Showing 57001 words to 60000 words out of 98260 words

Chapter 20 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

218

Middle Ads

sani ba, ya san dole su ji damuwa da baƙin-ciki.

Ya daɗe a cikin kwamin wanka yana saƙe-saƙe, shi kaɗai yake sakarwa kansa murmushi, zuciyarsa cike da tunanin yanayin da suke ciki shi da ita ɗazu da safe. Ina ma a ce yanzu tare yake da ita a cikin kwamin wankan nan? Ya ma kasa kwatanta yanayin da za su shiga dan tsananin shauƙi. Sosai yake jin nishaɗi da farin-ciki, yayi mamaki ƙwarai. Abu ne da bai taɓa tsammani ba a ce wai aurenta ne zai tsunduma shi a cikin irin wannan kogin na tsananin shauƙi da tunanin ƙara'i da ƴar ƙanƙanuwar yarinya mai shekaru goma sha... matansa duk cikakkun mata ne da suka ba ishirin da biyar baya.

A lalace a sanyaye ya dinga komai shi yasa har aka kira sallar azahar bai kammala shiryawa ba, kiran sallar ne ma yasa ya ƙarasa da hanzari bayan ya koma banɗakin ya ɗauro alwala.

A kunnuwansu ya fice zuwa masallaci, har lokacin cikin su biyun babu wacce ta fito falon. Hallau dai a kunnuwansu ya dawo gidan bayan an idar da sallah ya ɗau makullin motarsa ya ja ya sake ficewa daga gidan.

Wani sabon ƙunci ne ya ƙara mamaye su, saƙar zuciyarsu da tunaninsu iri ɗaya ne.
'Gurin wannan shegiyar ya tafi.'
Wannan tunanin yasa duk suka fito daga ɗakunansu dan zuwa gurin juna su tattauna ko za su samarwa kansu hanya mai ɓullewa sai suka yi kiciɓus a falon. A tare suka kalli juna, duk su biyun mamakin yadda suka yi ƙozai-ƙozai suka zabge a lokaci guda suke yi a ransu amma babu wacce ta furta hakan ga ƴar'uwarta. Sharewa suka yi suka zauna waje ɗaya a kan kujerun falon.

"Rabi yanzu ya zamu yi?"

Ta kalle ta kawai, haka kawai ta ji tambayar ta ɓata mata rai. Ta mele baki gefe ɗaya ta kauda kai
"Ya za muyi kuwa Surayya da ya wuce muyi haƙuri? Tunda duk yadda muka tsara ɗazu ke kika wargaza mana shirin. Kawai daga ganinshi kin kasa cewa komai sai kuka kike yi, da yake ni ce nayi sunan tsiya ni kaɗai kike so in titsiye shi inbi ba'asin rashin adalcin da aka yi mana?"
Ta ja tsaki ƙasa-ƙasa ta sake kauda kai gefe ɗaya ranta na suya.

"Kiyi haƙuri, wallahi ɗazu kasa magana nayi dan baƙin-ciki. Amma yanzu zanyi mishi wurjan-jan idan ya shig..."

Dawowar motarsa yasa ta haɗiye sauran maganar a cikinta. Ƙofar shigowa duk suka zubawa idanu suna jiran su ga da wani ido zai shiga cikin falon ya kalle su?

Shi ma kamar ya san suna falon tsare gida yayi ya koma asalin Maheer ɗinsa da baya ɗaukar wargi ko raini ya murɗa hannun ƙofar falon bakinshi ɗauke da sallama.

Ganin yanayin da ya shiga yasa Surayya amsa sallamar ƙasa-ƙasa ta kauda kanta gefe ɗaya. Ita kuwa Rabi jijjiga ƙafafu kawai take yi tana cika da batsewa. Jira take ya ce kule ta ce cas!

Ya kalli Surayya da ɗaurarrar fuska mare walwala, ya miƙa mata ledojin abincin da yake hannunsa.
"Je kicin ki haɗo mana abinci ki kawo kan dining."
Yayi magana da tsayayyiyar muryar da ba shiri ta miƙe da sauri ta karɓi ledojin, jikinta na ɗan rawa ta nufi hanyar kicin da saurin gaske kamar za ta kifa saboda tsoro.

Masifaffen haushin ɓarin jikinta ne ya kama Rabi, ta ja tsaki a fili. Ta miƙe a fusace za ta wuce ɓangarenta ya daka mata wani gigitaccen tsawan da ba shiri tsoro yasa ta koma daɓas ta zauna a inda ta tashi.

"Ina kike shirin tafiya bayan na ce a haɗo mana abinci gaba ɗaya?"
Ya jefa mata tambayar cikin fushi yana ƙara tamke fuskarsa.

"Na ƙoshi."
Ta faɗa cikin fushi tana tura baki gaba kamar shantu.

"Zauna ina buƙatar magana da ku."

Fitowar Surayya da farantan abinci yasa shi tashi daga kan kujerun falon ya koma kan kujerun cin abinci. Yana zaune yana daddana wata sabuwar waya saɓanin ta shi da suka sanshi da ita har ta gama jera kayan abincin da duk wani abu da za su buƙata, ta zuba mishi a faranti ta tura gabanshi. Za ta zuba nata ya miƙa mata cokali ya umarce ta su ci tare.

A ɗarare take zaune kujerar kusa da tashi, cin abincinshi yake yi hankalinshi kwance. Ita kuwa dukda matsanancin yunwar da take ji dan ko karyawa bata yi tsattsakurar abincin kawai take yi saboda damuwa, tana ci tana share hawaye jefi-jefi.

Kaɗan ta ci ta ajiye cokalin alamun ta ƙoshi, za ta tashi ya ce ta zauna ta jira shi. Sai da yaci yayi ƙat sannan ya bata damar tashi suka koma kan kujerun falon.

Kusa da Rabi ta zauna, kamar haɗin baki duk sai suka sadda kawunansu ƙasa suka zabga tagumi, ababen tausayi ziryan dai ga duk wanda ya kalle su.

Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ya ajiye wayar hannunshi a gefe ya maida hankalinshi kansu ya fara magana a tausashe, cike da nutsuwa da baiwar balaga ta iya magana. Ƙwayoyin idanuwanshi suna zaga tsakanin duk su biyun.
"Ƙarin Aure umarni ne na Allah SWT ga duk wani namijin da ya san zai iya adalci a tsakanin matanshi. Na san duk ku biyun kunsan wannan ba sai na janyo muku wani ayar Alƙur'ani mai girma ko in kawo muku hadithin kuyi aure ku hayayyafa ba.

Amma duk da haka a matsayina na mijinku ina mai baku haƙuri, Allah ya huci zukatanku. Ba wai dan nayi muku laifin ƙara aure nake baku haƙurin ba, kawai ina ji a raina ne kamar ban kyauta muku da ban sanar da ku da bakina ba saidai ku ji a bakin mutane. Amma ina so ku sani nayi hakan ba don cutar da ku bane, ko kuma don in nuna baku da muhimmanci a guri na. Ko kaɗan ba haka bane, duk wacce ta ɗauki wannan tunanin ma ina so ta watsar da wannan daga zuciyarta. Allah ya sani ina son ku, kuma har gobe ina tsananin ƙaunarku. Ina martabaku da ganin darajarku, da waɗannan dalilan bazan taɓa yin wani abu da zai cutar da ku ba.

Batun ƙarin auren nan dukda na san da shi amma ɗaurin auren baga-tatan ya taso min jiya da daddare saboda wasu tarin dalilai da ni kaɗai na barwa kaina sani. Zanyi matuƙar farin ciki idan kuka haɗa kanku kuka rungumi ƙanwarku da hannu bibiyu, zanyi matuƙar farin ciki idan kuka tallafa min gurin sauke nauyinku da Allah ya rataya min a wuyana. Zanyi matuƙar farin-ciki idan kuka juya akalar kishinku gurin tsere da rige-rigen faranta min dan ku sami aljannarku. Ina fatan za ku yi haƙuri ku danni zuciyarku ku bani haɗin kai? ni kuma in Allah ya yarda baza ku taɓa kama ni da yunƙurin yin wani abu na rashin adalci a tsakaninku ba."

Shiru suka yi duk su biyun, aka rasa wacce za ta fara cewa komai. Amma tabbas tausasan kalamanshi sunyi nasarar zabge ɓacin ransu da kashi hamsin bisa ɗari.

"Kun yi shiru? Baku ce komai ba?"

"Insha Allahu za ka same mu masu yi maka biyayya da baka haɗin kai."
Surayya ta ari bakin Rabi ta ci musu wawwarar albasa.

"Na gode Sweetat."
Ya amsa yana sakar mata murmushi. Ya maida idanunshi kan Rabi
"Honey baki ce komai ba."

"Nima in Allah ya yarda baza ka samu damuwa daga gare ni ba. Ka yi haƙuri da rashin kunyar da na yi maka ɗazu."
Ta faɗa a sanyaye, cike da kunya.

Murmushi yayi kawai ita ma yayi mata godiya. Nan ya dararrashe a falon ya ci gaba da jansu da hira. Tun suna ɗari-ɗari har suka sake aka fara wasa da dariya a tsakaninsu irin wanda ba'a taɓa yi ba tun da suka yi aure.

Yinin ranar gaba ɗaya bai sake fita ko ina ba sai masallaci, shi ma da an idar da sallah ya gama lazumi nan da nan yake komawa gida.

Hakan ba ƙaramin farin-ciki ya tsunduma zukatansu a ciki ba, sun tabbatar ko da yana son amarya to su ma fa har lokacin ƴan gaban goshi ne. Sun kuma ɗaura ɗamarar ƙara zage damtse gurin tarairayarsa da nuna masa kulawa, a taƙaice dai ko waccensu tata ta fissheta.

Har washe gari da ya ƙarasawa Surayya kwanan girkinta suna ya fita Ofis da nufin idan ya koma gida yamma Rabi ce za ta amshi girki suna cike da nishaɗi. Saboda jiya bai je ofis ba aiki cakuɗe mishi yayi duk yadda ya so ya samu damar leƙa Bilhaƙƙi bai samu ba, kuma ya kira wayarsa da take hannunta a kashe. Shi kuma yana jin kunyar kiran su Ummee ya ce a bata wayar ko da ya kira gaishe su kawai yayi ya katse, sai da yamma ya samu ya yakice aikin ƙarfe huɗu ya bar Ofis saɓanin biyar da yake tashi kai tsaye ya nufi gidan Malam. Zuciyarsa cike da ɗoki da mararin son ganinta.

Ko da ya isa gidan su Ummee basa nan, sai ƴanmatan gidan ya tarar a kicin suna toya wainar fulawa. Har da ita a cikinsu, suna tsaye gaban Gas ana zuba ƙullun tana soyawa suna wasa da dariya haɗe da caccafkewa, har da Asma'u da ta zo daga Maru.

"Asma'u saukar yaushe?"
(Asma'u idan ba ku manta ƴar wajen Ummee Balaraba ce, sa'anni suke ita da Saudat amma tun tana ƴar ƙarama Malam ya bada ita ga ƙanwarsa Aunty Ramatu da take aure a Maru saboda bata taɓa haihuwa ba. Zamanta a can yasa hausar zamfara ya kama bakinta raɗam)
Ya tambaye ta yana murmushi.

"Daɗa Yaya jiya munka taho da yamma ni da Aunty. Ina yini?"
Ta zube tana gaishe shi cike da ladabi.

Da murmushi ya amsa ta sannan ya amsa gaisuwar Saudat da Bilhaƙƙi da suka haɗa baki gurin gaishe shi. Duk da a gaban ƙannenshi ne ya kasa ɓoye ƙwayoyin idanunshi wajen kallonta, ta yi mishi kyau sosai. Ta sha gayu cikin riga da sket na atamfa, kayan sun kamata tsam sun fito da hips ɗinta, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya, gashin kanta da ta ƙarasa tsefewa ta wanke tas ta kame shi da ribom jelarshi ya sauko ta ƙasan ɗaurin ɗan kwalinta.
"Ina su Mummy?"
Yayi tambayar hankalinshi a kanta.

Hankalinta yana kan wainar fulawa bata san ma da ita yake yi ba sai da Saudat ta zungureta a gefen ciki.
"Sun tafi unguwa."
Ta amsa tana hararar Saudat.

Ficewa yayi daga kicin ɗin ya shiga falon Ummee ya zauna yana jiranta.

"Amaryar yaya ke fa yake jira..."

"Inji wa?"
Ta yi saurin katse saurin katse Saudat tana dariya.
"Zaman jiran dawowar su Ummee yake yi ba ni ba yarinya."

"Daɗa ke kam Matar Yaya na raina wayonki, wa ka whaɗa miki a wagga zamani ana sake da tarairayar mai gida? Billahillazi idan kika yi sake waɗannan manyan matan nashi za su saye hilin zuciyarsa ke kina nan sake da baki. Kinga tai ki tarairayi mai gidanki kawo suyat in amshe ki kafin ki dawo"
Asma'u ta faɗa tana kame da haɓa cikin mamaki.

Dariya tayi kawai ta aje cokalin juyawar ta fice daga kicin ɗin ta nufi gurinshi. Daga bakin ƙofar falon ta turje bayan ya amsa sallamarta, ta kalle shi fuskarta babu walwala sosai.
"In kawo maka wainar fulawa?"

Hannu yasa yafito ta alamar ta je gare shi.

Tana yauƙi da yanga yana bin ta da ido har ta ƙarasa kusa da shi ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafunshi.
"Ga ni"

"Ina wayata?"

Tashi tsam tayi ta nufi cikin ɗaki da nufin ɗauko masa sai ya bi bayanta. Suna shiga ya janyota tsam ya rungume a ƙirjinsa yana sauke wasu wawayen ajiyoyin zuciya akai-akai. Luf tayi a kirjinsa suna shaƙar ƙamshin juna.
"Babe baki yi kewa ta ba ko?"
Ya raɗa mata a kunne.

"Ummm kamar yadda kaima baka yi tawa ba..."

Haɗe bakinsu da yayi guri ɗaya ya fara aika mata da wani sassanyar sumba a nutse yasa tayi luf tana ƙara ƙanƙameshi, jin da yayi kamar za ta zame yasa hannu biyu ya ƙara tallafo mazaunanta ya ci gaba daga inda ya tsaya, tsawon lokaci har tsayuwa na neman gagararsu sannan ya saki bakinta ya ja ta ya zauna a gefen gado ita kuma ya zaunar da ita saman cinyoyinsa. Kanta na kwance kan kirjinsa yana shafa gashin kanta.
"Idan za mu kwana mu yini bazan iya kwatanta miki yadda na kwana na yini cikin kewarki ba. Ya jikinki?"

Ta ƙara langaɓe kanta sosai kamar za ta shige cikin ƙirjinsa, ta tura baki a hankali ta ce.
"Ni na ji sauƙi."

"Ciwon bayan da kafar duk sun tafi?"

"Eh"

"To Allah ya ƙara miki lafiya Babe. Tashi ki ga abinda na kawo miki."
Ta mike za ta sauka daga kan cinyarsa ya sake zaunar da ita, ya dauki ledar da ya shiga da ita ya buɗe sai ga kwalin waya sabuwa dal. Samsung ce sak irin ta hannunsa da yake bata aro, ya ɗauko sabon layin mtn ya saka a ciki sannan ya kunna wayar.
"Wannan wayarki ce, daga yau bazan sake baki aron tawa wayar ba..."

Tsananin murna yasa kafin ya rufe baki ta sake ruƙunƙumeshi tana dariyar farin-ciki.
"Na gode Gangaran..."

"Ke tsaya. Ki canza min suna, bana son Gangaran ɗinnan da kike ce min."

Tana dariya ta kalle shi da sigar tsokana ta ce
"Laaaa fassarar sunanka ne fa."

"Na sani ai, amma bana so kina ce min."
Ya faɗa yana canza fuska.

"Tom, sorry Heart."
Tayi maganar tana shafa saitin zuciyarsa.
"Zan nemi sunan soyayya mai daɗi in dinga faɗa maka ka ji?"




BILHAƘƘI


Ya ɗaga kai kawai alamar ya ji. Ya sake kallonta sama da ƙasa, gaba ɗaya hankalinta yana kan wayar da ya kawo mata, ta shiga nan ta fita can. Ya raɗa mata a kunne.
"Kinyi kyau Babe. Amma ire-iren waɗannan kayan da suke fito miki da shape ki daina saka su a nan gidan, ki adana su sai kin je can gidanki sai ki dinga min kwalliya da su. Zan shiga kasuwa gobe in nemo miki dogayen riguna masu kyau ki dinga sakawa a nan. Kin gane?"

Murmushi tayi, ta ɗaga kai ta kalle shi tayi far da ƙwayoyin idanunta.
"Na gane, na gode Gangar... Au! Ba Gangaran ba. Yi haƙuri."
Ta ƙarasa maganar haɗe da ƙanƙame shi tana dariya. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta runtse idanuwanta da suke cike da shauƙi.
"Bir tanem. Thank you Bir tanem."

"Bir tanem?"
Ya maimita sunan da ta raɗa mishi da sigar tambaya, fuskarsa cike da mamaki bayan ya ɗago kanta daga ƙirjinsa suna kallon-kallo.

Ƙasa sosai ta yi da idanunta, suka yi wani lauuuu kamar tana jin bacci, ta ɗaga mishi kai alamar eh.

"Waw!! Fassara min. Yadda kika furta sunan yayi daɗi sosai a kyakkyawan bakinki. Bir tanem! Da wanne yare ke nan? ba turanci bane ko?"

"Eh ba turanci bane, a wani yaren fassararshi sunan soyayya ne. Ka nemo fassarar..."
Sallamar su Ummee da ta ji sama-sama a can tsakar gidan yasa ta yi saurin miƙewa daga jikinsa tana zazzare idanu kamar wacce ta yi wa Sarki ƙarya. Bai ji abinda ta jiyo ba sai da ta ankarar da shi
"Wayyoo... Su Ummee sun dawo."
Ta yi kwaɓa-kwaɓa da fuska kamar za ta fashe da kuka.

"To miye dan sun dawo?"
Ya tambaye ta cikin rashin damuwa, fuskarsa fal da murmushi. Hannu ya miƙa zai sake janyo ta jikinsa da sauri ta zille ta nufi wardrope ta buɗe tana duba wayarsa a inda ta ajiye.

Jin su Ummee sun shiga cikin falon dole ya miƙe yana ya fita falon, suna haɗa ido ya fara sosa ƙeya cike da kunya.
"Aunty sannunku da dawowa."

Duk su ukun sai suka bishi da idanu, sai Mummy da Aunty suka murmusa ita kuwa Ummee ta haɗe girar sama da ƙasa ta ce
"Me kake nema min a cikin ɗaki?"

Wuf sai ga ta ta fito kamar an jefo ta, ta zunduma hijabin sallarta gaba a baya. Daga kallo ɗaya za a gane duk a ɗimauce ta ke. Ta ɗaga hannuwa duk biyu sama tana nuna musu wayar
"Allah ba komai Ummee, kinga ma wayarsa ya ce in ɗauko masa."
Duk sai ta basu dariya, ɗakinta ta shige ta ƙyale su a nan.

"Daɗa ango kake ɗiyana Maheer, ƙyale Aunty Balaraba da wasu tuhume-tuhume. Yo a ina za a raba Ango da amaryarsa. Tai ka sha sharahinka ka jiya? Ya gidan? ya sauran iyalan naka?"

A saɓe ta samu ta fice daga falon bayan ta miƙa masa wayarsa. Shi kuma ya zauna suna gaisawa da Aunty da Mummy.

Suna can ɗakin ƴan mata Saudat tana ta tsokanarta ita kuma Asma'u tana koya mata yadda za ta tarairayi mijinta ba tare da kunya ba har ya fice daga gidan bata sani ba.
"Yo wallah ko Aunty bar ganinta kamar ta whara tsohewa in kinkaga yadda take tarairayar Alhajinta abin zai baki mamaki. Wallah a can duk tsuhwar mace sam bata sake da gyaran jiki da tarairayar mai gida. In kinka zauna nan sake da baki kina ji kina gani garin kallon ruwa kwaɗo zai ɗamra miki ƙwahwahu..."
Duk su biyun dariya suka kwashe da shi saboda yadda ta furta ƙafafun da hausar gusau gwanin ban dariya.

Haka suka ci gaba da hirarsu mai haɗe da tsokana ta wani fannin kuma suna haɗawa da bata shawarwarin yadda za ta zauna da abokan zamanta. (kunsan dai mafiyawancin ƴan matan yanzu duk wani theory sun sanshi akan aure pratical ne kawai basu yi ba.)


****** *******


Bayin nata suna gama ficewa da sauri ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi, sosai ta fuskance shi tana ƙara miƙar da ƙafafunta.
"Hamisu ya ake ciki? Wannan karon me Malam ya faɗa maka? Yanayin fuskarka yana baiyana min kaman akwai wani mummunan abu da yake shirin tunkaro mu. Ina fatan ba akan mai wutsiya ba ce?"

"Ƙwarai kuwa a kanta ne Ranki ya daɗe."
Ya amsa

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login