Showing 36001 words to 39000 words out of 98260 words
ciccike da hawaye, hannayenta duk biyu dafe da ƙuncinta. Bisa ga dukkan alamu ta yi nisa sosai cikin zuzzurfan tunani.
A kallo ɗaya za a fahimci sunƙi-sunƙin damuwan dake danƙare a zuciyarta, tana zaune sanye da wata ɓingilar vest da ya wuce cibiyarta da kaɗan, sai kuma wani burgujejen wando gajere wanda shi ma da kaɗan ya wuce gwiwarta. Gashin kanta a cukurkuɗe a yamutse kamar yadda take, a tsakiyar gadon take zaune digirgir kamar wata tashin iskokai.
"Bibi?"
Ta kira sunanta da ɗan ƙarfi haɗe da sa hannu ta jijjiga kafaɗarta guda ɗaya.
Yadda tayi firgigit tana kallonta kamar wacce ta farka daga barci shi ya ankarar da Madam duk tsayuwarta a gurin bata san da ita ba, maganganun data yi ma ba lallai idan ta ji ta ba.
Kusa da ƙafafunta ta zauna suna fuskantar juna, ƙare mata kallo take yi ko zata ci nasarar gano abinda yake damunta amma bata gano komai sai ramewa kaɗan da Bibin tayi. Abin mamaki kuma abin tsoro ga Madam sai kawai ta ga tsiyayowar ruwan hawaye daga idanun Bibi. Zaro ido tayi a tsorace, a duk iya tsawon shekarun da suka ɗauka tare baza ta iya tuna wani lokaci da ɗigon hawaye ya sakko daga idon Bibi ba, amma yau Bibi ce da kuka kashirɓin? alamun rauni da ragwanta bayyane a idanunta ƙuru-ƙuru? wannan babban abin mamaki ne.
"Me yake faruwa? faɗa min me yake damunki?"
Ta sake jefa mata tambayoyin a karo na biyu, muryarta a tausashe.
"Madam..."
Taja sunan wasu sabbin hawaye suna sake gangaro mata shar-shar kamar an buɗe famfo.
"I'm in love !!"
Ta sake faɗa a sanyaye tun kafin Madam tayi yunƙurin magana.
"I love him with all..."
"Ina fatan dai wasa kike min?"
Ta katse ta da sauri, idanunta a warwaje.
"Na taɓa yi miki irin wannan wasan? da gaske nake yi. Kinga nan?"
Ta kamo hannunta guda ɗaya ta ɗora a ƙirjinta dai-dai saitin zuciyarta.
"Kwanaki uku kenan kamar daƙiƙa na agogo duk bugawa ɗaya yana bugawa ne da tsananin soyayyarsa, tun da nake a rayuwata ban taɓa kasancewa a irin wannan halin ba, da gaske ina sonsa, soyayya mai tsanani fiye da yadda kike tunani, ina sonsa fiye da duk wani soyayya da kika taɓa gani wata mace ta yi wa wani namiji a rayuwarki..."
Fincike hannunta tayi taja da baya a tsorace, ta kalleta zuciyarta cike da fatan maganganunnan da take furtawa su kasance mafarki tayi.
"Bibi? kina cikin hayyacinki kuwa? ina fatan dai ba shaye-shaye kika fara yi ba tare da kin sanar da ni ba?"
Tayi mata tambayar cikin ɗan tsawa, fuskarta bayyane da matsanancin mamaki da zallar takaicin maganganun Bibin.
"Madam pls ki taimake ni, jiya ya tafi ya barni ba tare da yayi min sallama ba... ya tafi da zuciyata ba tare da ya bani tasa zuciyar ba kamar yadda nake muradi. Ki taimake ni... ji nake kamar zan mutu. Ina son shi. Ki dawo min da Maheer ɗina pls idan ba haka ba zan fita nemansa da kaina..."
"Bibi ki dawo hayyacinki pls! kin manta abinda Oga ya faɗa miki? kin manta kashaidin da ya miki? wane mai gangancin ne yayi kuskuren shiga cikin rayuwarki? wani mahaukacin ne mai wannan kasadar? ki faɗa min in sa a ɓatar da shi a duniyar nan tun kafin yasa kwaɓarmu tayi ruwa. Gara ya mutu, ya tunkuyi burji dan rayuwarsa sam bata da amfani..."
"Maheer...? Maheer ɗin nawa za ki sa a ɓatar? Maheer ɗin nawa kike so ki hallaka? Maheer ɗin nawa ne kike cewa rayuwarsa bata da amfani?"
Ta sauko daga kan gadon ƙirjinta na sama da ƙasa ta nuna ta da yatsarta manuniya ta ci gaba da cewa.
"Wallahi kar ki kuskura, karki kuskura. Ba ke ba har Ogan wannan kashaidi ne mai harshen damo. Ina rayuwata yadda naga dama ne, babu wanda ya isa ya kafa min doka ko wani sharaɗi da banyi niyyar yi ba. A cikinku duk wanda yayi kuskuren taɓa min wanda nake so wallahi zai ga abinda baya so. Idan kuma kina ganin cika baki nake yi..."
Tayi ƙwafa ta jujjuya ƙwayoyin idanunta cikin fushi
"Dan Allah ki kwatanta taɓa shi"
Tana kaiwa nan wayarta ya kwaɗa kiran sallar azahar rangaɗaɗau da muryar ladani mai tsananin daɗi da garɗi.
Bata ƙara saurarar Madam ba ta shige ban ɗaki dan ɗauro alwala, jikinta babu inda baya rawa da karkarwa. Rabon da ta yi sallah akan lokaci ita kanta ta manta, sai ta kwana biyu ma bata yi sallar ba, idan ta tashi yi kuma buga-buga kawai take yi ba tare da kiyaye farillai, sunnoni, da mustahabban sallar ba. Alwalar ma sam ba cika ta take yi ba, tana sallar ne kawai dan kiyaye ɗaya daga cikin ababen da ta koya a gurin Maman Ushe, amma bayan haka babu wani abu da take aikatawa da zai nuna ita cikakkiyar musulma ce.
Dan ta Madam Mary ma da tuni ta daina sallar tunda ita ma ba yi take yi ba, rayuwarta take yi mai ƴanci. Ba zuwa coci babu yin sallah, bata da wani takamaiman abin bauta da ya wuce tana bin duk abinda Oga ya gindaya mata.
Doguwar riga mai ɗan dama-dama ta lalubo a cikin jibgin gogaggun kayanta tasa, rigar da kaɗan ya wuce gwiwarta bai kai idon sahu ba, kuma ya matse ta tsam! Haka nan dai ta lalubo baƙin siririn gyalen doguwar riga ta naɗe kanta da shi ta fuskanci gabas ta tada sallah ƴar faki kamar yadda ta saba.
Kamar kububuwa fuuu ta fice daga cikin ɗakin tana harhaɗa hanya, lallai ya zama dole a wannan karon su dakatar da Bibi daga iskancin da take aikata musu. Dole su ɗauki mummunar mataki a kanta ta bi abinda Oga ya shimfiɗa mata, idan kuma taƙi dole su ɗauki matakin ƙarshe a kanta.
Ko da ta sallame shiru tayi tana tunaninshi, lokaci ɗaya kuma sai ga hawaye shar! Bata saba idan ta bubbuga sallah tayi addu'a ba yanzu ma zaune tayi tana tunanin rabuwarsu ta ƙarshe a shekaran jiya da yamma.
'Cikin tsananin sa'a ta tarar da ƙofar ɗakin nasa a buɗe, a hankali kamar ɓarauniya ta buɗe ƙofar ta shige cikin ɗakin. Bata ganshi a falo ba sai motsin ruwa da take ji a banɗaki, hakan yasa ta gane wanka yake yi.
Bayan tafkeken labulen da ya rufe windo taje ta maƙale yadda bazai ganta ba. Har ya fito ya gama shiryawa bata leƙo shi ba dan bata san me zata gani ba, sai da taji yana fesa turare alamun ya gama shiri, ko da ta leƙa kanta sai taga ya bata baya dan haka da saurin gaske ta ƙarasa gurinshi ta rungume shi da sanyin murya mai kama da raɗa tace
"My love..."
A gigice ya juyo dan ta bala'in shammatarsa, yana haɗa idanu da ita ya finciketa daga jikinsa cikin tsananin fushi ya bata mari mai kyau a kuncinta na dama.
"I love you..."
Wani mahaukacin marin ya sake sauke mata a kumatunta na hagu saida tayi taga-taga kamar zata kife a kasa amma ta cije ta tsaya.
Murmushi kawai tayi, idanunta ciccike da hawaye.
"Ina sonka ne fa..."
A zuciye yasa hannu yayi mata wani mugun shaƙa kamar mai neman fitar mata da numfashin ƙarshe, nan da nan ta fara ganin bibbiyu, ta fara jan numfarfashi a wahalce tana lumshe ido tana buɗewa, ya kusanto da ita jikinsa sosai ido cikin ido yake watsa mata wani matsiyacin kallo.
"Kin ɗauka na rasa yadda zanyi da ke ne na ƙyale ki har kika zame min maƙale mata? ba fa tsoronki nake ji ba. Kawai ina tausayinki ne ganinki ƙaramar yarinya. Wallahi daga yau idan kika sake zuwa nan nema na saina sassaɓa miki kamanni, shashasha kawai. Ko mata sun ƙare me zanyi da ƴar iska irinki ƙaramar karuwa?"
Yaja tsaki ya watsar da ita a wajen, inda Allah ya taimaketa kusa da gadon ɗakin suke da ba ƙaramin buguwa zata yi ba, da ya watsar da ita sai ta faɗi a kan katifa tana maida numfashi a wahalce.
Ɗan ƙaramin jakar da ya zubo kayanshi kala biyu ya ɗauka ya ɗauki wayarsa ya nufi ƙofar ɗakin da ya ji ana ƙwanƙwasawa. Yusuf ne yake tambayarsa
"Ka gama ne?"
"Eh ! muje kawai. Ni yanzu zan wuce sai ku taho idan motocin kayan sunyi gaba. Sam banso na kwana uku a garin nan ba, amma tunda buƙata ta biya Alhamdulillah."
Yana gama faɗin haka yaja ƙofar ya rufe kamar ba kowa a ciki suka sauka ƙasa yaba su makullin ɗakinsu, shi kuma suka fita da Yusuf a motarsa.
Basu yi nisa ba ya sauke shi a bakin titi ya ba motar wuta ya ɗauki hanyar barin kacia dan komawa kaduna.
So hana ganin laifi, bata ji haushinshi ba. Sam bata ji haushin abinda yayi mata ba. A maimakon ta ji a ranta ta tsane shi wani matsanancin soyayyarsa ne yake sake tumbatsa a zuciyarta, kawai sai ta lumshe idanu tana murmushi, bubbuɗe hancinta tayi ta ci gaba da shaƙar daddaɗan turarensa da ya kama ɗakin. Sai da ta gaji da kwanciya ta yunƙura da ƙyar ta sauka ta hau mota ta koma gida'
BILHAƘƘI
Ya ci gaba da kallon yadda ta zabge ta lalace lokaci ɗaya, da ganin yanayinta duk ta jigata. Kamar ba Surayya mai garin jiki da tsananin gayu ba, yanzu duk ta koma wata iri ta canza kamanni saboda tsananin ciwon da ita kaɗai tasan yadda take ji a jikinta. A cikin kwanaki uku kacal, iya binciken likitoci har lokacin basu samu nasarar gano takamaimai abinda yake damunta kuma yake haddasa mata haɓo a kai akai ba.
Ƙarin ruwa kawai suke ta mata sai kuma manyan magunguna Antibiotics da ake ta ɗura mata, har lokacin dai sauƙi sai na musulunci. Ciwon ma kamar gaba yake yi, hankalin Maheer da na iyayenta a matuƙar tashe yake. Hatta Rabi da ba wani zaman lafiya suke yi ba a tsakaninsu tana matuƙar tausaya mata.
Tsawon kwanakin da ta yi a asibitin tana kwance ne sharɓan kamar gawa, bugawar numfashinta ne kawai ake gane tana da rai. A hakan da take ciki duk bayan awa ɗaya jini zai ɓalle mata ta hanci ta baki, sai an ɗauki tsawon lokaci daƙyar likitoci suke samun nasarar tsayar da jinin.
Yini ɗakin da take kwance yake yi cike da mutane ƴan dubiya, wani lokacin ma har sai likitocin sunyi kora, da yake asibitin private ne ko wane lokaci ana iya zuwa duba mara lafiya.
Ta ko wane ɓangare addu'ar fatan samun sauƙi ake yi mata daga bakunan mutane daban-daban.
Tunda abin ya faru Malam Abdulganiyyu baya nan, sunje wani taron Semina na kwanaki huɗu da sauran manyan malamai a Abuja. Duk abinda ya faru ta waya ya samu labari, sai yau ya dawo dan haka kai tsaye ya umarci direbanshi ya wuce asibiti ya duba jikin Surayya bayan ya kira Maheer ya faɗa mishi asibitin da aka kwantar da ita.
Ya girgiza da ganin yadda ta koma a cikin ƙanƙanin lokaci, zuciyarsa ta ƙara cika da tsoron Allah.
'Lallai ɗan Adam ba a bakin komai yake ba, idan Allah yaso cikin ƙanƙanin lokaci sai ya jirkita ma mutum halitta. Allah yasa muyi kyakkyawar ƙarshe. Ameen'
Tunanin da ya gama yi kenan a zuciyarsa, fuskarsa bayyane da matsanancin tausayinta, dafa ƙarfen gadon da take kwance yayi ya fara jero mata addu'o'i yana tottofa mata, ya ɗauki tsawon lokaci yana addu'ar a zuci sannan yayi magana a fili
"Ubangiji Allah ya bata lafiya."
"Ameen Malam."
Mutanen cikin ɗakin suka amsa gaba ɗaya, fuskokinsu duk a jagule saboda damuwa da halin da take ciki.
Malam ya maida idanunshi kan Rabi da take rakuɓe can gefe guda kusa da Mummy Salamatu, sanye da zumbulelen hijabi har ƙasa. Ita ma duk ta faɗa kamar wacce lafiya bata wadace ta ba.
"Rabi'atu ance kuna tare wannan abin ya faru da ita. Menene zallar gaskiyar abinda ya faru a lokacin?"
Cikin nutsuwa ta fara kora mishi bayanin, idanunta a ƙasa cike da tsananin ladabi da kunyarsa da take matuƙar ji. Ga wani kwarjini na musamman da Malam ɗin yake da shi ga duk wanda ya tsaya a gabanshi.
"Ina fitowa daga ɓangarena zuwa cikin babban falo na ganta a tsaye tana waya fuskanta cike da nishaɗi tana dariya, ko da na saurara dakyau sai na fahimci da Ya Maheer take waya saboda irin kalaman da na ji tana furtawa. Tsaki nayi na wuce kicin na ɗauko kofi ina dawowa cikin falon ban zauna ba na nufi ɓangare na, banyi nisa ba naji ta ƙwalla ihu mai ƙarfi ta faɗi ƙasa, ko da na isa gurinta da gudu sai naga wani baƙin abu yana fita daga baki da hancinta. Shi ne na kira mai gadi ya taimaka min ya kira wani maƙwafcinmu muka kawo ta asibiti"
Shirun da ta yi shi ya fahimtar da shi ta gama magana, girgiza kai yayi alamar ya gamsu da duk abinda ta faɗa.
"Allah ya bata lafiya. Magaji muje in ga likitan nata ko?"
Ya faɗa yana kallon Maheer sannan ya nufi hanyar ficewa daga ɗakin, zuciyarsa cike da saƙe-saƙe.
Tsawon kwanaki uku kullum sai yayi mafarkin yarinyar nan tana neman taimakonsu a cikin mabanbantan yanayi, a jiya da yayi mafarkin ya ga wasu matsafa suna zagaye da ita suna azabtar da ita, tana kuka take miƙo ma Maheer hannu shi kuma ya juya mata baya. A can gefe guda kuma yaga Surayya cikin wani yanayi. Abu guda da ya iya fahimta a yanzu da yaga halin da Surayya take ciki shi ne tabbas ciwonta yana da alaƙa da waɗancan matsafan, in dai kuwa haka ne zamanta a asibiti bashi da wani amfani tunda basu da maganin ciwonta. Fagen nasu ne na manyan malamai.
Bayan musayar gaishe-gaishe cikin girma da mutunta juna ba tare da ɓoye-ɓoye ba kai tsaye ya faɗawa likitan abinda yake ransa.
"Likita sallama muke buƙata fa."
Hankali a tashe likitan ya fara tambayarsa.
"Malam lafiya? Wallahi muna iyakar ƙoƙarinmu akan ciwon nata, kar kaga kaman mun gaza ne. Kasan ciwo shiganshi ne babu wuya amma sauƙi dole sai a hankali. ku ɗan ƙara mana lokaci kafin kuyi tunanin canza mata asibiti."
"Dr. Ni bance kun gaza ba, kuma ba asibiti zamu canza mata ba. Ciwon nata ne dai idan ka lura da yadda kuka kasa gano ainahin abinda yake damunta za ku fahimci sam ba maganin asibiti take buƙata ba, za mu koma gida ne mu gwada magunguna daga Alƙur'ani da Sunnah. Insha Allahu muna fatan dacewa a wannan ɓangaren."
Cike da gamsuwa Likitan yayi musu fatan dacewa sannan ya rubuta musu takardan sallama, har ɗakin ya bisu yana musu fatan alkhairi. Iyayenta sun miƙa wuƙa da nama ga Malam ɗin, suna da kawaici da kyakkyawar shaidan da gangar Malam bazai yi abu dan ya cutar da Surayya ba.
Shima Maheer kanzil bai ce ba har suka tattara yana su yana su aka kwashe ta ranga-ranga zuwa gidan Malam.
Da yake gidan yalwatacce ne a wadace babban ɗaki guda aka ware mata kusa da na Ummee aka kwantar da ita, daman akwai komai a ɗakin. Yayar mahaifiyarta Inna Lantana ita ce zata ci gaba da jinyarta dukda sun san iyalan Malam baza su taɓa gazawa gurin kulawa da ita ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci Malam ya fara mata zafafan addu'o'i a cikin ruwa ana bata tana sha, ya rubuta duk magungunan da yake buƙata ya aiki Maheer babban shagon islamic chemis ya sissiyo mishi, nan da nan ya harhaɗa duk abubuwan da yake buƙata ya ba da ana mata amfani da su, a kullum kusan kwana yake yi yana salloli da yi mata addu'ar Ubangiji ya kawo mata sauƙi da gaggawa.
***** ******
"Yusuf ko?"
Ta tambaye shi tana nuna shi da yatsarta manuniya, zuciyarta cike da addu'ar Allah yasa shi ɗin ne.
"Eh! ni ne"
Ya amsa fuskarsa yalwace da murmushi.
Cike da ɗoki da tsananin murna ta ƙara matsawa kusa da shi kaɗan, ta cigaba da magana tana ɗan dariya
"Ka gane ni kuwa? ni ce kwanaki na tambaye ka sunan abokinka..."
"Ba abu bane mai sauƙi mutum mai hankali ya manta fuskar kyakkyawar yarinya kamarki fa. Yau kuma me kike so?"
Ya katse ta shima yana dariya.
"Shi nake so"
Ta faɗa a shagwaɓe, sai kuma kunya ta ɗan kama ta da sauri ta rufe rabin fuskarta da hannunta ɗaya tana dariya.
Maida hankalinsa yayi gaba ɗaya a kanta yana jin maganganun da ta zo mishi da su.
"Da gaske nake jin tsananin son abokinka, amma shi sam ya ce baya ƙaunata."
Sai kuma tayi rau-rau da idanu ciccike da hawaye, iya dauriya tayi gurin hana hawayen zubuwo, ta daure ta cije ta ci gaba da kora mishi bayanin da ke cin zuciyarta.
"Soyayya... soyayyar nan da nake ji na shi a zuciyata wani abu ne da ko a muggan mafarkin da nake yi wallahi ban taɓa hasashen zai iya faruwa da ni ba, sam!
A halin da nake ciki yanzu da tsarin rayuwar da nake yi soyayya bata dace da ni ba. A takaice soyayya ɓatan hanya tayi ta faɗa min. Ya zanyi? Dan Allah ka faɗa min yadda zanyi? kwata-kwata kwanaki biyar ne da haɗuwata da shi amma yadda nake ji a raina kamar na shekara ɗari da shi a zuciyata. Ina azabtuwa da soyayyarsa fiye da yadda kake tsammani."
Ta nuna saitin zuciyarta da hannu, zafafan hawaye na tsiyaya daga idanunta.
"Ji nake kamar nan zai iya tarwatsewa matuƙar ban mallaka mata abinda take tsananin so a cikin ƙanƙanin lokaci ba. Allah ya jarabceni, da gaske Allah ya jarabceni. Dan Allah ka kwatanta min inda yake da zama.
A kanshi na yarda da zancen bahaushe da yake cewa garin masoyi baya nisa, yadda nake ji a raina tabbas zan iya binshi duk nisan duniyan da yake. Zan ci gaba da naci ina bibiyarshi har zuwa lokacin da zai fuskanceni ya karɓi soyayya ta. Dan girman Allah ka taimaka min, wallahi da gaske nake yi. Kuma ko