Showing 42001 words to 45000 words out of 133328 words
idan kuma babu sai ki yi hakuri har Allah ya kawo”
Sai ta mike tsaye.
“Tsakani da Allah Faruq kana cutar da ni, yanzu haka zan yi ta zama cikin matsi? Kamar mu muka fi kowa? Duk wani abun da nake so baka iya siya min sai idan na siyawa kaina ko kuma an aiko min daga gidanmu, ni gaskiya na gaji kana cutar nan kuma na san Allah zai saka min domin baya son zalinci”
“Gaskiya ne, Rafi'a baki da tunani ko kadan, kan mu farau talauci? Ko kuma mutum yana yi ma kansa arziki ne? Halin nan naki ya ishe ni..!”
“Da ya isheka da ka sauwake min, da ya isheka da ka samawa kanka mafita, tsakani da Allah Faruq idan ba kaddarar aure ba babu abun da zai hada ni aurenka, daman can na dauka zaka samu aiki rayuwa ta tafi mana da kyau, ashe hauka nake, gashi na gagara samun abun da zan ci ma”
“Saki kike so?”
“Eh saki nake so, ka sake ni Faruq ka sake ni idan ka haihu”
“Zan nuna miki na haihu”
Yana fadar hakan ya wuce cikin dakin da bokitin ruwan ya shiga bandaki ya watsa ruwan ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya dauki makullin shagonsa ya saka aljihu, dayan aljihun kuma ya saka wayarsa, ko da ya fito tana zaune falon tana jiran ya mika mata takardar sakinta, tana ganinshi gabanta yai mugun faduwa.
Be kulata ya nufi kofar fita daga falon yai ficewarsa rai a bace.
Sai da ya fita sannan ta tashi ta fita ta rufe gidan ta dawo falo ta zauna, can kuma ta tashi ta fita ta dauko ludayi ta zo ta zauna ta bude kokon ta mutsa.
“Ba zan saka sugan ba”
Ta fada tana wurgar da kullin sugan ta fara shan kokon lami ba suga, ludayi biyu tai sai gata ta tashi ta nufi inda kullin sugan ya fashe ta kwaso a hannun ta nufo kokon ta zuba, ta zauna ta fara sha. Rabi ta sha ta bar ba Sultan dake bachi rabi, domin ta san bayan ya sha yanzu da rana ma zai iya nema.
Tashi tai ta koma saman kujera ta zauna, ta mika hannu ta dauki keypad din da Umma ta siya mata kamin ta siya mata smartphone, tsaki tai bayan ta shiga contact dinta ta fito ta shiga inbox dinta, nan babu komai domin sabun line ne da tai welcome back, hakan yasa ta ji babu dadi domin wanda ya saba rika babbar waya yana chatting idan ya rasata zai ji kamar ya koma a wata karamar duniya.
“Allah tsinewa Aljanin nan, ya dauke ni ya kai ni Kano kuma gashi nan ya rasa wayata da atm dina da yan kudina, Allah kasa min, Wallahi Faruq be da kashin arziki gashi nan na rasa komai”
Ta fashe da kuka. Kamar jira ake ta fara kukan sai ga kiran Ramlee ya shigo wayarta, share hawayenta tai sannan tai picking call din ba dan ta gane mai kiran ba domin number babu suna.
“Hello”
“Baturiya ya kike?”
“Lafiya kalau Ramlee ce?”
“Ni ce fa baki gane ni ba?”
“Number ba suna wayata ta bata ne na yi welcome back kuma numbers din ba su dawo ba”
“Garin ya? No wonder na yi ta kirankin number ki ban samu ba, na yi mamaki domin na san baki kashe waya”
A nan Baturiya ta labarta mata abun da ya faru, sai Ramlee ta saka mata dariya.
“Farin jininki yayi yawa Baturiya abun har da su Malam aljani? Shiyasa na ji muryarki wani iri kuka kike ne?”
“Ba dole ba Ramlee ina cikin matsala, ina son na ci da dadi na saka mai kyau amman abu ya garara, yanzu ko wayar nan tawa da ta bata ai daidai ne ya siya sabuwa amman sai da Umma ta siya min karama”
“Fee'at kenan, wannan fa duk kika so, da kin yarda da yanzu kin dangwali arziki har ma ki raba mijinki ciki, Wallahi Baturiya da zaki sake jiki yadda kike da kyau nan da har kyautar gida sai kin yi ma wasu”
“Ramlee ina fa da aure har da”
“Mace nawa ce mai yaya uku hudu har biyar take biyawa kanta bukatar da jikinta? Ke ko a unguwarku idan aka ce za a bude wasu matan auren ki ga sirrinsu zaki sha mamaki Wallahi, ba ki san cewa aure yana rufa miki asiri ba? Ko da kin samu wani abu ba za a zargeki ba? Yadda kike da kyau nan Baturiya ba ke ba ko ni da maza suke ganin hotunanki a wayata suna hauka sai na samu arziki, wai kin san ma dalilin daya saka na kira ki?”
“Sai kin fada”
“Wallahi wani ne ya sake ganin hoton ki yace kina cikin irin matan da yake so, na fada masa ke ba irin mu bace amman ya saka ni gaba wai na lallaba masa ke dan Allah, kuma babbar mutum ne dan siyasa, yanzu haka haka 100k ya bani wai na baki na wankan hoton da kika yi”
Baturiya ta mike tsaye tana dokan kirji idonta kamar za su fito.
“Dubu dari fa kika ce Ramlee”
“Wallahi ga su nan, tun shekaran jiya ya bani su jiya ma daker ya bar ni na yi bachi sai damuna yake da maganarki a waya kamar zai min kuka, shiyasa ma na kira ki da safen nan, Allah yasa ma mijinki baya nan”
“Baya nan ya aje min wani shegen koko ya fita”
“Kin gani yanzu da kina da kudi sai abun da ranki yake so zaki ci, idan kina free anjima zan zo na dauke ki a motata muje na siya miki sabuwar waya”
“Da kudin?”
“Aa da kudina dai, wacan kudin a cewa yai a baki kuma zan danka miki abun ki a hannu, amman ki yi tunani idan kika bada kai me kike ganin zaki samu? Bayan shi ma akwai maza da yawa musamman ace kina samun sakewa ana zuwa da ke hutu abuja ko kasar waje? Hmmmm Hajiyata ai kin take”
“To zunubin fa?”
“Allah gafurun raheem ne, kuma ban ce zaki dauwama a haka ba idan kin yi kin samu dan abun da kike so, sai ki daina amman ki yi tunanin future dinki dana yaronki koma nace yayanki na nan gaba Baturiya”
“Shikenan zan yi tunani”
“Yauwa Tawan haka nake son ji, ki yi tunanin kamin na zo kin ji? Yau ko wayar 500k kike so zan siya miki ita da yardar Allah”
Baturiya ta yi murmushin jindadi.
“Na gode kawata Allah ya bar min ke”
“Ameen Allah ya bar mu tare”
“Ameen”
Ta sauke wayar tana ta murna.
“Bari na yi sauri na gyara gidan kamin ta zo”
Ta dauki zane ta fara kabe kujerun, sai ta ji an kwankwasa kofar gidan, saurin saving number Ramlee tai sannan ta goge kiran da tai mata domin a tunaninta Faruq ne ya dawo. Sannan ta nufi kofar gidan ta bude sai tai arba da Malam Musa dilalin, cikin mutunci suka gaisa duk da kasancewar babu mayafi a jikinta sai hullar dake kanta.
“Mai gidan yana nan kuwa?”
“Aa ya fita”
“Oh dan Allah idan ya dawo ki ce masa na zo maganar kudin hayar nan, masu gida sun matsa, ko jiya da dare masifa yake ta min domin ganin yake kamar an bani kudin na kashe ne”
“Idan ya dawo zan fada masa, dazun ma yake cewa da ya ganka da ka saka masa number mai gidan domin yana son yai magana da shi”
“Indai maganar haya ne kar ma yayi domin Alhaji Sule be da mutunci ko kadan”
“Aa karka ce haka Malam Musa, bari na dauko wayar”
Kamin ya sake cewa wani abu ta juya da sauri ta koma cikin gidan ta dauko wayarta ta mika masa.
“Saka masa number a nan”
Be karbi wayar ba, ya ciro tasa wayar ya karanta mata number ta saka a wayarta.
“Idan ya zo zan fada masa sai na ba shi number”
“To yayi na gode”
Ta rufe gidan tana murmushi ta dawo falonta tana kokarin saving din number.
“Ba Alhaji Sule kake ba ko Alhaji lule kake sai na ci ubanka, talauci ya matsa shi ne kai kuma zaka kunno mana wata wutar dan kana da shegen tsohon gida”
Ta fada tana ƙwafa.
FARUQ POV.
Ya lalaba aljihunsa ya ciro naira 100 da ta rage masa ya mikawa Aisha.
“Je ki siyo koko ku sha”
Aisha ta saka hannu biyu ta karba.
“Yaya Wallahi ko jiya Mama ba tai bachi ba, yanzu ma jikinta zafi yake”
Ajiyar zuciya ya sauke.
“Jarabawa ce, ga rashin kudi, ga rashin mata ta gari, ga rashin lafiya Alhamdulillah”
Ya fada yana kallon mahaifiyarsa dake lullube bata ma san ya zo ba, karasa yai kusa da ita ya yaye mayafin data lulluba da shi ya taba jikinta sai ya ji shi da zafi sosai.
Mikewa yai tsaye ya fito daga dakin cikin wani irin yanayi na rashin jindadi. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya rike a hannu yana kallo, ya san ko siyar da ita yai kudin ba zai isa ya kai Mama asibiti ba, jinginar daya bada ma daker ya samu ya biya mutumen ya karbo wayar. Bakin kofar dakin ya zauna ya dafe kansa, yana mamakin lamarinsa wani lokacin shi kansa abubuwa suna daure masa kai, ga karatu yayi kuma ya fito da kwali mai kyau amman aiki ya gagareshi, wadanda sukai karatu tare wasu duk sun samu aiki har sun bar kasa, wasu kuma suna Abuja wasu a manyan mukana gobnati wasu a manyan bankuna da kamfani amman shi ya kare a shagon Barber, shi ma daker ya samu wani kawunsa ya bude masa shagon.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allah ka kawo mana sauki”
Ya furta yana dago kansa ya shiga contact dinsa ya nemo number abokinsa kuma amininsa Nura.
Wayar bata dade tana ringing Nura ya dauka.
“Hello Faruq”
“Na'am Nura ya gida?”
“Lafiya kalau kwana da yawa”
“Sai godiya, ina su Sakina”
“Lafiya kalau”
“Wallahi Nura ina cikin matsala”
“Subhanallahi miya faru?”
“Abubuwa da yawa, yanzu dai wanda ya fi damuna rashin lafiyar mahaifiyata, kudi nake so rance idan zan samu na kaita asibiti”
“Kash.... Wallahi Faruq yau da 500 na tashi na basu su karya, ka san abu ga ma'aikaci idan ba albashi akai ba, ba mu da kudi, kuma gashi albashin na jihar zamfara sai a hankali anki a gyara mana, ga kayan masarufi sai tashi suke, abun da zaka siya da 20k yanzu sai 40k shiyasa albashin baya mana auki”
“Haka ne, Allah ya sauwake”
“Ameen, amman da zaka iya da kaje gidan Alhaji Mu'azu Shimkafa ance suna da Foundation na taimakon marayu da mabukata, amman idan baka jin kunya kasan wasu basa son zuwa irin abu na neman taimako”
“Haba Nura ina zancen kunya ga mai nema, suna nuna mutun a tv ne?”
“No babu ma wanda zai san an maka, amman ance Dattijon yana taimako sosai gaskiya, ban san yadda ake bi ba, amman dai idan kaje can gidansa ba rasa taimakon da zai maka ba, har aurarwa suna yi ga marayu su masu komai”
“Ai ban sani ba, ina dai jin ana fadarsa Tsohon Minister kudi ko? Ban san yana taimakom nan ba Wallahi, amman zan je yanzu Inshallah na gode sosai”
“Allah yasa a dace, ya bata lafiya anjima zan shigo na dubata Inshallah”
“Okay”
Ya dauke wayar daga kunnesa ya mike tsaye da sauri sai a lokacin ya tuna da be tambayi unguwar da yake ba. Hakan yasa ya sake kiran number Nura.
“Baka fada min sunan unguwar ba?”
“Shimkafi Road, kana shiga unguwar kace gidan Alhaji Mu'azu Shimkafi kake nema, za a nuna maka”
“Okay”
Ya saka wayar aljihu be ma koma cikin gidan ba ya nufi titi, da kafa ya taka tun daga gadar gaba har unguwar Shimkafi road, akwai tazara amman a haka yai ta cin kasa saboda babu ko naira aljihunsa.
Kamin ya karasa shiga cikin Quarters din wayarsa tai ringing, yana ciro wayar ya duba, a take gabansa ya fadi ganin number Malam Musa Dillali, hakan nan dai ya daure ya dauka.
“Hello”
“Hello Faruku haka ake daga karbar number sai ka ba matarka ta ciwa mutun mutunci?”
Tsaya yai daga tafiyar da yake fuskarsa da mamaki.
“Wane mutum kuma?”
A nan Malam Musa ya fada masa yadda sukai da Baturiya dazun sannan ya dora da abun da mai gidan ya fada masa.
“Wata kila kiransa tai ta ci masa mutunci, yanzu ya kira ni yana ta masifa wai wata ta kira shi Baturiya ta zage shi, ya baku daga yau zuwa gobe ku tashi ku bar masa gidansa”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Wallahi Malam ban san Matata zata yi haka ba, kuma Wallahi ban ce zan karbi number sa ba”
“To yanzu dai sai ku san abun ba, Baturiya ko balaraba ta ja maka”
Malam Musa na fadin haka ya kashe wayar, Faruq ya dafe kansa.
“Na shiga uku wai me ke damun Rafi'a ne? Ta sake janyo mana wata fitinar kuma? Ina ruwanta da mai gida?”
Wani irin kololon bakinciki ne ya taso masa, sai ya ji kamar na runtse ido ya bude a gansa a kabari ya huta, yana fama da wasu matsalolin yanzu kuma ta ballo masa wani.
“Wallahi yau sai na miki mugun duka, Rafi'a sai kin dawo hayyacinki in ma baki da hankali sai kin yi shi”
Ya fada rai a bace, duk abun da take masa na bacin rai bata taba mata masa rai irin wannan ba, domin be san inda zai je ba idan ya bar gidan haka nan ya cigaba da tafiya ransa a bace. Da tambaya ya aka nuna masa kofar gidan Alhaji Mu'azu Shimkafi, Gate din gidan kadai a abun kallo ne, balle kuma farar ginar da aka kawata da farin fenti ga shuke shuke itatuwa da fulayoyi, idan ka daga kanka kuma sai ka hango gidan sama daga can cikin gidan an kawata ko'ina da gilasai komai a tsare kamar ba za a mutu ba. Faruq ya girgiza kai.
“Allah man yasha'u, ka baiwa bawa ba dan kana son shi ba, kuma ka hana Bawa ba dan baka son shi ba, Allah ka bamu na mu arzikin na halal, yanzu nan gidan mutum daya ne”
Ya fa da yana mamakin tarin dukiyar dake gidan. Karasa yai bakin gate din yana kallon security cameras daka laka hagu da dama na gidan sannan ya kwankwansa kofar gate din. Ba dade wani police ya bude masa yana sanye da uniform dinsa.
“Malam Lafiya?”
Faruq ya mika masa hannu suka gaisa cikin mutumci.
“Dan Allaj ina son ganin mai gidan ne matsala ce da ni”
“To ganin mai gidan a yanzu ai, sai an jira domin be fito ba, idan zaka iya jira a nan wajen idan ya fito sai ka tare shi da matsalarka, duk dai baya son a ana mishi haka amman karka nuna masa na san da zuwan ka”
“Ba Matsala na gode sosai”
Faruq ya nemi wani gurin ya zauna a nan kusa da gate din, shi kuma police din ya koma cikin gidan ya maida gate din ya rufe. Be yi minti talatin da zama ba, aka sake bude gate din sai dai wannan karon gate din gaba daya aka bude ganin mota zata fito yasa yai saurin mikewa tsaye a zatonsa mai gidan ne sai ya nufi motar da sauri, ganin ya nufota yasa ta tsaya ta sauke gilashin motar tana kallonsa.
“Ya akai?”
“Daman na dauka mai gidan ne shi nake son gani”
“Saboda me kake son ganinsa?”
Ya tambaya tana kare masa kallon from head to toe.
“Taimako nake nema”
Hannu ta saka ta cire katon gilashin idonta.
“Okay idan ana neman taimako sai azo har kofar gidan mutum a takura masa? Baka san yadda zaka bi ta Foundation ba? Ba ma taimako a gida sai ta karkashin kungiya, kaje can ka samu kungiya karka sake zuwa nan, Talauci ba hauka ba ne”
“Haka ma Arziki ba hauka ba ne malama, karki nemi fada min maganar banza saboda na zo nema a gidanku, ni ba wulakantaccen ba ne”
“Really”
Ta bude motar ta fito tana masa wani banzan kallo.
“Dubi ka! Ka zo nema a gidanmu kuma kana cewa kai na wulakantacce ba ne? To waye kai? Kai kama isa ka zo nema a gidanmu kuma fada min maganar banza?”
“Maganar banza ana furtata ne a lokacin banza kuma ga mutanen banza irinki”
“Ni...”
Ta nuna kanta Faruq ya daga mata kai cikin bacin rai daman be gama wankewa daga na matarsa ba ita kuma tana neman kara masa wani, hannu ta daga zata mare shi sai ya rike hannun da mugun karfi ya jefar da shi.
“Kika kuskura kai hannunki a fuskata sai na illataki, dan ina neman taimakonku ba shi zai baku damar wulakanta ni ba”
Bata sake ce masa komai ba ta juya da sauri ta isa gurin gate din ta buga da karfi, daman Police din ya rufe gate din a lokacin daya bude mata ta fita, da sauri ya bude sai ta nuna masa Faruq.
“Ku rike mutumen can”
Da sauri ya fito shi da wasu Police din biyu suka nufi inda Faruq yake tsaye suka rike shi, ita kuma ta nufi cikin gidan da saurinta kamar zata tashi sama, Talba dake kokarin tashin motarsa yana kallonta ta danna door bell din kofar be kula ta ba ya ja motarsa zuwa gate ya hanna horn, dai dayan Police din ya dawo ya bude masa gate din ganin suna rike da Faruq ga kuma motar Leila dake bude a kunne yasa shi tsaya ya sauke gilashin motarsa.
“Lafiya?”
“Wallahi ba mu san abun da ya faru ba, Hajiya Leila ce tace a rike shi”
Talba ya kalli Faruq daga sama har kasa, be masa kama da yan ta'addaba, kuma ya san halin yar'uwarsa mafi akasari fadan da take da mutane ita ce bata da gaskiya. Hakan yasa shi tambayar Faruq dake kokarin fisge kansa daga rikon da Police din suke masa.
“Malam Lafiya?”
“Lafiya ce zata saka Police rike ni? Daman idan za ku taimaki mutum sai kun wulakanta shi”
Faruq ya fada cikin fusata, hakan yasa Talba ya bude motar ya fito ya nufo inda suke tsaye.
“Ku sake shi”
Ya fadawa Police din sai suka saki Faruq, Talba ya saka hannayensa aljihu yana kallon Faruq.
“Bari na fada maka wani abu, ba a min tsawa kuma ba a fada min bakar magana, amman na maka uzuri saboda na fahimci kana cikin bukatar taimako ne, and bana son na yi ma mutun wani abun ta dalilin taimako, da ace a hanya na hadu da kai da zan iya maka cin mutunci fiye da kima, now