Showing 30001 words to 33000 words out of 133328 words

Chapter 11 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

460

Middle Ads

ko kuma dai wasa ce”

Ta fada tana tashi tsaye.

“Matarku kuma?”

Ta tambaya domin tantancewa.

“Eh mana ba matar Faruq ba ce Rafi'ah?”

“Ka san Faruq ne?”

“Sosai ma tare muka yi makaranta da shi”

Ta kara zaro ido.

“Na shiga uku”

“Gaskiya abokinmu yayi dacen mata, kina da kyau”

Ya rubuto mata, sai ta koma ta zauna tana kokarin kwantar da hankalinta.

“Da alama shi ma shegen ne”

‘Allah sarki, ashe kun yi karatu tare’

Ta amsa masa.

‘Eh sosai ma, na zo har aurensa ai, kuma ko lokacin da kika haihu na so na zo ban samu dama ba, ya Babyn?’

‘Lafiya Kalau, ya naka iyalin?’

‘Ni kam da saura har yanzu ban yi aure ba, sai na samu mai kyau irinki’

‘Hmmm kana koda kyau na kamar gaske’

‘Da gaske ne mana, Faruq be taba fada miki kina da kyau ba’

‘Uhmmm’

Shine reply din da tai masa sannan ta kashe data ta aje wayar, ta nufi inda Sultan yake yana bachi ta tashe shi ta bashi ragowar kazar jiya ita ma ta ci ta koshi sannan ta shirya masa ita ma ta shirya ta dauki jakarta da mayafi ta riko hannun Sultan suka fito daga cikin gidan, sai da ta kulle gidan sannan ta nufi makontansu ta bada ajiyar Sultan ita kuma ta kama hanyar titi, ba yau ta saba satar hanya ta fita ba, wani lokacin idan ta tambaya ya yana ta ma fita take wani sa'in kuma bata ma tambayarsa, gashi idan ya fita baya dawowa sai dare, inda ba wani abun ya bijiro ba. Ko ma ya dawo ya tarar bata nan sai dai yayi hakuri ya danne abun a zuciyarsa.

“Malam tsohuwar kasuwa”

Ta fada bayan ta tsaya da mai adaidaita, kai kawai ya daga mata, sam bata lura da kofatun dake kafunsa ba ta shiga, sai da ta gyara mayafinta da face mask din dake fuskarsa sannan ta aje jakarta gefe. Kamar ance duba ki gani tana kallon bayan kansa sai ta ga kan kamar na tsuntsu har wani rawa yake kamar zai fado ga bayansa duk gashi kamar dabba.

“Malam tsaya na fasa zuwa...”

Ta fada da sauri tana runtse ido, sai mai Napep din ya faka gefen titi, tsabar tsoro yasa bata tsaya daukar jakarta ba ta fita da sauri tana haki, tana fita mai Napep din ya cigaba da tukinsa kamin ta rufe ido ta bude har ya bacewa ganinta, baya tai da sauri tana kara zari ido.

“Innalillahi”

Bata karasaba ta ji kamar ta taki abu, sai ta juya da sauri ta kalli Mahaukacin dake bayanta ya tara uban gashi ga tufafin jikinsa duk datti, wani irin tsalle ta daka ta ranta ana kare, wani irin gudun bala'i take mahaukacin na biye da ita shi ma da gudunsa. Wani shagon dake titi ta nufa kamin ta isa mutanen dake gurin suka watse da gudu domin sun san mahaukaci ba ya yi ma mutum da sauki, ita kanta bata taba sanin tana da gudu ba sai a yau, tana karya kwana ta samu wani gida ta shige ta turo kofar gidan da karfi ta rufe, tana ta haki kamar numfashinta zai fita. Mutanen gidan suka fito da sauri suna kallonta.

“Lafiya?”

Sun tambaya domin kama tai musu da mahaukaciya, kanta babu dankwali balle mayafi ga kafafuwanta babu talkami sai uban datti da suka yi, gashin kanta ma dake fake har ya yamutse, gumi sai sauko mata yake.

“Mahaukaci ya biyo ni....”

Ta fada daker tana haki, idonta har wani zurfin wahala sukai.

“Subhanallahi tsokanarsa kika yi?”

Dayar ta tambaya tana kokarin gyara goyonta, kamin ta amsa mata suka ji aka dukan kofar da karfi.

“Zai iya balla mana kofa fa”

Baturiya ya kauce jikin kofar da sauri ta dawo cikin mutanen tana kallon kofar.

“Ban tsokane shi kasuwa zan je sai mai Napep...”

Bata karasa ba tai shiru tsabar fita da numfashinta yake da karfi.

“Wallahi haka yake, ranar fa tun daga rijiyar zaki ya dinga bin Marwa har unguwa uku”

Baturiya ta kalli mai maganar, daman tun daga jin yanayin maganarsu ta ji ta banbanta data Zamfara, domin su kananci suke yi, gashi kuma an fadi rijiyar Zaki da unguwa Uku, wanda ta san ba a Zamfara unguwar take ba.

“Baiwar Allah nan kuma wani gari ne?”

“Kano... ”

“Kano....?”

Ta maimaita tana zaro ido, sai ta fadi a gurin zaune ta fashe da kuka.




________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai, muna da kwalli mai karfin gaske (Mujarrabun sadidan) Akwai na farin jini for yan mata da Zaurawa. Akwai wanda ba a bawa mai kishiya, akwai na mazajen da kr neman mata, muna da rantse baki da kishiya, muna da back to virgin, for yan matan da kaddara ta fadawa, ko Zaurawan dake son zama yan mata, akwai jigida mai kyau, muna da man ayu 100% natural. Akwai na maza masu hannun Dambe.
Hajiya sai n gwada akan san na kwarai, ba cuta ba cutarwa, duk wanda kika siya sai kin dawo.

Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
*💔 BAKAR WASIKA 💔*


By Khadeeja Candy


Page -9️⃣

If you're not living around these people, you will never know what they are going through, fiye da haka ma yana faruwa, kawai dai Allah ya tsare mu su kuma yai musu mafita.
Tun daga jin sunan Labarin kun san abun da ya kunsa. Ban san abun da readers suke so ba, idan an saka kudi da luxury life sai ace writers suna bude idon mutane, and when we're talking about reality kuma ba mu tsira ba, anyway if you don't like the story you can quit it.

                  ***        ***        ***

Har past 12am Talba yana zaune bangaren Momy doing nothing, haka nan kawai yake jin yanayinsa sai a hankali. Idan zaka tambaye shi damuwarsa ba zai ce maka ga matsalarsa ba. Mikewa yai tsaye ya isa gaban plasma ya kashe sannan ya wuce kitchen domin samu abun da zai sakawa cikinsa, rabonsa da abinci tun da rana, ko lunch din Momy ta hada be ci ba. Tea ya fara hadawa kansa sannan ya bude freezer dake kashe ya dauko cake ya kunna oven ya saka shi a ciki, sannan ya dauki tea ya rike a hannunsa yana ta kallon harabar gidan ta windows kitchen din, ko ina haske ne kamar rana.
Juyowa yai a hankali jin kamar shesshekar kuka a falo, aje cup din dake hannunsa yai ya tako a hankali zuwa bakin kofar kitchen din ya tsaya. Sai ya hango Leila zaune a bakin stairs din sanye da kayan bachi riga da wando sai kuma safar dake kafarta, kanta ba dankwali sai hawaye take tana kallon wani bangare na falon, sam bata lura da shi ba har sai da ta juyo tana cigaba da rera kukan a hankali. Suna hada ido sai tai sauri share hawayenta ta dauke kai sannan ta mike tsaye ta juya a hankali zata hau stairs din.
Har tai rabi ban da  kallon mamaki babu abun da Talba yake mata.

“Leila...”

Ya kira sunanta kamar wanda baya son magana, tsayawa tai cak gabanta na mugun faduwa, domin har ga Allah bata dauka yana zaune a falon har lokacin ba, da b zata fito daga dakinta ba, juyowa tai a hankali sai dai bata yarda ta kalleshi, sanin kanta ne ba zai tambaye ta me take yi ma kuka ba, kiran sunanta kawai da yai ya isa ya sanar da ita cewar tambayar damuwarta yake.

“Na yi mafarkin tsoro ne...”

Ta fada tana wasa da yatsun hannunta, bata tsaya jiran abun da zai ce mata ba ta juya da sauri ta haura sama. Da kallo ya bita har ta bace masa sannan ya juyo ya dawo cikin kitchen din, mamaki karara a fuskarsa.

‘Mafarki tsoro?’

Ya maimaita aransa, idan mafarkin tsoro tai me zai saka ta fito a nan ta zauna ita kadai?

“Ko dai saboda ni ne?”

Ya tambayi kansa yana kokarin kai hannunsa ya dauki tea, domin ya san abun da zai tashi hankalin Leila ba karami ba ne, and bayan shi ba ya ji akwai wani abu da zai saka Leila ta yi kuka ko ta shiga damuwa. Kamar wanda baya son bude baki haka ya kai cup din a bakinsa ya soma sha a hankali, dayan hannunsa ya saka a aljihu yana kallon oven din sai dai gaba daya tunaninsa ba a nan yake ba.
Sai da ya sha rabin tea sannan ya kashe oven din ya ciro cake din daya dumama ya aje, ya dauki tissue ya saka a hannunsa sannan ya fara daukar cake din yana ci. Bayan ya gama ya kashe wutar kitchen din ya fito falo ya kashe wutar sannan ya wuce bangarensa. Shirt din jikinsa ya fara cirewa wanda hakan ya bawa kyakkyawar surarsa da murdaden kirjinsa bayyana, a kafadarsa ya dora rigar sannan ya nufi wani madaidaicin daki dake hannunsa na dama, a hankali ya murda kofar ya bude ya shiga, kai tsaye ya nufi teburinsa ya ja kujera ya zauna ya bude system dinsa yana duba sakon da Jahid ya turo masa na adadin kudin da za a kashe wannan watan na gidan marayu.

“Okay”

Ya furta sannan ya rufe system din ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kunna data ya shiga WhatsApp.

‘Zan rubuta maka cheque gobe, after that, ka bincika abun da yan gudun hijira suka fi bukata ka kirga ko nawa za akashe na mutun 300’

Bayan ya gama rubuta masaya kashe data ba tare da ya duba sako ko daya da yake shigo masa ba, balle har ya amsa. Fitowa yai daga dakin ya nufi Bedroom dinsa yana shiga ya aje rigar dake kafardarsa a muhallinta ya cire jean din jikinsa ya nufi bathroom ya jika jikinsa da ruwa ba tare da ya saka sabulu ba yai alwala ya fito, sai da ya tsane jikinsa sannan ya nufi closet din ya dauko kayansa na bachi.
Wando kawai ya saka domin abu ne mai wahala ya kwana da riga komai tsananin sanyi, sai dai ya rufa da bargo, riga na cikin abun da ke takura shi ta hana shi sakewa idan zai yi bachin dare.


BATURIYA POV.

“Wallahi tun da nake a rayuwata ban taba zuwa Kano ba, ni fa ban taba barin Zamfara ba”

Ta fada tana fyace hancinta daya cika da majina tsabar kukan data sha.

“To ya akai kika zo nan?”

“Agwagwa da buje na shiga nace ya kai ni tsohuwar kasuwa sai na ga kansa yan rawa kamar dan tsuntsu, bayansa kuma da gashi shine nace ya sauke ni yana sauke ni na fito da sauri, sai wannan mahaukacin ya biyo ni”

“Minene kuma Agwagwa da buje?”

Ta kalli wanda tai tambayar da idanuwanta da sukai ja abun ka da farar mace.

“Keke Napep”

“Oh Allah na wata kila aljanine ya dauke ki, kin san fa ance suma suna yin Napep din”

“Ga zahiri na gani, wata kila da bance ya tsaya ba da yanzu na tsinci kaina a Russia ko Iraq”

“Lallai kuwa abun na su ba wuya, to yanzu kina da waya a tare da ke?”

Sai a lokacin ma ta tuna da jakarta, domin wayarta da kudinta har da makullin gidanta suna cikin jakar.

“Na shiga uku Wallahi jakata na cikin napep din aljani nan kuma ya tafi da ita”

A take ta fashe da sabon kuka, domin ta san samun wata wayar ma agareta yanzu abu ne mai wahala.

“Subhanallahi, to kina da number wani akai ko mijinki ko Baba?”

“Babana ya mutu sai dai mijina kuma shi ma ya siyar da wayarsa, yau ina cikin ukuba”

Ta kara fashewa da kuka.

“Baki da number kowa akanki”

“Akwai ta yayata da Mamana”

Sai da ta share hawayenta sannan ta karbi wayar ta saka number Mama tana shiga aka dauka.

“Hello Sallamu Alaikum”

“Mama ina cikin matsala Mama gani a Kano”

“Kano kuma Rafi'a? Gurin me?”

A nan ta labarta mata abun da ya faru, cikin labarin tafi nanatawa Mama cewar wayarta na cikin jakarta kuma ya tafi jakar, da alama ma batan wayarta yafi mata zafi fiye da ganin kanta da tai a Kanon cikin kankanen lokaci, yan kudinta ma duk suna ciki. Kamar wata sabuwar mahaukaciya haka Baturiya ta zama har wani yamutsar kai take.

“Wallahi Takauci be yi ba, daman ance idan mutum ya kwana arba'in be ci nama ba idan yai maka baki zai ya kama ka, gashi nan ai laifin Faruq ne”

“Wanene kuma haka?”

Sai tai shiru bata fada ba, domin bata son tace mijinta ace bata jin magana tun da har ya hanata fita kuma ta fita duk kuwa da kasancewar ba wannan ne karo na farko da ya hanata kuma ta fita ba.
Account din mai POS din unguwar aka karba aka turawa Mama ta turo mata kudin mota, aka ciro mata sai dai tafiyar ba zata yi a yau ba domin yamma ta yi gashi kuma hanyoyin nigeria babu kyau a dole ta hakura sai gobe da safe ta kama hanyar dawowa Zamfara.

Kamar kullum sai bayan sallah isha'i Faruq ya dawo gida. A bakin kofar gidan ya tsaya ya kwankwasa yana sauraren ta bude masa amman shiru bata bude masa ba, ya sake kwankwasa nan ma ba a bude masa ba, yayi haka kusan sau hudu sai a na biyar ya saka makullin hannunsa ya murda ya bude kofar daman can a tunaninsa ko ta rufe kofar ne daga ciki kamar yadda ta saba, sai dai tun a yanayin yadda ya tararda gidan ya tabbatar masa da matarsa bata nan. Yayi sa'a akwai wutar nepa sai ya kunna gulob din waje dana falo ya shiga daki ma ya kunna, tsaye yai yana karewa dakin kallo komai a watse kamar yadda ya fita ya bar shi, daman yana fita ta shirya ta fita bata tsaya gyaran komai ba. Gashi kuma be tararda ita ba, ajiyar zuciya ya sauke.

“Rafi'a Allah ya shirya ki”

Ya furta cikin yanayin dake nuna alamar be jidadin daya sami gidan a haka ba, babu abun da ya fi bakanta masa rai ma kamar tararda ita da be yi ba a gidan, ko da yake halinta ne ko da ba zuwa unguwa ba takan fita makota tai taje can tana hira ko ta rika musu aiki alhalin ga nata aikin na gidanta ta bari, sai dai shi ya kasa sabawa da wannan halin, domin duk mai mata baya son ya shigo gida ya tarar matarsa bata cikin gidan idan ba da wani dalili ba, babu irin fadan da be mata ba amman bata canja ba, har ya gaji ya saka mata ido.
  Gadon ya fara gyarawa sannan ya kwashe kayan data bari ya aje su a guri daya, ya gyara shimfidar Sultan ya dauko tsintsiya ya share dakin har zuwa falo, sannan ya zauna saman kujera ya daga kansa sama yana tunanin halin damuwar daya samu mahaifiyarsa a ciki, kusan kullum uwarsa bata rabuwa da damuwa domin idan babu na abinci akwai na rashin lafiyarta, sai dai a yanzu ta fi shiga damuwar fiye da koyaushe, a da tunanin na yadda zamu samu abun da za su sakawa bakinsu ne ko kuma na maganinta tsabanin yanzu da tunanin aurarda yarta wanda kanwace a gurin Faruq ya hanata sakat, ba Mahaifiyarsa kadai ba, idan aka fasa auren nan shi kansa zai shiga damuwa balle kuma ita kanwar tasa, domin mijin yace ya gaji da daga auren da ake ta yi, su kuma ba su da wani abun aurar da ita a yanzu, sadakin da suka karba da dadewa Mama ta saka shi a cikin kasuwancin da take ta zimmar zata dan juya ko zata samu riba, sai gashi ba wan ba kanen wato ba uwa balle kuma riba, daman sana'ar talaka sai Allah, balle kuma irin nata sana'ar da ake ci ciki.
Bayan matsalar kanwarsa ga matsalar kudin hayan da ke jiransa next week, gashi ba shi da mafitar kudin a halin yanzu, dan aikin da yake ta applying shi ma shiru kamar wanda ya zagi gobnati.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ya furta yana dafe kansa.

“Allah ka kawo min sauki Allah ka yi min mafita”

Ya fada yana mikewa tsaye ganin har goma ta kusa matarsa bata dawo ba, duk yawunta bata wuce tara na dare sai idan biki ake ko kuma wani abu ke saka ta kai dare, ko da makota ta shiga bata wuce 9pm.

‘Ina tunanin tafiya nijar zai fi min gurin ginar zinari, sai dai shi ma ai dole sai ka samu kudi, samun wanda zai baka rance ma a yanzu ai aiki ne’

Ya nufi kofa yana ta sake-sakensa da tunanin inda zai samu mafita. Babu waya a hannunsa balle ya kira ya tambayi inda take domin ya bada wayar jingina tun shekaran jiya ya karbo musu abinci, hakan yasa ya fara nufar gidansu Maman Amira makociyarsu domin Baturiya tafi zuwa can ta wuni saboda suna da rufin asiri daidai gwargwado, ba shi ma ko mutanen unguwar sun shaidi Baturiya da son shigewa masu kudi, idan ka ga tana shiri sosai da mutum to mai rufi asiri ne.
Cikin almajiran dake zama bakin kofar gidan ya kira daya ya aike shi cikin gidan ya kira masa Rafi'a, almajirin na shiga ya fito dauke da Sultan dake bachi ya mikawa Faruq.

“Ance wai bata nan, tun dazun da ta shigo bar Sultan tace zata je kasuwa bata dawo ba, kuma ta kira wayarta a kashe”

Cikin fargaba Faruq ya karbi dansa ya juya yana yi ma almajirin godiya ya koma gida, kwantar da shi yai ya fito waje zuwa gurin mai shagon daya bada jinginar wayarsa.


AMINATU POV.

Sai da yamma lis ta farka, ta dade da farkowa daga

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login