Showing 48001 words to 51000 words out of 98260 words

Chapter 17 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

215

Middle Ads

ta ƙi amsawa. Sai da ya kasa kunne sosai sannan ya ji kamar shessheƙar kuka.

Yaye labulen ƙofar yayi yana kallonta, yadda ta ƙudundune a kan gado tana kukan sai abin ma ya bashi dariya, kamar wata ƴar Bebi.
A hankali ya shiga cikin ɗakin yana ƙare mata kallo har ya ƙarasa kusa da gadon
"Keeee... kukan fa? Uhmm! Wa ya taɓa ki?"

Kanta na tsakankanin cinyoyinta take tura baki, a zuciyarta ta ce
'Ko rarrashi ma bai iya ba.'
Kasa haƙuri tayi ta ɗago da kanta fuska jage-jage da hawaye ta galla mishi harara, ta sake maida kanta ƙasa ta ci gaba da kukan.

"Kukan na shagwaɓa ne kenan?"
Ya taɓe baki ya ci gaba da cewa.
"Madallah! Ci gaba da yi. Ni bari in wuce tunda ba ki da abin cewa."

Jin zai tafi da sauri ta ɗaga kanta ta kalle shi, sai taga yana nan inda yake tsaye.
"Toh ba kai bane..."
Sai kuma tayi shiru ta juya mishi ƙeya tana kumbure-kumbure da baki.

Ya kalli gashin kanta da yake yala-yala mai yalwa ba laifi, ba shi da cika sai tsawo, washar da shi a ido kamar tayi saloon, ya sauka har ƙasan kafaɗunta, rabin kan a tsefe rabi a kitse.
"Amma ba na hana ki zama babu ɗankwali ba?"
Yayi maganar a tausashe.

Da sauri ta yayimi hijabinta da yake ajiye a gefe ta rufe kan, ta juyo gaba ɗaya tana kallonshi idanunta a nannarke.
"Ayya mana Ya Maheer ayya... dan Allah ka bani in ƙarasa zuwa dare ka ji?"

"Na ƙi"

"Dan Allah fa na ce?"

"Tom na ji."

"Za ka bani?"
Ta tambaye shi cike da ɗoki tana murmushin farin-ciki.

"A'a! yanzun nan fa kika gama galla min harara..."

"Ayya mana... to yi hakuri ka ji Yaya Maheer ɗina? Magajin Malam. Babangidan Ummee da Mummy. Gangaran ɗin Bilhaƙƙi da gaskiya ba da kanka a sare ka je gida ka ce ya faɗi."
Ta ƙarasa haɗe da ƙyalƙyalewa da dariya da sauri ta koma can cikin gadon ta duƙunƙune kanta da bargo, har lokacin bata daina dariyar ba.

Shima murmushi yayi kawai yana kallonta, ya rasa inda ta koyo harhaɗa wannan sunayen da kirarin da take mishi a wasu lokutan, duk da ta canza sosai amma har lokacin wannan masifaffen surutun nata musamman a gabanshi bata daina ba.
"Zo kiji."

Maƙale kafaɗa tayi alamun ta ƙi.

"Shi kenan! ashe bakya son wayar."

"Laaa ina so mana, dan Allah ka bani."
Ta dirgo daga kan gadon ta bi bayanshi suka fice daga ɗakin. Da sauri ta cimmishi a falon suka jera kafaɗa da kafaɗa dukda ya kere ta tsawo sosai.

"Allah zan cewa Malam ya sai min waya tunda jan rai kake min duk sadda na ce ka bani aro..."

"Karki ce mishi, zan sai miki nan gaba kaɗan idan lokaci yayi"
Ya faɗa muryarsa ƙasa-ƙasa ganin sun kusa isa inda su Ummee ke zaune a tsakar gidan suna shan iska.
Gaishe su ya sake yi a karo na biyu yayi musu sallama da cewar zai wuce gida. Saƙon gaisuwa ga matansa suka bashi ya kama hanyar ficewa daga gidan tana biye da shi a baya.
"Ba ni to."
Ta faɗa tare da miƙa mishi hannu.

Wayarsa ya zaro a aljihu ya miƙa mata, sai da ta kusa karɓa sai ya janye wayar ya hanata.
"Awa ɗaya kacal na baki Yarinya zan dawo in karɓi wayata."

"Eh na yarda."
Ta amince da sauri tare da miƙa hannu a karo na biyu.

"Ke na ma fasa..."

"Ummee kin ga..."

"Riƙe riƙe ba dan halinki ba."
Ya miƙa mata da sauri ta fisge ƙiris ya rage wayar ta faɗi a hannunta tayi saurin cafewa.

"Bilhaƙƙi ya aka yi?"
Mummy ta tambaye ta daga can inda suke zaune, hankulansu ita da Ummee duk yana kansu.

"Ba komai Mummy."
Ta waigo kanshi tayi mishi gwalo ta juya cikin gidan da sauri.
"Ka gaida Antoci na"

Ya tsinkayi muryarta lokacin da take daf da shigewa ɗakin Ummee. Murmushi kawai yayi ya fice daga gidan, ya ɗauki motarsa a ƙofar yaja da sauri ya nufi gida ganin magrib ta kawo jiki, baya so a kira sallah yana hanya.

Ita kuwa can cikin ɗaki ta ƙule tayi ɗai-ɗai a kan gado ta buɗe wayar, wani korian film mai kyau ta ɗauko a youtube yau kwanaki uku kenan, ta fara kallo sai ya amshi wayarsa. Shi yasa kullum idan ya shigo ta dinga binshi tana mishi na ci kenan shi kuma yana ja mata rai, sai yau Allah ya ɗora ta a kanshi ya sake bata wayar.

A hankali zamanta a gidan yasa wani gwaggwaɓar shaƙuwa ya shiga tsakaninshi da ita. Tun yana ɗari-ɗari da ɗaɗɗaure mata fuska har ya watsar da komai yake kallonta da babbar matsayi irinta Yaya da ƙanwarsa.

Idan ya shiga gidan bai ganta ba ya dinga damuwa kenan yana nemanta ɗaki-ɗaki tunda sam ba fita take yi ba. Idan bacci take yi haka zai ta jan ƙafa ko zata tashi, idan bata tashi ba sai ya fice yana jin wani irin babu daɗi a zuciyarsa.

Ita da Saudat da suke sa'anni kansu a haɗe yake, danma ita Bilhaƙƙi bata saba irin harka da sa'anninta ba sai ya zama ta fi sakewa sosai da su Ummee.

Ta fara kallon kenan kiran Surayya ya shigo wayar, ta gane hakan ne ta hanyar sunan da yayi saving ɗin lambarta.
"First wife"
Ta maimaita a fili tana kyaɓe baki, shere wa tayi har kiran ya katse ta sake maida hankali kan kallon da take yi.
Ganin kiran ya sake shigowa a karo na biyu kawai sai ta danna madannin amsa kira ta ɗauka, lokacin da kiran yake gaf da tsinkewa.
"Sweetat ina ka tsaya ne?"

Duk yadda taso danne dariyar ta kasa, sai da ta ƙyalƙyale da dariya jin yadda Surayyan ta maƙe murya ita a dole shagwaɓa take yi wa miji.
"Aunty ba shi bane, yana hanyar zuwa gida. Kila ma yanzu yana daf da isa..."

"Ke dakata da Allah ! Faɗa min, me wayarshi take yi a hannunki?"
Ta tambaye ta cikin fushi da ɗaga murya, sarai ta ji dariyar da ta yi mata kuma ta san da ita take yi.

Wata dariyar ta sake yi, cikin rashin damuwa da tsawar da tayi mata ta ce
"Tunda yana hanyar gidan idan ya isa sai ki tambaye shi. Bye... ki gaida ɗayan Auntyn."
Ta katse wayar tana ci gaba da ƙyalƙyala dariya da gangar dan dai ta ƙara kunnata.

Ta kuwa ci nasarar hakan, dan sansarai tayi da wayar a hannunta ranta a ɓace, ita dai har a zuciyarta Allah ya sani ta tsani wannan Bilhaƙƙin. Ba dan komai ba kuwa sai dan irin yadda take wani shisshige wa mijinta bayan kuma basu haɗa komai ba. Ta ja tsaki ranta yana ƙara ɓaci, bari ya koma gidan zai same ta
'cikin hikima zan bugi cikinshi inji wai me ke tsakaninsu ne ma? Kar muna nan sake da baki garin kallon ruwa kwaɗo yayi mana ƙafa.'
Ta sake jan tsaki a karo na biyu zuciyarta na ƙara ƙuntata
"Shegiya da wani ƙulu-ƙulun idanu irinna mage."
Ta faɗa a fili tana yanƙwane fuska kamar za ta fashe da kuka.

Tana nan zaune har ya isa gidan, da yake gwana ce gurin ƙwarewa da abar sai ta watsar da komai a fuskarta ta fara tarairayarsa, dan ranar girkinta ne.

Bata tarbe shi da maganar komai ba har ta haɗa mishi ruwan wanka ta taya shi ya sheƙa wanka, ya ɗaura alwala ya fice zuwa masallaci. Ko kafin ya dawo ta kusa cika ɗan madaidaicin teburin cin abincin da kala-kalar cimar da ta shirya mishi. Yana dawowa a gurguje ta barshi ya leƙa Rabi dan ganin halin da ta yini ya dawo ta ja shi zuwa gurin cin abinci.
"Ai na kira wayarka na ji wannan baƙuwar yarinyar ta gidan Malam ta ɗauka..."

"Yanzu ai ta wuce baƙuwa, ta zama ƴar gida."
Ya katse cikin yanayin rashin ba wa maganarta muhimmanci.

Ba ta daddara ba ta sake cewa,
"Hakane kuma. Amma fa nayi mamaki sosai, dan har saida na tambayeta me wayarka take yi a hannunta amma sai tace min idan ka dawo in tambaye ka."
Ta ƙarasa maganar fuskarta na burtso da yanayin ɓacin ran da take ta dannewa a can ƙasan ranta.

Ya kalle ta sosai, sai kuma yayi murmushi ya ci gaba da shan fruit salad ɗin da ta haɗa mishi.
"To shi ne kike tambayar tawa kenan kamar yadda ta umarce ki...?"

"A'a fa!"
Ta katse shi da sauri, ta ɗanyi murmushin yaƙe tare da saurin gyara zancen tun kafin ya ƙara cewa komai.
"Kawai dai ganin yadda kake kaffa-kaffa da wannan babbar wayartaka saboda muhimman abubuwan da kake adanawa a ciki yasa nayi tambayar. Bayan wannan babu komai Sweetat."

Shiru yayi kawai bai tanka mata ba, dan ya kwantar mata da hankali sai ya haske ta da tattausan murmushi mai narka zuciya. A can ƙasan ransa ya ce
'Mata? mata? sai a barsu da halinsu na kishi'


*******

A cikin waɗannan watannin da suka gabata abubuwan duk sun zo wa Malam da iyalan gidansa da sauƙi fiye da duk yadda suke tsammani.

Bilhaƙƙi ta warware sosai ta zama ƴar gidan Malam, idan ka kalleta kamar ba ita ce cikakkiyar ƴar rawan galar nan da tayi fice sosai a garin kacia ba. A yanzu ta zama wata nutsattsiyar yarinya wacce ilimin addini da kyawawan halaye suka ratsata sosai da sosai.

Ta ƙara girma da cika, hankali da nutsuwa ga wata kunya ta musamman duk sun mamaye ta. Idan ta zauna tana yawan tunanin
'ita kam da me zata saka wa waɗannan iyalan?'
Sai wani sashe na zuciyarta ya amsa mata da
'Sai dai addu'a kawai da fatan su cika da kyakkyawan ƙarshe.'
Duk wani nauyi na ibada da Allah ya wajabta a kan wani baligin musulmi Malam da iyalansa sun koyar da ita. Ta koyi yadda za ta bautawa mahaliccinta da cikakken sani akan bautar, ta san farillai, sunnoni, mustahabbai na duk wani bauta da zata yi wa mahaliccinta.

Da yake tana da matuƙar ƙwazo da ƙoƙarin mayar da kai akan duk abinda tasa gaba nan da nan ta iya harhaɗa baƙaƙe na larabci sai ƴan ƙalilan abinda baza a rasa ba. Ta san ƙabli da ba'adi, ta samu ilmi sosai daga ƙananun littattatafan addini irinsu Ahlari, Arba'una hadith, Sirah, Risala da sauran littafai.

Malam da kanshi yake ƙara mata karatu safe da yamma. Tana da haddar izufi goma cas a ƙwaƙwalwarta, daga Suratul Ahƙaf zuwa Suratu Nasi. Har lokacin kuma bata daina ɗaukar karatun Alƙur'ani mai girma da sauran littattafai a gurin Malam ba.

Madam Mary kuwa basu sake jin motsinta ba tun bayan da ta hayo iyaye na ƙarya ta kawo su a matsayin iyayen Bilhaƙƙi, cikin ƙanƙanin lokaci Malam ya ramfo su. Yayi musu kaca-kaca sannan ya kore su daga gidan, haɗe da zazzafan kashaidin muddin ta ƙara taka ƙafarta a cikin gidan ta tabbaci haƙiƙa hukuma ce zata raba su.
Tun daga ranar bata ƙara waiwayar gidan ba, ko a wane hali take ciki ma oho. Ta tafi, amma kafin tafiyarta ta ɗaukar mishi wani alwashi ɗaya.
"Gidannan da Bibi take ciki shi ne ya zama babban garkuwa kuma kariya a gare ta. Amma ina tabbatar maka da cewa duk ranar da ta sa ƙafa ta fice daga gidannan ka tabbaci haƙiƙa babu inda za ta faɗa sai hannunmu."

Wannan maganar da tayi ya tsayawa Malam a rai, dukda kuwa a gabanta ya nuna ko a jikinshi. Da wannan dalilin ne ma yasa tsawon watanni shidan da Bilhaƙƙi tayi a gidan ko ƙofar gida bai barta ta fita ba.

Dangane da batun tsafe-tsafen da suke damfare a jikinta kuwa da baiwar da take da shi na lalata abu idan abun ya ɓata mata rai yanzu duk sunyi sanyi sosai, Malam yana iya ƙoƙarinshi gurin yi mata zafafan addu'oi ya tofa a ruwa ya bata ta shanye safe da yamma. Kuma basa bari ta zauna cikin rashin tsarki saboda shaiɗanu, ako wani lokaci suna iya ƙoƙarinsu gurin ƙirƙirar duk abinda zai sanya ta cikin farin-ciki. Ko da kuskure ta aikata a hikimance cike da tausasan kalamai suke nusar da ita ba tare da lamarin ya ɓata ranta ba. Kusan a ko wani lokaci duk inda take zaune za a sami karatun Alƙur'ani mai girma yana tashi a gurin ko nesa kaɗan da inda take zaune.




BILHAƘƘI



"Shirya muje ki raka ni gidan Malam ɗin."

"Yeeee... thank you Sweetat. I love you"
Tsananin murna yasa ta kama ƙuncinshi ta sumbace shi bayan zaƙaƙan kalaman soyayya da take ta furta mishi akai-akai. Nan da nan ta miƙe a zabure kamar yayi mata allurar ƙarfi saɓanin da da jikinta yake a sanyaye tun da yace zai fita zuwa gidan Malam ya amso wayarsa.

Kallonta kawai yake yi yana murmushi, kamar ba yanzunnan ta gama yi mishi ƙorafin bai dawo gida da wuri ba amma yana shirin sake fita. Tun da ya ce zasu je tare bakinta ɓakwui.

Da yake a shirye take da kwalliyarta cas tun wanda tayi daf da ya shiga gidan na tarbar maigida, ko da tayi sallah shafa hoda ta sake yi ta zizara kwalli da man baki a lallaɓɓanta shi yasa har bayan sallar isha'i tsaf take. Gogaggen hijabinta ta ɗauka ta saka ta fita zuwa gurin mota shi kuma ya shige ɓangaren Rabi dan yi mata sallama.
"Ko kema zaki je ne?"

"A'a kuje kawai! Allah ya tsare. A gaida su Ummee."

"Ameen. Ok za su ji Insha Allah."
Ya amsa tare da sa kai ya fice daga falon.

Hankalinta yana kan Tv a tashar arewa24. Shirin Tarkon ƙauna suke nunawa, tana bala'in son shirin ko da wasa ba ta so wani guri ya wuce bata kalla ba. Ko a jikinta har ta ji ficewar motarsa daga gidan.

A mota sai hira take ƙoƙarin jan shi da shi amma ya ƙi sakin jiki, amsar shi baya wuce eh ko a'a. Haka kawai yake jin jikinshi kamar babu daɗi, tun da suka fito daga gidan yake jin zuciyarsa cike da tunanin Bilhaƙƙi. Duk ya ƙosa ya isa gidan yayi tozali da kyakkyawar fuskarta. Surayya da taga bai son hirar sai ta ja bakinta ta tsuke, a maimakon zaman shirun sai ya ƙara volume ɗin labaran duniyar da ya kunna a radion motar. A haka har suka isa gidan Malam.

Ko da suka shiga gidan hankalin iyalan gidan a tashe yake, gaba ɗaya iyalan gidan har da Malam suna tattare a ɗakin Ummee. Bilhaƙƙi ce ba ta da lafiya.

Tun dawowarta gidan idan akwai wani babban matsala da take fuskanta bai wuce ciwon cikin da take yi duk wata idan al'adarta zai zo ba. Ciwo ne na kwana ɗaya, amma kafin ya zo ya tafi sai ya wujijjiga ta ya fitar da ita daga hayyacinta.
A zamanin zamanta a gidan Madam tun da ta mallaki hankalinta ta fara al'ada da wani mugun ciwon ciki da mara Oga ya bada wani magani aka ba ta tasha, tun wancan lokacin bata ƙara fuskantar matsalar ciwon cikin ba sai dawowarta gidan Malam. Duk wata idan zai zo tana tsananin shan azaba, kullum kamar ma ciwon ƙara gaba yake yi. Duk wata tsananin ciwon yana wuce na watannin baya. Yau tun bayan sallar magrib take kwance tana kuka da gurmususu haɗe da juye-juye kamar mai naƙuda, har zuwa bayan sallar isha'i ciwon bai faɗa mata ba.

Dr. Bilyaminu da ya kasance shi ne likitan iyalin Malam tun su Maheer suna yara ƙanana wannan karon ma dai shi yake tsaye a kanta, magungunan sauƙaƙa zugi ya bata kamar yadda ya saba sannan ya ja Malam zuwa falon shi.
"Malam kamar yadda na sanar da kai fa irin wannan matsalar ba mu da wani tsayayyen maganin da zamu bata ya yaye mata ciwon gaba ɗaya. Sai dai mu bata magungunan da zasu sauƙaƙa mata ciwon har zuwa lokacin da zai tafi gaba ɗaya. Amma dai kamar yadda na sanar da kai a baya yau ma zan sake maimaita maka, irin wannan matsanancin ciwon marar na al'ada da wasu mata suke fama da shi mafiyawancinsu da sunyi aure suke dainawa. Ina ga in dai ba akwai wata matsala bane kayi ƙoƙarin aurar da ita, da yaddar Allah ciwon nata zai zama na ƙarshe ke nan. Idan kuma bayan auren ciwon bai tafi ba sai mu zurfafa bincike mu ga menene ya ci gaba da haifar da matsalar."

Ajiyar zuciya mai nauyi Malam ya sauke, ya sharce wani zazzafan gumi a goshinshi. Fuskarshi baiyane da matsanancin damuwa ya ƙara kallon likitan a karo na barkatai
"Na gode Likita. In Allah ya yarda zanyi ƙoƙarin aiwatar da shawarwarin da ka bani. Ciwon ya isa haka nan, yarinyar tana tsananin bani tausayi. Allah yasa dai auren ya zama sanadin kawo ƙarshen ciwon."

"Ameen ya Allah."

Da wannan maganar suka cimma matsaya guda, ya sallami likitan yayi mishi tattaki har zuwa ƙofar gida, ya juya cikin gidan falon Ummee. A daidai lokacin Surayya da Maheer suka sa kai cikin gidan bakunansu ɗauke da sallama.

Kai tsaye ɗakin Ummee suka nufa inda suka hangi ƙafafun takalma masu yawa a ƙofar ɗakin.
"Malam lafiya kuwa?"
Yayi tambayar yana tsaye daga bakin ƙofa, kallon fuskokinsu yake yi yana karantar damuwar da suke ciki. Nan da nan hankalinsa ya fara tashi, fuskarsa cike da taraddadi da tsoron irin amsar da zai fito daga bakunansu.

Kafin wani a cikinsu ya bashi amsa Surayya ta zube a ƙasa cike da ladabi da biyayya ta fara gaishe su, duk sai suka maida hankali kanta suna amsa mata gaisuwar cike da kulawa.

"Yaya, Bilhaƙƙi ce babu lafiya. Ciwon cikinta ne ya tashi."
Saudat da take zaune a kujera mafi kusa da shi ta amsa mishi da muryarta ƙasa-ƙasa. Kallonta yayi kawai, da fuskar rashin fahimtar abinda take nufi. Bai taɓa katarin zuwa gidan a lokacin da take cikin tsananin ciwon ba sai yau, sai dai wani

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login