Showing 18001 words to 21000 words out of 98260 words

Chapter 7 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

227

Middle Ads

sai narkarta yake yi ta ko ina kamar Allah ne ya aiko shi, ita kuwa duk da tsananin azaban da jikinta ke karɓa sam bakinta yaƙi mutuwa kuma taƙi saduda, bama-baman zagi take ta ɗura mishi kamar tsohuwar bamagujiya tana jifanshi da duk muggan maganganun da suka zo bakinta.
"Wallahi yau sai dai ka kashe ni ko in kashe ka, mugu, azzalumi, maciyin amana. Abinci ne bazan daina saidawa a bakin titi ba tunda dai baka ɗauke min nauyin da musulunci ya ɗora maka ba. Musuluncinka bai ƙare ka da komai ba sai zalunci da butulci, in Allah ya yarda ko ka mutu wuta ne makomarka..."

Saukar ƙatuwar sanda ta ji a gadon bayanta ba zato ba tsammani, nan ta gantsare ta sake ƙwalla ihu ta juya a gigice dan ganin wanda ya aikata mata haka, ido biyu sukai da sarkuwarta Baba Lauratu, zubewa tayi a tsakar ɗakin zuciyarta a ƙuntace ta sake fashewa da wani matsiyacin kuka tana sauraren baƙaƙen maganganun da take yaɓa mata.
"Muguwa mai baƙar aniya, tubabbiyar banza da wofi. Bakinki ya sari ɗanyen kashi azzaluma, in Allah ya yarda ke ce zaki ƙarke a jahannama a wutar ma kina can ƙasan ƙoli, kafira kawai."
Ta maida kallonta kanshi cikin masifa tana nuna shi da tsinin sandar hannunta ta ci gaba da zazzaga ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.
"Masa'udu indai na isa da kai kuma ka haifu a cikina a yanzunnan ba sai anjima ba ka sau auren wannan tubabbiyar, kuma saki uku nake so kayi mata ta yadda baza ta sake maƙale maka ba, idan ba haka ba yanzunnan zan ɗaga maka nono Wallahi."

Da ita da take kukan, da shi da yake tsaye kamar zaki dan tsananin fusata yana ta sauke numfashi ɗif suka yi kamar ruwa ya cinye su, a take kuma sai jikinshi yayi mugun sanyi, nadama mai tsananin gaske ya rufe shi. Sai kuma zuciyarsa ta cilla da shi tunanin shekaru biyar baya da ya maƙalƙalewa Mary Barnabas har ya samu nasarar cusa mata matsananciyar soyayyarsa a duk wani lungu da saƙo na zuciyarsa, tun a lokacin ita Mary so tayi su ringa watsewarsu ba tare da zancen aure ya shigo ba a matsayinsa na musulmi ita kuma mabiyiyar addinin kirista amma sam yaƙi yarda da hakan.

Sau ɗaya ya taɓa gwada yunƙurin kusantarta amma tunda ya fahimci ita budurwa ce dal a leda ya fasa mugun nufinshi, ya sha tsananin wahala kafin ya iya yaƙin shaiɗan ɗin da yake ta ƙawata masa ya keta rigar mutuncinta. Daga lokacin iyakar rungume-rungume da tsotse ke shiga tsakaninsu ba ya taɓa bari su keta iyaka.

Daga baya kuma sai ya fara kwaɗaita mata batun su yi aure, tun tana noƙewa tana turjewa har dai ta amince da gaske zata aure shi, amma da sharaɗin bazai tursasata shiga addininsa ba, ya ce ya yarda.

Ko da ya jewa da iyayensa batun aurenta sai sukayi tsalle suka dire kan cewar sam bai isa ya kawo musu Ahlul kitabi cikin zuri'arsu ba.

A nata ɓangaren ita ma mahaifiyarta tace sam bazata auri musulmi ba, akan maganar aurennan sau goma sha biyar ana tale ta a zaneta a coci amma duk ta jure ta shanye tace in ba Masa'udu ba sai rijiya mai kwalabe.

Da taga ma bai dawo garin Kacia ba daga zuwa sanar da iyayensa zaunannun hayin rigasa kawai sai ta tattara ƴan kayanta ta bar ƙannenta biyu mata da mahaifiyarta dan mahaifinta Barnabas ya dade da mutuwa ta gudu gurinsa, daman tana da cikakken adireshinsu shi da abokinsa Umar da suke zuwa cirani a garin kacia.

Ko da taji halin da yake ciki da iyayensa sai tace in dai musulunta zaisa iyayensa su amince ya aureta ta amince za ta musulunta, amma tana so ya ɗaukar mata alƙawarin duk runtsi, duk wuya, komai wahala da juyin juya hali na rayuwa kar ya taɓa wulaƙanta ta.

Ba tare da tunanin komai ba ya ɗau mata wannan alƙawarin sannan ya ƙara da cewar duk wani daɗi na duniya zaiyi iya ƙoƙarinsa wajen jiyar da ita ko da shi zai ƙuntata kansa da tasa rayuwar. Ba tare da ɓata lokacin komai ba suka je gurin wani limami ya musuluntar da ita, ko da suka yi mishi bayanin halin da suke ciki ya tausaya musu ƙwarai, bayan kwana biyu ya ɗaura musu aure akan sadaki naira dubu goma bisa shaidar abokan mahaifinsa biyu ba tare da sani ko yardar mahaifiyarsa da ƴan uwansa ba.

Jagora yayi wa Limamin har gida yayi wa mahaifiyarsa zazzafar nasiha, ya jawo mata ayoyi da hadithai masu nuni akan cikar imani ta hanyar yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau, ya nusar da ita ɗimbin lada da romon da bawa yake sharɓa a wajen ubangiji idan yayi sanadiyyar musuluntan mutum ɗaya a ƙarshe ya dire da faɗa mata ɗaura auren Mary wacce musuluntan da tayi ya maida ita Maryam da Masa'udu ƙwallin ƙwal ɗin yaronta namiji a cikin ƴanuwansa mata bakwai, yaron da ta gama tattalinsa da ɗora burin duniya a kansa tana ganin nan gaba kaɗan shi ne zai zama Ɗangwaten hayin rigasa gaba ɗaya.

Nan Liman ya cigaba da ƴan nasihohinsa da fatan alkhairi wa auren amma abinda bai sani ba tun da ya faɗi tabbatuwar auren ta daina fahimtar abinda yake cewa har ya kwashi tsumman ƙafufunsa ya ƙara gaba.

Kamar gaske ta basu ɗaki guda a cikin gidan da cewar su zauna amma zuciyarta cike da alwashi kala daban-daban na yiwa tubabbiyar gashin ƙuma a tafin hannu har sai azaba yasa ta bar gidan da ƙafafunta.

Tabbas tayi nasarar hakan, a hankali da zuga da makirci da sharrin abinda bata yi ba tace ta yi saida ta sa Maryam ta fice daga zuciyar Masa'udu, duk abinda yayi niyyar yi dan ya kyautata mata sai Baba lauratu tayi fiti-fiti ta hana, ta ƙara da ce masa ita mace ba a gwada mata tsananin daɗi in ba haka ba sai ta lalace, balle ma ita tubabbiya ai sun saba da wahala, matan kirista su suke noma su ciyar da mazajensu.

A hankali har ya sangarce ya ci gaba da neman matan banza a waje dukda kuwa tsananin ladabi da biyayyar da Maryam take masa, tana iya ƙoƙarinta gurin shanye duk wulaƙancin da suke mata bango da bango, ba ga uwar ba ba ga ƴan'uwansa mata da shi kansa ba.

Sana'a iri-iri tayi dan ta rufawa kanta asiri, gorin haihuwa kuwa da yana fitowa a jiki da ya fito mata dan tsananin gorin da suke mata, amma a gefe guda Baba Lauratu murna take yi da rashin haihuwar dan ta ce Allah ya kyauta ta haɗa jini da tubabbiya.

A gurinsa ta ƙara gogewa da hausa ƙwarai kamar jakar kano, daman kuma ko a kacia suna cikin hausawa ne, tana ji sosai, a yanzu kam idan ba faɗa aka yi ba babu wanda zaice ba asalin bahaushiya ba ce.

A lokuta da dama idan ta zauna tana kuka tana yawan tunanin wai dama haka musulunci da musulmai suke? Ita dai bata tsinci komai a musuluncin ba sai baƙin ciki da takaici da ɗumbin da na sanin shiga cikinsa.
(Wa'iyazu billah. Ta haɗu da baragurbin musulmai😢😢)

Abinda ya zafafa rikicinsu a kwanakin shi ne saida shinkafa da miya da ta fara yi a bakin titi kusa da shagon wani mai saida miniras, Allah ya sa mata albarka sosai take ciniki a gurin, shiga ta mutunci take yi kuma bata yarda wani maganar banza ya shiga tsakaninta da maza, tana da almajirai biyu da suke mata wanke-wanke da miƙa abinci.

Ganin rayuwarta ya fara canzawa tana cikin walwala sai ƴan uwansa da Baba suke ta zuga shi da lallai ya hana ta saida abincin in ba haka ba zata kwaso cikin da ba nashi ba ta kawo mishi, dan duk unguwa an san bin mazanta take yi tana fakewa da sunan sayar da abinci...

"Dan ubanka tunanin me kake yi? Za ka sauta ko sai na tsine maka?"
Ta katse mishi zuzzurfar tunanin da yake yi cikin masifa da ɗaga murya.

Ya kalle ta a hankali, ita ma shi take kallo, idanunta cike maƙil da hawaye, amma a hakan ƙoƙarin murmushi take yi dan ta nuna mishi ko ya sake ta bata da asara, fuskarta dama da hagu sashin yatsunsa ne kwance, bakinta a fashe, ya aune ya kumbura suntum, kyakkyawar halittarta duk ya canza zuwa mummuna dan tsananin dukan da ta sha, wani matsanancin tausayi da ƙaunarta da ya daɗe baiji irinsa ba ya tsirga a filin zuciyarsa.

Ya maida kallonsa kan Baba Lauratu, a sanyaye kuma cike da ladabi ya fara magana.
"Baba kiyi haƙuri, idan na sake ta zata iya komawa ruwa cikin addininta na kirista..."

"To ta koma mana dan Ubanta. Ai daman ko yanzu ba musulma bace tunda bata shekara arba'in a cikin musuluncin ba, manyan malamai sun tabbatar da hakan. Maza sakatta mu yarda ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda."

Ya zube a gabanta ya riƙe ƙafafunta da niyyar fara mata magiya.
"Baba..."

Ta katse shi da sauri ta hanyar fincike ƙafafunta ta ɗaga murya ta fara addu'ar cikin sauri
"Ya Allah ka tsi..."

"Baba zan sake ta, dan Allah karki ƙarasa"
Ya katse ta da faɗan haka cikin gunjin kuka kamar mace.

Jikinsa na kyarma ya rarrafa kusa da ita ya haɗa hannayensa biyu alamar roƙo, sai kuma ya miƙa hannu kamar zai ruƙo nata hannun da sauri ta ja da baya kamar ta ga kumurcin maciji.
Bai damu ba ya fara magana sauri-sauri murya da jikinsa babu inda ba ya rawa.
"Maryam ! ki yi haƙuri. Ban taɓa tunanin a nan kusa zanyi da na sanin irin abubuwan da na daɗe ina miki ba, a yau da Allah ya fargar da ni sai kuma na rasa damar da zanbi gurin gyara kuskure na. Duk da nasan zaiyi wahala ki iya yafe min amma dai bazan gaji da roƙon ki yafe min ba. Maryam dan girman Allah ki yafe min, ina roƙonki ko da kin tafi dan Allah karki koma cikin addinin kirista... Na sake ki ! Saki uku!!"
Yana ƙarasa sakin ya zube wanwar a gurin yana jan numfashi sama-sama kamar mai cutan asma.

Suman wucin gadi ta yi, Allah ya sani ta so Masa'udu so mai tsanani, duk da irin azabtar da ita da yake yi bata taɓa tsannanin akwai saki a tsakaninsu ba, yanzu da sakin ya afku sai tayi tsam da ranta jijiyoyin shige da fice wajen kai saƙonni a ƙwaƙwalwarta suka tsaya da aiki na wucin gadi.

Ƙaƙƙarfar guɗar da Baba Lauratu ta daddage ta rangaɗa shi yayi nasarar dawo da ita cikin haiyacinta, bakin ta kamar gonar auduga, burinta ya cika. Yau dai Allah yayi sun rabu da alaƙaƙai.
"Zaman me kike yi? ai sai ki yunƙura ki fice mana daga gida tunda igiyoyin da suka sarƙafa mana sun tsittsinke..."

"Dakata Baba Laurata !"
Tayi ƙarfin halin dakatar da ita cikin tsawa tare da ɗaga mata hannu. ɗan ragowar jarumtar da ya rage mata ta tattaro ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta babu inda ba ya mata ciwo.
"Ta fi nono fari, ɗanki ga shi nan ki jiƙa shi ki sha. Idan kinso ki aure shi ƙarewar hana shi auren tubabbiya..."

"Keeee karki kawo min iskanci da zancen banza irin naku na kafurai"
Ta katse ta cikin zafin rai ta ɗaga sandar hannunta da nufin sake kwaɗa mata.

Caraf ta riƙe sandar tana gwalalo ido waje
"Wallahi kika sake duka na saina zubar da ke a nan gurin, matsiyaciya wacce bata san Allah da ikonsa ba."
Yarɓar da sandan tayi Baba ta tafi taga-taga kamar zata faɗi ta yi ƙoƙarin tsayawa.

Bata sake kallonsu ba ta nufi ma'ajiyar kayanta ta ɗauki doguwar riga ta canza riga da zanin jikinta da suka yayyage. Ta ɗauki wani siririn gyale ta rufa a kanta ta ɗauki jakar hannu inda take tara ƴan kuɗaɗenta ta nufi hanyar ficewa daga ɗakin hannunta jaye da akwatin kayanta.
"Masa'udu na barka har abada, kamar yadda na bar maka addininka har abada."
Daga haka bata ƙara cewa komai ba ta fice daga ɗakin ta bar gidan gaba ɗaya, tana fita taga wani mai mashin ta ɗare a kai ta ce ya kaita bakin titi.


*******


Duk yadda ta so ta ƙarfafi kanta kar ta sake kuka ta kasa, bata san lokacin da wani ƙaƙƙarfar kuka ya sake ƙwace mata ba. Da saurin gaske ta sa hannu biyu ta toshe bakinta ta rufe fuskarta dan kar hankalin mazauna cikin motar ya dawo gare ta.

"Ki yi haƙuri"
Ta ji saukar kalmar da ƙaramar murya kamar a tsakiyar kunnenta, a hankali ta ɗago kai dan ganin mai maganar sai tayi arba da kyakkyawar fuskar yarinyar da take zaune kusa da ita.

Tsawon minti biyu suna musayar kallo sai yarinyar ta haske ta da tattausan murmushi, ta miƙa mata wani ɗan ƙaramin tsumma.

Fahimtar abinda take nufi yasa ta karɓa ta fara share hawayen fuskarta, tana gogewa wasu sabbi na sake gangarowa har ta goge gaba ɗaya bayan ta samu nasarar tsaida kukan da ƙyar.

Pure water ta miƙa mata mai sanyi, ba tare da musu ba ta karɓi ruwan ta huda ta fara sha wani sanyi yana kwarara a zuciyarta.
"Na gode. Ya sunanki?"

"Bibi"
Ta amsa a hankali bayan shirun da tayi na second talatin kamar baza ta amsa ba.
Dan ma kar ta sake tambayarta sai ta sanya tafukan hannayenta duk biyu ta rufe fuskarta tana tunani kamar mai bacci.
'Maman Ushe ta mutu, Indo ta mutu, Mal Muntari ya mutu, Raliya ta mutu. Ya zama dole ta gudu daga layin mai dubun tsumma in dai tana so ta cigaba da rayuwarta.
Ta ji lokacin da aka zo gurin Mal daga gidan hakimi da cewar a tafi da ita ana tuhumar ita mayya ce, tun a lokacin ta yanke wa kanta shawarar abinda zai fisshe ta, da wannan dalilin yasa ta ɓuya can bayan gidan gurin shuke-shuke har sukai kiciɓis da Indo tana fata da mugun alkaba'i a kan Maman Ushe.

Ko da Indo ta koma ɗakinta ta faɗi cikin mawuyacin hali bata fito daga maɓoyarta ba, da yake mutan gidan suna cikin tashin hankali shi yasa ma babu wanda ya tuna da ita balle har a neme ta. Indo tun kafin a kaita asibiti ta ce ga garinku nan.

Mal Ali da duk wani wanda ya kusance su da al'ummar unguwa sun shiga cikin tashin hankali matsananci, rashin mata biyu a lokaci ɗaya ƙarfin imani da addu'a ne kawai ya hana Malam Ali zaucewa.

Cikin dare ta yiwa gidan kallon ƙarshe ta bar kowa da komai na gidan ciki har da sunan Amirah da Maman Ushe ta raɗa mata ta fice daga ita sai kayan makarantan jikinta da naira saba'in a aljihun wandonta.

Tafiya kawai take ba tare da sanin inda take jefa ƙafafunta ba ta wayi gari a bakin titi misalin ƙarfe takwas da rabi na safe, motocin Ganjal sai wucewa suke kwandastoci suna ta shelar
"Kasuwa... kasuwan bacci."

Ba tare da tunanin komai ba tasa hannu ta tsaida motar.
"Yarinya ina za ki?"

"Kasuwa"
Ta amsa shi da sassanyar murya.

"Naira hamsin"
Ya faɗa mata bayan ya sauka daga kujerar farko ta shige ciki, har motar zata tashi ta hangi mai pure water sai ta sayi guda ɗaya.

Sun fara tafiya ba daɗewa Maryam ta tsaida motar ta shiga bayan ta ce ita ma kasuwa za ta...'

"Bibi kina bacci ne? mun iso fa."
Maryam ta katse mata tunanin da take yi ta hanyar jijjiga ta da ɗan ƙarfi dan ta dawo cikin haiyacinta.


******* *******

"Mary kwana da yawa? gaskiya mun daɗe bamu haɗu ba, amma bana tunanin wannan ƴarki ce dan naga ba ƙaramar yarinya bace, ko sistan mai gidanki ce?"

Taja tsaki fuskanta a ƙuntace, duk da tayi wanka kuma ciwukan jikinta duk anyi dressing ɗinsu ta ci abinci mai rai da lafiya ta sha magunguna har lokacin tsamin da jikinta yayi bai saki ya koma mata dai dai ba.
"Mercy daina tuna min batun ɗan iskan nan. Mun rabu da shi gaba ɗaya."
Ta maida kallonta kan Bibi da take barci hankalinta kwance, ita ma anyi mata wanka an canja mata kaya da sabbin ƙananun kaya ƴan kanti riga da wando.
"Wannan yarinyar a mota muka haɗu, fahimtar da nayi bata san kowa ba kuma bata san inda zata je ba tsawon lokaci tana zaune a gefen titi shi yasa na taho da ita dan kar ta faɗa mugun hannu. Idan ta samu nutsuwa zan tambayi inda iyayenta suke sai in mayar da ita."

"Ok ! kin kyauta. Ni zan fita, akwai komai da zaki iya buƙata, idan kuma kina son wani abu ki kira Grace ki yi mata magana. Maybe zan dawo kunyi bacci."
Makullan motoci huɗu da suke zube a kan ɗan ƙaramin teburin gilas ta ɗauki guda ɗaya ta nufi hanyar ficewa daga falon, Maryam tana mata fatan dawowa lafiya.

'Tun a hanya da ta tuna yanayin yadda jikinta yake ciki ta yanke shawarar baza ta koma garinsu a wannan halin da take ciki ba. Dole ta nemi inda zata huta ta samu nutsuwa raunin jikinta su warke kafin ta koma gurin mahaifiyarta da ƴan uwanta ta basu haƙuri, tana cikin tunanin ne ƙawarta Mercy Abom ta faɗo mata a rai, tana zaune ne a Kamazou, ta san babu inda zata je ta samu tarba ta mutunci da girmamawa da ya wuce gurin Mercy, dan haka kai tsaye ta yanke shawarar nufan can ita da Bibi.

Kamar yadda tayi tsammani kuwa Mercy ta tarbeta da tsananin murna, ta kaisu har cikin tanƙamemen ɗakin barcinta, ta haɗa musu ruwan wanka mai zafi suka gargasa jiki. Ba tare da ɓata lokaci ba ta kira likita ya duba ta ya bata magani, ta bada umarnin a haɗa musu lafiyayyen abinci har saida suka ture. Kafin ta fita tace su shiga duk inda suke so a tangamemen gidan nata su yi duk abinda suke so ta basu dama.

A cikin kwanaki goma da suka biyo baya Mary wacce ta daina sallah, kuma ta

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login