Showing 63001 words to 66000 words out of 98260 words
mai tsawata miki a gidanku. Na biyu kuma yanayin irin shigar da kike yi mai baiyana tsiraici da yadda sam bakya shakkar ki taɓa jikina. Dalili na uku kuwa bai wuce yadda ke kika fara furta min kina so na ba. Bazan ɓoye miki ba da gaske a baya ina ganin bazan taɓa iya son duk yarinyar da ta ce tana so na ba. Abinda zai baki mamaki wallahi a wancan lokacin duk sadda na miki wulaƙanci na kore ki kika fita kina kuka mugun zafi nake ji a zuciyata. Kuma ko da baki zo gidan Malam ba ni da kaina na san akwai lokacin da zuciyata za ta gaza jure zazzafar tunaninki dole sai na koma Kachia na nemo ki a duk inda kike. Ki daina tunanin bana sonki kinji Tatlim? Ban ma san yadda aka yi soyayyarki tayi min kamun kazar kuku haka ba. Da gaske soyayyarki a zuciyata mai zafi ce sosai, ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kan cewa ban taɓa faɗawa kwatankwacin soyayya irin ta ki ba."
Wayyooo daɗi, ina aljannah ta faɗa dan murna. Duk wani ƙunci da damuwa da take ciki waɗannan daɗaɗa kuma zaƙaƙan kalaman na sa sun yaye mata. Tsananin farin-ciki yasa ta rungume shi tsam, da ta ga duk hakan ma bai gamshe ta ba fuskarsa ta kamo da hannunta biyu tana aika mishi da zafafan sumbata a duk inda bakinta ya kai.
Nan da nan ta kiɗima shi da zazzafar salonta tun yana murmushi har saida ya tallafota sosai ya fara maida mata da martani. Nan kuma sai idanunta suka fara raina fata da ta ji yana ƙoƙarin zuge mata zip ɗin rigarta ta baya, ƙam ta riƙe hannunshi tayi narai-narai da ido alamun ya dakata haka.
"Tatlim pls ki barni kinji."
Ya faɗa da shaƙaƙƙen murya yana kallonta da idanunsa da suka canza launi zuwa ruwan ɗorawa-ɗorawa.
"Bir.... ta... nem... hotel ne fa."
Tayi maganar a rarrabe idanunta ciccike da hawaye, kamar za ta rushe da ihu.
"Na sani. Ba wani abu zanyi ba. Just...."
Sai kuma yayi shiru, ya fesar da wani zazzafan huci ta bakinshi, ya cije leɓensa na dama, ya runtse idanu. A sanyaye ya waske da cewa
"Kawai ina so ki gwada waɗancan kayayyakin da na siyo miki ne in gani ko sunyi daidai"
Ya ƙarasa maganar tare da nuna jakar da ya taho da ita da yatsarshi manuniya.
A zabure cike da tsoro ta miƙe zaune daga jikinsa, yanayin da ya shige lokaci ɗaya ya kiɗimata ya kaɗa mata hanji. Jakar ta ja ta nufi hanyar banɗaki
"Bari inje in gwada."
Da idanu ya raka ta har ta ɓacewa ganinsa, a sanyaye ya miƙe ya cire rigar jikinsa da ta fara yamutsewa ya koma kan gado ya kwanta, idanunsa na fuskantar saitin banɗakin.
A cikin bayin ta daɗe tana gwaggwama numfashin tsoro kafin tayi ƙoƙarin daidaita kanta, da ta kalli fuskarta a jikin madubin da yake manne a bangon gabas na bayin kuwa ba ta san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata. Jambaki da man bakin da ta rangaɗa a leɓenta sun rabe sun shanye tas a tsakaninsu gurin tsotse-tsotse. Runtse idanu tayi tana tuno yanayi mai daɗin da take shiga idan suna tare, lokaci ɗaya kuma sai kunya ta kamata, hannu biyu ta sa ta rufe fuska tana dariya. Da ƙyar ta iya watsar da tunanin komai ta fara ciro kayan ɗaya bayan ɗaya take sakawa a jikinta, idan ta shirya tsaɓ sai ta fita ta nuna mishi, ya ce yayi kyau sannan ta koma cikin bayin ta canza wani.
Dogayen riguna ne ƴan dubai masu tsananin kyau har kala bakwai. Rigunan sunyi mata kyau sosai, kuma daidai jikinta kamar ya san size ɗinta. Sai da ta gama gwada dogayen rigunan ta fahimci ashe ba su kaɗai bane, akwai ƙananun kayan bature har kala huɗu a ciki sai kuma Inner wears danginsu P/B🙈🤣
Mutumiyarku an daɗe ba'a haɗu da ƙananun kaya ba. Jujjuya kayan taitayi a hannunta tana murmushi da hasashen irin haɗuwar da za ta yi a cikin kayannan. Wata ficiciyar riga mai masifar kyau kalar pink da duk tsawonta bai wuce iya gwuiwa ba ita ce ta fi ɗaukar hankalinta. Hannun rigar ɗaya siriri ne kaman na vest ɗayan kuma ɗan daidai.
"Wawwww!"
Ta faɗa a fili tana sakin murmushi haɗe da juyawa gaba da baya tana kallon kanta a madubi bayan ta saka rigar a jikinta.
Sai da ta canza tafiya ta fara wani sassanyar salo ta buɗe ƙofar bayin ta nufi gurinshi tana yauƙi haɗe da rangaji kamar reshen bishiya a lokacin iskar damina.
"Sevgilim look at me..."
Ta faɗa cike da yanga tare da juyawa gaba da baya a gabanshi tana fari da idanu.
Ya kasa cewa komai, runtse ido yayi kawai, a zuciyarsa yake tasbihi ga ubangijin da ya ƙawata halittarta kuma ya mallaka mishi ita a matsayin matarshi. Kasa haƙuri yayi sai da ya janyo ta jikinshi yana ta sassake ajiyar zuciya a jejjere kamar wanda yayi tseren gudu.
Ita ma a wannan karon ka sa hanashi yin abinda yayi niyya ta yi, idanunta a runtse har ya zare mata rigar a jikinta. Ya kalli ababen da suke ta tsole mishi idanu har ya ɓalle abinda ya tare idanunshi daga ganinsu gaba ɗaya. Runtse ido yayi ya rungume ta tsam, tsawon wasu daƙiƙu sannan ya ɗago ta yana sake ƙare mata kallo sama da ƙasa. Har lokacin idanunta a rufe suke
"Tatlim... miye wannan?"
A shaƙe ya tambaye ta tare da kai hannu ya shafi zanen mai kama da kalangu da suka fito raɗam a saman na shanunta.
Kunya yasa ta sake ƙanƙame shi.
"Nima ban sani ba fa. Haka nan na girma na ga zanen shi ma yana ƙara fitowa raɗam a jikinsu."
A kunyace ta raɗa mishi haka a kunne.
Bai yi yunƙurin keta iyaka ba dan bai manta a inda suke ba, ƙara rirriƙe ta yayi a jikinsa kamar yana tsoron za a ƙwace mishi ita, ya gyara musu kwanciya sosai a kan gadon. Cikin ƙanƙanin lokaci wani daddaɗan bacci mai cike da zaƙaƙan mafarkai ya kwashe su duk su biyun.
BILHAƘƘI
Karfe shida da minti hamsin dai-dai Bilhaƙƙi ta farka. A lokacin har an idar da sallar magrib, motsin da tayi shi ya farkar da Maheer daga daddaɗan barcin da yake yi.
"Babe ya aka yi?"
Yayi maganar a hankali, har lokacin idanunsa suna lumshe.
"Kalli lokaci ka ga, kamar ma an idar da sallah fa."
A hankali ya buɗe ƙwayoyin idanunsa da har lokacin suke cike da barci ya zube su a kanta, suka yi kallon-kallo da murmushi a fuskokinsu. Sai kuma ya kauda fuskarsa ya maida kan agogon bango.
"Subhanallahi."
Ya faɗa cikin sauri. Za ta miƙe ya riƙe ta a jikinsa. Ya tashi daga kwancen suka miƙe zaune gaba-ɗaya.
"Muje inyi miki wanka, sai muyi alwala muyi sallah."
Dariya tayi kawai, ta sake sunne kanta a ƙirjinsa cike da kunya.
"Je ka fara yi, idan ka fito nima sai inyi."
Murmushi yayi, ya shafi gashin kanta, ya ɗago fuskarta ya sumbace ta a goshi. Ya ɗauko rigarta da ke ajiye a gefensa ya sa mata. Ya sauke ta a gefe sannan ya sauka ya nufi banɗakin. Sharp-sharp ya watsa ruwa, ya ɗauro alwala ya fito sai ta shiga. Ita ma nan da nan ta gama ta shirya cikin kayanta da ta fito da su daga gida ya ja musu jam'in sallar magrib.
Ta so su tafi bayan sun idar da sallah ganin dare yana ƙara nisa ya ce shi yunwa yake ji, dole ta jira yayi musu odar abinci. Hankalinta gaba ɗaya yayi gida shi yasa tsattsakurar abincin kawai ta yi, shi ma ba wani sosai ya ci ba suka harhaɗa kayansu suka fito.
"Me kike so in siya miki?"
Suna hanyar komawa gida yake tambayarta haka.
"Bayan duk waɗannan siyayyar?"
"Eh mana. Za muyi tafiya gobe da Malam, bana so bayan na tafi kafin in dawo ki nemi wani abu."
"Ni dai bani da buƙatar komai. Ina za ku je?"
Tayi tambayar idanunta yana kanshi.
"Bauchi."
Ya amsa a taƙaice.
A ƙofar Ostrich backery ya faka motar ya ce ta jira shi minti biyu. Bai daɗe da shiga ba ya fito hannunshi riƙe da ledoji masu tambarin backery ɗin. Ya shiga ciki ya aje ledojin a kujerun baya na motar, ya ja suka ci gaba da tafiya.
"Amaryar sarkin Bauchi Abdulfah na biyu ƙanwar Hajiya mahaifiyar Malam ce. Ita ce zamu je gaisarwa, gobe zamu yi sammakon tafiya saboda mu isa da wuri kar dare yayi mana a hanya, ni da Malam da Mummy."
"Allah ya kaiku lafiya."
"Ameen ya Allah."
Ya amsa fuskarsa na baiyana jin daɗin addu'ar da tayi musu.
Haka kawai ta ji a ranta tana mararin zuwa bauchin, hannunta ta kai ta dafa hannunshi guda ɗaya kalle ta.
"Bir tanem ko za ku je da ni...?"
"No ki haƙura kawai Tatlim. Tafiyar akwai nisa bana so ki wahala, muma kwana biyu kawai za muyi. Kuma Malam ya ce idan mun dawo weekend na sama za ayi biki ki tare a ɗakinki."
Ya kalle ta da murmushi ya ci gaba da cewa
"Kinga ko a irin wannan lokacin da nake gab da gurzar angwanci duk wani abu da zai jigatar min da ke bazan yadda ya kusanto ki ba."
Dariya suka yi duk su biyun. Haka suka ci gaba da hira cikin nishaɗi da ƙoƙarin fayyacewa juna duk yadda suke ji a zukatansu har suka isa gidan Malam. Bai wani jima ba bayan ya sauke ta ya shiga mata da duk siyayyar da yayi mata cikin gidan. Sama-sama suka yi magana da Malan ya bar gidan da cewa sai ya zo gobe da safe.
****** ******
Kallonta yake yi yana ta doka murmushi har ta ƙarasa kusa da shi ta zube a gabansa, kanta a ƙasa ta fara gaishe shi yana amsa mata a tausashe. A ko wane lokaci idan ya kalleta yana jin wani ƙauna ta musamman a zuciyarsa game da ita, har yau ya rasa gane dalilin da yasa haka. Yadda yake jinta kamar wata ƴarsa da ta fito daga tsatsonsa, balle yanzu da sanadin da zaisa ta ci gaba da dauwama a ƙarƙashin iyalansa ya auku ba ƙaramin murna yake ji ba.
"Bilhaƙƙi an maimaita haddar jiya ko?"
"Eh na maimaita Malam, na iya ma. In biya maka ka ji?"
Ta ƙarasa maganar tana kallonshi da murmushi.
"A'a ki biyawa Umminku. Yau ita za ta ƙara miki karatun. Yanzu wanka zan shiga, akwai tafiyar da za muyi da maigidanki da safennan."
"Bauchi ko? na manta ya faɗa min jiya. Allah ya kaiku lafiya ya dawo mana da ku lafiya."
"Ameen ya Allah. Allah ya miki albarka."
"Ameen."
Harta kai bakin ƙofar falon za ta fita sai kuma ta koma ciki ta zauna a inda ta tashi.
"Malam ko za kuje da ni? Na ji ya ce har da Mummy za ku tafi."
"Kina son zuwa ne Bilhaƙƙi?"
"Eh ina so. Har ma nayi mishi maganar ya ce in haƙura garin akwai nisa."
"Eh da nisa kam."
Shiru yayi kamar shi ma zai ce ta haƙura da son zuwan, sai kuma ya ce.
"Ki shirya tunda kina son zuwa, zan nemar miki izini a wajensa."
Murna kamar me a zuciyarta har ya gaza ɓoyuwa a fuskarta.
"Tam! na gode Malam. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana."
"Ameen."
Ya amsa addu'ar shi ma yana dariya. Da idanu ya raka ta har ta fice daga falon. Girgiza kai kawai yayi ya yunkura da Bismillah ya tashi ya nufi banɗaki don yin wanka.
A can cikin gidan ita ma cike da ɗoki ta faɗawa Ummee da ita za a je, Malam ya ce ta shirya su tafi tare. Wanka ta faɗa cikin ƙanƙanin lokaci ta fito ta fara shiryawa, tana shirin tana harhaɗa kayan sawarta da duk wani abu da ta san za ta buƙata a cikin kwanaki biyun da za su yi. Ganin har da ita za aje Saudat da Asma'u suka ce suma za su Malam ya ce a'a. Sai dariya da gwalo take musu tana tsokanarsu.
Ko da Maheer ya isa gidan ya ganta cikin shiri bai ce mata komai ba, don Malam ya kira shi a waya kafin ya isa yayi mishi maganar. Bai wani so tafiyar da ita ba amma tunda Malam yasa baki ba shi da ta cewa, ko da ta gaishe shi bai nuna mata komai ba ya amsa. A tsaitsaye suka karya sannan suka miƙi hanya bayan sun ja addu'oin da fiyayyen halitta SAW yayi umarnin yi ga duk wani matafiyi. Ita da Mummy suna zaune a kujerun baya na motar, Maheer shi ne direba. Shi kuma Malam yana zaune a kujeran mai zaman banza. Suna barin kaduna an fara miƙar hanya sosai Malam ya kunna radion suna sauraren labarun duniya, jefi-jefi kuma suna hira kan abinda suka ji an taɓo a labarun duniyar.
A wani ƙauye suka tsaya yin sallar azahar da la'asar, suka ci abincin da Mummy ta yi musu guzuri sannan suka sake ɗaukar miƙaƙƙiyar hanyar tafiya, sun fara tafiya ba daɗewa wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
Bai fi saura minti talatin su isa cikin garin Bauchi ba ta fara wani irin mummunan mafarki mai cike da ababen tsoro.
"Karki kuskura ki ce za ki shigo cikin garinnan... babu dai-dai da ke a masarauta... Mai wutsiya ki koma inda kika fito ko kuma in hallaka ki..."
Yanƙwanannen tsohon mai ɗauke da jajayen idanu da zaƙo-zaƙon haƙora ne yake mata wannan kashedin yana nuna ta da wani dogon sanda. Ya bugi ƙasa da sandar nan take wasu ƙananun halittu masu kama da kwaɗi suka fara fitowa ta ƙarƙashin ƙasa kusa da inda yake tsaye, ita ya nuna musu da sandar hannunshi yana wasu irin surutai nan take suka yi kanta da gudu kamar tarin ƙudaje saboda yawansu suna yi mata feshin wani abu mai kama da dafi.
Tsananin tsoro da firgici ya sa ta yanka wani ƙaƙƙarfar ihu ta fara cure jikinta a guri ɗaya tana dunƙulewa haɗe da tattakure ƙafafunta a cikin motar, duk yadda ta so ta buɗe idanunta ta kasa buɗewa. Kamar daga sama ta ji muryar Oga yana mata magana a cikin ƙwaƙwalwar kanta.
'Bibi... Karki shiga wancan garin... ki dawo gare mu... har yanzu muna jiran ki dawo gare mu... matsayinki a cikin ƙungiya yana nan yana jiranki... Ki dawo kafin Garkuwa ya saukar miki da mummunan bala'i a kanki...'
Suffar shi ne ya baiyana tsaye a gabanta cikin mummunan shigarsu ta ƙungiyar tsafi yana jifanta da mummunan murmushi. Hannunshi ɗauke da wani ƙaton ƙoƙo da bata san ko miye a ciki ba. ƙananun halittun suna ƙarasawa kusa da ita ya fara watsa musu wani baƙin abu da yake cikin ƙoƙon, duk wanda baƙin abun ya sauka a kan shi sai yayi bindiga ya tarwatse a gurin.
"Ku ƙyale ni... na barku har abada... Yanzu ni matar wani ce...ku ƙyale ni na ce..."
Ta faɗa cikin ƙaraji da murya mai matuƙar amo da sauti, lokacin ne kuma ta samu nasarar buɗe idanunta gaba ɗaya tana kallon Oga fuskarta na baiyana matsanancin fushi.
Wannan tsohon yana ganin Oga ya ɓace daga inda yake tsaye. Wani abin mamaki kuma sai
motar ta fara jijjiga tana layi da su a kan titin kamar za ta kifar da su. Gaba ɗayansu sun shiga cikin ɗimuwa da ruɗewa sai salati suke yi da sallallami tare da jan duk wata addu'a da tazo bakinsu. Duk yadda Maheer ya so ya dakatar da motar ya kasa sai da Malam ya fara janyo karatun alƙur'ani mai girma farkon suratul baƙara, duk su biyun sai suka ɗauki karatun da ƙarfi. A hankali motar ta fara rage gudu da hajijiyar da take yi har ya samu damar faka motar a can gefen titi.
Ihu ta sake ƙwallawa a karo na biyu ta ƙara wage manyan idanunta da suke fari ƙal babu ko ɗigon baƙi a ciki. Oga take gani zaune a gefenta yana ƙoƙarin zuba mata wani farin abu a jikinta. Cikin fushi ta kai mishi wani mugun shaƙa a wuya da hunnunta duk biyu tana magana da murya mai tsananin amo
"Na ce ku ƙyale ni inyi rayuwata ko...? Baza ku barni ba...? Me yasa dole sai da ni a ƙungiyar...?"
Wani kakkaifar walƙiya ne ya fito daga idanunta ya daki jikin Oga nan take shi ma ya ɓace.
Abinda bata sani ba Mummy ta shaƙe wa wuya domin ita Oga take gani, nan da nan Mummy ta fara jiyo ƙamshin barzahu, nan take ta fara kakari, duk yadda take ta ƙoƙarin ɓamɓare hannun Bilhaƙƙi daga wuyanta ta kasa, wani mugun ƙarfi ne ta ke da shi kamar ta shaƙe ta da rodi haka ta ji hannayenta.
Tsakanin Malam da Maheer har rige-rigen zuwa bayan motar suka yi don kai wa Mummy ɗauki kafin ta hallaka ta.
Malam ya fara jan Mummy ganin haka sai Maheer ya fara ƙoƙarin ɓamɓare hannayen Bilhaƙƙi a wuyanta.
A fusace ta ɗago kai za ta yi magana ƙwayoyin idanunsu yana haɗuwa sai tayi laƙwas, jikinta ya saki, ƙarfin nan da take ji duk ya tafi. Lauuu ta yi za ta zube da sauri ya tare ta ta zube a jikinsa.
Malam matarsa ya ja suka koma gaban motar yana ta jera mata sannu, gorar ruwan swan ya ɗauko ya buɗe ya kafa mata a baki. Kaɗan ta sha ta cire goran a bakinta, idanunta jajur, sai haki take yi tana sauke numfashi akai-akai. Inda Allah ya taimake su hanyar babu cunkoson motoci sosai, motoci biyu ne suka tsaya don basu taimakon gaggawa ganin kuma al'amarin yazo da sauƙi sun samu nasarar tsayar da motar ba tare da an samu hatsari ba sai suka yi musu fatan alkhairi da addu'ar kiyaye gaba suka wuce.
"Magajin Malam ka kula da matarka a nan. Ni bari in lallaɓa in tuƙa motar mu isa cikin gari. Kafin mu isa