Showing 96001 words to 98260 words out of 98260 words

Chapter 33 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

223

Middle Ads

ma ya kashe wayar gaba ɗaya don kar ta kira shi. Zuciyarshi cike da tunanin zai daure bazai sake tada mata da zancen yaushe ne za a yi bikin ba.

Kafin ya koma falon ƙoƙarin daidaita fuskarsa yayi dan kar su gane damuwarsa, kamar ba wani abu da ya faru haka suka ci gaba da hira cike da raha da farin ciki. Har zuwa lokacin bacci. Suka raka Surayya har ɓangarenta tare da yi mata sai da safe. Shi kuma da Rabi mai girki suka nufi bangarensa.

Kyakkyawar tsarin da suka ɗauka a tsakaninsu ke nan tun kafin shigowar Bilhaƙƙi gidan. Sun yarda duk irin tsarin da suka shimfida na zaman gaskiya da amana a tsakaninsu idan ta zo kan wannan turbar za ta bi. Yanzu zaman lafiya suke yi sosai ba kuma zama na yaudara ba. Suna yawan nuna ƙaunarta da suke yi a gabanshi duk don su ƙarawa kansu kima da martaba a idanunsa, yo miye a ciki? wayayyun mata ne ke taya mijinsu son abinda yake so.

Burinsu ya cika kuwa, domin sosai yake jin daɗi tare da alfahari da hakan a fili da sansanin zuciyarsa. Girmansu ya ƙaru a idanunsa, ƙaunar da yake musu ta sake ninkuwa a zuciyarsa.


******* *******


A can ɓangaren zugudi tayi da waya a hannunta tana mamakin kashewar da yayi, ba zato ba tsammani sai hawaye ya ɓalle mata. A daidai lokacin Mamanta da ta dawo ɗaukar karatun addini daga gurin malamar da aka ɗaukar mata tana zuwa har gida ta koyar da ita tayi sallama a cikin ɗakin, tarar da ita tana kuka ya ɗaga mata hankali.

Da sauri ta cire hijabin jikinta ta nufe ta da sauri tana tambayar
"Beby Bilhaƙƙ lafiya? Me yake damunki?"

Da yake buɗaɗɗiyar yarinya ce da bata iya ɓoye ɓoye ba wayar kawai ta miƙa mata
"Mamana wai ya gaji da jira na. Nima gaskiya na gaji. Allah idan baku shirya bikin nan nan kusa ba ni zan tafi kaduna in kyale ku. Haba dan Allah! tuntuni an ɗaura aure amma har yau ba a yi biki ba? Ni dai wannan tsare-tsaren na mulki sun ishe ni haka nan. Kawai ko ba a samu babban gidan ba a kaini nashi gidan haka nan zan zauna a ƙuntacen."
Tana zuwa nan a maganar kuka ya ci ƙarfinta, daman ita ma bala'in kewar mijinta take yi kawai tana daurewa ne don kar a ce bata da kunya.

Mustapha da har ya sa kai zai shiga ɗakin nata da yaji irin maganganun da takewa uwar kawai sai ya tsaya a bakin ƙofar. Murmushi yayi da ya fahimci ta kai ƙarshen maganganun sai ya juya kawai ya nufi can cikin gidan ɓangaren Takawa.

Ko da yaje suka gama maganganunsu suna dariyar shirmen Bilhaƙƙin ɓangaren Mahaifiyarsa ya nufa. Ita ma ta ci dariya ya gama yiwa twins wasa ya koma ɓangarensa.

Wanka ya tarar Rebeccah tana yi, dole ya zauna a gefen gadon zaman jiran fitowarta.

Ko da ta fito wankan tattausan murmushi suka fara aikawa junansu sannan tayi mishi sannu da zuwa, da hannu ya yaficeta ta tafi gurinshi. Bai damu da ruwan jikinta ba ya zaunar da ita kan cinyarsa yana sansanar ƙamshin jikinta.
"Ina Beby?"

"Hmmm! Baby rigima? Ɗazu ta gama kukan mijinta na fushi da ita, ko mu kaita ko ta tafi da kanta."

Dariya yayi mai isarsa sannan ya ce
"Ke kinga laifinta? Mu iyayenta muna nan muna zuba soyayya da ƙara'in sabon amarci amma ita mun kyale ta ko oho."

Ɗan dukan ƙirjinsa tayi cike da soyayya ta shagwaɓe murya tare da cewa
"Kai Musty...?"

"Ai gaskiya ne Umm Bilhaƙƙ! ɗazun ai ina jin sadda take miki kuka da ƙorafin. Shi yasa ban shiga ba na koma muka ƙare magana da Takawa. Yanzu dai in Allah ya yarda nan da kwanaki uku za a mika ta gidan mijinta. Daman Takawa ne ya ce a bari a siyawa mijinta babban gidan da zai ishe su a wadace tunda babu isasshen lokacin yin gini. To kuma an samu, gobe in Allah ya kaimu za a yiwa Hajiya Ladidi Turkiyya magana ta haɗa mata komai na kayayyakin ɓangarenta. (Wata hamshaƙiyar Hajiya ce mai kawo nagartattu kuma haɗaɗɗun kayan ɗaki masu shegen kyau da masifar tsada daga ƙasar turkiyya. Iya kuɗinka iya shagalinka)

Har ma fa yayi waya da Malam ya sanar da shi duk halin da ake ciki saboda su ma sauran matan su samu daman gyara ɓangarensu su tare kafin a kaita."

"Hakan yayi kyau Ɓarina. Amma gidan a wadace zai ishe su ko?"

"Za suyi maneji dai Zumata, 4 bedroom flats ne ɓangare huɗu. Sai BQ daga can baya. Ba laifi tsarin gidan yayi kyau sosai kuma akwai wadataccen fili, dan akwai tazara tsakanin ko wane ɓangare ta yadda ba wacce za ta takurawa wata. Takardun gidan da komai ma gobe za a kaiwa Malam shi kuma ya damƙawa mijin nata kyauta halak malak daga Takawa."

"Madallah. Allah ya basu zaman lafiya..."

Daga nan kuma wasan ya fara sauya salo dan haka na ja tsumman ƙafafuna na ƙara gaba.

Washe gari da wuri Hajiya Yagana ta dira a gidan ta ƙalƙale Bilhaƙƙi da masifaffen fitinannen gyaran jiki irin na tsadaddun amare masu tsananin gata. Na kwanaki uku kacal aka yi gyaran amma kamar an shekara ana yi saboda yadda ta canza gaba ɗaya.

A rana ta huɗu bayan sallan azahar aka ɗauki Amarya Bilhaƙƙi cikin jerin gwanon motoci kamar wata ƴar gwamna aka nufi kaduna gidan mijinta da ita.

Don tsananin gata rakiyar Amarya har da uwa da uba, bayi biyar mata Takawa ya haɗo ta da su dukda ta ce ita ɗaya ko biyu sun ishe ta. Sai da aka zo tafiya da ita kuma dakyar aka ɓanɓare ta daga jikin kakanninta. Ta sha kuka su kuma sun jiƙa ta da zafafan nasiha da jan kunnen haƙuri da duk irin rayuwar da aka tarar a gidan aure.

Gidan Malam suka fara sauka suka huta, aka ci abinci, Hajiya Yagana ta sake sallawa amarya wanka aka tsantsara mata makeup mai sauki aka zuba mata tsadaddiyar alkyabba sannan aka mika ta gidan mijinta.

Ɓangaren Amarya fa yayi masifar haɗuwa, da ganin irin shirin da aka yiwa ɗakunan za a san amarya jinin sarauta ce. Sai fatan Allah ya bada zaman lafiya. Ameen

KANWA TA KAR TSAMI ƘWARNAFI YA KWANTA😍😍🥰🥰🥰🙈🙈🙈

Saboda tsananin zumuɗi, ƙosawa da kishi Ango babu wani abokin da ya ɗauka don ya raka shi ɗakin Amarya.

Kayan siyan bakin da ya siyawa amarya ledoji uku ya siyi komai don tsananin son gwada adalci tsakanin matansa. Ko da ya isa gidan bai nufi ɓangarenta kai tsaye ba, ɓangaren Surayya ya nufa.

Ya fahimci yanayin damuwar da ke tattare da ita dukda tana ƙoƙarin ɓoyewa, don haka cikin hikima ya zauna ya dararrashe yana janta da hirar soyayya tare da ƙara yaba kyan tsarin kayan da aka zuba a ɓangarenta, sosai iyayenta suka yi ƙoƙari bayan dubu ɗari da hamsin hamsin ɗin da ya ba ko waccensu kyauta ita da Rabi.

Tun tana shan ƙamshi har saida ta saki suna hira da dariya, ita da kanta ta tunatar da shi dare ya fara yi ya kamata ya je gurin amaryarsa.

Ya ɓata fuska kaman wani yaro ƙarami
"Ni fa yau bani da abokai ku ne manyan ƙawayena. Muje dan Allah ku raka ni ke da Rabi. Ni tsoron zuwa ma nake yi."

Dariya taita ƙyalƙyalawa yana ta zuba maganganun raha har suka isa ɓangaren Rabi, ita kuwa idanunta jajur suka tarar da ita.

A nan ma ya ƙara dararrashewa har da kwanciya wai shi kanshi ciwo yake yi.
"Ni dai ku barni in kwana a nan gobe sai inje gurin amaryar"

"A'a hakuri zaka yi Oga. Wannan rashin adalcin ba da mu za a yi ba."

Haka nan yana turjewa kaman baya so har suka raka shi ɗakin Amaryarshi, basu wani zauna ba suka yi musu sai da safe suka fice ko waccensu idanunta ciccike da hawaye. Ganin haɗuwar falon kawai da ɗakin da take ciki sai da ya ƙara tayar musu da hankali.

Dukda dare ne amma da yake ko ina tar yake da hasken wutan lantarki sun fahimci kayan ɓangarenta ba ƙananun kaya bane, ga wani abin burgewa yadda babu tarkacen kaya komai an saka shi ne a tsare cike da ɗaukar hankali.

Yana raka su bayan ya rufe babban falon ya koma ɗakin da ta ke, kan gadon cak ya haye tare da shigar da fuskarshi cikin hulan alkyabbarta yana sunsunarta.

"Fatabarakallahu ahsanul khaliƙeen"
Ya faɗa da wani sassanyar murya tare da sauke mata hular alkyabbar gaba ɗaya daga fuskarta.

Kallon ƙuda suka yi na minti biyar kowa a cikinsu fuska cike da murmushi. A hankali ya kai hannu ya janyota jikinsa ya rungume tare da yin baya baya har ya kwanta a kan gadon ita kuma tana kwance a ƙirjinsa
"Tatlim wallahi tallahi ina matuƙar son ki."

"Nima ina son ka Gangar..."

Haɗe bakinsu da yayi yana tsotsan harshenta kaman ya samu sweet ya hana ta ƙarasawa. Sai da ya gamsu don kanshi sannan ya sake ta.

Shi ya zare mata alkyabbar daga jikinta sannan ya koma falon ya ɗauko ledojin da ya shigo da su.

Duk abinda ya siya ƙin ci tayi ta ce ta ƙoshi a gidan Malam, tatacciyar madara kawai yasha ya bata tasha kamar yadda fiyayyen halitta yayi umarni.

Ya umarce ta taje tayi alwala suyi sallah.

"Ni fa nayi isha'i a gidan Malam har da shafa'i da wuturi."

"Babe wannan ai Nafila ce zamu yi."

Nan da nan tayi alwalar shi kuwa sai da yayi wanka sannan ya ɗauro alwala. Bayan sunyi sallah yayi musu addu'oi sosai, ya tattambayeta abubuwa game da addini. Alhamdulillah ta amsa komai yadda ya kamata.

Nan suka canza kaya zuwa na bacci cike da ɗoki. Mutumiyarku Hajiya Bilhaƙƙi da farko biye masa tayi tana ƙoƙarin maida martanin duk wani tsotse tsotse da rungume rungume, saida kida ya fara canzawa sannan rawar ma ya fara canjawa.

Sai kuka da majina tare da rokon dan Annabi ya kyaleta, da wuya yayi wuya ne ta fara kiran Mamanta da Babanta, kai a ranar har Malam sai da ta kira.

Shi kuwa goga bai kyale ta ba sai da kanwar nan ta kashe tsami ƙwarnafi ya kwanta.

Da kanshi ya kaita banɗaki yayi ta canza ruwan zafi yana gasa mata jiki, a karshe ya biya mata da wankan tsarke ya douko Babensa a galabaice ya kwantar a kirjinsa suka yi bacci.

Washe gari babanta da yaje gidan makullin motoci biyu ya damƙawa Surayya da Rabi kyauta halak malak! Tare da rokon alfarmar a zanansu da Bilhakki suji tsoron Allah su dinga nusar da ita duk wani kuskure da ta aikata.


Ƙarshe


Alhamdulillah


Sai mun haɗu a JA GABA bayan sallah in Allah ya yarda. Na gode kwarai da jumirin bi na da hakuri da ni har muka kai karshen wannan littafin🥰🥰🥰🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Wallah wannan page ɗin babu editting, idan kunga kuskure afuwan Sweethearts🥰🥰🥰

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login