Showing 54001 words to 57000 words out of 133328 words
Zaunawa tai tana haki, ji take kamar taje ta tambaye shi wace yarinya ce sai dai ba wannan damar domin ba ya hira da ita, da ma dai Amal ce ita kam har sirri yake da ita.
“Wace yarinya ce Talba zai kwana da ita a ransa? Ban gane ya kwana da ita a ransa ba, as how?”
Wannan karon a fili tai tambayar tana hade yawun bakinta, sai kuma ta mike tsaye.
“Ko dai yayi ne dan na ji haushi? Amman kuma be taba min haka ba”
Ta dafa kanta tana jin kirjinta kamar zai rabe biyu, ita kamta da akai musu baiko bata tana jin yace ya kwana da ita a rai ba sai wata? Wacece ma? Ba kasafai yake saka mutane a rai ba balle har ya kwana da su amman yace da yarinyar na kwana a raina.
Haka ta sake sake a ranta, wani irin zafi ta ji zuciyarta na mata, irin zafin da bata tana jin irinsa ba, wata kila sabida bata tana jin Talba yana maganar wata mace a gabanta ba, hasali ma ba zata ce ga wata mace da yake so ko take burge shi ba, ko akwai be tana nunawa ba balle har ya fada.
“What if wani abun bacin rai tai masa?”
Ta sake tambayar kanta tana cire hular kanta, sam bata taba sanin wani abu wai shi kishi ba sai yanzu, domin Talba be taba yin maganar wata mace a kusa da ita ba, shiyasa kullum hankalinta a kwance yake bata da haufin komai, sai dai a yanzu tana jinta a cikin wani irin yanayi marar misaltuwa saboda ya furta ya kwana da wata a ransa.
“Ko dai bata masa rai tai, ai be kamata ya kwana da ita a ransa ba, Indai har macece ko yaya ne be kamata Talba ya kwana da ita a ransa ba”
Ta fada tana wasa da wayar hannunta, can kuma ta busar da iskar bakinta ta shiga contact dinta ta nemi number Ali ta kira shi. Kara wayar tai a kunne ta fara safa da marwa, kamin yai picking har ta matsu.
“Hello Leila”
“Ali ya weekend?”
“Alhamdulillah”
“Am akan maganar da kuke da Talba ne yanzu”
“Okay...”
Yayi shiru yana jiran yaji abun da zata ce, sai ta rasa ta inda zata fara ta san duk irin wayon da zata yi ba zai taba fada mata sirrinsa da Talba ba, sai dai idan ba sirri ba ne.
“Ban fahimci abun da kuke magana akai ba, kuma na ga kamar ransa a bace”
“Leila”
“Na'am”
“You should feel free to ask when ever kika ga Talba a damuwa ko matsala, shi ne fa mijin da zaki aura a tare zaku gina rayuwa idan kuna irin wannan zaman rayuwarku ba zata taba yin dadi ba”
“Na sani, amman ka san halin abunka, zan iya tambayarsa ya ki fada min ni kuma na damu ne kawai”
“Ki saka a rayuwarki ba ki da wanda yafi Talba, idan har kin damu da damuwarsa ya kamata ki tambaye shi”
“Zan yi haka, amman for now ina jin akan wata yarinya ce da na nuna masa jiya tana bukatar taimako, yar gudun hijira ce”
Shiru tai kamar mai tunani.
“Subhanallahi, tana ina yanzu?”
“Asibitin mu”
“Okay Allah ya bata lafiya, amman idan ana bukatar taimako Ali kai na gida ne, ka san yadda komai a Foundation din mu yake, ba sai ka sake yi masa magana ba, domin ba zan taba lamunta Talba ya kwana da tausayin wata a ransa ba, an yi na farko kuma na karshe, bana son ya kwana da kowa a cikin ransa sai ni”
“Ameen”
Ya amsa addu'ar da tai a farko yana murmushi, sannan ya aje wayar ba tare da ya sake ce mata komai ba domin ya san kishi ne.
Sai ta sauke ajiyar zuciya tana dan jin sauki a ranta.
“Ranki ya dade, Hajiya ta ce a kira ki”
Ta juyo da sauri ta kalli Mairo, sai kuma ta rufe da masifa domin ba karamin razana ta tai ba.
“Wai miyasa komai ba ku iya yinsa a cikin natsuwa ne? Mi yake damunku ne? Wannan ya zama na karshe da zaki sake kira sunana da karfi I'm not your mate”
Ta karasa tana jan tsaki sannan ta nufi hanyar shiga babban falon, bata ko tsaya kula Mairo b dake aikin bata hakuri. Ko da ta isa dinning din kowa ya hallara har sun fara cin abinci.
“Ina kika je?”
Momy ta tambaya tana kallonta.
“Waya na amsa”
Ta fada sannan taja kujera ta zauna tana mikawa Daddy gaisuwa. Sai da suka nisa da cin abincin sannan Daddy yai gyaran murya ya ce.
“Ina son na yi wata magana mai muhimmanci, Shiyasa na bukaci a shirya mana abun karyawa a nan, musamman mahaifiyarku”
Jin hakan tasa kowa ya kalleshi har Momy.
“Allah yasa ba laifi na yi ba”
“Laifi kika yi kuma babba, laifin da ban saka ran zaki yi ba a matsayinki na uwa, sam ban tsammaci haka daga gareki ba, ban yi zaton rana zata zo da zaki dubi dana ki fada masa cewar ba ke kika haife shi ba...”
Talba ya tsaya da cin abinci ya dago ya kalli Daddy dake maganar cikin tsananin bacin rai, Momy kuma tana kallon Talba a tunaninta shi ya fadawa Daddy abun da ya faru.
“Again?”
Momy ta tambaya tana cigana da kallon Talba rai a bace.
“Ba shi ya fada min ba wacan karon ma ba shi ya fada min ba...”
Kamin Daddy ya karasa Amal ya karba tana kallon Kabir.
“Ni na fadawa Daddy, ni kuma Ya Kabir ne ya fada min”
Momy ta kalli Amal kamin ta kalli Kabir.
“Na ji na yi laifi amman Amal bata fada maka danka yana wuce gona da iri ba?”
Da wani irin karfi da fusata Daddy ya daki teburin cin abinci.
“Da na be yi komai ba Amina... Wannan dalilin ne yasa na tara ku duka anan, saboda Leila ba zan yarda ki rika batawa Mu'azz rai ba, ko da rana daya bana jin ya taba miki wani abu da zai banban taki da uwar data haife shi, akan me zaki zabi raba kan yarana? Ko bana da rai shi zai yanke hukunci a gidan nan kuma shi zai dauki dawainiyar komai, na tara ku a nan ne saboda na ja miki kunne kuma. Yaranki su daina kokarin wuce guri ko da mafarki ban tsammaci zaki iya furta kalaman da kika furtawa dana ba, saboda abun da Amal ta fada min jiya ban samu bachi da kyau ba, ko kadan bana son abun da zai raba kan yayana kuma bana fatan Allah ya nuna min ranar da Talba zai ji bakincikin rashin uwa”
Yana kawai nan ya mike tsaye a fusace ya nufi dakinsa, kowa shan jinin jikinsa yai har Talba din da Daddy yake masifa saboda shi, domin ya san indai akansa ne tsab Daddy zai iya fushi da shi ko yai masa fada. Amal ma tashi tai da sauri ta bi bayan Daddy, domin ta san sakamakonta gurin Momy.
Momy da hawaye ke sauko mata ta kalli Talba tace.
“Mutum baya kuskure ne? Ni kaina na ji cewar ban kyauta ba, na ji cewar be kamata na furta kalaman nan ba”
Talba yayi saurin girgiza mata kai.
“Haba Momy kamar baki san halin Daddy ba? Yanzu zai hau kuma yanzu zai sauko, be kamata wannan ya dame ki ba, kin mu sanin Daddy fa, muma a tare muka bude ido muka ganku please ki yi hakuri dan Allah”
“Ka yi hakuri kai ma, ban kyauta ba na sani, Allah ya muku albarka”
Ameen. Duk suka amsa har Leila sannan ta mike tsaye ta nufi hanyar bedroom din Daddy, hakan yasa Leila ma ta tashi ta nufi hanyar fita daga part din gaba daya.
“Daddy's Boy?”
Kabir ya fada yana kallon Talba, sai Talba yai murmushi kadan.
“Har yanzu Daddy be yarda na girma ba, yana ganina kamar jariri”
“Maybe sai ka yi aure ka haihu ya ga ka fara bawa yayanka kulawa”
Ya dan tabe baki kadan.
“Ni ma ina son ganin haka, you know i love children alot, but before then ya kamata ka iya bakinka, Amal parrot ce ba komai ake fada mata ba, yanzu kaga abun da taja mana”
“Da gangan na fada mata ai, saboda na san zata tseguntawa Daddy, sincerely speaking Momy bata kyauta ba, she shouldn't say that, we're one family be kamata tai haka ba, rai na be taba baci irin jiya ba”
Cewar Kabir with serious face. Talba ya dauki tea gabansa ya sha kadan.
“You know mata suna da rauni Kabir, kuma tunaninsu gajere ne, shiyasa ba a zure musu kuma ba a kuresu, idan bama dauke kai ga wasu abubuwan zamu yi ta ji da ganin abun da bama so, ya kamata ace muna yafiya da manta kuskure, no body above mistake”
“Yeah wani lokacin kuma muna yin abu saboda ya zame mana darasi so that kar mu sake aikata shi nan gaba”
Murmushi kawai Talba yai be sake cewa komai ba, ya cigaba da cin abinci har sai da ya koshi sannan ya mike tsaye ya dauki wayarsa ya nufi kofar fita yana jin wani irin kaunar Daddy, ji yake yafi kowa sa'a a duniyar domin ba kowa ke samu uba kamar yadda shi ya samu nasa ba, kaunar da Daddy yake masa bata misaltuwa shi kansa ya sani.
Fitowa yai daga bangaren gaba daya ya nufi bangarensa, yadda ya tsaya yana kallon harabar gidan sai rantse da Allah yau ya fara ganin gidan, sai hankalinsa na can wani gurin daban ya dade a tsaye sannan ya karasa entrance din ya murda kofarsa ya bude. Yana shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin shadda milk color ya saka hula sannan ya saka wallet dinsa da wayarsa aljihu da ya fito rike da makulli mota ya ja kofar.
Leila na tsaye jikin window dakinta tana kallonsa da murmushi a fuskarta har ya shiga motarsa ya danna horn aka bude masa ya bar gidan.
Sai ya fara biyawa ta shagon da yake siyen sweet da chocolate din da yake zuwa da su gidan marayu sannan ya wuce gidan abokinsa Ali domin a tare suka saba zuwa, wani lokacin Ali zai zo ya dauke shi wani sa'in kuma shi yake zuwa ya dauki Ali kamar dai yau. A bakin gate din gidan ya faka motarsa sannan ya ciro wayarsa ya kira Ali, Ali na yin picking sai ya kashe wayar ya aje. After like 5 minutes Ali ya fito ya bude motar ya shiga, Talba yai reverse sannan suka hau titi.
“Ina yara?”
“Lafiya Kalau Gwauro”
Ali ya amsa masa yana kallonsa fuskarsa da dariya. Talba be sake cewa komai ba har suka kusa isa sannan Ali ya dauko masa zancen Aminatu.
“PA ka ya turo kudi dazun Allah ya saka da alheri”
Nan ma Talba be ce komai ba, har sai da Ali ya dauko masa zancen kiran da Leila tai masa dazun yana murmushi, sannan ya kalleshi.
“Da kai tai waya da safe kenan?”
“Yeah kishi take wai ba zata iya daukar ka kwana da wata a rai ba”
“And...”
Ali ya kalleshi.
“And she's right”
Tabe baki Talba yai be sake cewa komai ba har suka isa gidan marayun, tun kamin ya karasa harabar yaran suka nufoshi a guje suna murna da zuwansa, murmushi ne ya cika fuskarsa farinciki marayu na daga cikin abun da yake faranta ransa, musamman kananan domin Talba mutum ne mai matukar son yara. Da sauri ya bude motar ya shafa kansa yana tambayar lafiyarsu, sannan ya mika hannunsa ya dauko alawar daya siyo musu ya bude ya fara raba musu.
“Uncle ni dai chocolate nake so”
Wata yar karamar yarinya ta fada, sai ya amsa mata in a funny way yana dariya kamar ba shi ba.
“Noooo chocolate dai anjima idan zan tafi”
Ali ya bude dayan side din ya fita yana amsa waya.
“Subhanallahi gani nan zuwa”
Ya fada sannan ya saka wayar aljihu ya zagayo side din da Talba yake zaune a motar.
“Zan barka nan na tafi asibiti”
Wani kallo Talba yai masa wanda ke nuna alama ce ta tambayar lafiya.
“Wai yarinyar nan aka samu ta suma hannunta nata zubar da jini kuma robar karin ruwa murde a wuyanta kamar an shaketa”
Shiru Talba yai fuskarsa da mamaki sannan ya fito cikin motar gaba daya.
“You can go with my car”
“Thank you”
Ali ya fada sannan ya shiga motar da sauri, Talba ya bude baya ya dauko ledar chocolate din sannan ya rufe har lokacin fuskarsa dauke take da mamaki, bin motar yai da kallo har sai da Ali ya fita gate din sannan ya maida dubansa gurin yaran sai dai gaba daya hankalinsa ya tafi akan dalilin da zai saka yarinyar ta aikata haka, he don't even think zata ma iya aikatawa kanta haka sai dai idan wani ne ya kashe ta ko kuma yake kokarin kasheta.
Be wani dade sosai kamar yadda ya saba yi ba domin hankalinsa gaba daya ya tafi gurin yarinyar, and baya son azahar tai masa a nan saboda a tare suke cin abincin rana da duka Family kamar yadda suke yi da safe on every weekend sai dai idan akwai wani uzuri. After like 2 hours da wucewar Ali ya turawa direbansa sakon inda yake. Sannan ya bude chocolate din ya shiga raba musu yana Murmushi kamar ba shi ba.
Bayan ya gama yai musu bankwana suka rakoshi har gurin da direban ya faka motar, domin ya dade a zaune cikin motar yana jiran Talba. Kamin ya karaso direban ya fito ya bude masa motar bayan ya shiga ya rufe, ya ya zagaya da gudunsa ya shiga driver side ya ja motar suka nufi gida.
Tafiyar minti talatin suka iso unguwar
shimkafi Quarters, Talba na hakimce cikin motar har direban ya faka motar a kusa da entrance din kofar Momy. Kamar ya bude baki ya ce ma direban ba bangaren Momy zai fara shiga ba, sai kuma ya ji ba zai iya ba, sai da direban ya bude masa motar sannan ya fito ya nufi bangarensa.
Yana shiga ya bedroom dinsa ya bude bathroom yai alwala ya fito yana rike da agogon hannunsa, a inda ya saba aje shi ya aje sannan ya nufi inda Capet dinsa ta sallah take shimfide yai ikama ya fara gabatar da sallah nafila. Kamin ya sallame limamin gidansu ya fara kiran sallah hakan yasa yana sallamewa ya fito daga bangarensa ya nufi masallaci gidansu inda dukansu suke sallah da kuma ma'aikatan gidan.
Bayan saukowa daga sallah azahar ya nufi bangaren Momy sai kamshi turare yake kamar wanda ya lullube jarkar turaren a jikinsa. Sai da ya danna door bell din sannan kuma yai knocking sai ga Zulai da gudunta ta bude masa.
“Sannu da zuwa ranka ya dade”
Kai kawai ya daga mata sannan ya nasa kafarsa cikin falon, saman sofa ya zauna yana kallon Plasma dake ta aikinta, babu kowa a falon sai Leila dake zaune a dinning rike da waya, yana shigowa sai duk hankalinta ya tattara ya koma kansa. Be yi minti biyar da zaman ba aka sake danna door bell din, Mairo dake kitchen ta fito da gudu ta nufi kofar ta bude, daman idan ba yan aikin gidan ba ko Kabir sai Amal sune kawai suke iya bude kofa idan ana kwankwasa, Leila tana ganin ta fi karfin haka, Talba kuma jin kai ba zai bar shi ba.
“Baaba na nan?”
“Ban santa ba gaskiya”
Shiru yai yana kallon sabuwar yar aikin domin be taba ganinta ba, duk kuwa ba da yawan zuwa yake gidan ba amman dai akan aikoshi daga kauye gurin Kakarsa Baaba dake aikin gidan, hakan yasa police din dake gadin gidan suka san shi basa hana shi shiga a duk lokacin da ya zo.
“To Hajiya fa?”
Ya sake tambaya, sai Mairo ta amsa masa.
“Eh tana nan wa za a ce mata?”
“Ki ce mata Shamsu ne jikan Baaba”
“Toh”
Ta saki kofar falon dake bude ta nufi hanyar upstairs. Leila a hango shi ta mike tsaye da sauri.
“Ki ce masa Baaba bata nan”
Ta fada kamar wanda ya rikice. Mairo ta juya da sauri da zimmar fada masa, sai Talba ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu. Mikewa yai tsaye ya nufi kofar Leila na ganin haka ta nufi upstairs da gudu.
Shamsu na ganin Talba ya dan risina masa yana gaishe shi.
“Shamsu”
“Na'am ranka ya dade ya gida?”
“Alhamdulillah, lafiya dai?”
“Lafiya Kalau, daman daga can gida ne suka ce na zo na duba Baaba ko lafiya kwana biyu ba a samun wayarta”
Kamar an dasa ice haka Talba ya tsaya jikin kofar yana kallon Shamsu da mugun mamaki, kwakwalwarsa ta cika da tarin tambayoyi, sai ma ya rasa abun da zai ce wa Shamsu.
Yawun bakinsa ya hade a hankali yana kallon Shamsu har ya bude baki zai yi masa magana sai ya ji muryar Momy dake saukowa tana kiran sunan Shamsu da far'arta, abun da bata saba yi ma talaka ba musamman wanda yake karkashinta.
16
*Khadeeja Candy*
Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
*Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
“Shamsu ne?”
“Eh Hajiya ina wuni?”
“Lafiya kalau shigo mana”
Talba ya juyo tana kallon Momy dake amsa masa da far'arta kamar ba ita ba. Sai kuma ya juya ya kalli Shamsu dake kokarin shigowa.
“Baaba ka zo nema...?”
Kamin Shamsu ya ce komai Momy ta daka masa tsawa.
“Talba ka barshi ya huta ya sha ruwa mana, Mairo akai shi karamin falo a kawo masa ruwa”
Momy ta karasa