Showing 15001 words to 18000 words out of 98260 words
ƙwaƙwalwar kifi gare ki, shi yasa kullu yaumin a doɗe kike."
Ita ma ɓata fuskar tayi, zagin ya shige ta, har ta buɗe baki zata yaɓa mata baƙaƙirin sai ta maze, da tayi wani tunani kuma sai ta saki fuskarta ta fara dariya.
"Yi haƙuri aminiyas, wai dan girman Allah da gaske kike yi?"
"Wallahi Allah da gaske nake miki, idan kuma kina tantama ki tashi muje gidan Harisatu ki tabbatar da gaskiyar zance na."
"Ki bari dan Manzo?"
Ta sake tambayarta cikin tantama zuciyarta cike taf da wasi-wasi da shakkar abinda Magajiyar ta faɗa mata.
"Ah ! Zancen kike so Indo, ai kuma sai kiyi."
Ta juya mata baya ta janyo matankaɗin da yake ajiye can gefe ɗaya ta fara rairaye tsakin masara.
"Haba mana ƙawalli, ke da zaki rakani gidan mai zobian ya kuma za ki tatago aiki? yi haƙuri zo muje mu dawo tun da kince nan layin bayan ku ne, kamar na san zan tadda harkar arzikin nan yau duk ƴan kuɗaɗe na hansin hansin ne."
"Yanzu na ji batu, haba! Da ana nuna miki ga Annabi kina kaucewa, dan ma kin samu za a taimaka miki? Na yi wa mutane hanya gurin mai zobia sunfi mata hamsin, duk cikinsu banji wacce ta kawo ƙorafin buƙata bata biya ba."
Nan ta janyo wani tsumman gyale a cikin ɗaki ta yafa a kai suka kama hanyar ficewa daga gidan, sai kuma ta buɗe ƙaton muryarta tana magana da wacce suke zaman haya tare a gidan.
"Kuluwa ga sanwar fate na nan a wuta ki dinga duba min kar ruwan ya ƙone, yanzu zan dawo. Idan Baban khalifa ya dawo a ce mishi na je amso daddawa maƙwafta."
Bata jira amsawarta ba suka fice daga gidan, suna tafe tana ƙara ƙarfafawa Indo gwuiwar tabbas buƙatarta zata biya.
"Ni fa daman ba komai yasa kika ga ina zizzillewa ba kinsan abinda baka yi farkon yinshi ba yana da wahalar farawa lokaci ɗaya, har ga Allah ban taɓa bin gidan malamai ba balle har in kai sunan Karime, a duk wani abu na zamantakewarmu baki na yake ƙwatata a gurinta da gurin Malam."
"Kar ki damu Indo, ba saɓo fa zaki aikata ba. Na ji malamai da yawa suna faɗin babu laifi mace ta nemi taimako a kan miji ko kishiyarta matuƙar taga a zamantakewar nasu ana cutar da ita."
"Uhmmm! Magajiya ke nan!"
Ta sake faɗin haka zuciyarta cike da kokwanto da rashin yadda da abinda Magajiyan ta ce.
Sun isa ƙofar gidan ta sake jan tunga ta tsaya hannayenta duk biyu riƙe da ƙugunta.
"Amma Magajiya kina ganin idan na je zan samu maganin matsalolina?"
Wani dogon tsaki ta ja ranta a ɓace, cikin faɗa ta fara magana
"Kinga Indo in dai kina kokwanto zuciyarki bata bada gaskiya akan aikin mai zobia ba daga nan kawai ki wuce gidanki nima in wuce gida na, dan Billahillazi in akwai rashin yadda ko tayi miki aiki bazai ci ba."
"Maganar bai kai haka ba, yi haƙuri mu je."
Ta faɗa cikin sadaƙarwa da miƙa wuya.
"Kin yadda?"
"eh"
"Kin miƙa wuya?"
A wannan karon kai kawai ta gyaɗa kamar ƙadanguruwa, alamar da ke nuna ta miƙa wuya.
"To ki sa a ranki wannan tsintacciyar magen ta gidanku kamar ta ƙara gaba cikin duniyar ne, ita kuma Karime ki ɗauketa a matsayin bandaro ko kuma ince koma bayan-baya a gurin Malam Ali. Babu wacce zai dinga gani da haske kamar fitila da tsananin ƙyalli kamar tauraruwa sai ke Indo. Bani hannunki nan"
Ta damƙi hannunta da sauri suka faɗa gidan mai zobia da ƙarfin jiki da na zuciya.
Da yake ita sananniya ce kuma tsohuwar customer ce da take kawo mata da yawa masu zuwa ayi musu aiki kai tsaye ɗakin mai zobian ta shiga dukda ta ga wasu mata kusan su takwas a zaune a benci suna zaman jiran layi ya zo kansu. Nan take kuwa aka ba Indo umarnin ta shiga ciki bayan an sallami matar da take cikin ɗakin.
"Ki shiga, zan jira ki a nan. Kar kiji tsoron komai kiyi mata bayanin duk abinda kike buƙata."
Magajiya ta faɗi hakan tana kallon Indo, sai da taga ta shiga cikin ɗakin sannan ta nemi guri can gefe guda ta zauna tana jiran fitowarta.
Indo na shiga ta ga wani abin mamaki, bisa ga yadda Magajiya taita bata labarin Mai zobia a zatonta tsohuwar mace za ta gani, saɓanin tunaninta sai ta ga matashiyar mace ce, a ƙiyasce ma baza ta haura shekaru ashirin da biyar ba zuwa ashirin da bakwai. Kyakkyawa da ita, alamar hutu baiyane ƙarara a jikinta. Duk da baƙa ce amma baƙinta irin mai kyau ɗinnan ne da sheƙi, ɗakin kuma a gyare tsaf-tsaf babu tarkace, an malaye tsakar ɗakin da tattausan kafet ita kuma mai Zobia tana zaune a gefen wani ƙaramin gado na bono da wasu kwanduna a gabanta...
"Ba a kalle-kalle a nan, idan baki da matsala kina iya fita ta gaba ta shigo"
Mai Zobia ta faɗa bayan ta zabgawa Indo harara da juyayyun idanunta masu matuƙar ban tsoro.
Ba shiri ta zube a gabanta tana kwasan gaisuwa, sai inda-inda take yi cikin ɗimauta.
Hannu ta ɗaga mata alamar dakatarwa ba tare da ta amsa mata gaisuwar ba.
"Ina Zobia?"
Da saurin gaske ta warware ƙullin kuɗi a haɓar zaninta ta zaro gudan naira hamsin sabuwa fil ta miƙa mata.
Da hannu biyu ta buɗe kuɗin ta ƙura ma hamsin ɗin idanu kamar tana karantar wani abu a ciki, minti biyu tsakani sai ta fara wani surutai shi ba hausa ba shi ba larabci ba.
"Indo..? Ige ke tare da ke mi'am matsalarki?"
Mai Zobia ta tambayi Indo da hausar zamfaranci.
"Ƴar kishiya ta ita ce babban matsala ta a yanzu, ba ƴarta bace ta cikinta tsinto ta tayi a daji watanni huɗu da suka wuce, yarinyar nan ta zame min alaƙaƙai. Hankalin mijina gaba ɗaya ya koma kan wannan tsintacciyar magen ne da kishiyata.
Idan zai yiwu ina so a kaɗa min wannan tsintacciyar can duniya, ta nisance mu, kar ta ƙara waiwayar rayuwarmu. Sannan ina so kishiyata ta zama koma baya a gurin mijinmu, ya zama a duniyar rayuwarshi babu wata mace da zai dinga gani da haske sai ni."
Ko da ta gama saurarenta bata ce komai ba ta ci gaba da kallon kuɗin. Can kuma sai ta kalli Indo ta ƙara maida hankalinta kan kuɗin
"Gaggarumin bala'i nih hango tahe gare ki da iyalinki Indo, ita wagga ɗiya da kika kahwa wa ƙahon zuƙa zata tahi ta barku kamar yadda kika biɗa, amma ba yanzu ba da sauran lokaci, sannan tabbas zata bar wawakeken giɓi ga rayuwarki. Abu ɗai zani ƙara miki ga wagga batu nawa shi ne ki kula sosai, wagga ɗiya da munka yi duba a kanta sosai bata nuhinki da komai sai masifa, kamar yadda a kullun kika nuhinta da sharri.
Gobe ki sayi ƙwarya ta nono kindirmo ga bahillata da ɗaurin huhun goro ki aiko mana da shi. Tashi ki tai mun sallame ki."
A hanyarsu ta komawa gida hankalinta in yayi dubu duk sun tashi, cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka kaɗa jajur! Karime ta sha tsinuwa da Allah ya isa ita da tun farko ta kasance sila ta ɓullowar shaiɗaniyar yarinyar cikin rayuwarsu.
Magajiya dai sai dannarta take yi tana bata baki, da haka har suka ƙarasa bakin titi inda zata hau ƴar ƙumbula zuwa layinsu na mai dubun tsumma.
"Indo kar dai ki manta da Kwaryar nonon da Huhun goron."
Sai kuma tayi sasarai a tsaye
"Magajiya? kin san kuwa da har na manta? to ni ina zan samu kuɗi? siyo kayan nan fa hidima ta wajen dubu biyu da ɗari biyar idan ma basu haura hakan ba..."
"Wannan kuma ai matsalarki ce Indo, tunda kinci ladan kuturu ya zama dole kiyi masa aski. Idan ba haka in suka shanye miki hannu ko ƙafa wallahi babu ruwana, karki kuskura ki faɗi suna na.
Ki bar ganin Mai zobia kamar yarinya manyan baƙaƙen aljanu tamanin da takwas ne a kanta, su suka buɗa mata idanu tana bada maganin duk wani ciwo na duniyar nan. Na ga kanki yana rawa dan haka ki kula, ni kinga tafiyata."
Saboda haushi bata jira ta samu ƴar ƙumbular ba ta tsallaka titi ta koma gidanta, tana tafe a hanya tana ta mita kamar cin ƙwan makauniya.
****** ******
BAYAN KWANA HUƊU da faruwar al'amura a lokacin har Amirah ta ji sauƙi sosai ta fara zuwa makaranta.
Ana tashinsu bata tsaya wasa ba ta nufo gida kai tsaye, turus tayi a tsaye tana kalle-kalle, yadda ta ga mata har huɗu a ɗakin Maman ga Malam tsaye a bakin ƙofar yana ta sharce gumi alamun hankalinsa a tashe yake shi ne abinda ya ɗaga mata hankali, ta sake kallonshi a tsorace jin da tayi ko sallamarta bai samu sararin amsawa ba.
"Abba sannu da gida."
Ta faɗi muryarta a sanyaye.
"Yauwa Amirah, kin dawo? yi maza ki shiga ɗakin Indo ki canza kaya ki ci abinci kinji ko?"
Yayi maganar da sanyin murya, akwai alamun ruɗu da ɗimauta a muryarsa.
"To Abba"
har ta kusa shiga ɗakin Indo sai kuma ta juyo ta kalle shi.
"Mama bata dawo bane?"
Kafin yayi magana Indo ta fito daga banɗaki hannunta riƙe da buta tana gantsare-gantsare da ciccije baki, hannunta na hagu riƙe da kwankwasonta.
"Ke keh lafiya ko? kar ki kuskura ki shiga min ɗaki."
Ta daka mata tsawa ta ƙarasa jikin ƙofar da sauri ta tare bakin ƙofar dan kar Amirah ta shiga cikin ɗakin.
"Haba Indo, me yake damunki? baki ganin halin da Karime take ciki ne...?"
"Dan Allah Malam dakata. Ba fa na ce taje daji kunama ta harbeta ba, kuma ma naga tun kafin tafiyarta jejen ai ta tanadi abincin da ita ƴar gwal ɗin zata ci idan ta dawo makaranta, dan haka ta wuce ɗakin wacce take zamanta ba ni ba"
Wuf ta shige cikin ɗakinta tare da danno ƙofar ɗakin tana haki, hannu bibiyu ta sa ta dafe ƙirjinta zuciyarta cike fal da tunanin maganganun mai zobia.
'Wannan yarinyar tauraruwa ce mai wutsiya, ganinta sam ba alkhairi bane. A yadda take sam baza mu iya cutar da ita ba, amma idan muka bi ta jikin abokiyar zamanki muka raunata ta zaki iya samun cikar burinki na barin yarinyar cikin rayuwarki. Amma fa akwai matsala kafin faruwar hakan, wace irin matsala ce dai bamu sani ba.'
Ba tare da wani zuzzurfar tunani ba ko hangen abinda zai je ya zo kawai ta ce ta amince, ko ma mai zai biyo baya a shirye take.
'Da kyau! ki sa ido ranar laraba, duk abinda ya faru ga abokiyar zamanki mune sila. Makarin aikinki shi ne ki nuna tausayinki ga Karime a ranar larabar, idan kika yi hakan duk aikinki zai lalace, idan hakan ya faru mu kuma babu hannunmu.'
Duk waɗannan maganganun sun yi su ne ranar lahadi da ta je kai musu ƙwaryar nono da huhun goro kamar yadda aka umarce ta, tsabar masifa da son ganin burikanta sun cika ƙaramin gadon da yaranta suke kwana ta ɗaga ta saida a wulaƙance ga wata Dillaliya da take bayan layinsu.
Tayi matuƙar ƙoƙari gurin kiyaye duk sharaɗin aka gindiya mata, ido kawai ta zuba tana jiran ganin biyan buƙata. Tun misalin ƙarfe goma da rabi da aka kwaso Maman Ushe ranga-ranga daga gona kunama ta harbe ta ko kallo na mutunci da tausayi bata yi mata ba duk kuwa da yadda take ta gurmususu tana salati da sallallami dan tsananin azaban da take ji, anyi allurai an bata magungunan gargajiya amma har lokacin dafin bai daina yawo a jikinta yana wahalar da ita ba.
Yayyinta mata biyu ne a kanta sai manyan ƙawayenta guda biyu.
Amirah ko da ta shiga ɗakin ta ga yadda jikin nata yake sai ta fasa kuka, ko abincin ta kasa ci, rakaɓewa tayi a tsakar gida tana kuka da addu'ar Allah ya ba Mama sauƙi.
Suna cikin wannan halin aka aiko daga ƙofar gida wai ana sallama da Malam Ali, a firgice ya fita wajen da takalman ƙafarsa haɗin bauta.
"Malam Ali saƙo ne daga gidan Hakimi, yace lallai a tafi da kai da wannan baƙuwar yarinyar ƴar wajenka wacce mai ɗakinka ta tsinto. Tuhumar *MAITA* har biyu ne a kanta, mun samu labarin duk wanda yayi faɗa da ita a cikin mawuyacin hali yake ƙarewa, a taƙaice ma dai yarinya Raliya da Mal Murtala suna can fadar Hakimi cikin mawuyacin hali sai kiran sunanta suke yi, shi yasa aka bamu umarni lallai mu tafi da kai, ita, da kuma ita mai ɗakin naka da ta tsinto ta. Domin sarkin Mayu na hayin Mal Bello ya tabbatar mana da cewa samun warakarsu Mal Murtala ya rataya ne a wuyan ita wannan tsintacciyar yarinya ta wajenka bayan ta tsallaka su."
"Waw... wane irin magana kake min haka??? Amirar ce mayya? nawa take da har za a mata wannan ƙazafin?"
Mal yayi maganar cikin rawar murya da ɗimaucewa, sai sharce gumi yake yi kamar ya haɗiyi gatari.
Ko kafin ɗan aiken ya amsa mishi Inna Talatuwa ta fito a ruɗe tana hawaye
"Malam ka zo ka ga halin da Yaya karime take ciki..."
Da saurin gaske ta koma cikin gidan jin muryar Inna Asabe babbar yayarsu tana kwantsama salati mai tafe da ƙaƙƙarfar kuka.
"Dan Allah ayi min afuwa, a halin da ake ciki yanzu bazan samu amsa kira ba. Mai ɗakina wacce ta tsinto wannan yarinyar da kake magana ita ce a cikin mawuyacin hali na rai kwakwai-kwakwai. Ita kuma yarinyar tana makarantar boko bata dawo ba"
Bai jira amsawarshi ya faɗa cikin gidan da sauri dan ganin a wane hali ake ciki.
'Matsiyaciya, Annoba. Da zata mutu ma da an rage mugun iri...'
Haɗa idanun da tayi da Amirah yasa gabanta ya buga dam! Duk da idanun yarinyar ciccike yake da ruwan hawaye hakan bai ɓoye canja launin da ƙwayoyin idanunta suka yi ba.
Ta balla mata harara, da masifa ta ce
"kallon me kike min haka?"
Bata yi magana ba, tsawon wasu daƙiƙu suna musayar kallo sai kuma Amirah ta fara matsawa kusa da ita, daman suna tsaye ta can bayan banɗakin gidan ne inda aka shuka rama da zogale. Indo tana tsinkar rama ne ta jiyo salatin da Inna Asabe tayi shi ne take zancen zuci da fatan Maman Ushe ta mutu ba tare da sanin zancen zucinta ya fito fili ba.
Idanunta sun rufe da tsananin son cikar burinta ba ta da masaniyar Amirah tana rakuɓe a can gefe guda inda in ba tsananin lura mutum yayi ba ba lallai ya ganta a gurin ba.
Ta tsorata sosai da yadda ta ga yarinyar ta nufo ta amma sai ta maze ta tsaya ƙyam dan ta ga abinda zai faru, a duke dai ta san baza ta doku ba.
"Fata kike yi Mama ta rasu ko? to ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, burinki zai cika. Amma fa ke ma zaki mutu, idan kuma za ki zauna gadin duniyar ne to ga ki ga ta nan."
Bata ƙara cewa komai a kan haka ba ta fice daga gurin, ta barta a tsaye ƙiƙam kamar wacce aka zare wa laka.
Wani abin mamaki kuma sai jikinta yayi mugun sanyi, zuciyarta ya cika da wasu tunane-tunane marassa amfani. Tsananin tsoro da fargaba ya kama ta, ramar da bata ƙarasa tsinka ba kenan a saluɓe ta bar kwanon da ta fara zuba wanda ta tsinka a ciki ta kama hanyar komawa ɗakinta.
Kamar ta leƙa ta ga halin da Karime ke ciki sai kuma ta fasa shiga ɗakin.
Tana daf da shiga ɗakinta taci wani mugun tuntuɓe da dandamalin ƙofar ɗakinta ta kifa ciki, ƙwalla ihu tayi a gigice nan da nan jini ya ɓalle mata ta hanci ta baki.
A wannan lokacin su Malam suna zagaye da Maman Ushe da jikinta ya saki gaba ɗaya, alamun mutuwa ya baiyana a jikinta ƙuru-ƙuru, da ganin haka ba ɓata lokaci Malam ya fara biya mata kalmar shahada tana maimaitawa a hankali cikin shaƙewar murya, matan kuma sai kuka suke yi zuciyarsu na ƙara cika da tsananin tsoron Allah, lallai mai rai ba a bakin komai yake ba.
Tashin hankalin da suke ciki yasa ba wanda ya bi ta kan ihun da Indo tayi, daman duk suna cike da ita ganin yadda take nunawa a fili ciwon Maman Ushe bai dame ta ba. Ta biya kalmar shahada sau huɗu a na biyar mala'ikan mutuwa ya zare ranta.
BILHAƘƘI
Ta sake shan gabanshi cikin matsanancin kuka, zazzafar marin da ya kimtsa mata ma shanyewa tayi ta girgije kamar ba ita ya mara ba, ita kam ta gaji, ta kai maƙura gurin gajiya da mugayen halayensa da na ƴan'uwansa. Yau gara a yi ta ta ƙare a tsakaninsu. Ta cigaba da magana a hargitse cikin kuka.
"Masa'udu ya kake so inyi maka ? so kake in dinga bauta maka? to bari ka ji, duk yadda kake ganina kamar wulaƙantacciya wacce bata da wani makomar da ta wuce ta inuwarka da nake a ƙarƙashinta bazan zauna da ƙuruciyata ka ƙarasa kashe min rayuwa ba. Kar ka manta na canza abubuwa da dama saboda kai, na rabu da ƴan uwana da iyaye na duk saboda makahon son da nake maka, na rabu da addinina na shigo naka saboda tsananin son da nake maka. Amma saboda kai butulu ne duk waɗannan sadaukarwar da nayi dan kai baka kalle su a matsayin abinda zaisa ka mutuntani ba? A shekarunmu na biyar da aure ban tsinci komai da zan iya ƙararwa na jin daɗin rayuwa ba a gurinka da azzaluman ƴanuwa da mahaifiyarka..."
Kafin ta rufe baki ya kai mata wani ɓarin makauniya nan take tayi juyin masa a tsakar ɗakin.
Ƙaƙƙarfar ihu ta ƙwalla a gigice dan tsananin azaba ta sake tashi gadan-gadan tayi kanshi da dambe tana yaƙushinshi haɗe da cizo duk ta inda ta samu dama, shi kuwa ya ware ƙwanji