Showing 1 words to 3000 words out of 98260 words

Chapter 1 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

207

Middle Ads


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*BILHAQQI*

*Fikrah writer's association*

*Fareedah Abdallah*

*Na fara da sunan Allah mai ni, mai ku, mai kifaye😍🤲🏼*

*Shimfid'a*

A jihar Kaduna, a k'aramar hukumar Kajuru, a cikin k'auyen Rimau, a wani d'an k'aramin gida da yake bayan gari.
K'arfe biyu da minti talatin da takwas na daren ranar juma'ar shekara dubu biyu da d'aya.

Jikinsa na kyarma ya d'aga kafarsa ta dama da kyar ya tura k'ofar gidan ya bud'e. Hannayensa duk biyu suna dafe da 6angaren cikinsa na dama, duk da dafewar da yayi bai hana jini d'iddiga daga in da ya dafe ba.

A hankali cike da karfin hali da jarumta ya ja k'afafunsa zuwa cikin gidan, idanunsa sai lumshewa suke yi suna bud'e wa dan tsananin galabaita da jigata. Daga yadda yake tafe yana harhad'a hanya zai baiyana matsanancin halin da yake ciki, idan yayi taku d'aya sai ya tsaya ya nisa tsawon wasu dak'iku kafin ya k'ara taku na biyu.

Sai zurga-zurga take yi a d'an tsukukun tsakar gidan kamar mai yin safa da marwa, ta goya hannayenta duk biyu a baya. Idanunta suna ta tsiyayar da hawaye, fuskarta na baiyana matsanancin tashin hankalin da zuciyarta take ciki, daga yadda kirjinta yake bugawa akai-akai ta san akwai wani mummunan al'amari da yake shirin faruwa da ita. Wannan tsawon awoyin da ya d'auka bai shigo ba tana ji a jikinta ba lafiya bane.
'Tabbas ba lafiya bane. Ita ta san Mahaifinta Luka da d'an uwanta Zidane tun da dad'ewa sam basa nufinta da alkhairi. Balle kuma sun shigar da Pastor Nuhu cikin al'amarin, ta san sai abinda hali yayi. Shi yasa ko da sak'on kiran ya riske su tayi kokarin hana shi amma ya kafe kai da fata akan sai yaje. Fuskarsa cike da tattausan murmushi ya fice daga gidan yana d'aga mata hannu alamar sai ya dawo.'

Ko kad'an bata ji tsoron tsalawar da dare yayi ba, idanunta na kan saitin kofar gidan tana jiran ta ga shigowarsa a cikin hasken farin watan da ya wadaci tsalar gidan tar a daren goma sha hudu.

Lokacin da taga shigowarsa da saurin gaske kamar za ta kifa k'asa ta k'arasa gare shi, a hankali ta rik'o shi zuwa jikinta, da ita da shi sai kyarma suke yi kamar ana kad'a musu ganga. Da ta fahimci halin da yake ciki lokaci d'aya ta sake fashewa da kuka mai tsananin k'arfi tana kallon cikinsa in da ya dafe da hannayensa, tsananin tsoron abinda za ta gani yasa ta kasa cire hannayensa.

Da tsananin k'arfin hali ya tattaro d'an sauran jarumtar da ya rage masa ya haske ta da tattausan murmushi, taga-taga suka yi dan nauyinshi ya fara rinjayarta kamar za su kifa da saurin gaske ya dafe bango da hannunsa na dama. Zame wa yayi ya zauna a k'asa bayansa jingine da bangon ita ma ya zaunar da ita a gefensa, har lokacin k'afafunsa sai rawa suke yi.

A karo na biyu ya sake tattaro dauriyar da ta rage masa ya sakar mata murmushi. Sam ta kasa mayar masa da martani, kuka take yi bilhaqqi. Zuciyarta cike da tsanar irin wannan bak'in rayuwa da bak'ar al'ada ta garinsu da mutanen cikin garin. Ga wata bak'ar al'ada da suka d'orawa kansu tun zamanin iyaye da kakanni.

Hannunsa ya sake d'agawa a kasalance ya shafi cikinta. Gabansa ne ya fad'i, ya dago kanta daga kirjinsa ya tsattsareta da kallon tuhuma da idanunsa da suke lumshewa suna bud'ewa.
"In... In...ina ciki na?"
Ya jefa mata tambayar yana harhad'a kalmomi cike da k'arfin hali.

Da saurin gaske ta mik'e tsaye daga jikinshi ta nufi cikin d'an akurkin d'akin da sassarfa. Ba a jima ba ta fito hannunta dauke da wani abu da aka nannad'e cikin jallabiya ta maza. Ta ajiye a jikinsa sannan ta bud'e rufar gaba d'aya sai ga kyakkyawar jinjira fara sol ta baiyana. Kanta har zuwa gaban goshinta lullu6e da bakin gashi luf-luf irin na jarirai. Baccinta take yi hankalinta kwance.

Kyarmar da jikinsa ke yi ne ya k'aru da sauri ya ruk'unkume jinjirar a k'irjinsa. A karo na farko tun faruwar cukurkudaddun al'amuran ya ji zubowar wasu zafafan hawaye daga idanunsa. Bai damu da ya share ba ya maida hankali kanta gaba daya ya k'ure ta da kallo mai baiyana neman k'arin bayani.

"Dazuh... Bayan fitarka na haihu... Shi ne na yanke mata cibi na goge jinin jikinta ina jiran ka dawo..." Ta amsa cikin kuka mai tsanani.

Murmushi yayi ya janyota jikinsa ya rungume ita da Babyn yana sauke ajiyar zuciya, zafafan hawaye ke fita daga idanunsa yana sauka a gadon bayanta. A karo na farko zuciyarsa ta karye, irin karyewar da bai ta6a tsammanin zuciyarsa zata yi ba a gurin fuskantar gaggarumin k'alubalen da yake gabansu tun bayan faruwar aurensa da Rebecca.
'An katse mishi hanzari... Tabbas an katse mishi hanzari... Shi Mustapha bai ta6a tsammanin k'arewar al'amarinsu a d'an k'ankanin lokaci haka ba'
Ya aiyana hakan a zuciyarsa.

A raunane ya fara magana kamar mai rad'a yana bubbuga kafad'unta alamun rarrashi.
"Da gaskiya a cikin tsananin k'aunar da nake miki Rebecca... Da gaskiya a cikin alkawuran da na sha d'aukar miki Rebecca... Na tabbatar da gaskiya a cikin tsananin son da muke yi wa Junanmu. Na so kwarai in zame miki tsanin da zaki taka ki kai k'ololuwa ta jin dad'in rayuwa Rebecca... Amma da yake komai na al'amarin bawa yana faruwa ne bisa yarda da amincewar Ubanjina. Tun kafin a haife ni rubuce yake a cikin kundin Kaddarata. Tafiyar tamu ba mai tsawo bace ni da ke, cikin k'ank'anin lokaci har mun zo iyaka... Fata d'aya gare ni Rebecca. Alfarma d'aya nake nema a gurinki kafin in koma ga mahalicci na. Ki musulunta Rebecca, ko bayan ba raina ki musulunta. Tabbas da gaskiya a cikin Addinina..."
Yana zuwa nan a maganarsa ya fara jan numfashi mai karfi sauri-sauri, can kuma sai ya sarke da wani irin tari mai k'arfi, tsawon lokaci yana yi ita kuma tana jera mishi sannu tana hawaye, yadda take ji a jikinta tabbas da tana da iko da ta amshi duk ciwukan da yake ji a jikinshi. Ita ta cancanci mutuwa ba shi ba, bai kamata ita ta aikata laifi a hukunta shi ba, wannan bak'in hukuncin nata ne ita kad'ai, Musty bai san komai ba janyo shi kawai tayi cikin al'amrin, salin-alin ya kamata ya su rabu ba tare da ya d'and'ani wani azaba ba.

Kaki yayi ya tofar bayan tarin ya lafa mishi, ko da ta kalli abinda ya tofar ba komai bane sai wani dunkulallen jini hade da majina. Gabanta ya sake fadi, za ta yi magana ya riga ta, hannayensa duk biyu dafe da kirjinsa, a yadda yake ji yanzu kirjin har ya fi mishi azabar ciwo a bisa cikinsa, idanunsa suna kan jaririyar.
"Ga amanar 'yata nan a hannunki. Duk runtsi duk wuya da juyin-juya hali irin na kaddara ina fata ki kasance tare da ita. Ki bata kyakkyawar tarbiyya, ki rene ta akan turbar addinina. Na rada mata suna BILHAQQI..."

"Fad'a min ya zan zama musulma? Me zanyi dan in cika maka burinka?"
Ta katse shi ba tare da ta jira ya aje numfashin maganarsa ba, da sanyin murya ta fadi hakan tana kallonshi.

A zabure ya dago kai yana kallonta, zuciyarsa tumbatse da farinciki. Sai hamdala yake jerowa a fili cikin dauriya da cije baki. Har zai biya mata kalmar shahada sai kuma yayi shiru yana karantar yanayinta.
"Kin tabbata bisa son ranki za ki musulunta ko kuwa dan ki faranta min rai ne?"

"Duk biyun"
Ta amsa kai tsaye tana kallonshi cikin hawaye.

Har yayi shiru sai kuma ya karanta mata kalmar shahada ta maimaita. A take ya fara dariya tana taya shi da murmushi kamar anyi musu albishir din warwarewar duk matsalolin da suke gabansu, a daidai lokacin sai nepa suka kawo wuta, dukda kwan lantarki d'aya ne a tsakar gidan sai ya hadu da hasken farin wata ya sake haske cikin gidan. Yadda yake dariyar sai ta ga yayi masifar yi mata kyau, kamar a ranar ta fara ganinsa.

Fuskarsa ta kamo da hannayenta duk biyu ta hade bakinsu wuri d'aya tana aika mishi da wasu zafafan sakonni masu wuyar fad'e a baki, lumshe idanu kawai yayi yana amsar sakon cike da nishadi, hannunsa d'aya dafe da kan diyarsa yana shafawa. Tsawon lokaci sannan ta sake shi ta shige cikin d'an akurkin d'akinsu da sauri.

"Alhamdulillah, ko yanzu na koma ga Allah buri na ya cika."
Ya fada a fili yana murmushi, a hankali ya warware jallabiyar da aka nad'e jinjirar a ciki, ashe akwai zani a ciki sai ya warware zanin. Sanyin da taji ya fara ratsata da yadda yake jujjuya ta yasa ta bud'e manyan idanunta ta fara callara kuka irinna jarirai, lokaci guda kuma ta fara karkata bakinta gefe daya tana cigaba da kuka, Da alamun abincinta take nema.
"Reza zaki dauko min a ciki"
Ya fada a hankali bayan ta fito daga dakin, hannayenta rike da zannuwanta guda biyu da dankwalinta.

Cikin dakin ta koma ta dauko masa sabuwar reza ta kawo masa, bata tambaye shi me zaiyi da rezar ba sai ta tsugunna a gefensa tana kallonsa.

Ya haske ta da murmushi, tsawon wasu dakiku yana kallonta har lokacin jinjira Bilhaqqi bata daina kuka ba.
"Ki yi hakuri Ummu Bilhaqqi. Wannan abinda zanyi mata shi ne zai tabbatar da nasabarta, ko bayan raina duk tsawon zamani kiyi kokarin sada ta da masarautar Maru, ta jihar..."
Kafin ya karasa maganar tari ya fara sarke shi, cikin sauri ya farke rezar ya tsaga gefen hagu na kirjin yarinyar, ta sake callara ihu kuwa cikin k'araji, runtse ido yayi ya sake tsagawa ya maida tsagun kamar tauraro, d'an gefen nononta kadan yayi tsagun, gurin sai tsattsafar jini yake yi. Ita kuwa Bilhaqqi kamar zata shid'e dan tsananin kukan azaba, ko da ya mikawa uwar ta saka mata nono a baki kin kar6a tayi ta cigaba da tsalla kuka. Sai kawai suka zuba mata ido, zukatansu fal da tausayin gudan jininsu, kamar za su fashe da kuka.

Dan wani tunani tayi da sauri ta mika mishi ita bayan ta sake nad'e ta da zani ta nufi cikin kicin, yanar gizo-gixo ta yayo mai yawa ta zo ta manna ma yarinyar a gurin da yake zuban jinin, wani abin ban mamaki nan da nan jinin ya tsaya.

Tana saka mata nono a baki ta kar6a da karfinta tana ja tana kuka-kuka, daga baya kuma sai ta ci gaba da sha tana sauke ajiyar zuciya har ta d'an samu nutsuwa kad'an.

Sake nad'e ta tayi sosai ta maida ita cikin d'aki ta kwantar da ita. Ta dauko wani garin magani mai ruwan kwai a farin roba ta fito da shi ta hada da yanar gizo-gizo ta ajiye guri daya, a hankali ta daga rigar jikinsa sai ta ja da baya da sauri bayan ta kwallah k'ara a tsorace, yadda taga cakar wuka ya shiga sosai ta san ikon Allah ne kawai ya kawo Musty har yanzu yana raye. Kuka mai k'arfi ta sake fashewa da shi ta dawo kusa da shi da sauri tana rawar d'ari, ta bude robar maganin da ta had'a da yana ta zuba mishi sosai a gurin, ashe zaman da yayi jini duk ya 6ata mishi wando sosai, zuba maganin da ta yi a gurin kamar ta tado mishi da wani azababben ciwo ne, cikin kankanin lokaci har ya fara fita daga haiyacinsa.

Idanunta sunyi jajur saboda tsananin tashin hankali, dankwalinta ta ninka sosai ta danne ciwon, fuskanta hawaye shabe-shabe da majina, ta dauki zaninta ta raba biyu ta daure mishi cikin tun daga gaba har baya, tsananin azaba yasa ya sume a gurin, bata lura da halin da yake ciki ba ta koma cikin daki ta goya yarinyar a hankali saboda ciwon da yake kirjinta, ga danyen cibin da ba a gasa ba sai d'aurewar da aka yi da zare, a hankali ta fara callara kuka ita kuma ta cigaba da jijjigata ta rufe ta da zani, idanunta ne suka sauka a kan agogon dakin, karfe uku da minti ashirin da d'aya, da sauri ta fice gurin Musty bayan wani tunani ya darsu a zuciyarta.
"Musty... Musty... Lets go... Ya kamata mu bar kauyen nan yanzu, na san Bro Zidane bazai kyale mu ba..."
Ta fada a hankali tana jijjiga shi alamar ya tashi, hankalinta ne ya k'ara tashi bayan ta lura da halin da yake ciki.
"Musty..."
Ta sake kiran sunanshi cikin kuka.
Wata wawiyar bugawa kirjinta yayi lokacin da ta ji kamar hayaniyar matasa daga can nesa sun nufo gidansu.

Ta mike tsaye da sauri, kofar gidan taje ta lek'a, tabbas hayaniya take jiyo wa, kunnenta ba k'arya yaji ba.

Tayi diri-diri tayi gabas tayi yamma, ta rasa wak'ar farawa. Hannu biyu ta dora a kai ta fashe da kuka mai tsananin karfi, Bilhaqqi ma da bata san wace wainar ake toyawa ba ta sake callarewa da matsanancin kuka. Bata bi ta kan 'yar ba ta shige d'aki da sassarfa ta ciko kwano da ruwa ta zo ta antaya mishi tun daga kanshi har jikinshi, tai tsai da ranta cikin kuka tana fatan ya farfad'o, shiru kake ji bai farfad'o ba. Ta zazzaro ido a tsorace, ta daga hannunsa ta saki ya tafi yaraf, ta sake ja da baya a tsorace.

Duk da bata san mutuwa ba ta fara tunanin Musty babu. Runtse idanu tayi da karfi, wani abu mai kama da dutse ya danne ta a kirjinta, idanunta suka soye, banda matsanancin zafi babu abinda suke mata, lokaci daya suka kada sukai jajur kamar jan gauta.

Jin hayaniyar yana kara kusantowa daf da gidan yasa tayi saurin nufar 'yar karamar katangar da ta zagaye gidan, tana tafe tana waiwayen Mustafa ko zai motsa har ta kama katangar gidan ta tsallaka ta baya, duk ihun da Bilhaqqi take yi bata bi ta kanta ba ta fara gudu a cikin dajin kamar wacce zata kai takarda, burinta kawai ta isa gidan kafin lokaci ya kure mata, duk da wani sashe na zuciyarta yana tunatar da ita babban kuskuren da take niyyar tafkawa...


********* *********


Tun daga nesa tururin zafin da yake cin gidansu gagga-gagga yake buso mata. Tana tafe da sassarfa cikin fita haiyaci, idanunta a rufe suke saboda tsabar rud'ani, babu abinda take tunani sai Musty masoyinta da yake cikin gidan.

Duk da tana jin hayaniyarsu a gurin alamun har lokacin basu tafi ba baisa ta fasa abinda tayi niyya ba, kofar gidan ta nufa gadan-gadan. In dai Mustynta yana ciki gara ta shiga su k'one tare, ta gaji da hayaniyar wannan duniyar mai cike da rud'ani, gara ta bi masoyinta su had'u a sabuwar rayuwa tare

Zidane ya fara lura da ita kafin ta k'arasa cikin fushi da masifa ya karasa gare ta, ganin kamar bata lura da shi ba yasa shi sa kafafunshi ya kwashe ta ta zube a k'asa.

Nan da nan sauran matasan suka zagaye ta hannayensu d'auke da muggan makamai, ta bugu kwarai a k'asan, kokarin tashi zaune take yi tana cije baki ya kamo yalwataccen gashin kanta da fadin da tayi yasa d'ankwalinta ya fice ya dankwafar da ita a kasa, bai bata damar cewa komai ba ya gaura mata wani gigitaccen mari da yasa ta sake zubewa a gurin, bakinta ya fashe dan tsananin azaba.

Bata jira ya daga ta ba ta yunkura ta

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login