Showing 81001 words to 84000 words out of 98260 words

Chapter 28 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

220

Middle Ads

ƙaran da yake yi. Nan wani irin mugun wari da tsananin ɗoyi ya turnuƙe ɗakin, ga wani hayaƙi da yake tashi da ƙauri kamar na ƙonewar wani abu mai bala'in wari.

Su Madam da sauran ƴan ƙungiya sai guje-guje suke yi hankalinsu a tashe suna neman wajen ɓuya, sunsan yau sai dai wani ikon Allah. Da alamun ƙarshensu ne ya zo, ga shi kuma sam tsafinsu na ɓacewa ya ƙi aiki a daidai wannan lokacin, kamar makafi kuma ganin ɗakin tsafin suke yi a dunƙule kamar ƙwallo, sun rasa hanyar da za subi su fice daga ciki.

Oga kuwa da ya fahimci manufarta na son kawo ƙarshen komai da kowa na cikin ƙungiyar a zuciye ya miƙe tsaye ya tashi sama suuuu sai ga shi a gabanta, hannunshi ya miƙa da ya zama kamar wani igiya ya shaƙo wuyanta ya matse sosai yana ƙoƙarin hallakata.

Nan fa ta fara kakari da fisge-fisge tana zazzare idanu, duk yadda ta so ita ma ta shaƙo shi suyi mutuwar kasko hannunta sam ya ƙi kaiwa wuyansa.

A daidai wannan lokacin kuma da tsananin ƙarfin addu'a Allah ya ba su Maheer ikon shiga cikin gurin, don da farko ko da suka isa gurin suna kallon ƙofar shiga gidan amma da sunyi yunƙurin shiga sai wani ƙaƙƙarfan iska ya watsar da su baya. Sun jigata sun wahala sosai, wani tunani da ya ɗarsu a ran Maheer yasa ya fara karatun Alƙur'ani da buɗaɗɗiyar muryarsa mai daɗin sauraro, Luƙman ya rufa masa baya, sai kuma ƙalilan daga cikin musulman cikin ƴan sandan suma suka rufa musu baya da karatun.

Da wannan karatun suka sake dosar ƙofar gidan bisa ga mamaki ga sauran jami'an da ba musulmai ba sai suka ga sun danna kofar gidan sun shiga ciki, aka bar sauran jami'an a waje, domin har lokacin su sun kasa shiga.

Ko da suka shiga gidan sai suka ga ɗaki ne ƙwalli ɗaya a tsakar gidan, da suka shiga ciki ta tsakiyar ɗakin suka ga matattakala ya gangara can ƙasa, ta wannan hanyar suka bi sai ga su a tsakiyar gurin meeting ɗin.

Ganin abinda yake faruwa a saman ɗakin tsakanin Oga da Bilhaƙƙi yasa cikin sauri Luƙman ya saita ƙafar Oga ya sakar mishi harbi bayan yayi basmala da ƙarfi. A gigice ya sake ta zata faɗo ƙasa da saurin gaske Maheer ya caɓe ta faɗa hannunsa, shi kuwa Oga yana riƙe ƙafarsa ya faɗo ƙasa tim yana rarraba idanu tsakaninsu.

Kafin yayi wani yunƙuri na yin tsafi Luƙman ya sakar masa wani gigitaccen naushi a mahangurɓa. Ihu ya sake ya buɗe baki zai yi wani abu ɗaya daga cikin jami'a ya sake sakar mishi harbi a kafaɗa. Nan Luƙman ya ci gaba da sakar mishi naushi da zafafan maruka a kumatun dama da hagu, sai da ya farfasa mishi baki da kumatu a kumbure wasu jami'ai uku suka cukwuikwuiyeshi aka maƙala mai ankwa hannu da ƙafa.

"Duk wanda ya sake motsawa zan harbe shi har lahira."
Luƙman yayi furucin cikin tsawa tare da sakin wani ƙaƙƙarfan harbi a saman ɗakin.

Nan su Madam kowa ya tsaya a tsorace yana rawan banjo saboda gigita. Ɗaya bayan ɗaya aka iza ƙeyarsu zasu fice daga ɗakin.

Bilhaƙƙi na saɓe a kafaɗar Maheer cikin wani mawuyacin hali, sun kusa fita gaba ɗaya daga ɗakin tayi magana da ƙyar muryarta na ciccijewa
"Gan...gaa...ran...! Umma...ta..."

Nan fa suka sake komawa ciki a gigice amma duban duniya sunyi basu ga Rebecca ba. Babu komai a ciki sai wani ɗan ƙaramin ɗaki mai ɗauke da wani ƙaton Gunki da tarkacen kayan tsafi, sai kuma nan babban falon da suke meeting ɗin ƙungiya.

Hankalin Maheer da Lukman idan yayi dubu ya tashi, ga Bilhaƙƙi a lokacin ta suma bata san inda kanta yake ba. Anyi tambayar duniya Madam Mary da Oga sun ce basu san inda Rebeccah take ba. Sai da Lukman ya tattarasu kaf Oga da sauran ƴan ƙungiya ya ce ya rantse da girman Allah idan basu faɗa mishi inda suka ɓoye Rebeccah ba zai harbe su ɗaya bayan ɗaya sannan ya kulle su a cikin gidan ya cinna musu wuta.

Jin hakan da suka yi ne ya kaɗa hanjin cikinsu, Mercy ta ce sun ɓoye ta ne a gidanta da ke Sabon tasha. Jin hakan yasa aka kwashe su gaba ɗaya zuwa caji ofis, Lukman ya bada umarnin aka cinnawa gidan wuta, gurin ƙonewar gidan sai fashewar wasu abubuwa da iface-iface suke ta ji marassa daɗin sauraro.


******* ********


A can Masarautar Bauchi na Abdulfahi na biyu kuwa labarin yadda ɗansu Almustapha yayi rayuwa a cikin duniya ya jijjiga tunaninsu.

Anyi wa Baffah Yalleru kyauta mai girma cike da sakayyar alkhairi da alkhairai. Lokacin da zai koma gida Takawa ya haɗa shi da dogarai don a ga mazauninsu, aka raka shi har rugarsu ɗauke da sha tara ta arziki.

Basu ɗauki al'amarin iyalan Mustapha da wasa ba, ran Takawa yayi mummunan ɓaci da jin abinda ya faru da ɗansa na cikinsa ƙarƙashin masautar Zazzau.

Yasa magatakarda ya rubuta doguwar wasiƙa ya tada jakada tun daga Bauchi har masarautar zazzau akan abinda ya faru da kuma abinda yake buƙata ayi mishi yanzu.

Sarkin Zazzau ma sam baiji daɗin abinda ya faru ba, domin akwai ƙawance mai girma a tsakanin masarautun biyu. Ya maida saƙon wasiƙar ban haƙuri sannan ya ce za a shirya komai kafin isowarsu. Shi ma Sarkin Zazzau ba tare da ɓata lokaci ba ya tada jakada har zuwa masautar kajuru da abinda yake buƙata a tabbatar mishi kafin isowar Sarki Abdulfatahi na biyu.

Nan fa hankalin Sarkin kajuru ya tashi, domin abinda ya faru ko kusa bai samu labari makamancinta ba. Jami'an Soji da suke bada tsaro a nan ƙaramar hukumar kajuru saboda yawan rikice-rikicen da ke faruwa na ƙabilanci ya ɗiba ya haɗa su da dogarai suka tafi har ƙauyen Gefe dan a binciko labarin halin da Rebeccah da ƴarta Bilhaƙƙi suke ciki. Amma wani abin ban takaici basu sami wani gamsasshen bayani game da yarinyar ba, Rebeccah ma wai wasu da ba a san ko su waye ba sunje garin da sojoji kwanaki can sun tafi da ita.

Jin zaluncin da suka aikata yasa Sojoji da umarnin Sarkin kajuru suka kama Zidane da duk abokansa da suke da hannu a cikin aikata al'amarin, Pastor Nuhu, Luka mahaifin Rebeccah aka wuce da su Kaduna aka watsar a State CID bayan anyi musu mugun duka an sauya musu kamanni, shi Zidane ma har da karaya a kafarsa ta hagu, da hannunsa na dama amma ko ta kanshi basu bi ba.

Samun cikakken labarin rasa Rebeccah da ƴarta Bilhaƙƙi ne ya dakatar da zuwan Sarki Abdulfatah da jama'arsa. Yarima Mustapha kam ƙara shiga cikin tashin hankali yayi da tunanin wane hali iyalinsa suke ciki? A dole dai yake ƙoƙarin danne damuwarsa ganin yadda Takawa yasa aka tara manyan malamai suka fara karatun Alƙur'ani don yin sauka, da yin addu'ar duk inda iyalanshi suke Allah ya baiyana su da gaggawa. Ga kuma yadda ta ko wane ɓangare Iyaye da kakanninshi da sauran masu muƙami a masarautar kowa ƙoƙarin faranta mishi yake yi.

"Ƙarya ne wallahi. Mustapha bazai taɓa dawowa ba, Na shuri ya tabbatar min yadda Mustapha ya bar nonon uwarsa bazai taɓa komawa ba haka yadda ya bar masarauta bazai taɓa waiwayarta ba..."
Da sauri Chiroma da ya shiga ɗakin a lokacin ya haɗa hannuwansa duk biyu ya toshe mata baki hankalinsa a tashe, ƙasa ƙasa ya fara zabga mata masifa kamar tana jinsa
"Ki yiwa girman Allah Yaya Safara'u ki rufa mana asiri ki daina wannan sambatun tona mana asirin da kike yi. Mustapha dai tabbas ya riga ya dawo masarauta ni da idanuna na ganshi. Gara ma ki farfaɗo ki daina wannan sambatun da kike yi ko zamu san na kwatanci. Idan ba haka ba kina ji kina gani mulkin da kika yi shekara da shekaru kina ƙwaƙwa da tanadi a kai zai suɓuce miki..."

Wal kamar kawo wutan nepa ya ga ta buɗe jajayen idanunta duk biyu ta zuba su a kansa. Da sauri ya cire hannunsa a bakinta ya ja da baya a tsorace.

Yunƙurawa tayi daƙyar ta miƙe zaune tana ciccije fuska, a hankali ta buɗe bakinta da yake mata wani mugun ɗaci kamar wacce ta kurɓi maɗaci ta ce
"Chiroma da gaske ne Mustapha ya dawo masarauta?"

Sai da yaja da baya sannan ya amsa ta
"Ƙwarai da gaske ne Yaya. Ni ganau ne ba jiyau ba..."

"A wani hali Muzaffar yake ciki?"
Ta sake tambayarshi a cije tana wani jijjiga ƙafafu irin na bosawa

"Har yau ba wani canji, ciwonshi sai gaba yake yi. Yanzu fa ɗakin da yake ciki ma indai ba alurar bacci aka zurkuɗa masa ba babu mai iya shiga. Hauka tuburan yake yi! A wani ƙaulin ma naji ƙishin-ƙishin Mai martaba ya bada umarnin a kaishi asibitin mahaukata na garinnan..."

"Je ka karɓa min takardar sallama gurin likita. Yanzunnan!"
Ta ƙarasa maganar haɗe da daka masa wani gigitaccen tsawa.
A sukwane ya fice daga ɗakin kamar zai kifa saboda sauri.

Ƙasa ta ƙurawa idanu har lokacin ƙafafunta basu daina girgiza ba. Sunƙi-sunƙin tashin hankali da damuwa ne danƙare a zuciyarta amma tana ƙoƙarin dannewa.

Lallai Tauraruwa mai wutsiya ta cika hatsabibiya, tun bayan bayyanarta manyan masifu da damuwoyin da take tunanin ta shafe babinsu a doron ƙasa take ta tono mata. Wani abin mamaki a tarihin rayuwarta sai ga hawaye ya zubo mata shar...

'Ita Safara'u ƴar sarkin wokari yau ita ce take zubar da hawaye a kan Safiyya? Shekarunsu takwas da sarki Abdulfatahi ya auro Safiyya ƴar mitsitsiyar yarinya mai shekaru goma sha biyu. Safiyya ƙanwar matar wazirin Maru ne abokinsa, daga kai ziyara ya ganta ya ji yana so nan take kuwa aka aura mishi ita.

Da farko ta ɗauki yarinyar ne a matsayin wulaƙantacciya masu haye a sarauta, ta ci gaba da zuba mulki yadda take so. Hankalinta bai fara tashi ba sai da taga Safiyya da ciki bayan shekaru biyu da auro ta, ita mai shekaru goma da auren mai martaba ko ɓatan wata bata taɓa yi ba.

Duk yadda ta so zubda cikin Allah bai nufa ba sai da aka haifo Almustapha, tun daga nan ta ɗau karan tsana na duniya ta ɗora masa. Ido rufe ta fara neman hanyar da za ta kauda shi amma bokan da Jakadiya ta kawo mata na shuri ya ce dole ta jira sai ya shekara sha biyar.

A shekaran da Mustapha ya ɓata Allah ya bata ciki ta haifi Muzaffar bayan uban magungunan da ta karɓa hannun malamai mabanbanta.

Dukda ta haife shi tun yana ƙarami da ɗan matsala kamar wawa wannan bai dame ta ba, hausawa sunce da hanau gara mannau. Duk yadda za a yi dai shi ne babban ɗan mai martaba da bayan mutuwan sarki zai gaji mulki. Haka ta ci gaba da murza mulki a cikin gidan yadda take so, kowa a ƙarƙashinta yake, a zuciyar mai martaba ita ce gaba. Ita ce uwar Magajin sarki.

Ɓullowar ciki kwatsam a jikin Safiyya bayan shekaru ashirin da ƴan kai da ɓatan Mustapha abin yayi mugun ɗaga mata hankali. Ita tasa Malamai sukai ta kwantar da cikin har lokacin haihuwar ya wuce sosai, ko an ɗaura mata ruwan naƙuda sai dai ta ƙaraci shan azaba ta wartsake ba haihuwa babu alamarta.

Rayuwarta ta ko ina yayi haske, ta gama ganin gaggarumin hadarin ruwan farincikin cikan burinta a ko wane lokaci zai iya ɓallewa. Sai yanzu kuma kwatsam a ce komai ya tarwatse? haskenta da sannu sannu yana ƙoƙarin dusashewa? Bazai yiwu ba, tabbas baza ta taɓa bari haskenta ya dusashe cikin lokaci ƙanƙani haka ba. Tunda ta samu labarin Safiyya ta haifi ƴan biyu ta sume sai da ta kwana ta yini bata farfaɗo ba, ta farfaɗo ke nan kuma Jakadiya ta tare ta da labarin dawowar Mustapha, tsananin gigita yasa ta ƙara sumewa...'

"Yaya ga takardar sallamar na karɓo."

Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tare da katse duk wani tunani da take yi, ta yunƙura da ƙyar ta miƙe ta bi bayansa.



BILHAƘƘI


Tun isarta gidan ta samu irin tarbar da take buƙata daga gurin bayi da barorinta. Sai kai kawo suke yi suna shige da fice da yi mata fatan ƙara samun sauƙi.

Hatta Mai babbar ɗaki (Umma mahaifiyar Takawa) ta aike Jakada na musamman a ce mata tana mata sannu da jiki da barka da dawowa. Uwar soro ma ta aika ɗan aike dukda ta ji haushin rashin zuwanta da kanta.

Abinda ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai shi ne ganin babu Takawa kuma ba ɗan aikensa. Daman tana ƙule da shi akan faɗa mata da Chiroma yayi tun da ta kwanta tsawon kwanaki biyu a asibitin sau ɗaya ya je duba halin da take ciki.

Tana hakimce a falonta tayi ta zuba idon ganin Mustapha ya je kai gaisuwa gare ta amma shiru take ji, har aka idar da sallar isha'i. Dan haka ta aika gurin Fulani Safiyya a faɗa mata ga ta nan zuwa ganin jarrirai da murnar dawowar ɗanta Mustapha.

"Amma Ranki ya daɗe kina ganin za ki iya zuwa?"
Jakadiya ta tambaye ta tana mamakin ƙarfin halin da take gwadawa gurin ɓoye ɓacin rai da tashin hankalin da take ciki.

"Eh zan iya. Gara inje Jakadiya. Annamimiyar nan ta riga ta tarwatsa duk wani aikin da Na shuri yayi min. Yanzu idanun kowa zai kasance a kaina ne, rashin zuwan nawa zai ɗarsa wani zargi a zuciyar ma su burin ganin baya na, ni kuma sam bana son haka.

Ke dai ki tabbatar kin shirya yadda zan gana da Na shuri a daren yau, da zafi-zafi gara in tari komai kafin al'amuran su ƙarasa lalacewa."

"To shi kenan Ranki ya daɗe. An gama! Allah ya iya mana da iyawarsa."

Bata amsa addu'ar ba har ta fice daga falon cikin rakiyar bayi da kuyanginta ta nufi ɓangaren Sarauniya Safiyya.

Duk yadda lungu da saƙo da ko wane kusurwa na cikin falon yake tashin daddaɗan ƙamshi sai wani huhhura hanci take yi tana basarwa kamar ta shaƙi wawwaran tusa. A hakimce ta zauna a kan kujeran kamar falonta, wani abu da tayi da ya bugi ran Sarauniya Safiyya ko da su Mummy suka kai mata jariran ƙin karɓarsu ta yi, ta wani yanƙwane fuska tana lelleƙa fuskokinsu daga nesa.
"Na gansu! ku mayar da su kawai."
Tayi maganar tana alamar kore su da hannu a wulaƙance. Ta maida hankalinta kan Safiyya ta ci gaba da cewa
"Safiyya waɗannan yara ƴan firirit da ganinsu an ga kalar hanji. Yadda tsufa ya fara kama ki ma anya za su sami ruwan nono a jikinki?"

Murmushin yaƙe tayi wanda ya fi kuka ciwo, da fari rasa abin cewa tayi tana ta jan a'uziyya a zuciyarta. Don yadda zuciyarta ke lugude da ɓacin ran action ɗin Fulani Taka da kuma irin baƙaƙen kalaman da ta sassaƙa mata idan ta buɗe baki tabbas zazzafar baƙa za ta faɗa, tsawon daƙiƙu casa'in zuciyarta ta fara sauka saboda addu'oin da take yi. Ta sake gyara zamanta akan kujerar da take kai tana ta sakin murmushi kamar ba ta da wani ɓacin rai
"In banda abin Fulani Safra'u, haihuwar da ba ni na isa inba kaina ba ai kinga bani da ikon haifosu yadda kike so. Kuma cikin hukuncin mai kyauta da ƙari maimakon ya bani ɗaya ƙato sai ya bani biyu lafiyayyu. Allah da yayi wannan ikon a kaina ai kinga shi zai tsatso da ruwan nonon da zasu sha su ƙoshi. Kinga yau kwanansu biyu har yau basu fara shan madara ba saboda suna da wadataccen ruwan nono a jikin wannan tsohuwar dai da take zaune a gabanki..."
Sallamar Mustapha da sa kanshi a cikin falon yasa ta maida hankalinta kanshi tana murmushi.

Ita kuwa Fulani Safra'u bata gama farfaɗewa daga suman baƙaƙen kalaman da ake caccaɓa mata ba ta tsinci muryar Mustaphan a cikin falon. A hankali ta ɗaga jajayen idanunta ta mayar a kanshi. Gabanta ya yanke ya faɗi daram da taga ingarman jarumi lafiyayyen matashin da yake tafe a nutse har ya zauna kusa da ƙafafun Fulani Safiyya. Babu inda ya bar mahaifinsa kamar Abdulfatahi yayi kaki ya tofar. Kanta ne ta ji ya fara juyawa da ita kamar ana kaɗa ta a jikin fanka, nan ta fara gani bibbiyu kamar mai ciwon hawan jini, a sama ta tsinci muryar Safiyya tana cewa

"El-Mustapha baka ga Ummanka a zaune ba? ta shigo ganin ƙannenka ne da murnar dawowarka. Duk da itama ta cancanci a je mata barka da murnar bayyanar babban ɗanta"
Fulani Safiyya ta faɗa tana nuna mishi ɓangaren da Fulani Taka take zaune, fuskanta cike wani lallausan murmushi. Zuwa wannan lokacinta ranta fes dan furzar da kyawawan martani masu cike da hikima da tayi ya goge duk wani ɓacin rai da shigowar Fulani Taka ta ƙunsa mata.

Hankalinshi ya maida inda take nuna mishi fuskarsa da ɗan murmushi. Ya ɗan sunkuyar da kanshi alamun girmamawa
"Ranki ya daɗe barka da dare. Mun so mu shigo har can ɓangaren muyi miki sannu da jiki, amma sai muka yi tunanin mu bari ki huta zuwa gobe. Allah ya ƙara miki lafiya."

"Ameen"
Ta amsa a daƙile kamar mai ciwon haƙori, ƙirjinta sai lugude yake yi. A muryarsa ma cike da kwarjini sak irinta Mahaifinsa Abdulfatahi. Jin da tayi baƙin ciki na neman karta da sauran kwana ga yadda idanunta suka ciccika da hawaye, baƙin ciki ƙarara baiyane a fuskarta yasa da sauri ta miƙe da nufin ficewa ba tare da ta yi musu sallama ba.

Taga-taga tayi kamar za ta kifa ta yi saurin dafa kujera tana jin saukar muryar Mustapha a kunnenta kamar yana doka taɓarya a ƙirjinta.

"Subhanallahi. Hattara dai Umma."

A sukwane ta fice daga falon tun kafin damuwa da baƙin ciki su ci ƙarfin zuciyarta su burtso waje, asirinta ya tonu ta hanyar fashewa da kuka.

"A huta gajiya Ranki ya daɗe."

Tsananin ruɗewa da ɗimauta ya hana ta gane a cikin su biyun wa yayi mata wannan sallamar mai kama da ta rainin wayau?


****** *******


Tsawon awa biyu ke

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login