Showing 42001 words to 45000 words out of 98260 words
ta glass ɗin motar dan ganin a wane hali take ciki? sai yaga har lokacin tana nan kwance cikin fita haiyaci kamar yadda ya ɗaukota.
"Assalamu alaikum."
Malam ya faɗa a tausashe sannan ya miƙa mishi hannu suka yi gaisuwa irinta addinin musulunci.
"Malam lafiya dai ko? yanzu mun idar da sallah aka sanar da ni kana jira na a waje."
Nan ya faɗa mishi duk yadda suka yi da su Agness sannan ya buɗe mishi bayan motar dan ya ga mara lafiyar. Gabanshi ne ya faɗi, nan da nan fuskar yarinyar cikin mafarkin da yake yawanyi a cikin kwanakin nan ya faɗo mishi a rai
'kamar ita?'
Ya tambayi kansa a zuciyarsa. Sai kuma ya rufe ƙofar motar da sauri ya kalli direban, ganin hankalin mutane ya fara dawowa kansu ya ce.
"Bari mai gadi ya buɗe get ka shiga da motar sai mata a cikin gida su sauketa. Babu wani ƙarin bayani da suka yi maka kawai cewa suka yi ka kawo ta nan gidan?"
Ya tambaye shi fuskarsa cike fal da mamaki.
"Eh Akaramakallahu."
Ya amsa yana sussunkuyar da kai.
"To madallah. Ba laifi. Allah ya bata lafiya. Juyo da motar bari inyi magana da mai gadi ya buɗe maka ƙofa."
Ya nufi cikin gidan da sauri shi kuma direban ya shiga motar dan juyo da ita ya shiga gidan kamar yadda Malam ya umarceshi.
****** *******
Danƙareren agogon bangon falon ya kalla, fuskarsa baiyane da matsanancin mamaki bayan ya ajiye wayar da ya amsa kiran Hajiya Shafa, ƙarfe goma saura kwata na dare.
'Wasu baƙi mata ne za su zo ganina a wannan lokacin baza su jira gari ya waye ba?'
Ya tambayi kansa da kansa a zuciyarsa, amma da yayi tunanin ƙila ƙaƙƙarfar uzuri ne da baza a iya jiran wayewar gari ba sai ya zura takalmansa ya nufi cikin gidan ɓangaren Hajiya Shafa inda baƙin suke.
Sallama yayi a ƙofar ɗakin ya jira aka amsa daga ciki kafin ya cusa kanshi cikin falon idanunshi cikin na maiɗakinsa.
"Malam barka da shigowa"
Hajiyar ta faɗa a ladabce, saida ya amsa sannan ta nuna mishi baƙi matan da suke son ganinshi.
Ya kalle su a karo na farko yana karantar yanayinsu a cikin hasken ƙwayayen lantarkin da suka haske ɗakin kamar rana, sun sako dogayen riguna baƙaƙe har ƙasa, sun naɗe kawunansu da gyalen rigunan kamar wasu zuri'ar larabawa.
A karo na farko suka gaishe shi idanunsu a ƙasa, kujerar kusa da Hajiya Shafa ya zauna sannan ya amsa gaisuwarsu a mutunce.
"Madallah. Bayin Allah daga ina kuke? Ban shaida fuskokin ba."
Kafin su ce komai ɗaya daga cikinsu ta fara shessheƙar kuka tana jan hanci, sannan ta fara magana da rawar murya
"Malam ni sunana Maryam, ita kuma wannan ƴar'uwata ce sunanta Aisha. Ɗazu mun fita siyayya kasuwa da muka dawo sai bamu tarar da ƙanwarmu da bata da lafiya a gida ba. Ko da muka tambayi masu aikin da suke tare da ita sai suka ce wai an kawo ta nan gidan. Shi ne muka zo mu tafi da ita."
Shiru yayi yana karantar yanayinta, baisan me yasa ba haka kawai yake ji a ransa bai yarda da su ba. Tun ɗazu da aka kawo mare lafiyar yasa su Hajiya Shafa suka yi mata wanka da ruwan magani, suka saka mata kaya na mutunci, ko da ya ƙare mata kallo da kyau ya fahimci tabbas ita ce yarinyar da yake mafarki tana neman taimakonsu. Rayuwa take a tsakankanin matsafa ko daga ina take bai san wane dalili ne yasa Ubangiji ya turo ta gurinsa ba, dan haka zaiyi iya bincike sosai har sai ya gamsu da gaskiyarsu kafin ya basu ita, ko zai basu ita ma sai ta samu lafiya sosai ya ji daga bakinta tabbas waɗannan ɗin yayyinta ne kamar yadda suka faɗa sannan zai damƙa musu ita.
"Amma abin da mamaki, kika ce ita ɗin ƙanwarku ce?"
Ya tambayi wacce ta kira kanta Maryam yana tsattsare ta da idanunsa masu cike da kwarjini.
Majinar kuka ta sake ja ta ɗago jajayen idanunta karaf suka haɗa ido, saukar da nata idanun tayi ƙasa jikinta babu inda baya rawa
"E ! Eh wallahi da gaske nake yi. Aisha kiyi mishi bayani mana."
Ta ƙarasa maganar tare da zungurin cinyar abokiyar tafiyarta.
Cike da taraddadi da maganarta mai baiyana alamar ita yare ce dukda hausan ya zauna a bakinta ita ma tace
"Malam ka taimaka ka bamu ita, idan muka koma gida ba da ita ba wallahi iyayenmu zasu yi fushi da mu..."
"Ma sha Allahu! Tunda iyayenku suna raye gobe in Allah ya kaimu ku dawo tare da su. Akwai wasu ƴan tambayoyi da zanyi musu idan na gamsu da amsoshin salin-alin zan baku ita ku tafi."
Yayi maganar da dakakkiyar muryarsa tare da miƙewa tsaye alamun ya gama saurarensu.
Tsam suka yi da ransu, cikin su biyun an rasa wacce zata sake cewa komai. Kawunansu a ƙasa alamu ƙarara ba hakan suka so ji daga bakinsa ba. Maryam ta sake fashewa da ƙaƙƙarfar kuka ta zube daga kan kujeran gwuiwoyinta a ƙasa.
"Dan Allah Malam kayi haƙuri karka jefa mu cikin bala'i, wallahi idan muka koma gida ba tare da Bibi ba zamu shiga cikin mummunan masifa..."
"Wa'iyazubillahi! sai kace ba musulmai ba? wane irin masifa kuma ana zaune ƙalau? anya ma maganganun da kuka faɗa min gaskiya ne? Ban ga alamun gaskiya a tattare da ku ba. Shafa'atu kira min Lukman yazo da yaransa su bincika min waɗannan mutanen ban yarda da su ba."
Da sauri suka miƙe tsaye jin ƙarshen maganarsa, sum-sum suka nufi hanyar ficewa daga falon ba tare da sun sake cewa komai ba.
"Ku tsaya mana idan ku yayyinta ne da gaske..?"
"Za muje mu taho da iyayenmu ne."
Maryam ta faɗa cikin zafin rai tana zura takalminta da yake ajiye a ƙofar ɗakin, ita kuwa Aisha har ta kusa ficewa daga gidan zuciyarta cike da tsoron tsohon Malamin mai masifaffen wayau da saurin fahimta.
Tana fita ta ƙaramin ƙofar gidan Maheer yana sanyo kanshi zai shiga gidan, kaucewa yayi har saida ta wuce sannan ya shiga yana waigenta. A zuciyarsa yake tunanin su kuma waɗannan me ya kawo su gurin Malam a daren nan? Dan ya ga Aisha jingine da motar da suka zo da ita tana jiran fitowar Maryam daga cikin gidan.
Ko da ya shiga cikin gidan kai tsaye ɗakin Mahaifiyarsa ya nufa nan ya tarar da su suna kakabin maganar.
"Gara da kayi musu haka Malam, kana ganin waɗannan matan ka ga tsofaffin kwanti-kwan. Fuskarsu ta sha bilicin da ganinsu ba mutanen arziki bane. Idan ka gama binciken in da gaske ƙanwar tasu ce a basu ita daga baya amma ba a wannan halin da take ciki ba."
"Ni duk ba ma wannan ba Shafa'atu. Ɗazu direban nan yace min ƴanmatan da suka ce ya kawo ta nan gidan sun faɗa mishi ita tace su kawota nan ɗin kuma ita ta bada kwatancen nan gidan. Dole ina buƙatar yi mata wasu ƴan tambayoyi bayan ta warke kinga batun in basu ita ma bai taso ba."
Ya maida hankalinsa kan Maheer yana amsa gaisuwarsa sannan ya ce
"Yauwa Magaji, zo ka gani."
Ya ja shi har zuwa ɗakin baccin Ummee inda aka kwantar da Bibi akan gadonta, dukda akwai hasken ƙwanlantarki a ɗakin sai da ya sake haska mishi fuskarta dan ya ganta sosai.
"Ko kasan wannan yarinyar?"
Gabanshi ne yayi mugun faɗuwa, cikin ƙanƙanin lokacin walwalarsa ta ɓace ransa yayi mummunar ɓaci. Tsaf ya gane ta, yo ai dole ne ma ya gane ta, duk da tsananin tsanar da yayi mata da kuma ko a mugun mafarki baison ya ga fuskarta ba'a ɗauki dogon lokacin da zai ganta ya ce ya kasa shaida ta ba.
'Yanzu wannan mayyar yarinyar har nan gidan iyayenshi ta biyo shi kenan?'
Kamar zai ce wa Malam bai santa ba amma da yake ƙarya ba halinshi bane sai kawai ya ɗaga kai, alamun eh ya santa.
Cike da ɗoki Malam ya dafa kafaɗarsa fuskarsa fal da murmushi ya sake maimaita tambayar
"Da gaske ka santa Magaji?"
"E na santa Malam, amma ba a garinnan na santa ba."
Ya amsa muryarsa a cuccushe.
Hannunsa kawai Malam yaja suka fice daga ɗakin zuwa ɓangarensa, Hajiya Shafa ma da tayi niyyar biyo su dan jin inda aka haihu a ragaya dakatar da ita Malam yayi yace ta koma ta kunna wa mare lafiyar karatun Alƙur'ani mai girma ta jira dawowarsu.
Suna shiga ya maida ƙofar falon ya rufe, ya zaunar da Maheer akan kujera shi ma ya zauna a gefensa kamar wasu abokai.
"Magaji faɗa min inda kasan yarinyar nan ka ji? kar ka kuskura ka ɓoye min komai nima akwai abinda zan faɗa maka game da ita."
Nan da nan Maheer ya warwarewa mahaifinsa inda ya santa da duk abubuwan da suka faru tsakaninshi da ita, yana maganar shi kuwa Malam murmushi kawai yake yi yana jinjina girman hikima da iko irin na Ubangijin sammai da ƙassai mai kowa mai komai.
'Yana nan yana ta addu'ar Allah ya bata kariya a duk inda take ashe ta taɓa haɗuwa da ɗansa wanda a mafarki take kira garkuwarta harta faɗa cikin matsanancin soyayarsa.
Ko da ya fahimci Maheer ya gama ba shi labarin sai shima ya fara warware mishi bayanin duk irin yadda yake ganinta a cikin mafarki da yadda take neman taimakonsu. Ya ƙarƙare maganarsa da cewa
"Da wannan dalilin yasa ko da na dawo Semina naga halin da Surayya take ciki ba wani ci gaba a asibiti shi yasa nace a sallame ta, kuma kaga cikin hukuncin Allah yanzu an samu ci gaba sosai tana mommotsa jikinta kaɗan-kaɗan, babbar matsalar kawai a yanzu maganar da bata iya yi sai dai tayi ta bin mutane da kallo."
Kanshi ne ya buga, ransa ya ƙara ɓaci, zuciyarsa ta sake cika da matsananciyar tsanarta, babu abinda ya fahimta a maganganun Malam sai ciwon da Surayya take yi da sa hannun Bibi a ciki. Shi kam ko da matan duniya sun ƙare me zaiyi da wannan ƴar iskar yarinyar? yarinya ƙarama amma tun bata tafasa ba tana neman ƙonewa...
"Magaji tunanin me kake yi haka ina ta magana ka yi shiru?"
Malam ya katse mishi tunani ta hanyar girgiza kafaɗarshi da sauri.
"E... na'am?"
Ya faɗa a ruɗe, ganin irin kallon da Malam yake mishi sai yayi ƙoƙarin daidaita kanshi cikin nutsuwa ya sake cewa
"Ni abinda ban fahimta ba zaman me zata yi a gidannan Malam? yarinyar nan tun a garinsu na fahimci ba ƴar arziki bace ko daga irin kayan da take sawa masu baiyana tsiraicinta. Ni ina ga idan sun zo gobe kawai ka basu ita su tafi da ita can su ƙarata, idan akwai abinda zamu taimaka mata da shi bai wuce addu'a ba. Amma ni dai ban goyi bayan zamanta a gidannan nan ba..."
"Gidanka ko gida na?"
Malam ya katse shi cikin fushi fuskarsa a tamke, ashe tunda Maheer ya fara magana yanayin fuskarsa ya canza amma bai lura ba sai da ya dire.
"Ka yi hakuri Malam, Allah ya huci zuciyarka. Duk yadda ka ce haka za a yi."
Ya faɗa a ladabce hankalinsa a tashe.
"Babu komai Magaji, je kaga iyalinka ka wuce gida, sai gobe idan Allah ya kaimu."
Yana gama faɗin haka ya shige ɗakin barcinsa ya barshi nan a tsugune.
Gwuiyawunshi a saɓe ya miƙe ya fice daga falon, gurin Mahaifiyarsa ya koma sai ya tarar da ita tana sallar shafa'i da wuturi, daga can cikin ɗakinta kuma inda Bibi ke kwance karatun Alƙur'ani mai girma ne yake tashi a hankali cikin zazzaƙar muryar Alaramma Abdullahi Abba, cikin suratul Baƙara aya ta ɗari da biyu.
Ɗakin Mummy ya shiga ya tarar da ita da casbaha a hannunta, da alamun ita ma sallar ta idar.
"Magajin Malam ne a daren nan?"
"Ni ne Mummy, barka da dare"
Sama-sama suka gaisa saboda dare yayi, yayi mata sai da safe ya fice daga ɗakin.
Ko da ya leƙa ɗakin da Surayya take sai ya tarar duk sunyi bacci ita da Inna Lantana, dan haka ya fice daga ɗakin yaja musu ƙofar ya kulle.
Gurin Ummee ya koma yayi mata sai da safe ya fice daga gidan ya hau motarsa a waje ya nufi gidansa.
A wannan daren ko Rabi sai da ta fahimci yana cikin damuwa, yadda ya koma gidan ba haka yanayinsa yake sadda ya bar gidan ba, sam ya kasa walwala.
Tayi tunanin ko jikin Surayya ne sai yace mata ba haka bane, juyin duniya kuma yaƙi faɗa mata abinda yake damunshi dole ta ƙyale shi ta zuba mishi ido.
Ya daɗe baiyi bacci ba sai juye-juye yake yi yana saƙawa yana kwancewa, shi kaɗai yaita jan tsaki zuciyarsa a ƙuntace, har gaf da asubah sannan wani nannauyan ɓarawo bacci yayi nasarar sace shi cike da muggan mafarkai mabanbanta duk a kanshi da Bibi.
****** ******
"Mery..."
Aka ƙwalla kiran sunanta cikin murya mai tsananin ƙarfi da hauhawa wanda yasa duk wani lungu da saƙo na cikin babban ɗakin tsafin amsa kuwwar sunanta. Cikin tsawa da baiyana tsananin fushi aka cigaba da magana da muryoyi mabanbanta daga ko wani bango na ɗakin
"Garkuwa yana daf da yayi mummunar fushi da ke Merry... ki kawo Bibi a cikin ƙanƙanin lokaci matuƙar kina so Garkuwa ya share miki hawaye... Merry... Merry... Merry..."
Aka ci gaba da ƙwalla kiran sunanta cikin sauti mai baiyana ƙwaƙƙwaran kashaidi da jan kunne, hakan yasa ta ƙara ruɗewa, tana gurfane gwuiwa bibbiyu a gaban Oga, yafe take da wani jan ƙyalle a jikinta saɓanin sauran ƴan ƙungiya da suke sanye da shuɗayen riguna da jan ƙyalle a kawunansu, wannan jan ƙyallen da ta yafa babban alama ne da yake nuna ita mai laifi ce a ƙungiyar. Ba abinda take yi sai kuka.
"Karki bari fushin Garkuwa ya sauka a kanki dan rayuwarki za ta ɗaiɗaice... rabuwar Bibi da ƙungiya tamkar tarwatsewar rayuwarki da na duk wani makusancinki ne Merry..."
Ɗif sautin muryoyin ya ɓace kamar anyi ruwa an ɗauke, can kuma sai aka ƙyalƙyale da wani matsiyacin dariya da murya mai kama da na gyare, tsawon lokaci kafin dariyar ma ta ɗauke ɗif!
Hannu Oga ya miƙa mata ta kama da sauri, jikinta babu inda baya rawar ɗari.
"Sadaukar da jinin wacce kike tsananin so a zuciyarki dan lallashin Garkuwa ya ƙara miki lokaci."
"Rose"
Ta kira sunan tana kuka, ƙannenta biyu duk ta sadaukar da su a ƙungiyar, a yanzu babu wacce take ji tana so a zuciyarta da ta wuce Rose ɗin, ita ma ga shi yau ta bada jininta.
Runtse ido yayi ya daki bangon yamma na ɗakin sai ga hoton Bibi ya baiyana a kwance tana bacci cikin kwanciyar hankali, a gefenta Ummee ce take sallar nafila. Ga karatun Alƙur'ani da yake tashi a hankali cikin ɗakin.
"Kinyi sake Merry, kin bari Bibi tayi masauki a muhallin da duk tsafin matsafi sai dai ya zuba mata ido. Matuƙar tana tare da waɗannan iyalan babu wani abu da muka isa mu aika mata daga nan. Aiki ne ja a gabanki, cikin sati biyu ki san duk yadda za kiyi ki rabata da waɗannan mutanen ki dawo da ita cikinmu, suna da matuƙar haɗari a gare mu, ko ma me za kiyi dole ke kiyi in ba haka ba duk abinda Garkuwa ya saukar miki ki kuka da kanki."
Ya zagi bangon nan take hoton ya ɓace komai ya koma yadda yake kamar wani abu bai taɓa baiyana a gurin ba.
Dungulmin hannunsa ya nuna a jikin bangon kudu yana ƙwalla kiran sunan Rose haɗe da wasu surutai na tsafi da shi kaɗai yasan ma'anar abinda yake faɗe, nan take hoton Rose ya baiyana a jikin bangon kamar a majigi, tana kwance a kan gadon asibiti tana bacci cike da kwanciyar hankali. Alamun sauƙi sosai ya baiyana a jikinta, dan har ta ɗan ƙara kumari saboda hutu da kyakkyawar kulawar da take samu a asibitin.
Kunnenta ya daka nan take jini ya fara ɓulɓulowa daga cikin kunnen kamar an buɗe famfo, da sauri ya tara babban ƙwarya jinin yana zuba a ciki har saida ya cika taf sannan jinin ya daina zuba hoton Rose ya ɓace, ya ɗauko ƙwaryar da hannu biyu ya ɗaga sama ya runtse ido yayi wasu maganganu sai ya sake ƙwaryar, kamar zai faɗo sai kuma ƙwaryar yayi sama a hankali har ya isa saman rufin ɗakin ya tsaya cak.
Nan take masu matsaloli a ƙungiya suka fara zuwa gaban Oga ɗaya bayan ɗaya suna yi mishi sujada sannan su faɗi matsalolinsu shi kuma ya miƙa musu koke a gurin Garkuwa, da haka har suka gama taron duk suka ɓace kowa a cikinsu ya baiyana a makwancinshi.
BILHAƘƘI
"Ki yi haƙuri mana Marry, kiyi shiru haka nan. Is ok! Ni ina ganin kuka da damuwa ba shi ne solution ba. Ki kwanta ki huta gobe sai muyi maganar yadda zamu ɓullowa Malamin nan tunda kina da isasshen time da za ki dawo da ita."
Tayi maganar cikin rarrashi, ta juya mata baya tana ƙara jan bargo, hannu ta miƙa ta ja wani ɗan igiya a gefen gadon nan take ƙwan lantarki mai haske ya ɗauke mai duhu ya baiyana. Rufe idanu tayi alamun ko wane lokaci tana maraba da ɓarawo bacci yayi awon gaba da ita.
Taja wani dogon nishin kuka mai tafe da kakkauran majina, tissue ta ɗauka a gefen gadon ta fyace majinan, sai kuma ta ci gaba da sauke ajiyar zuciya akai-akai, ita kam ta shiga uku sau uku.
Babu abinda yake ƙara ɗaga mata hankali a duk cikin abinda yake faruwa da ita sai idan ta tuno jimlar
'Fushin Garkuwa yana daf da sauka a kanki Merry...'
Da ta zo nan a tunaninta sai wasu sabbin hawayen su sake ɓalle mata shar-shar kamar an buɗe famfo.
Tsawon shekarun da tayi a ƙungiyar mutane biyu kawai ta