Showing 27001 words to 30000 words out of 98260 words

Chapter 10 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

228

Middle Ads

ba ya ciwo har zuwa lokacin da DPO Peter ya iso ya bada umarnin a sallame mu bayan ya kafa min waɗannan sharuɗɗan. Dan Allah Bibi ki kyale ni, ko zan iya shiga inyi wankan?"
Ta katse ta da maganganun cikin zafin ran da take ta yunƙurin dannewa.

"Madallah, ba laifi, Hakan yana da kyau. Ki je kawai."
Sai kuma ta ja wani dogon tsaki ta dangwarar da kofin hannunta ta fice daga falon zuwa harabar gidan.

Itama bata jira komai ba ta shige ɗakinta, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da tayi arba da makeken gadonta, a zuciyarta take saƙe-saƙen me ma ya kamata ta fara yi a farko? Gargasa jiki da ruwan zafi, wanka, bacci ko cin abinci? Daga ƙarshe dai ta faɗa banɗaki bayan ta tsayar da shawarar yin barci a ƙarshe.


****** *******


"Me kake cewa ne Yusuf? Sam ban fahimce ka ba. Ta ya za a ce an rasa kaya a gurin mutanen nan? yanzu kana nufin har Alhaji Barazana baisa baki sun baka kayan ba?"
Ya ƙarasa maganar cikin damuwa yana ƙoƙarin zama a kan kujerar.

"Ƙwarai kuwa Yallaɓai, wallahi duk yadda kake tunanin al'amarin ya wuce nan. Wani irin zazzafar doka shugabannin suka kafa ma sauran ƙananun ƴan kasuwan na duk wanda aka kama ya fitar da kaya ko rabin buhu ne ba tare da farashin ya tashi sosai zuwa yadda suke buƙata ba tara ne mai tsanani a kan mutum. Kuma ka san bara duk manoman sun faɗi warwas irin muguwar faɗin da basu taɓa tsammani ba, shi yasa yanzu suka ja tsayin daka baza su saki kayan ba sai farashi ya haura aƙalla zuwa ashirin da biyar..."

"Kai ! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Wannan wani irin mugun ƙari ne har na dubu sha uku a lokaci ɗaya? mu nawa muke saida kayan?"
Ya katse mai maganar ta can ɗaya ɓangaren cikin matsananciyar damuwa, bai jira ya ci gaba ba ya ce
"To yanzu dai ya kake ganin za a yi? menene mafita da hanyar ɓullewa? kasan dai dole muna buƙatar kayannan ko da babu yawa tunda har muka yi saken da ya ja baya sosai a gurinmu. Amma kun shiga har maraban walijo duk babu kaya?"

"Duk bakinsu ɗaya fa Yallaɓai, ƴan kasuwan gaba ɗaya suna bin umarnin dokar nan. Tunanin da muke yi ko zaka shigo da kanka ne kuyi magana da Alhaji Barazana tunda shi ne shugaban ƴan kasuwan? ina ga idan aka yi haka ko bamu samu kayan da yawa ba za mu samu kaɗan, kuma ko sunyi mana ƙarin kuɗi zasu sassauta farashin saboda ganin idanunka da kuma daɗewar da aka yi ana cinikayya a tsakani."

"Ok! To ina ga hakan za a yi. Gobe juma'a ko? asabar da sassafe in Allah ya yarda zan taso da wuri."
Da haka suka yi sallama ko wa ya katse wayar, tallabe kansa yayi da yake tsananin sara masa kamar zai faɗo, sai a lokacin ya lura da zamanta can gefe ɗaya, tana ta cika da batsewa da huci ita kaɗai kamar zata yi bindiga.

"Sannu da zuwa."
Tayi maganar a kumbure.

Lumshe kyawawan idanunsa yayi yana hamdala a zuciyarsa.
'Ɗan Adam ba ya rabuwa da matsala daga wannan sai wancan'
Tunanin da yake yi kenan a ransa.

Bai amsa sannun ba sai kawai ya miƙa mata hannu alamar tazo gare shi. Jan fasali da hura hanci ta ci gaba da yi kamar baza ta amsa kiran ba, sai kuma ta miƙe tana yauƙi ta isa gurinshi ta tsaya ɗan nesa kaɗan da shi.
"Ga ni"

Ko kafin ta rufe baki yasa hannu ya janyo ta gaba ɗaya ta faɗo jikinsa, za ta fara zille-zille ya riƙe ta sosai ya gyara mata zama a kan cinyoyinsa, yadda take kumbura baki ita a dole har lokacin fushi take yi shi ne abinda ya ba shi dariya ya kasa dannewa har saida ya murmusa. Hakan ya ƙara ƙular da ita ta ci gaba da yunƙurin tashi daga jikinsa amma ko gezau bata yi ba dan riƙon da yayi mata ba na wasa bane, sake tunawa da abinda ya faru a jiyan yasa kawai ta fara hawaye.

"Kuka kuma? Amma ba nayi maganin wannan damuwar ba?"
Yayi maganar a tausashe yana ƙoƙarin ɗago fuskarta dan su haɗa ido.

"Honey jiyan fa..."

Ba zato ba tsammani kawai ta ji bakinsa cikin nata yana aika mata da wani sassanyar salon kiss mai mugun daɗi da kwantar da hankali, hakan shi ya kashe bakinta da jikinsa gaba ɗaya, ya hana ta ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa, tun tana turjewa har ta bada kai bori ya hau ta fara mayar masa da martani.

"Bana son kina damuwa a kan abinda bai kai ya kawo ba kinji Honey? ko kina so ciwo ya kama min ke?"
Yayi tambayar yana riƙe fuskarta da hannunsa biyu, yana ta sakar mata tattausan murmushi mai kashe zuciya.

Girgiza kanta kawai tayi alamar a'a.

"To ki bar damuwa, komai ya wuce. Ba na son nacin magana, Allah yana tare da masu haƙuri."

"Tam! ya wuce."
Ta amsa da sanyin murya tana ƙara lafewa a kan ƙirjinsa. Ɗan kwalin kanta ne ya zame yiri-yirin kitsonta suka bayyana.

Shafa kitson ya fara yi yana bata labarin tafiyar gaggawa da ta kama shi zuwa Kacia jibi da safe.

"Ni dai Honey sam bana son kana yawan zuwa kudancin kadunan nan, su baza su iya shawo kan matsalar bane har sai ka je?"

Yayi ƴar dariya kawai, shi kanshi ba son tafiyar yake yi ba, amma ta kama mishi kamar dole ne yaje, kaya sunyi ƙasa sosai a shagunansu, sakankancewar da suka yi a ko wane lokaci za a iya samun kayan yasa ya saida Buhu ɗari wa Alhaji Baballe, ga shi tun ba a je ko ina ba sun fara nema.
"Ba daɗewa zanyi ba, idan na samu yadda nake so kwana ɗaya ma kacal zanyi..."

Siririyar sallamar da Surayya tayi da cusa kanta cikin falon yasa ya tsaida maganar da yake yi, shi kaɗai ya amsa sallamar ita kuwa Rabi ƙara narkewa tayi a jikinsa tana sake ƙwaƙume shi.

Ita kuma ganin yanayin yadda suke yasa ta juya da sauri da nufin komawa inda ta fito, ranta banda tafarfasa babu abinda yake yi saboda tsananin kishi, nan take ta fara saƙe-saƙen da ta san a halin da za ta tarar da su kenan da bata shigo ba.

"Madam bismillah mana, ina za ki je kuma?"
Ya tambayeta bayan ya fahimci abinda take ƙoƙarin yi.

Murmushi ta ƙawata fuskarta da shi sannan ta juyo ta kalle su, ta kalli fuskarsa ta kalli hannunsa da yake shafa gashin kan Rabi, shi baima san me take kallo ba ya ci gaba da abinda yake yi, bisa ga dukkan alamu sosai yake jin daɗin haka, ita kuwa Rabi tayi luf kamar ƴar kyanwa, har wani lumshe ido take yi dan tsananin jin daɗi, zuciyarta cike fal da farin ciki. Har wani tunani take yi a ranta
'Anya akwai abinda yafi miji ya nuna yana tattalin mace a gaban kishiyarta daɗi?' Rai fes sunan wani zani, a ɓoye sai doka murmushi take yi.

"Ƴallaɓai dama gani nayi ka dawo baka fito ka duba ni ba kamar yadda ka sabawa duk wacce ba ta da girki, shi yasa na shigo in duba Allah yasa dai lafiya."
Ta ƙarasa maganar a hankali, a sace kuwa gallawa Rabi wata muguwar harara tayi kamar idanunta zasu faɗo, tayi ƙwafa a hankali yadda ba wanda zai jiyo ta.

"Lafiya ƙalau ne fa, na shigo ina waya da Yusuf, bayan na gama kuma ƙanwarki ta tsare ni da shagwaɓarta. Afuwan Sweetheart, bari inyi wanka ga ni nan fitowa. Kin yini lafiya ko? ya jikinki?"

"Lfy kalau, da sauƙi, a fito lafiya Yallaɓai. Bari in jira fitowarku a falo..."

"Baby muje in taya ka wankan"
Ta faɗa a shagwaɓe tare da miƙewa tsaye, ta ja hannunsa suka shige cikin ɗaki ɗan ɓingilin sket ɗin jikinta ta ɗagawa, santala-santalan cinyoyin Rabin duk a waje.

Shi kuwa kamar raƙumi da akala yake bin ta a baya, yana tafe yake amsawa Suraiya ba tare da ya waiga ya sake kallonta ba.
"To Madam, sai na fito"

Da sauri ta fice taja ƙofar da ƙarfi ta buga gam dan haushi, a jikin ƙofar ta tsaya dan jiran ko ɗaya daga cikinsu zai biyo jin ba'asin buga ƙofar da tayi sai ta ji shiru, cikin falon ta koma tana ta masifa ita kaɗai kamar taɓaɓɓiya.
"Shegiya, da kwasassun ƙafafu kamar na agwaga, za ki gani in dai ni ce, ramuwar gayya zan miki da ta fi ta gayya zafi. Jarababbiya daga yin faɗa jiya har sun shirya yau dan tsananin fitina."
Taja tsaki, ta sauke wani zazzafar huci ta baki kamar kububuwa, ta riƙe ƙugunta da hannu bibiyu tana safa da marwa a tsakiyar babban falon, daga ƙarshe ta zube kan kujera a kan kujera a kasalance kamar wacce aka naɗawa mugun duka, kishi sai nuƙurƙusarta yake yi, ba abinda take haskowa a ƙoƙon zuciyarta sai hoton miji kuma abin sonta Maheer tare da kishiya kuma maƙiyiyarta Rabi suna tsotse-tsotse da shafe-shafe a cikin bahon wanka.

Lokacin ne taga yayi mata wani mugun tsawo saboda munanan saƙe-saƙen da zuciyarta yake mata. Shiru-shiru basu fito ba ta wuce ɓangarenta zuciya na ƙuna, idanunta ciccike da hawaye ta maida kofar falonta ta datse, har tana danna key saboda ko sun fito kar ma ya neme ta.

Hannayensu sarƙe da juna kafaɗunsu na gogayya suka fito daga cikin ɗakin suna ƙyalƙyala dariya, sanye suke da ƙananun kaya na shan iska duk su biyun saboda yanayin zafi da garin yake ciki. suna zama akan dining table ɗin ya ce
"Je ki yi wa Auntynki magana ta fito muci abinci."
Ɗif ta ɗauke wuta, duk wani fara'ar fuskarta ya ɓace. Ɗan jim tayi kamar baza ta je ba sai kuma ta miƙe dan cika umarnin da yayi mata bayan ta tuna da halinsa na rashin son wargi, yanzunnan idan tayi wasa sai ya saɓa mata ya canza yanayin walwalar da suke ciki.
"Honey?"
Ya kira ta lokacin da har ta kusa ƙarasawa ƙofar ɗakin Surayyan, waigowa kawai tayi tana kallonsa.

"Dawo ki zauna, bari inje da kaina. Na tuna ɗazu ko da na dawo ban shiga na duba halin da take ciki ba."
Tsawon minti uku yana ƙwanƙwasa ƙofar amma ta ƙi buɗewa, kuma tana jinshi tayi biris da shi, da ya gaji sai ya koma ya zauna.
"Ina ga tana banɗaki, mu jira ta minti biyu."

Hira suka ci gaba da yi sama-sama suna zaman jiran fitowarta, ita kuwa tayi bulum-bukwui a cikin ɗaki kaman baza ta fito ba.
"Honey ko inje in sake ƙwanƙwasa mata ƙofar?"
Rabi ta tambaye shi tana kallon agogo ganin lokacin ya ja sosai har an kusa kiran sallah.

Cikin sauri ya dakatar da ita.
"No ƙyale ta kawai, idan na dawo sallah sai mu ci abincin na san zuwa lokacin ta gama abinda take yi."

Sai da ta gama ɓata musu lokaci har aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i a masallatan kusa da su sannan ta fito tana ɗingishi, fuskarta cakuɗe da yanayin ban tausayi, idanunta har da guntun ƙwallah ta ƙarasa kusa da su, ta fara magana a raunane.
"Sweetat..."
Sai kuma tayi shiru hawaye suka ɓalle mata shar-shar kaman an buɗe famfo.

Gabanta ne ya faɗi, bata san me kuma za ta zo da shi ba, ita dai Allah ya sani har tsoron makircin Surayyan take yi. Tagumi tayi kawai tana kallo da saurarenta dan jin da wacce kuma ta zo yau.

Ya kalle ta sama da ƙasa sheƙeƙe, yana ta ƙoƙarin danne ɓacin ranshi dan kar Rabi ta fahimta. Da ya rasa ta cewa sai kawai ya jefa mata tambayar
"Lafiya?"

"Santsi ne ya kwashe ni nayi muguwar zamewa a bayi, ka ga har na gurɗe ƙafata..."

"Allah ya kyauta, sai ki nemi man zafi ki shafa. Idan kinso ki fito muci abinci bayan na dawo masallaci."
Ya faɗa cikin rashin kulawa da ba maganarta muhimmanci, haka kawai yake ji zuciyarsa bai gamsu da gaske ta faɗi ba. Dan ma kar kukanta ya karya mishi zuciya sai ya shige banɗakin falon ya ɗauro alwala.
"Honey na wuce masallaci."
Ya faɗa idanunsa a kan Rabi, da ɗan murmushi a fuskarsa.

"Tam ! A dawo lafiya Honey"
Ta amsa ranta ƙal bayan tayi fari da idanunta, har bakin babban ƙofar falon ta raka shi sannan ta juya ciki dan sauke nata faralin, tana tafe tana karkaɗa ƙugu da satar kallon Surayya da tayi poster a inda take tsaye baki da hanci hangame, fuska duk hawayen makirci kamar mai shirin ɗaukar hoto.


****** ******


Maheer Abdulganiyyu Mai Anini ingarma kuma kyakkyawan matashi mai ji da samartaka ɗan kimanin shekaru talatin da uku.


BILHAƘƘI


Haifaffen unguwar rimi ne a cikin garin kaduna. Mahaifinsa Malam Abdulganiyyu da uwargidansa Hajiya Balaraba haifaffun jihar zamfara ne a ƙauyen Maru. Tun duniya na kwance aiki ya dawo da shi garin kaduna a lokacin bai daɗe da yin auren fari ba, dukda iyayensa basu so ba a dole dai suka haƙura ya tattara ya dawo garin kaduna.

Tsawon zama a kaduna da gogayya da zallar hausawa yasa ko cikin maganarsu shi da matarsa sai jefi-jefi ake gane su zamfarawa ne.

Ta ko wani fanni na ilmin boko da islamic gangaran ne, mutum ne da ko wani lokaci hannunsa a buɗe yake. Kuma babban malami ne a nan unguwar rimi da kewayenta. Ga shi da balaga ta iya wa'azi da iya nasiha wa al'umma, cikin hikima yake isar da saƙon Allah da fiyayyen halitta SAW, da waɗannan dalilan yasa al'umma suke matuƙar ƙaunarsa da ganin girmansa.

Shekaransu uku a kaduna Allah ya albarkace su da samun haihuwar Maheer, nan da nan kuma sai haihuwar ta buɗe musu dan shekara ɗaya da rabi tsakani Balaraba ta haifi ƙanwarsa Shafa'atu, Lukman ya biyo bayanta shekara ɗaya da wata takwas tsakani, daga nan kuma sai haihuwar ta tsaya cik!

Ba sa jimawa sosai basu je mahaifarsu sun gaida iyayensu da sauran dangi ba, duk wani abu da zai faru na jaje ko na murna suna tafe shi da iyalansa. Amma sam baya daɗewa saboda aikinsa.

Shekarun Lukman uku a duniya Malam Abdulganiyyu ya ƙara auren wata bazaura mai suna Salamatu, a zahirin gaskiya sadakarta mahaifinta ya ba shi amma ko da wasa bai taɓa furtawa Balaraba sadaka aka bashi ba, ba dan komai yayi hakan ba kuwa sai dan ya kare wa amaryar martabarta a idanun abokiyar zamanta da ƴaƴansa. Da yake tsayayyen namiji ne a tsakanin iyalansa kuma adalin miji da tsananin sa'ar da aka yi duk suna da hankali sai suka haɗe kansu sosai kamar ya da ƙanwa.

Nan kuma haihuwa ta ƙara buɗe ƙofa a gidan suka fara yi a jejjere, Salamatu ta haifi huɗu, Mustapha, Saudat, Fahad, Faruk.

Ita kuma Balaraba ta ƙara yara uku suka zama shida, Badiyya, Asma'u da ɗan auta Yunus.

Tsananin haɗin kan da yake tsakanin iyalan gidan idan ba saninsu sosai aka yi ba babu yadda za a yi a gane ƴaƴan wannan ɗakin da ƴaƴan wancan ɗakin, yaran suna kiran Hajiya Balaraba da Ummee, ita kuma Hajiya Salamatu suna kiranta da Mummy.

Maheer ya taso nutsassten yaro ne mai tsananin ƙwazo da son karatun boko da islamiyya. Mutane da dama a waje suna kiranshi da magajin Malam ne dan duk cikin ƴaƴan gidan shi ne ya ɗebo Malam sak kamar yayi kaki ya tofar.

Kuma a fannin malanta ma shi ne dai ake ganin bisa ga dukkan alamu zai iya biyo Malam ɗin, dan yana shekaru goma sha biyu ya sauke Alƙur'ani mai girma, sauka ta gaske ba karatun zuƙu ba kuma ko a lokacin yana da haddar izufi goma sha biyar a kwanyarsa.

Wani dabara da hikima da Malam ɗin yake yiwa duk yaransa shi ne sai sunyi nisa sosai a karatun addini sannan yake saka su a makarantar boko.
(Wannan wata hikima da baiwa ce irinta Alƙur'ani mai girma. Insha Allah matuƙar yaro ya fara buɗe ƙwaƙwalwa da sanin alƙur'ani sosai kuma ya samu ƙwarewa a karatun Alƙur'anin duk wani karatu da zai biyo bayanta bi'iznillahi za ta zo da mugun sauƙi wa ƙwaƙwalwar yaro ko yarinyar. Wannan kaifiyyan ce an gwada an gani kuma an dace. Allah yasa mu dace)

Yana da shekaru goma sha takwas cif ya amsa sunansa na Mahiru (Gangaran) a fagen karatun Alƙur'ani mai girma, ya haddace ta tsaf kuma yasan tafsirin duk ayoyinta, kuma karatunshi bai tsaya a nan ba sai da ya haɗa da haddar wasu ƙananun littattafan addini. A lokacin ne kuma alƙiblar karatun nasa ya nutsa cikin karatun boko gadan-gadan, a fagen karatun addinin ma ba tsayawa yayi ba, ci gaba yayi da neman ilimi lungu da sako na zaurukan malamai daban-daban, dukda haka dai babban malaminsa Mahaifinsa ne Malam Abdulganiyyu.

A kance taura biyu ba sa taunuwa lokaci ɗaya amma ga Maheer ya haɗe biyun ya taune su tsaf ba tare da ya jigata ko ya galabaitar da haƙoransa ba.

Haka suka ta so har girma shi da ƴan uwansa, kyawawa kuma nutsastsun yara masu cike da tarbiyya ababen koyi ga sauran yara, da rayuwa mai cike da nasara.

Shafa'atu tana kammala secondry Malam ya aurar da ita ga ɗaya daga cikin ɗalibansa Nuhu, daman tun tana ƴar ƙanƙanuwa Nuhu yake son aurenta har ma yayi wa Malam ɗin magana. Aka yi sa'a kuma ita ma Shafan ko da ta girma bata watsa mishi ƙasa a ido ba, tana son shi. Har ta ƙare karatun aka yi auren cikin mutunta juna.

Cike da nasara Maheer ya haɗa digirinsa na farko ya samu aiki a matatar ruwa da yake cikin garin kaduna.

A lokacin kuma sai ƴan mata suka fara kawo mishi cafka ta ko wane ɓangare, a gefe guda kuma manyan aminan Malam guda biyu sun nuna sha'awar son haɗa shi aure da ƴaƴansu mata. Da yake baida wani zaɓi kuma ba shi da wacce yake so sai kawai ya barwa Malam ɗin

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login