu ce, ta dame ni da kuka na tambaye ta me ke damunta bata fada ba”

“Tana ina?”

Ya tambaya daga dayan bangaren.

“Gata nan kusa da ni”

Ta mikawa Aminatu wayar, sai ta karba ta kara a kunne.

“Hello”

“Shalele lafiya kike kuka?”

Ta yi shiru tana kallon Madina.

“Ko saboda na tuna miki da baya ne?”

“Aa bana son zama a nan ne?”

“Ba ki son zama kuma? Miya faru?”

“Ba komai ni dai bana son nan ka zo ka dauke ni”

“Ana miki wani abu ne da baki so?”

“Aa ni dai ka zo ka tafi da ni”

“Okay zan zo”

“Yaushe?”

“Yanzu ko anjima”

“Toh”

Ta mikawa Madina wayar. Sai Madina ta karba ta kai kunnenta.

“Hello”

“Akwai abun da akai mata ne?”

“Wallahi babu, amman ban sani ba ko ita tana da abun da take son fada maka”

Ne sake cewa komai ba ya kashe wayar yana busar da iskar bakinsa. Ali ya kalleshi.

“Ya akai?”

“Shalele ce, wai ba zata zauna a gidansu Madina ba tana son na zo na dauke ta”

Ali ya masa wani kallon na mamaki.

“Ka kaita ina?”

Sai ya daga kafadunsa ya jingina da motarsa.

“Wannan abun yayi yawa Talba? Sunan ma da kake mata ka daina domin Leila ba zata jidadi ba idan ta ji, kuma karka dauko ta daga can”

“Idan kuma ana mata abun da bata so fa? Wata kila suna musguna mata ne, ba zata iya fada ba ne a gaban Madina”

“Okay let assume that ana mata wani abun, idan ka dauko ta gidanku zaka sake maida ta saboda Daddy yace ka kawo ta? Kana ganin tunani ne mai kyau ka dawo da ita bayan Momy bata nan kuma saboda yarinyar komai ya faru?”

“Ba gida zan kaita ba?”

“To ina zaka kaita? Talba ka yi tunani please... Gidan wata gwaggonka ko yar'uwarka? No suma ba su maka kallon mai hankali da tunani ba”

Ya mike tsaye yana kallon Ali.

“Okay then zan ajeta a gidana i think babu wanda zai takura mata a can kuma ina da iko da can ai”

Ali yayi dariyar mamaki.

“Like seriously? Talba kana magana kamar baka san illar abun da zaka aikata ba?”

“Idan na kaita can fyade zan mata? Saboda gani dan'iska ko?”

“No don't take it serious, amman dai kasan idan mace da namiji suka ke be a guri daya shedan ne na ukunsu, yarinyar kyakkyawa kamar wannan, kai kuma gaka lafiyayyen mai bukatar aure? Duk abun da musulunci ya hane mu da shi ya kamata mu nisance shi, And aje wannan ma a gefe baka tunanin wasu za su iya amfani da wannan damar su yi blackmailing dinka? Kuma ya kake tunanin Daddy zai ji idan ya san ka aje ta a gidan ka yarinyar da ba matarka ba”

“Me kake son yanzu na yi? Kai ma fa kasan halin da yarinyar take ciki! Bata da kowa sai ni sai Allah”

“Bata da kowa dai sai Allah, kai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login