Showing 3001 words to 6000 words out of 133328 words

Chapter 2 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

453

Middle Ads

tsaye a fusace har tana jefa da empty cup din dake gabanta, a take ya fadi kasa ya fashe, kamar zata tashi sama haka ta nufi upstairs. KB ya wara ido.

“To ni ina ruwana, can ta matse muku, a takaice dai ni kadai zan karya a yau... Fine”

Ya sake bude wata kular ya shiga zubawa kansa ferfesu.



FARUQ POV.


Ya aje kofin garin dake hannunsa yana kallon dansa.

“Ka koshi ko?”

Sultan ya daga masa kai yana murmushi kamar yadda shi ma yake masa murmushin. Faruq ya dauke shi ya dora saman kafafuwanta sannan ya kalli Mahaifiyarsa cike da damuwa.

“Mama bari mu tafi kar dare yai mana”

“Kara ka tafi da wuri kam tun da a kafa zaka je”

Ya mike tsaye.

“To sai da safe ayi ta mana addu'a dai”

“Addu'a ai dole ce Faruq, Allah ya tsare, Sultan sai da safe ko?”

“Sai da safe Mama”

Sultan din ya fada da muryarsa da be gama kwarewa da iya magana ba. Daukarsa Faruq yai ya fice daga gidan, a kafa ya taka tun daga unguwar dallatu har Gadar Baga, ganin Sultan ya fara bachi sai ya dora shi a kafada Faruq, yana tafe gabansa na faduwa har ya iso gidansa. Sai da ya saka hannunsa aljihu ya lalaba garin kwakin dake cikin aljihun wandonsa da sugar ya tabbatar suna nan sannan ya kwankwasa kofar gidan. Yayi kusan rabin awa a tsaye sannan Rafi'a ta bude masa. Ganin babu komai a hamnunsa yasa ta ja tsaki.

“Mtcheesss”

Be ce mata komai ba ya saka kafarsa ya shigo cikin madaidacin gidan na zaman mutum daya, sannan ya maida kofar gidan ya rufe. Da sallama ya shiga cikin falon amman ta ki amsa masa sai latsar wayarta take kamar bata san da shigowarsa ba. Be damu ba domin in da sabo ya saba da halin matarsa. Dakinsu ya shiga ya kwantar da Sultan sannan ya dawo falo ya zauna kusa da ita, kana ya ciro garin da ba zai wuce gwangwani daya da rabi ba da surga ya mika mata.

“Ga dan abun da muka samu”

Daga shi har garin kallon uku saura kwata ta watsa masa.

“Gari fa nake gani Faruq?”

“Shi ne”

Ya amsa mata kamar wani yaronta.

“So kake jinina ya tsotse ne? Kara min jinin ma ya gagara? Haba Faruq, na wuni ban ci komai ba kuma yanzu ka shigo min da gari?”

Ta masa maganar kamar zata fashe da kuka, ya sauke ajiyar zuciya a hankali.

“Haba Rafi'a tun da kika ga na shigo miki da gari ai kin san ban samu komai ba ne, shagon na mu sabuwar unguwa ce ba a samun ciniki sosai, tun da na fita har babu wanda ya zo aski, wannan garin ma sai da na biya ta gida Mama ta siyo min aka jikawa Sultan ya sha sauran ne na kawo miki, Wallahi ni tun karin safe da na yi ban sake cin komai ba, kara ke na bar miki gwangwani biyu na wake...”

Be marasa ta mike tsaye tana masa ihu.

“Kai ka so Faruq kai kaso zama da talauci, sa'aninka suna can sun gina manyan gidaje wasu na da manyan motoci, su ci mai kyau su saka mai kyau, amman kai dube ka? Suturar kwarai ma ta gagareka, ni kaina da nake matarka ina kunyar a tararda ni a gidan nan, gida duk ya lalace, da an yi magana kace komai zai wuce sai yaushe zai wuce? Shekara biyar fa da aurenmu Faruq, ka dube ni ka gani tsabar kyau Baturiya ake ce min fa! Amman na kare a aurenka, auren kaddara auren cin garin kwaki, dan sunan mai dadi ma baka iya kirana da shi ba, Rafi'a Rafi'a, Fee'ah Fee'ah haka ake kirana ba Rafi'a ba”

Ta nufi dakinta a fusace, shi kuma ya lumshe idonsa yana jin zafin maganar da ta fada masa. Yana zaune a falon har 11pm na dare sannan ya tashi ya rufe kofar falon ya kashe wutar ya shiga dakin ya shiga bathroom yai fitsari ya wanke kafafunwasa da fuskarsa sannan ya dawo dakin ya kwanta bayanta, can kuma ya tashi zaune yai ma dansa addu'a sannan ya kashe wutar dakin, ya dawo bakin gadon inda ya saba kwanciya yai tasa addu'ar, ya ciro wayarsa ya aje a gefensa ya kwanta, a hankali ya kai hannunsa ya fara shafata sai ta buge masa hannun ta tashi zaune.

“Miye haka? Ka dawo min da garin dan jinina ya tsotse, kuma yanzu ka zo min na maka me? Da safe kuma dan ka ya dame ni da kayan fitsari tun da an gagara sai masa pampas, ga wannan tsinannen cikin wahala da yake jini, haba duk ni kadai? Wai kai baka da imani ne?”

“Rafi'a wai miyasa bakinki ba shi da linzami ne?”

Ya fada a fusace yana kokarin danne fushinsa.

“Shi bakin nawa ai haila yake, kai kudi ka gani idan zan maka duk wannan, su masu kudi ka ga matansu na musu haka ne? Saboda sun ba su komai gurin kwanciya ma dakin yara daban ake amman kai ka hade ni daki daya da yaronka, anjima kace min na taso muje falo ko? To ba zan je ba”

Sauka yai daga saman gadon gaba daya ya fice daga dakin, be tsaya a falo ba tsakar gidan ya fita gaba daya ya zauna saman turmi ya daga kansa sama.

“Kun faya kun sai kai Allah”

Ya fada yana kallon yadda taurari suka kawata samaniya.
Rafi'a na jin ya fitarsa tai azamar dauko wayarta touching, ta dauki keypad dinsa ta shiga contact list tana neman wata number.
MD Saleh a dai dai gurin ta tsaya ta bude sunan ta kwashe numbers din sannan ta maida wayar ta aje, sai tai saving number da Maryam Dahiru Sokoto, kana ta saka wayarta a silent ta kwanta.






________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
*💔 BAKAR WASIKA 💔*


By Khadeeja Candy


Page -2️⃣

“Akwai abubuwa da yawa da rayuwa bata iya tafiya sai da su, a ciki akwai numfashi ci da sha, da kuma soyayya. Bana jin zan iya rayuwa idan babu kai a kusa ni, zan iya rasa ci da sha kuma na rayu da soyayyarka”

Ta nade wasikar da ta gama rubutawa da hausar azami, tana murmushi sannan ta mike tsaye ta maida biron da littafin cikin jakarta ta islamiya ta rataya a jikin kusar dake gurin sannan ta saka hijabinta ta fito.

“Inna an gama?”

“Auta tun dazun na gama, kin yi sallah dai ko?”

Ta saka wasikar a cikin jikinta tana murmushi.

“Inna ke ma kin san bana wasa da sallah fa”

“Haka ne, Auta Allah ya miki albarka”

Inna ta fada Baba da ke zaune saman tarbarma yana sauraren redio ya amsa da Ameen yana murmushi. Sanusi ma dake aikin auna tuwon dawo a bakinsa ya so ma zolayarta kamar yadda ya saba.

“Ku na fasa mata kai da wannan kafafuwan nata kamar itace”

Aiko kamar jira take sai ta fara kukan shagwaba, musamman ganin duka gatanta suna nan Inna da Baba.

“Baba kana jinsa ko?”

Baba yayi dariya tare da kai hannunsa ya kashe redio dake gefensa, ya tofar da goron bakinsa. Yai mata alama da ta zo da hannu, kamar jira take sai ta karaso inda yake tana ta turo baki ita ala dole an taba ta.

“Auta Mamana, ki daina biyewa Sanusi, shi da yake ragon maza, ke da kike Jaruma, ki daina nuna musu rauninki, kin ga shi kin ga Rilwanu ki daina bari suna saka ki kuka, da an miki aure sai kun yi ta marmarinki”

Ta rufe ido da sauri cike da tsantsan kunyar irin ta ya mace bahaushiya. Hakan da tai sai ya kara saka Baba murmushi.

“Allah ya miki albarka ya nuna mana lokacin Autata”

Kasa amsawa tai da ameen domin Aminatu irin yan matan nan ne masu kunya da kawarda ido ga wasu abubuwan. Sai kawai ta mike tsaye har lokacin bata janye hannunta daga fuskarta.

“Wai kunya take, kunya kike kika yarda kina fita zance”

Sanusi ya fada yana dariya, a cikin hasken farin watan Aminatu ta watsa masa harara. Ta nufi inda kwallar tuwonta take ta nada ganwo ta dauka ta dora a kai sannan ta mika dayan hannunta ta dauki miyar dake cikin bokitin roba.

“Ni na tafi gurin sana'a ta”

Ta fada tana kara murda masa baki, Inna dai bata ce komai ba bayan murmushin da tai. Har ta kai bakin kofar fita daga gidan sai Baba ya kirata.

“Mamana”

Ta juyo.

“Na'am Babana”

“Allah ya miki albarka”

Sai ta amsa tana kallon gefen Sanusi.

“Ameen, yan bakinciki sai dai su mutu”

Ba Inna da Baba da Sanusi kadai ba, har Rilwanu da Iro da suka shigo yanzu sai da suka saka dariya, domin sun san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, inda Aminatu ta yi habaici ko shagube to ba zai wuce Sanisu ko Rilwanu ba take yi ma.

“Mai tuwo a bani na hansin”

Ko kallon Rilwanu ba tai ba ta saka kai ta fice tana cinno baki gaba kamar zai zazzago ya zubo kasa. Kusa da Baba suka zauna ko wane ya aje bindigar maharba da manyan wukaken dake hannunsu. Kana ganinsu ka ga zaratan jarumai, tun daga kirarsu har yanayin shigarsu da muryarsu. Domin suna daya daga cikin manyan yan saka na yanki, abu ne mai wahala ka ga gidan da ke da maza uku ko hudu baka samu yan sakai a gidan ba balle kuma gidansu Aminatu da suke da maza bakwai. Ba wuka ba ko bindiga bata huda mahaifinsu balle kuma su da suke shiga dajijikan kauyen neman barayi da kansu.

Tana yin nesa da gida kadan sai murmushi ya wanke mata fuska, a cikin abubuwan da tafi kaunar a rayuwarta akwai yan'uwanta, musamman Rilwanu Sanusi da Musa, domin sun fi sauran sake mata, da kuma kyautata. Gashi basa yarda ko da wasa wani ya nuna mata yatsa a waje balle har a taba ta.
A natse take tafiya, tana ta mikawa mutanen data sani kuma suka santa gaisuwa cikin girmamawa, musamman abokan mahaifinta, sai da ta kusa dandali sannan ta rage saurin tafiyarta da alama akwai wanda take jira ko take son hangowa, can kuma ta ja ta tsaya ta juyo tana kallon hanyar data fito sai ta hango masoyinta tafe da saurinsa cikin shigar kananan kaya, murmushi ne ya cika fuskarta, sai ta sauke idonta kasa domin bata jin kunyarta zata barta tai ta kallonsa har ya karaso inda take.
Sai da yai wani gyaran murya ya waiga ya ga babu mai ganinsu sannan ya ce.

“Auta”

“Na'am barka da dare”

“Yau ina fitilarta?”

Sai da yai maganar ta tuna da zancen wata fitila, sam ta manta bata zo da ita ba, sai a yanzu ta suna ta bar fitilar a dakin Inna bayan ta gama rubuta wasikar.

“Wallahi na manta ta”

Ta fada tana dukawa ta aje bokitin miyar dake hannunta, sannan ta saka hannu a cikin zanenta ta dauko wasikar ta mika masa, ya karba da dayan hannunsa dayan hannun kuma ya mika mata tasa wasikar.

“Na je gida na karbo miki?”

Ta zaro ido.

“Kai Baba yana nan fa, ni ban saba aikin maza a gidanmu ba”

Yayi yar dariya yana kokarin magana suka ji muryar Sanusi.

“Auta...”

Ba karamin tsoro Aminatu ta ji ba, domin bata saba tsayuwa da maza har a ganta ba, duk kuwa da kasancewar ta kai munzalin da zata iya yin hakan, amman kunya da tsoron yayyunta ya hana ta yin haka, duk inda ta san idan ta tsaya da wani za a gani ayi mata magana ko fada bata yarda ta tsaya a gurin. Maniru ne ya soma wayancewa ya mikawa Sanusi hannu suka gaisa, Sanusi ya amsa yana musu dariya.

“Ka ce na zama yaya daga yanzu”

Maniru yayi dariya Aminatu kuma ta duka da sauri ta dauki bokitin miyarta daman tuwon yana saman kanta.

“Ga fitilar in ji Inna”

Ya mika mata yar karamar touch light din dake hannunsa, sai ta karba da sauri ta juya ta cigaba da tafiya cike da tsananin kunya gabanta sai faduwa yake. Sai da tai nisa sannan Sanusi ya kalli Maniru ya ce.

“Maniru idan kana son Aminatu ai gidansu ya kamata ka ta fi ba wai ka rika tare ta a hanya ba, amman irin wannan ai ba lallai ne kowa yai maka fahimta mai kyau ba”

“Wallahi Sanusi ina son zuwa, ita take hana ni, sai tace tana jin kunya kuma yayyunta za su iya mata fada”

Sanusi yayi dariya.

“Shirmen ta ne, ba a aure mu za mu yi, idan ka shirya kawai ka min magana zan sanar da Baba sai a komai cikin mutunci”

“Maa Shaa Allah, na gode sosai daman ni abun da nake nema kenan domin na gaji da zageye zageyen nan Wallahi”

“Inshallahu zan yi magana da Baba, duk yadda ake ciki zaka ji”

Sai da Maniru ya sake mika masa hannu suka gaisa sannan ya wuce yana ta jindadi abun nema ya samu.
Aminatu na daya daga cikin irin yan matan nan da suke da farin jinin siyarda sana'a musamman a dandali duk kuwa da kasancewar ba wani kula samari take ba, amman abu ne mai wahala ta je da tuwo ta dawo da shi sai ta saida kaf wani lokacin ma har ta karbi na wasu ta siyar musu, saboda tsabtarta da kuma dadin miyar Inna. Har ta gama sai da tuwon ta nade komai nata a guri daya Wasikar da Maniru ya bata tana cikin jikinta, a dayan bangaren kuma tana ta tunanin yadda zata shiga gida, domin ta san abu ne mai wahala ace Yayanta Sanusi be fada cewar ya ganta da Maniru ba, ba fada kadai ba wata kila har doka sai ta sha a gurin Yayanta Amadu. Da gangan ta ki yarda ta je gida da wuri duk kuwa da kasancewar ta siyar da tuwonta a cikin lokaci, sai ta zauna a gurin tana ta kallon mutane fuska ba yabo ba fallasa, ba zaka iya karantar damuwarta ba, sai dai hakan kuma be isa ka fadi cewar tana cikin farinciki ba.
Har kusan 11 na dare bata tafi gida ba tana zaune a gurin sai ta fakaici idon mutane sai ta matse yan kwalla da suke cika mata ido, sai kuma ta dan turo baki, sai kallon mutanen dandalin take sai ka rasa wa take turowa bakin. Ganin babu sarki sai Allah yasa ta mike tsaye ta dauki robar ta dora a kai tai ma abokan sana'arta sallama, ta fara tafiya kamar bata son zuwa, ta san inda bata je ba sai an aiko nemanta kamar yadda ake idan ta dade bata dawo ba, dan haka bata da wata mafita data wuce ta koma gida.





TALBA POV.

Yana shakimce cikin mota har Ali ya iso gurin motar ya bude front seat ya shiga ya zauna yana kallon abokin nasa

“Lafiya dai?”

Talba yaja wani dogon numfashi ya sauke sai huci yake, har ya bude baki zai yi magana sai kuma ya shiru ya maida dubansa wani gurin. Ali na ganin hakan yai dan murmushi.

“Leila ta tabo ka kenan?”

Talba ya kalleshi da idanuwan dake nuna bacin ransa karara kamar yadda fuskarsa ma ta kasa boye bacin ransa.

“Wai yarinyar nan ni zata wulakanta?”

Magana yake kamar wuta na fita a bakinsa. Ali ya masa kallon natsuwa.

“In I'm not mistaken ka sake mata maganar auren kenan?”

Shirun da Talba yai ne ya tabbatarwa da Ali eh ce amsar tambayar.

“Amman ta wace siga kai mata maganar?”

Talba ya watsa masa wani banzan kallo.

“Kamar wani karamin yaro zaka tambaye ni wace Siga nai mata maganar?”

“No baka gane ba ne Talba, su fa mata yan lalabawa ne, kai kuma sai kace komai da karfi da isa zaka yi ba haka ake ba”

Talba ya watsa masa wani kallo.

“Okay kamar ba baka san ni ba kenan? So kake na je na same ta ina lallashinta ta aure ni?”

“No kai baka gane ba, Talba wannan lokacin ya wuce da zaka dinga tirsasa mace ta yi maka abu any how, na san Leila tana sonka amman kai din ne wani iri”

“Kai Ali duk fa mace da zan aura alfarma zan mata, ba dai ita ta min ba, ina da kudi ina da kyau ina da ilmi ina da addinin da har a kasar waje za a iya bani aure balle a nigeria a nigeria ma a gidanmu”

“Ka ga matsalar ka ba, wani irin alfarma tun da har kuna son junanku? Kar fa ka manta Talba Leila a waje tai karatu kuma wayayyiyar mace ce mai son burgewa, Talba dan kalaman nan na soyayya baka san kai mata ba, dan morning text din baka tura mata, balle har ka kirata ku yi fira, ko ka dauke ta ku fita, mata suna son wannan”

“Ba zan yi ba, ina namiji zan wani zan wani rika lallaba mace, idan ma zan mata sai an yi aure, amman ba a yanzu ba ai sai ta raina ni, besides muna gida daya zan rika mata haka?”

“To miye a ciki, ai an san aurenta zaka yi tun da an muku baiko, kai komai sai kace na zafi zaka yi, idan ka sake mata ba shi yake nufin ka bata umarni ta ki bi ba, dan Allah ka kirata yanzu ka bata hakuri”

Kamar wanda aka cewa cire ranka ka bata haka Talba yai ma Ali wani irin kallo na mamaki da tsoro a lokaci daya.

“Ni Mu'azzam Auwal Shimkafi zan kira mace na ce dan Allah ki yi hakuri? Macen da ba uwata ba? Malam dan Allah fitar min a mota”

“Talba mata fa sai da haka, kuma ka canja hali dan Allah”

“Ita ma ai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login