Showing 87001 words to 90000 words out of 98260 words

Chapter 30 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

211

Middle Ads

saurayin da yake tsaye a cikin hoton, sai kuma wani ƙaramin yaro da bai wuce shekaru huɗu ba, babu riga a jikin yaron aka ɗauki hoton. Abinda ta gani a ƙirjin yaron yasa ta miƙe tsaye
"Exactly akwai irin wannan zanen a ƙirjin Musty, kuma ita ma Baby Bilhaƙƙ akwai shi a ƙirjinta. Infact ma shi da hannunsa yayi mata zanen kafin ya mutu..."

"Wa yace miki ya mutu? Ai yana nan a raye. Ɗanuwanki bai samu nasarar ƙona shi ba saboda wani bawan Allah da yaje ya cece shi kafin a cinnawa gidan wuta..."

Tsananin ruɗewa da gigitar jin Mistyn ta yana raye bai mutu ba yasa ta tafi Suuuu a sume za ta zube a ƙasa, da sauri Ummi da ta ankare da abinda ke shirin faruwa ta tare ta suka zube ƙasa gaba ɗaya.





BILHAƘƘI


Tunda ta farfaɗo jikinta babu inda ba ya kyarma, sai tattakurewa take yi kamar mai jin sanyi. Hannunta na dama riƙe da na Ummee ta ke ta maimaita mata tambayar
"Don Allah Hajiya da gaske Musty yana raye? idan yana da rai to zaman me nake yi a nan? ku kaini gurinsa dan Allah. Akwai maganganu da dama da ya kamata in tattauna tsakanina da shi."

Ummee cike da tausayi ta ke tausarta da kyawawan kalamai na kwantar da hankali. Shi kuwa Malam ficewa yayi daga falon don tsananin tausayinta, bayan yayi mata alƙawarin gobe da sassafe idan sun wayi gari lafiya za suyi sammakon zuwa Bauchi dan ta ga Mustafanta.

Yadda ta ke gyaɗa kai da sauri kamar ƙadangaruwa tana mishi godiya da addu'ar Allah ya shirya mishi zuri'arshi shi ne abinda ya ƙara karyar mai da zuciya. Dauriya da jarumtakar ɗa namiji ne kawai ya hana shi ya zubar da hawayen tausayinta.

Bilhaƙƙi kuwa tunda ta ga Rebeccah ta farfaɗo lafiya gefe guda ta koma ta zauna sai wani murmushi ta ke yi ita kaɗai, tunaninnika ne kala daban-daban a zuciyarta.
'Ashe dai ita ma yarinya ce kamar ko wace ƴa mai cike da nagartaccen nasaba? Ita Billhaƙƙi ce jikar babban sarki kamar Abdulfatahi da Sarauniyya Safiyya? Ga mahaifiyarta Rebeccah a raye kusa da ita, ga mahaifinta can Mustapha ɗan Sarki gobe za ta je ta haɗu da shi. Iyalan Malam da ta ke tsanani ƙaunarsu a ranta ashe ƴan'uwanta ne na jini makusanta? Kai ita kam farin ciki yayi mata yawa...'

Fakar idanun mutane Maheer yayi ya ja hannunta da mugun sauri suka fice daga falon, ba ɗakin Ummee ya nufa da ita ba. Can ɗakinsu na ƴanmata ya zagaya da ita.

Suna shiga ciki ya ga Saudat ta barbaza littafai a gaba da alamun karatu take yi.

Idanu ya buɗe mata sosai tare da balla mata harara
"Dallah Malama fice mana daga nan."

Sum-sum ta kwashi takardunta ta fice daga ɗakin, sai satar kallon Bilhaƙƙi take yi tana gimtse dariya har ta bar ɗakin.

Yana ganin ta fita ya janyo ta tsam ya matse ta a ƙirjinsa da ƙarfi yana sauke ajiyar zuciya.

"Sevgilim za ka murƙusani."
Ta faɗa da muryar da ke baiyana tana jin zafin riƙon da yayi mata.

Sassauta riƙon yayi sannan ya ja ta suka zauna a gefen gadon. Kifa kanshi yayi a cinyoyinta yana sauke ajiyar zuciya sannu-sannu kamar mai shirin bacci.

Ƙura wa kanshi idanu tayi tana murmushi, kwantaccen gashin kansa mai kama da na fulani yaja hankalinta sosai. Sai ta miƙa hannu tana shafa gashin a hankali, hakan da ta yi sai ya ƙara kashe mishi jiki.

Da shaƙaƙƙiyar murya ya ce
"Tatlim! Ina buƙatarki. Yau ɗaya pls ki zo muje ki taya ni bacci, kinji?"

Narai-narai ta yi da idanu kamar za ta saka kuka, ina yaushe za ta iya bin miji ta ƙyale Mommanta Rebeccah?

Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa shi ɗaga kanshi daga jikinta suka ƙurawa juna idanu. Idanunshi sun ɗanyi ja kaɗan, fuskarsa nannarke da ɓoyayyiyar damuwa.

Ita kuwa yanayin tsoro da firgici shi ya fi bayyana a idanunta, sai wasu ɓoyayyun hawaye da suka kwanta a kwarmin idanunta na tsananin ƙaunar mijinta.

Janyota ya sake yi ya rungume tsam, a hankali ta ji yana zage zip ɗin rigarta ta baya. Bata yi yunƙurin hana shi ba, sai ta runtse idanu tana jin wani irin waiwayi a bayan kamar yana mata tafiyar tsutsa.

Tana ji tana gani har ya zare rigar gaba ɗaya a jikinta, ya ɓalle ɓallin bra ɗinta ya zaunar da ita a cinyarsa, hannu ya kai cike da shauƙi da sha'awa ya shafi zane-zanen. Shi masifar kyau suke masa a idanunsa, ga kuma ɗaukar hankalinsa da suke yi tun ranar da ya fara gani a jikinta.

"Amma gobe idan munje can babu wanda zai ce ki buɗe nan ya ga zanennan ko?"

"Haba dai!"
Tayi maganar a shagwaɓe. Kafin ya ce wani abu cikin kunya ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta ci gaba da cewa
"Kai kaɗai za kaita gani Sevgilim. Nan ba gurin ganin kowa bane, naka ne kai kaɗai."

Tsam ya ƙara riƙe ta, da baya ya kwanta a kan gadon ita kuma ya kwantar da ita a ƙirjinsa. Hannu biyu yasa ya riƙeta kamar yana tsoron wani zai ƙwace mishi ita.

Da yake yana tare da gajiya a jikinsa nan da nan wani daddaɗan bacci ya fara fisgarsa.
"Kin amince muje ki taya ni kwanan?"

"A'a ni dai! Zan kwana kusa da Mamana."
Ta faɗa a hankali.

Shiru yayi bai sake cewa komai ba, can sai ya miƙe zaune har lokacin tana jikinsa, rigarta ya mayar mata ya sauketa ta zauna a gefenshi.
"Zan tafi gida. Akwai abinda kuke buƙata kafin in wuce?"

A sanyaye ta gyaɗa mishi kai alamar a'a, tausayi ya bata sosai. Da ganin yanayinsa yana buƙatar jinta a kusa da shi, to amma ya zata yi mishi? ita ko babu Mamanta ma baza ta iya barin Ummee ta bishi zizi su kwana a hotel ba. Ya jira kawai har ayi bikinsu. Tana ji tana gani ya fice daga ɗakin fuskarsa cukwuikwuiye da damuwa.


****** *******


A lalace cike da sanyin jiki haka yake tuƙa motar har ya isa gidan. Ko da yayi sallama ya shiga ciki damuwar da yake ciki ne ya hana ya karanci yanayin da fuskokinsu suke ciki.

A sakarce duk su biyun suka yi mishi sannu da zuwa, basu jira amsawarshi ba suka ƙara mayar da hankali kan kallon da suke yi.

Shi ma yana amsawa ya nufi ɓangarensa, ko da ya shiga ɗakin cike da kasala ya zauna a gefen gado yana jiran shigowar Surayya ta haɗa mishi ruwan wanka, tunda ranar girkinta ne.

Ganin shiru bata shigo ba kawai sai ya faɗa banɗaki ba tare da wani damuwa ba. Jikinsa a mace yake, ga wata muguwar kasala da gajiya da take nuƙurƙusarsa. So yake ya kwanta da wuri saboda tafiyar da take gabansu gobe.

Yana fitowa ya ga Surayya tsaye ƙyam a tsakar ɗakin, ya kalle ta kawai, ita ma shi ɗin take kallo. Sai a lokacin ya lura da kwantaccen damuwar da ke kan fuskarta, amma saboda bai shirya fuskantar wata damuwar ba bayan wacce yake ciki mazewa yayi.

Ya watsa mata taurarin murmushi ya wuce ta ya nufi gefen gado ya zauna, hannunsa riƙe da ƙaramin tawul yana goge ruwan kansa da kafaɗunsa.

"Idan ka gama ga abinci can yana jiranka..."

"A'a Alhamdulillah! na ƙoshi a gidan Malam."

Ƙanƙance idanu tayi cike da masifa, ɓacin ranta sai ƙara hauhawa yake yi, kwanaki biyar kenan tun da ya tsiri tafiya bauchi har yaje ya dawo yana wani wofintar da su a wulaƙance.

"Ki shirya min kayan tafiya gobe da su Malam za mu sake komawa Bauchi..."

"Bauchi kuma? bayan tafiyar da kuka yi rannan?"
Ta tambaye shi cike da gatsali da rashin kunya.

"E"
Ya amsa ba tare da damuwa da yanayin yadda tayi maganar ba.

"Madallah! To muma mu shirya ka tafi da mu ke nan...?"

"Ina ɗin? A kan me zan tafi da ku?"

Ya tambaye ta yana kallonta da mamaki, zama sosai ya gyara a gefen gadon yana fuskantarta da jiran jin da wacce ta zo. Ya lura da take-takenta tsiya take ji, shi kuwa zai sauke mata duk wani abu da yake damunta.

"Can Bauchin, ko kana tunanin bamu san wancan tafiyar da Amaryarka ka tafi ba? Maheer wai me kake nufi da mu ne? Idan ka fara gajiya da mu ne tun kafin Amaryarka ta shigo gidannan ka sanar damu kawai. Ni gaskiya bazan iya zaman wulakanci da bandaro ba. Atoh! Tafiya ce ko dai gobe ka tafi da ni ni mai girki ko kuma kaima ka fasa tafiyar ka zauna a gida ka bani hakkina."
Tana zuwa nan a maganganunta kawai sai ta fashe da ƙaƙƙarfar kuka ta zube a tsakar ɗakin tana rerawa kamar karatu.

Shi kuwa kallonta kawai yake yi da mamaki, ashe Surayya ma fitsararriya ce bai sani ba. Lallai ya yarda ko wane gauta ja ne sai dai in bai sha rana ba. Wani ɗan tunani da ya gilma a zuciyarshi yasa shi sakin murmushi, ya fara magana a tausashe
"Kina tunanin ko da muka je can ɗin wani hutawa muka yi ni da Tatlim? Hmmm! Rashin sani ya fi dare duhu. Any way! Shi ke nan! Ki faɗawa Rabi ta shirya ke ma ki shirya goben mu tafi gaba ɗaya. Ku shirya da wuri don Malam ya ce tafiyar sassafe za mu yi."

A hankali ta ke rage sautin kukan kamar ana control ɗinta da remot har ta ɗauke sautin kukan gaba ɗaya. Ta miƙe tsaye bakinta a gaba ta fice daga ɗakin tana gunguni
"Oho dai! Idanma tsananin wahala kuke sha a can ɗin muma a je damu mu sha tare."

Shi dai ya raka ta da idanu har ta fice daga ɗakin gaba ɗaya. Murmushi ne ya sake kuɓuce mishi.
"Mata? Hmmm! Sai a barsu da halinsu."

Shiryawa ya ci gaba da yi har ya gama shirin bacci gaba ɗaya ya bi lafiyar gado, yayi mamaki da har ya kwanta bata shigo ba. Da yake yana tare da gajiya bai bari yayi zurfi a tunanin ba nannauyan bacci yayi awon gaba da shi.

A can babban falo kuwa Surayya da Rabi sun daɗe suna shirya yadda idan aka yi tafiyar za su haɗu su cusgunawa Billhaƙƙi.
"Ki ƙyale shegiyar yarinyar nan, da ƙafafunta sirara kamar ragowar amai da gudawa. Har fa yana wani ce min ba daɗi suke ji a can ɗin ba. Kila ko yana tunanin bamu san ƙanwar kakansu ita ce matar sarkin bauchin ba. Don Allah ina wata wahala da za a sha a kaiwa matar sarki ziyara?"

"Ke ma dai Surayya kamar baki san rainin wayau na ɗa namiji ba? Ai tsabar dabara ce yake neman shirya miki. Yayi tunanin ko za ki ce mun hakura da tafiyar. Ai yau kam kin gama burgeni, aikinki yayi kyau, daman ke ce kike mishi lakwa-lakwa yana taka mu yadda yake so. Tuntuni da mun haɗa kai ai wallahi da ba haka ba..."

"Ai yanzu duk wani batun rikici a tsakaninmu ya ƙare Rabi. Tunda an kawo wata rikicin me za muyi? mu haɗa kai mu kore ta tukunna sai mu cigaba da bugawa a tsakaninmu."

Dariya suka kwashe da shi gaba ɗaya, suna tuna yadda da suke yawan faɗa a tsakaninsu kamar masu ganin hanjin juna.

"Ke muje fa mu shirya kayanmu mu kwanta, dan ya ce gobe tafiyar sassafe za a yi inji Malam."
Daga nan suka yiwa juna sai da safe ko wacce ta nufi ɓangarenta, zukatansu cike fal da farin ciki.


******* *******

Sauri-sauri ta shirya saboda kusan duk an gama shiryawa ita ake jira, ba wani kwalliya mai yawa ta yi a fuskarta ba, ɗaya daga cikin dogayen rigunan da ya sai mata kwanakin baya ta zura ta naɗe mayafin.

Sosai ƴar doguwar fuskarta tayi kyau, dukda dai ta ɗanyi fayau alamun ramewa saboda rashin lafiyar da ta yi, don har lokacin wuyanta da kafaɗanta basu gama warkewa ba.

Tana fita falon tayi turus ta tsaya tana kallonsu, suma ɗin ita suke kallo tunda fuskokinsu na saitin ɗakin da ta fito ne.

Wani ɗan murmushi tayi da sassarfa ta nufi gurin Aisha matar Luƙman.
"Aunty Aisha ina kwananku? kun ƙaraso ashe? Sam banji shigowarku ba."

Da fara'a Aishar ta ke amsa mata gaisuwar, su kuwa fuskewa suka yi ko wacce ta ɗauki wayarta tana daddannawa, sun sha kwalliya na ƙure adaka kamar masu shirin halartar gasar zaɓen sarauniyar kyau. Sai yatsune-yatsune suke yi alamu dai na tsananin wulaƙanci.

Ita ma da yake ta fi su gigi suna gama gaisawa da Aisha bata ƙara kallonsu ba ta wuce ɗayan Bedroom ɗin Ummee inda Mamanta ta ke.

Ganin yadda Rebeccah tayi kyau cikin doguwar rigar atamfa ba ƙaramin daɗi ya tsunduma zuciyar Bilhaƙƙi a ciki ba. Duk wannan tsufa da lalacewar da ta yi kashi talatin da biyar sun ragu cikin ɗari. Ta ƙarasa cikin ɗakin da sassarfa ta rungumeta tana dariya
"Mamata kinyi kyau sosai wallahi, kamar ba ke ba. Anya ma idan Babana ya ganki zai gane ki kuwa?"

Zare idanu ta yi tana dariyar ita ma, ta ɗago fuskar Bilhaƙƙi suna kallon juna da murmushi a fuskokinsu, sai kuma idanun Rebeccah ya cicciko da hawaye
"Baby Billhaƙƙ a wancan lokacin da Babanki ya aure ni kamar ke nake, kyau da dirin jiki, gayu da kwalliyar sosai ni kika biyo. Idanunki da bakinki ne kawai irin na babanki. Amma exactly ke kamar ni ce da nake yarinya. Ko a yanzu ma Babanki zai sake so na a karo na biyu? kila ma yayi aurenshi ya auri hausawa yarinya ba kamar ni da na tsufa ba."
Sai hawaye suka zubo mata shar! Gwanin ban tausayi.

"Oh noo! Kar kiyi kuka Mamana. Malam ya faɗa min har yanzu Babana yana tsananin son ki. Har fa sun saka anje can ƙauye nemanki, da ba'a same ki ba har yanzu yana can yana ta damuwa da addu'ar Allah ya baiyana mu ni da ke. Wannan ai babban alamu na soyayya ce ko?"

"Eh Baby ta."
Ta amsa zuciyarta cike da jin daɗin maganganun.

Ummee ce tayi sallama ta shiga cikin ɗakin hannunta riƙe da kofi ta haɗo kakkauran tea a ciki, ɗayan hannun kuma riƙe da plate an zuba soyyyen dankalin turawa da ƙwai a ciki
"Ummu Bilhaƙƙi ga tea ki sha. Kinsan fa mikakkiyar tafiya ce a gabanmu. Malam ya ce kowa ya karya kafin a ɗauki hanya."

"Na gode Hajiya, Allah ya saka da alkhairi."

Bata saurari godiyar ba ta maida idanunta kan Billhaƙƙi da murmushi a fuskarta.
"Kije ku haɗa tea ke da Saudat, kwai da irish yana nan na ajiye muku a kicin."

"Tam! Sannu da aiki Ummee. Shi ne yau ma baki kira ni na taya ki ba?"
Tayi maganar a shagwaɓe.

"To yi hakuri, ai kullum indai lafiya kike tare muke yi. Har yanzu baki gama jin sauki ba shi yasa na barki ki huta. Je ki maza ku karya kar mu makara."

"Tam!"
Ta amsa a ladabce da murmushi a fuskarta, ta fice daga ɗakin da sassarfa.

Tana fita falon ta hange Maheer da Luƙman zaune a kan dining suna karin kumallo. Su kuma matan suna kan kafet sun shimfiɗa ledan cin abinci suna karyawa.

Kusa da su ta ƙarasa fuskanta na kan Luƙman ta fara gaishe su.
"Ya Luƙman ina kwana? Ya Maheer barka da safe."

Da fara'a suka amsa mata. Maheer sai laluben fuskarta yake yi dan su haɗa idanu amma ko kallon ɓangaren da yake zaune ta ƙi yi. Suna gama gaisawa ta wuce da nufin shiga kicin.

"Keeee!"
Daga can tsakiyar falon Surayya ta kira ta a wulaƙance kamar bata san sunanta ba.

Dukda faɗuwar da gabanta yayi, da yadda ranta ya ƙara ɓaci bata tsaya ba, balle kuma har ta juya. Tafiyarta bai canza ba daga inda ta nufa, sai da taji daga can Surayya ta sake cewa cikin fushi.

"Ke Bilhaƙƙi baki ji ina kiranki bane?"

Kamar baza ta tsaya ba sai ta tsaya, ta runtse idanunta, addu'oi take ta ja a zuciyarta sannan ta juya ta nufi gurin Surayyan.
"Aunty Keee fa naki ji kina cewa ni kuwa ko Ummee bata ce min keee. Ga ni."

Sai da taja wani dogon tsaki ta bita da mugun kallo cike da muzanci, ta nuna mata kofin da ta gama shan tea da yatsarta manuniya.
"Ɗauke wannan kofin ki kai kicin."

Duk mutanen falon basu ji daɗin yadda Surayyan ta yi wa Bilhaƙƙi ba, ba ma kamar Maheer da ya tsaya cak da cin dankalin da yake yi yana kallon Bilhaƙƙi har tazo ta wuce ta kusa da su hannunta riƙe da kofin, shi kaɗai ya ga yadda idanunta suka tara ruwa.

Ummee ma da ta fito tun sadda ta ji keee ɗin tana tsaye a bakin ƙofar ɗakinta tana ji tana ganin duk abinda yake faruwa ranta a ɓace. Wucewar Bilhaƙƙi yasa ita ma ta fito zuwa ɗayan ɗakinta inda Bilhaƙƙi take kwana. Sai a lokacin matan suka lura da tsayuwarta, tsuuuu suka yi musamman Surayya da ta yi rashin mutuncin.

Shi kuwa Maheer bai ma lura da Ummee ba, da sauri ya ture kujeran da yake zaune a kai ya bi bayanta zuwa kicin ɗin.

Tana shiga ciki ta dangwarar da kofin hannunta a saman cabinet, ta dafa cabinet ɗin ta ƙurawa kofin idanu zuciyarta na tuƙuƙi. Sai ga hawaye shar! Ita a rayuwarta ta tsani a wulakanta ta a cikin mutane.

A dai-dai lokacin shi kuma ya shiga cikin kicin ɗin, tana jin motsi a bayanta tayi saurin share hawayen amma bata san ya riga ya gani ba.

Ƙugunta ya riƙe ta baya ya juyo da ita yana tambayarta
"Kukan na miye?"

"Ba komai!"
Ta amsa a cushe tare da fisge jikinta, tana kyarma ta matsa kusa da gwangwanin madara da bounvita ta fara ambulawa a kofi ba tare da lura da zubarwar da take

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login