Showing 54001 words to 57000 words out of 98260 words

Chapter 19 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

214

Middle Ads

"Menene... uhmmm...?"

Ko kafin ya rufe baki ta kai mishi wani mugun riƙo tana tattakure jikinta a cikin nashi, tana ƙara riƙe shi sosai. Cike da raki da jin raɗaɗi ta ce
"Asssshhhhh... Gangaran, Marata..."
Sai kuma hawaye shar-shar kamar an buɗe famfo. Sai juye-juye take yi tana ƙara ruƙunƙume shi cike da azaban ciwo.

Hankalinshi ne ya ɗugunzuma, zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta. Da alamun ya manta ma a inda suke, ɗago ta yayi daga jikinsa ya ɗage rigarta ta ƙasa yasa hannu a ƙasan cibiyarta, da tunanin ko nan ɗin ne yake mata ciwo
"Sannu, Nan ne yake ciwon?"
Yayi maganar kamar yana mata raɗa.

"A'a ƙasa fa"
Ta amsa cike da shagwaɓa, wasu sabbin hawayen suna sake ɓalle mata.

A hankali ya ƙara ƙasa kaɗan da hannunsa yana shafa mata mara sai kuma ya cire hannunsa da sauri kamar wanda shocking ya ja. Duk da sanyin da ake yi a garin shi zufa yake yi, ya ja ta jikinsa ya rungume tsam-tsam a ƙirjinsa yana bubbuga mata baya alamun rarrashi.

"Baya na... cinyoyina ciwo... dan Allah ka danna min..."
Ta faɗa cikin matsanancin kuka da magagin ciwo.

Abin dariya abin tausayi, Bilhaƙƙi ke ciwon Maheer ke zufa da jin raɗaɗin a jikinsa, gaba ɗaya ma kamar a ruɗe yake, ya ruɗe ya susuce kamar wanda bai taɓa aure ba, shi bai taɓa ganin irin wannan ciwon a gurin matansa ba.

Shi kuwa ciwon mara kamar ana ƙara tunkuɗoshi sai gurmususu take mishi a jiki tana kuka, gaba ɗaya ta gama yamutsa gallalliyar shaddar da take jikinshi. Jin yadda take ta ƙara maimaita bayanta da cinyoyinta ciwo suke yi yasa shi miƙar da ƙafafunsa akan gadon ya kwantar da ita rub da ciki akan cinyoyinsa kamar wata ƴar bebi, ya yaye rigarta sama sosai ya fara danna mata bayan a hankali da hannayensa biyu haɗe da ɗan bubbugawa kamar yana lallaɓa jaririya tayi bacci. Cikin sa'a kuwa lokaci kaɗan sai ta fara sauke ajiyar zuciya, da alamun sosai take jin daɗin abinda yake mata.

Ya leƙa fuskarta yaga har lokacin idanunta a rufe suke, sai dabbara-dabbarar hawaye a kumatunta.
"Ciwon ya daina?"

"Ya yi sauƙi dai."
Ta faɗa a shagwaɓe kamar za ta sake fashewa da kuka.

Ajiyar zuciya ya sauke, ya kalli bayanta da yake buɗe, sai a lokacin idanunshi suka kai kan maɓallin bra ɗinta mai ruwan madara. Yayi kamar zai kai hannu ya ɓalle sai ya kwaɓi kanshi, ya maida idanunshi kan gadon bayanta. Fatan jikinta irin mai kyau ɗinnan ne ga sheƙi, ita ba baƙa ba ita ba fara ba.

Karaf idanunshi suka gangara har zuwa kan mazaunanta da tudunsu ya ɗago a wandon baccinta. Saurin watsar da wannan tunanin yayi a lokacin da yaji tana ƙoƙarin tashi daga jikinsa, a kunyace ta saukar da idanunta ƙasa ba ta yarda sun haɗa ido da shi ba, ta janye jikinta ta matsa daga kusa da shi.

Hannunta ta ɗaga za ta saukar da rigarta ta baya da sauri yasa hannunshi ya saukar mata da rigar.

"Na gode"
Ta faɗa da muryarta ƙasa-ƙasa.

"Keeee godiyar miye? aikina ne fa."
Yayi maganar fuskarsa fal da murmushi, ƙoƙarin haɗa ido yake yi da ita ta ƙi ba shi damar hakan, sai ya matsa kusa da ita, ita ma ta matsa baya. A haka ya matso ta matsa har suka ƙure ƙarshen gadon.

Sai kawai ta takure kanta a cikin cinyoyinta tana murmushi. Shi baisan duk kunya yake bata ba.

Kanshi ya cusa kusa da nata cikin raɗa ya fara magana.
"Da gaskiya amaryar Gangaran kinyi farin ciki kuwa? Wani tukwuici za ki bani yau da zai tabbatar min kina taya ni farin-cikin da zuciyata take ciki?"

"Kai Maheer... wani tukwuici kuma...?"
Tayi maganar cikin sakalci da wani irin wawuyar shagwaɓar da tayi mugun tafiya da ɗan sauran nutsuwarsa.

Kamar zai sake janyota zuwa jikinshi dan samun sauƙi-sauƙi sai kuma ya maze. Ya fara hurga idanunshi lungu da saƙo na cikin ɗakin yana ƙare mishi kallo, sai kuma yayi murmushi. A zuciyarsa ya ce
'Gaskiya cikin iyayenshi mata biyu duk wacce tayi tunanin mayar da Bilhaƙƙi ɗakin ƴanmatan gidan a safiyar nan da ta tabbata halaliyarshi ba ƙaramin taimaka mishi tayi ba. Shi kam da ya zai iya fita da wannan yamutsattsen kayan na jikinshi? Amma yanzu zai fita salin-salin ba tare da an ganshi ba tunda ɗakin yana can ta ƙarshen gidan ne, kuma akwai siririyar hanya ta baya da zai iya bi wacce in ba rashin sa'a yayi ba zai wahala iyayen su ga fitarshi.'

"Yanzu haka za ki ta fama da wannan ciwon har sai baƙon ya tafi? kwana nawa ne yake yi?"
Ya tambayeta da fuskarsa mai baiyana zallar tausayinta, alamun ya tuno irin azabar da ta gama sha ɗazun.

Wayyo Allah... ina ma ƙasa ta tsage ta shige don kunya, can gefe ta maida kanta da jikinta tana ƙara ɓoye kanta tsakanin cinyoyinta.
'Ita yana bata kunya wallahi, bata taɓa tsammanin akwai lokacin da zai zo da za ta dinga jin kunyarshi har haka ba. Ita yayi ya tafi ma kar Ummee ko Mummy wata a cikinsu ta shigo a gansu a yanayin da suke ciki.'

Da ya fahimci manufarta sai yayi dariya kawai, ya kwanta a kan gadon.
"Kinga yarinya gara ma ki faɗa min, idan ba haka nan yini nan kwana saboda idan ciwon ya motsa in dinga miki matsa miki baya da cinyoyi..."

"Wayyo Maheer ciwon na jiya da yau ne fa kawai. Ka ga ni na ma ji sauƙi, ka tafi in samu inyi wanka inje gurin Ummee."
Ta ƙarasa maganar idanunta a nannarke take kallonshi, kamar za ta saka kuka.

Da zallar gaskiyarsa ya ce
"Kinga muje kawai in taya ki wankan tunda baki gama jin ƙarfin jikinki ba..."

"Ni dai a'a!"
Ta katse shi da sauri tana wawware ido a tsorace.
"Ka bari zan iya yi da kaina. ka ga ni na warke ma gaba ɗaya dan Allah ka tafi."

Ya ɓata fuska kamar ya shaƙa
"Kora ta kike yi ko?"

Tayi narai-narai da ido ta matsa kusa da shi sosai
"Yi haƙuri ba fa haka bane Allah..."

"To yaya ne?"
Ya tambaye ta murya a tsaitsaye yana sake tamke giran sama da ƙasa.

Tsoro ne ya fara kamata, lokaci ɗaya yana neman koma mata wancan murɗaɗɗen Maheer ɗin da ta sani a farko wanda sam baya ƙaunarta. Idanunta a ƙasa take mummurɗa yatsun hannayenta
"Kawai... kawai... ina jin tsoron kar su Mummy su shigo. Ka yi haƙuri dan Allah..."

Wawan rungumar da ya kai mata ba tare da ta ankara ba yasa ta kasa aje numfashin maganarta dai-dai
"I'm sorry Babe. Da wasa nake miki tsawa."
Ya raɗa mata a kunnenta yana dariya ƙasa-ƙasa.

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta runtse ido, ƙara ƙanƙame shi tayi tana jin wani irin baƙon yanayi yana ratsa ƙashi da ɓargon jikinta.

"Je kiyi wankan anjima zan dawo kinji?"

Ɗaga kai kawai tayi alamar ta ji, bakinta nauyi yayi mata ta kasa amsawa. Raɗan da yake yi mata a kunne a jikinta ji take yi kamar yana mata tafiyar tsutsa.

"Me zan taho miki da shi?"
Ya sake raɗa mata da wani rikitacciyar murya, domin ba ita kaɗai take karɓar saƙon ba shi ma yana ji a jikinsa.

Ƙanƙameshi ta sake yi kamar za ta tsaga ƙirjinsa ta shige, ko kuma tana tsoron kar a raba jikinta da nashi. Da ƙyar ta yi ƙumajin buɗe tsukakken bakinta da yayi mata nauyi ta ce
"Bana buƙatar komai"

"Ba komai fa kika ce Babe ki tuna dai."
Yayi maganar yana dariya ƙasa-ƙasa.

Nauyayan idanunta da suka ƙara ƙasa-ƙasa ta sauke su a kanshi, ta tura baki gaba
"Ni dai ba komai..."

"Har Pad bakya buƙata?"

Ƙwace jikinta tayi da sauri ta dira daga kan gadon ta faɗa banɗaki ta danno ƙofar cike da matsananciyar kunyarsa.

Dariya yayi mai isarsa kafin ya ɗan gyaggyara rigarsa ya ɗauki hula, makullin motarsa, ƙaramar wayarsa ya fice daga ɗakin. Ta baya ya bi, yana tafe saɗaf-saɗaf yana waige-waige kamar mare gaskiya har ya fice daga gidan ba tare da ya haɗu da ɗaya daga cikin iyayen na shi ba.


***** ******


"Da girman kujerarki Sarauniya. Amarya a gurin mai martaba Sarki Abdulfatah na biyu. Ranki ya daɗe Innata ta kaina. Allah ya ja zamaninki ki daɗe kina yi ki ƙare da kyakkyawan cikawa."

"Ameen ya Allah."
Ta amsa daƙyar, muryarta baiyane da ƙasaita da matsanancin mulki. Ta sake gyara kishingiɗar da tayi a kan tuntum ɗin sarautar, ta gyara riƙon wayar a kunnenta tana jan fasali kamar baza ta ƙara tankawa ba.

Har sai da daga can ɓangarenshi ya ce
"Ina jinki Fulani."

"Abdulganiyyu ya iyalanka?"

"Duk lafiya ƙalau suke Fulani. Da fatan ku ma haka? Ya jikinki?"

"Jiki mun gode Allah Abdulganiyyu. Gamu nan har yanzu muna turawa."

"Ubangiji Allah ya raba ku lafiya Innata."
Yayi mata addu'ar muryarsa na baiyana tsananin tausayinta.

Daga can ɓangarenta hannu ta ɗaga ta shafi turtsetse cikin da ya turo sosai a cikin alkyabbar da yake jikinta, sannan ta amsa addu'ar a kasalance. Kafin ya ce wani abu ta ci gaba da magana jikinta a sanyaye, bisa ga dukkan alamu tana cikin tsananin damuwa amma fuska da muryarta na ƙoƙarin ɓoyewa.
"Abdulganiyyu ka san mun shiga wata na goma sha huɗu, har yanzu kuma ba wani motsi. Mai martaba ya fitar da ranar da likitocinsa zasu yi min aiki, nan da sati biyu za a fitar da cikin in dai har zuwa lokacin haihuwar bata zo ba. Ina jin tsoro Abdulganiyyu, da gaske ina matuƙar jin tsoro. Ban sani ba ko wannan cikin shi ne zai zama silar ajali na... Idan zai yiwu ina son ganinka kafin lokacin."

"Karki damu Ranki ya daɗe, babu komai da zai faru in Allah ya yarda sai alkhairi. Muna addu'a, kuma za mu ci gaba da bada ƙaimi, Ubangiji maji roƙon bawa ne. Na tabbata bai manta da halin da kike ciki ba, in Allah ya yarda addu'a ta karɓu sai dai jinkirin biyan buƙata. Ki kwantar da hankalinki kinji?"

"Insha Allah. Na gode Abdulganiyyu. Allah ya maka albarka."

"Ameen Inna. Na gode."
Ya amsa cikin jin daɗi, kafin ta ƙara cewa komai ya ci gaba da cewa
"Kamar yaushe kike buƙatar in zo?"

"Kar ya gaza nan da sati ɗaya. Idan ka yi jinkiri da yawa kuma nan da kwanaki goma."

"Tom In Allah ya yarda bazan wuce lokacin ba. Allah ya ƙara miki lafiya Ranki ya daɗe."

"Ameen ya Allah. Ka taho min da Magajin Malam, shi ma ya kwana biyu bai zo ba sai a waya yake gaishe mu."

"To za mu taho tare da shi. Sai mun iso."
Da haka suka ajiye wayoyin a duk ɓangarorin guda biyu.

Sa ke motsawa tayi cike da ƙasaita ta yunƙura daƙyar ta miƙe zaune daga kishingiɗar da tayi, nan take bayin da suke zagaye da ita wasu suna firfita wasu suna mammatsa mata ƙafafu suka fara jera mata sannu, haɗe da addu'ar Allah ya raba ta da cikin jikinta lafiya, Allah ya ja zamaninta.

Ta kalli Amintacciya kuma Shugabar bayinta mai suna Lantana ta yi ɗan murmushi ta ce
"Na gode Lantana, ku bani guri. Ina buƙatar in huta."

"Hutawarki lafiya Fulani, baya goya marayu. Allah yaja zamaninki ki daɗe kina yi a zuciyar mai martaba. Allah ya raba ki da cikin Yarima lafiya."

Tattausan murmushin da bai cika ɓacewa daga fuskarta ba ta sake sakar musu. A zuciyarta ta amsa kyawawan addu'o'insu. Ta yunƙura da ƙyar ta miƙe suna ta jera mata sannu, cike da nutsuwa take tafiya a hankali har ta shige can cikin turakarta.

Ta daɗe a tsugunne kanta a ƙasa kamar an manta da ita. Tun tana jero kirari Babbar baiwar da take gefenta tana amsawa har ta rasa abin cewa, tayi shiru tana jiran umarnin magana daga Sarauniya Safara'u, inkiya Fulani Taka.

Sai da ta mila ta mile ta gama jan fasali da tsananin mulki mai haɗe da jin kai cike da ƙasaita ta kalli gefen da take tsugunne, a wulaƙance ta ce.
"Wane hali Safiyya take ciki?"

"Har yanzu dai ba wani canji Ranki ya daɗe, tana nan jiya iyau. Ciki sai ƙara tsini yake yi babu wani motsi na naƙuda. Likitoci sun shawarci Mai martaba nan da sati biyu za a mata aiki a cire cikin, ya amince da hakan kuma ita ma ta amince. Ɗazu ta kira wani ɗan ƴar'uwarta da yake kaduna wai yazo tana son ganinshi kafin ayi mata aikin. Bisa ga dukkan alamu ita ma ta fitar da rai da rayuwar duniya."

Wani murmushi ta sake tana cije gefen bakinta na dama cike da mugunta, ta jinjina kai ta ce.
"Da kyau! Madallah! Haka muke son ji. Raliya a koma bakin aiki."

"Godiya nake Ranki ya daɗe. Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana. Ƴar sarki jikar Sarki Uwargidan Mai martaba Sarki Abdulfah na biyu, uwar Sarkinmu na gobe Yarima Muzaffar in Allah ya yarda."
Da waɗannan kirarin a bakinta har ta fice daga falon cikin sauri tana waige-waige da basasarwa, haɗe da bagararwa dan kar a gane daga inda ta fito har ta isa ɓangaren Sarauniya Safiyya ta koma bakin aikinta kamar babu inda ta je.

"Lami a isar wa da Ciroma saƙo ina son ganinshi."

"Angama Ranki ya daɗe."
Ta amsa da sauri ta duƙa kamar za ta yi mata sujada, sannan ta miƙe da sauri fice daga falon dan isar da saƙo ga Ciroma.


******* ******

Tunda yayi sallama a bakin ƙofar falon, ya ji duk su biyun babu wacce ta samu zarafin amsawa ya tabbatar liƙin da yake tunanin ya yi ya ɓalle.

Ɗan murmushi kawai yayi ya girgiza kai yana mamaki a ransa, ganin wani abin dariya a tsakanin matan nashi. Haɗin kan da tun da babu a tsakaninsu ne yau suke neman farawa tunda sun samu labarin yayi aure.

Duk su biyun suna zaune ne akan kujera mazaunin mutum biyu, sun zabga tagumi da hannu bibiyu fuskokinsu na baiyana yanayi na matsanancin jimami kamar waɗanda aka aika musu da saƙon mahaifansu na kwance a asibiti.

Yana shiga cikin falon duk suka miƙe tsaye a zabure suna binshi da mugun kallo, kamar wanda yayi musu wani gaggarumin laifi. Surayya da take gwana a gurin abin kawai sai ta fara hawaye tana nuna shi da yatsarta manuniya, ta ma kasa magana dan tsananin ƙuncin da zuciyarta take ciki.

Ita kuwa Rabi da take gwana a gurin tsiwa da fitsara ƙugunta ta riƙe da hannu bibiyu ta cokaɗo baki gaba, ta kalle shi da ƙananun idanunta da suka canza launi dan tsananin tashin hankali da masifar da yake cikinta.
"E lallai, ba shakka! Na yarda goro na sa zawo. Amma kafin in ce komai bari in fara tambayarka dan ka share min tantama. Wai da gaske ne jita-jitar da muke ji yau an ɗaura aurenka da wannan ƙwailar yarinyar mai sunan aljanu da take zaune a gidan Malam?"

BILHAƘƘI


"Shegiyar yarinya kullum muka je gidan Aunty sama Aunty ƙasa ashe ƴar kunama ce neman gurin harbi take yi. Faɗa min da gaske ka aure ta ko kuwa duk maganganun da muka ji rumous ne? Don mun kira wayarka fiye da sau talatin baka ɗauka ba."

Shirun da yayi bai amsa ta ba yana kallonta yana sakin murmushin da ta alaƙanta shi da na rainin wayau shi ne abinda ya ƙara ƙona mata zuciya. Ta ci gaba da binshi da kallo baki buɗe har ya shiga cikin falon sosai ya nemi ɗaya daga cikin kujerun ya zauna.

Irin yadda yayi gurin zaunawar duk su biyun sun fahimci a matuƙar gajiye yake. Ga wani mugun yamutsewa da shaddar jikinsa tayi kamar an ƙwato a bakin kura.

Ta sake runtse idanu zuciyarta na ƙara zafi cike da takaici, tunani take da saƙe-saƙe tunda a gidansu an ce mata bayan sallar asubah aka ɗaura auren kuma bai shigo gida ba sai yanzu sha biyu saura, alamun gajiyar da ta gani a jikinsa, yamutsewar kayansa, yalwataccen farin-cikin fuskarsa su suka haɗu suka tabbatar mata da aikin gama ya daɗe da gamawa tsakaninshi da Bilhaƙƙi.
'Ya rasa ranar da duk zayyi hakan sai a ranar girkinta?'
Sabbin zafafan hawaye masu mugun raɗaɗi ne suka sake ɓalle mata kamar an buɗe ruɓaɓɓen injin markaɗe ta ɓare baki ta fashe da ƙaƙƙarfar kuka, da mugun gudu ta tashi ta shige ɓangarenta tana kuka tana danne baki ta bugo ƙofar da ƙarfi.

Da kallo ya bita kawai, abin dariya abin tausayi har ta ɓacewa ganinsa sannan ya maida idanunsa kan Rabi da take ta cika tana batsewa. Ya shafi kwantaccen suman kansa ya ƙara sakar mata murmushi
"Ummm me ma kike cewa Honey?"

Wani mugun zuciya ne ya taso mata kamar za ta ɗuɗɗura mishi ashar sai tayi ƙumajin dannewa, ta buɗe baki za ta yi magana wani maƙoƙo ya taso daga ciki ya tsaya mata a maƙoshi, shi bai fito waje ba shi bai koma ciki ba kawai sai ta fara hawaye dan haushi.

"Yi haƙuri Honey, bari inyi wanka muyi magana."
Ya miƙe tsaye ya nufi hanyar ɓangarenshi ita kuwa ta bishi da kallon baƙin-ciki tana ta hawaye, sai da ya kusa ɓacewa ganinta ya juyo yana kallonta.
"Honey ko za ki taya ni wankan ne?"

Gudun hawayenta ne ya ƙara ƙarfi, da ta buɗe baki har lokacin maganar kasa fita tayi kawai sai tayi na Surayya da sassarfa ita ma ta wuce ɓangarenta tana kuka.

Murmushi kawai yayi ya shige ɓangarensa. Ya san al'amarin da ciwo, shi yasa sam baiji haushinsu ba. Kuma ya ɗauki ɗammarar lallaɓasu har ya kwantar musu da hankali in Allah ya yarda. Ƙarin aure a gurin ƴa mace abin baƙin ciki ne mai girman gaske musamman irin nashi auren da yazo bagatatan ba tare da sun

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login