Showing 51001 words to 54000 words out of 133328 words

Chapter 18 - BAKAR WASIKA complete

Start ads

24 Aug 2025

467

Middle Ads

ita, abu ga talaka bawan Allah kadan ya ishe shi.

“Amman Allah ya saka masa da alheri, Allah ya faranta rayuwarsa ya daummawar da farinciki a cikin zuciyarsa kamar yadda ya faranta ranmu”

“Ameen, ni kaina ina tafe a hanya ina ta masa addu'a, Wallahi na jidadi sosai, domin rashin lafiyar nan naki ya dame ni, yanzu ki tashi ki shirya mu tafi asibiti”

“Aa wace asibiti kuma Faruq? Ai ni yanzu na ji sauki, daman ciwon ai na rashin kudin ne”

Wata kalar dariya Faruq yai wanda ya manta rabon da yai irinta har ya manta.

“Haba Mama saboda ciwon ki fa naje karbo kudin nan, kuma har ga Allah ni asibitin nai niyar kaiki”

“Aa ai ciwo kuma ya warke, da aje a kashe kudin a banza ai kara a kara ayi hidima, Idan aka karbi kudin lefe aka rage wani abu cikin nan ai sai a dan kara, in yaso sai ka dauki rabi ka ba mai hayar ka bashi hakuri”

“Ai ba za su isa ba, 80k ne muke biya shekara”

“Eh ka bashi ko 50k ne dai ka bashi hakuri kamin Allah ya budo mana wata hanyar samu sai ka cika masa”

“To Allah ya sa ya yarda, wannan matar ta kira min ruwa, Wallahi na gaji da halin Rafi'a Mama kullum da kalar fitinar da take bullo min da ita, bata da wata magana sai ta na sake ta”

“Ka kara hakuri tana maka haka ne saboda tana ganin baka da kudin yin wani auren, da ace ta san kana da kudi da ba zata maka haka ba, koma na rayuwa dan hakuri ne wata rana zaka ga komai ya wuce kamar ba ayi ba”

“Allah ya kara min hakurin domin har ga Allah ta kai kulu, ba wai zan sake ta ba ne bana son shiga hakkinta ne”

“Yanzu dai tashi ka tafi gurin sana'arka in yaso gobe sai ka samu mai hayar na san zuwa lokacin ya huce sai ka ba shi hakuri ka bashi dubu hansin din, Allah ya warwareka yai maka albarka, zuwa da yamma zan tafi gidan Kanen mahaifinku na fada masa yayi ya aiko da kudin lefen sai a hada da dan abun da aka samu”

“Toh Allah ya taimaka ni zan tafi”

“Ka dai baro mata abinci ko?”

“Eh akwai Taliya da wake, da cefane, idan na koma anjima zan siya mana abinci ina son na cire 5k a ciki”

“To Allah ya taimaka yai maka albarka”

“Amin Mama Allah kara miki lafiya”

Ya fada yana mikewa tsaye sai ta bishi da kallo ina na uwa da da tana jin kaunarsa na karuwa a ranta, ta fi kowa sanin cewar idan Faruq yana da mafita da tuni ya share mata hawayenta.
Kudin ya ciro ya cire 50 na mai haya sannan ya cire 5k ya mika mata 43k da suka yi saura, sannan ya fito ya nufi gurin aikinsa.
A hanyarsa ta tafiya ya saye waina sannan ya karasa shagon daman yana da plate da spoon da dan copinsa a shagon bayan ya bude ya wanke plate din sannan ya zuba wainar ya ci, ya siyo ruwa ya sha, tukuna ya hau gyaran shagon kamar yadda ya saba.
Be tashi ba sai 7:30 daman haka yake tashi kamin ya isa gida 8 tayi sai ya tsaya yai sallah a massallacin unguwarsu sannan ya shiga gida. A duk lokacin da zai shiga gida da tunani da fargabar abun da Baturiya zata masa, amman a yau haushin shiga gidan ma yake ji, har be san ta inda zai fara mata ba idan ya shiga.
Kamar kullum sai da ya tsaya yai sallah, sannan ya biya gurin mai siyar da balangon unguwarsu ya siye na dubu daya, ya biya shago ya siye shimkafa da sauran kayan masarufi sannan ya nufi gidansa.
Yayi mamakin ganin kofar gidan a bude domin bata saba barin kofar a bude ba, rufewa take wai a cewarta masu kudi ma basa barin gida bude sai takawa, hakan yasa duk wanda ya zo sai ya kwankwasa mata sannan ta bude. Sai dai yau kofar a bude ya same ta, sai ya shiga rike da ledodin a hannu nan ma sai ya samu kofar falon a bude, be yi sallama ba ya shiga saboda ransa a bace yake. Sultan kadai ya samu a falon zaune yana shan bobo, Sultan na ganin mahaifinsa ya sauko daga saman kujerar da sauri ya nufe shi.

“Daddy sannu da zuwa”

Sai da ya aje ledodin hannunsa sannan ya dauki Sultan yana murmushi.

“Sultan ya keke?”

“Lafiya”

“Me kake sha?”

“Bobo Momy ta siya min Bobo”

Jimmm Faruq yai sannan ya sauke dansa ya bude masa ledar naman daya siyo ya aje masa a gabansa.

“Zauna ka ci”

“To”

Ya zauna da sauri ya fara ci yana ta murna.

“Momy ma ta siya min kifi dazun”

Faruq be sake ce masa komai ba ya nufi kofar dakin tana tabawa ya ji a rufe, sai ya juyo ya kalli dansa.

“Sultan ina mamanka?”

“Tana ciki”

Kwankwasa kofar ya fara yi.

“Rafi'a ki bude kofar nan”

Sai ta amsa masa daga can ciki.

“Wallahi ba zan bude ba, ai na san dokana zaka yi”

“Kin san abun da kika yi kenan?”

“Eh mana, haka kawai muna fama da talauci zai zo ya kara mana da wata damuwar kudin haya shiyasa na karbi number sa na zage shi ai”

“To kin jawa kanki ya bamu kwana daya mu tashi mu bar masa gidansa, Rafi'a mi yake damunki ne wai? Miyasa ke baki son zaman lafiya? Duk wani abu da zai tayar min da hankali shi kawai kike nema”

“Ai na bashi 100k yau, na biya shi kudinshi kuma ya bada takardar ya yarda mu zauna”

Natsuwa yake kokarin yi wai ko zai fahimci inda kalamanta suka dosa, ta bashi kudi haya?

“Rafi'a”

Ya kiranta a hankali, sai ta amsa daga jikin kofar da take, rike da sabuwar wayarta.

“Na'am”

“Maimaita abun da kika fada min”

“Na ce na bashi kudin hayar har na kara masa da 20k sama”

“Ina kika samu kudi?”

“Yaya ne ya ba ni Umma ta cika min sauran”

“Bude kofar nan mu yi magana”

“Ba fa zan bude ba, tufafin ka nan a falo na fitar maka, kuma abinci ka yana nan kusa da kujera, kai da Sultan ku kwana a falo ba zan bude ba”

Ba dukan abun da tai kawai take tsoro ba, har da na sabuwar wayar data siya da kuma kudin data biya hayar domin ta san abu ne mai wahala ya yarda da ita.

“Ki bude kofar nan Rafi'a ba zan dake ki ba, na taba dukanki ne? Duka ai ba halina ba ne ina son nai magana ta fahimta da ke”

Shiru tai masa kamar bata gurin.

“Na samu 100k yau”

“Da gaske? Ko dai dan na bude ne”

“Wallahi da gaske ne, Rafi'a i need to talk to you seriously ki bude kofar nan ko kuma na tafi na barki ki kwana a gidan ke kadai...”

“Wallahi Faruq dukana zaka yi idan na bude ni na san abun da na yi, duk abun da na yi ai dai ina sonka ka san dai ina sonka, bakin talaucin nan ne bana so, saboda farar kafa ce da kai Faruq, aurenka be karbe ni ba, da yanzu na yi arziki”

Ta fada da muryar dake nuna tana daf fashewa da kuka. Murmushi jin yadda ta juya abun zuwa kansa, wato shi ne mai farar kafa ba ita ba.

“Na ji bude mu yi magana”

Ta dade tana tunani sannan ta nufi karkashin filonta ta saka wayar, ta nufo kofar ta bude cike da tsiro sannan tai baya ta haye saman gado, shi kuma ya shigo cikin dakin yana kallonta, yana bude baki yai magana sai wayarta tai ringing, yanayin yadda ta razana kadai ya isa ya nuna bata da gaskiya, saurin nufar inda wayar take ta yi ta dauka ta kashe ta gaba daya.

“IPhone? Ina kika samu IPhone Rafi'a?”

Ta yi shiru sai kallonsa take. Shi ma kallon tsoro yake mata domin lamarinta a yanzu ya fara bashi tsoro ta fara wuce tunaninsa.

“Ko yaya ya siya miki?”

Nan ma shiru tai, at first ya fusata sai dai a yanzu kwakwalwarsa cike take da tunani kala kala. Karasa yai kusa da gadon ya zauna gabansa n mugun faduwa, yana ta kokarin ganin ya kawarta yaye yayen da zuciyarsa take son masa akan Rafi'a. Zaunawa yai bakin gadon yana kallonta.

“Rafi'a ki saka tsoron Allah a ranki, ina son ki san cewa duk abun da aka samu a duniyar nan a nan ake barinsa, ba a zuwa lahira da komai sai aiki da mutum ya aikata, Rafi'a dan Allah ki zama mai tunani ki duba future din Sulta da abun da yake cikinki, na san ni talaka ne ba zan iya miki komai yadda kike so ba, amman da ki je ki aikata wani mummunan abu da aurena kuma kina uwar yayana kara na sauwake miki ki auri mai kudi idan har hakan zai kawo miki mafita”

Yana maganar idonsa ya cika da hawaye, domin har ga Allah be fatar matarsa ta aikata abun da zuciyarsa take raya masa.

“Ina son ki Rafi'a amman Wallahi zan iya sauwake miki saboda yayana da aurena”

“Ni fa ba iskanci na yi ba, Wallahi ban taba iskanci ba”

Ta fada tana soshe soshe kamar mai kuraje.

“To ina kika samu wannan kudin da wannan wayar?”

“Yaya”

“Kin yarda na tambaye shi?”

“Eh na yarda”

Ido ya kura mata domin ya san karya take, yayanta yana da rufi asiri amman ba zai iya siya mata iPhone ba, duk be san ko wace irin iPhone bace amman ya san tana da tsada tun daga yanayin wayar da kuma yadda yake ganinta ga yan mata. Kasa yai da kansa ya lumshe ido be isa yace ba zata rika wayar ba tun da har ta danganta cewar yayanta ne ya siya mata, ya san idan ya hana mahaifiyarta zata saka baki ko kuma tace zata yi fushi ta tafi gida, ko ma suce ya rabu da ita.

“Ina da ciki idan ka dake ni ka daki cikinka”

Dagowa yai ya kalleta.

“Saboda ban da kudi shi ya baki damar yin duk abun da kike so?”

“To Faruq kai ma kasan ni ba ajin ka bace amman...”

“Haka ne...”

Ya fada sannan ya mike tsaye.

“Bari ki sauke abun da yake cikinki, labarin rayuwarki da tawa zai canja komai zai zo karshe”

“Da gaske?”

Ta tambaya cikin farinciki har ga Allah babu abun da take so kamar Faruq ya sake ta ta auri mai kudi, tana sonsa kan amman tafi son ta tafi inda zata huta. Kallonta kawai ya dauke kai ya fice daga dakin, falo ya dawo ya zauna yana kallon dansa cike da damuwa.

“Dady ba zaka ci ba?”

“Aa Sultan ci ka ragewa Momynka”

Ya fada yana shafa kansa cike da so da kauna, haihuwar da Allah ya bashi kadai ya san wani babban arziki ne.

15

Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa


*Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*



AMINATU POV.

Daga jiya zuwa yau da aka canja mata daki sai ta ci kadaicin ya karu, domin a can tana jin hayaniyar mutune a wannan dakin komai babu kowa sai ita kadai, sai duk ta ji tana kewar gidansu da rayuwarta ta baya.
Bata san dalilin daya saka aka canja mata daki ba, bata san ranar da wani zai zo nemanta ba, bata san ranar da rayuwarta zata koma daidai ba, har yanzu ji take kamar komai mafarki ne.
Tana fara tunanin ta ji wani irin tsoro ya taso mata, sai ta ji wani abu yana mata yawo a cikin kai karar bindigogi ya dawo mata hayaniyar mutane da rokon da Baba yake musu ya dawo mata kamar lokacin yake faruwa. Wani irin abu ta rika ji kamar kanta ba zai iya dauka ba, gashi tana son ta yunkura ta sauka saman gadon amman dama domin kafafuwanta basa iya komai a yanzu, bakinta ma ya dantse gam duk yadda ta so tai ihu ko kuka sai ta kasa. Ji tai bata bukatar komai a lokacin sai tafiyar da babu dawowa. Da wani irin karfi ta tashi zaune ta fisgi robar ruwan dake hannunta wanda hakan ya bawa jini hanyar fita ya fara zuba, jiki na rawa ta fisgo robar da karfin da bata taba sanin tana da shi ba sai karfen ya fado gefen gadon, bata tsaya komai ba ta hada robar a wuyanta tana kokarin aika kanta da kanta inda take ganin kamar idan ta tafi ta huta da komai.
Wannan karon ta samu sukunin bude baki, sai dai ko kadan hakan be bawa muryarta damar fita ba, hawaye kawai take babu kakautawa tana ta yaki da numfashinta, kamar an zare mata lakka haka ta ji wani abu ya sauko mata wanda ya zare duk wani sauran kuzari dake jikinta. Tun tana kallon kofa tana numfashi a hankali har numfashin nata ya fara nisa ta komai ya fara mata dishe dishe alamar ta fara ban kwana da duniya, ga jinin hannunta sai zuba yake.


TALBA POV.

As usual every weekend a falon Momy ko Daddy ake karyawa tare da kowa ciki har da Daddy da matarsa, sai dai mafi akasiri an fi cin abincin safe a bangaren Momy, Daddy zai zo bangarenta aci tare da shi, idan an gama ko kamin a fara duk wani mai wata bukata zai gabatar masa.
Sai dai wannan karon a bangaren Daddy Momy ta saka masu aikinta su kai komai wanda hakan ke nuna cewar a bangarensa za a karya.
Duk abun da ake Talba na zaune dinning yana lasa wayarsa, be dago ba har sai da ya ji saukowa Momy, sannan ya dago ya kalleta.

“Momy ina kwana?”

“Lafiya kalau an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah”

Ya amsa yana tashi tsaye sai da ya bar dinning din ta kira shi.

“Talba”

Juyowa yai ba tare daya amsa ba.

“Ka yi hakuri da abun da ya faru jiya, raina ne ya bace”

“Babu komai Momy, ke ai uwata ce Wallahi ban rike ki da komai a rai ba”

Wannan maganar da yai sai ya saka Momy ta dan ji nauyinsa, kasa hada ido tai da shi har ya juya ya fice daga falon. Kai tsaye bangaren Daddy ya nufa a bude ya samu kofar shiga falon, hakan yasa be yi sallama ba kamar yadda ya saba ya nufi gurin da suke karyawa.
Leila kadai ya samu zaune a dinning din ta saka plantain a gaba tana ci, tana sanye da wani jan yadi kanta sanye da bakar hula, fuskarta ta ji hoda sosai sai dan janbakin data shafa, ta yi kyau sosai abu ne mai wahala mace ma tai mata kallo daya ta dauke ido balle kuma namiji. Talba yaja kujerar dake facing dinta ya zauna yana kallonta, shi kansa ya san ta yi kyau, sai dai ba al'adarsa bace fadawa mutum cewar yayi kyau ko yana da kyau, musamman mace, no matter yadda take da kyau ba zai taba iya bude baki ya furta cewar ta yi kyau ba, kuma ba zai zake da yawa gurin kallo ba gudun kar a ankara da shi.
Dauke idonsa yai bayan ya zauna, sai a lokacin ya tuna cewar yau be tura mata sakon barka da safiya ba, kuma ba zai iya tura mata a yanzu ba gudun kar tace saboda ta yi kyau ne.
Gaba daya ya tattara hankalinsa ya maida gurin wayarsa, sai yai kamar be san da zaman Leila a gurin ba, ita kam daman gaisuwa ba halinta ba ne bata saba gaishe da mutane ba bayan Momy da Daddy, balle kuma shi duk kuwa da irin sanin da tai na son a girmama da yake, sai dai ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa duk kuwa da irin bugawar da zuciyarsa take after every blink. Har ga Allah bata iya fadar irin son da take yi ma Talba, da ace ta dauki biro da zayyano irin kaunar da take masa da alkalumman rubutu da takardun duniya sun kare bata gama rubuta irin kaunar da take masa ba. Sai dai har yanzu ta rasa gane manufarta a kanta, miyasa ba zai dauki rayuwa da sauki ba? Ya sauko da kai su yi soyayya kamar sauran masoya? Har yaushe zata yi ta jiran ya canja rayuwarsa? Anya ma zai canja din? Bata raba dayan biyu ba ta ji yana amsa waya, bata iya fadar cewar kiransa akai ba ko kuma shi ya kira domin wayarsa a silent take.

“Yeah ni ma na kwana da yarinyar nan a raina”

Furucinsa ne yasa ta kara tattara hankalinta tana saurarensa.

“Okay”

Shine last abun da ya fada sannan ya sauke wayar, ya daga kansa yana kallo Amal data nufo inda suke sanye da riga da wando yan patistan.

“Good morning Ya Talba”

“Morning Little Sis”

Ya amsa yana aikawa PA sa sakon kar ta kwana.

‘Ka yi magana da wannan number zai fada maka ko nawa yake bukata sai ka tura masa’

Aje wayar yai bayan ya aika sakon. Leila bata fahimci komai a wayar ba, sai dai ta fahimci da Ali yake magana domin yanayin yadda ya amsa wayar ya tabbatar mata da hakan. Sai da kalmar da ita na kauna a raina ya fi tsaya mata a rai.

“Wace yarinya ce?”

Ta tambayi kanta tana kallonsa, a take ta ji zuciyarta ta buga da mugun karfi, har sai da numfashinta yai sama, da sauri ta dauki cup din dake saman teburin ta zuba ruwan sanyi ta sha, sannan ta mike tsaye ta fice daga gurin zuwa karamin falon Daddy.

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login