Showing 78001 words to 81000 words out of 98260 words
a wannan yanayin har yaji yanayin saukar numfashinta ya canza, alamun ta samu barci. Bai yi ƙwaƙƙwaran motsi ba sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sosai, ya zame jikinsa a hankali ya kwantar da ita a kan gadon, ya zare hijabin jikinta ya gyara mata kwanciyar sannan ya ɗauki wayar ya matsa can gefe ya fara dudduba saƙonnin cikin wayar.
Dukda yana namiji al'amarin ya jijjiga shi, tsawon lokaci yana ta saƙe-saƙe da tunanin hanyar da zai bi ya taimake ta amma ya rasa na yi. Sai jan Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un yake yi.
Vidion ya sake kunnawa ya kure fuskar matar sosai da kallo, tabbas tana tsananin kama da Bilhaƙƙi. Babu tantama wannan matar ko ba mahaifiyarta ba ce to tabbas sun haɗa dangantaka ta jini a tsakaninsu. Kamannin yayi yawa.
Aje wayar yayi ya yakice tunanin komai a ransa ya shige banɗaki ya ɗauro alwala, nafilfili yayi ya haɗa da addu'o'i sosai a kan Allah ya kawo musu mafita da gaggawa.
Cikin hukunci na Ubangiji kuwa bai tashi a kan sallayar ba sai da yaji zuciyarsa ta tsayar mishi da ƙwaƙƙwaran shawara na hanyar da ya kamata su bi. Hamdala yayi ta yi yana godiya ga Allah har ya tashi ya ɗauko wayarsa.
Ƙaninsa Luƙman mai bi masa a haihuwa ya kira ya warware masa duk abinda yake faruwa. Maganganu mai tsawo suka yi sannan suka yi sallama kowa ya katse wayar.
Fita yayi ya ja ƙofar ya kulle ta waje, ya nufi ɗakin da Malam ya kwana jiya wanda yake kusa da nasa ɗakin dan ya ga ko Malam ɗin ya dawo daga turakar Takawa inda suke ganawa. Sai ya iske ya dawo sallah ma yake yi.
Ganin haka sai ya nemi guri ya zauna yana jiran ya idar da sallar.
"Magajin Malam? lafiya a darennan? Na yi tsammanin tuntuni ka yi barci?"
Tambayoyin da Malam ɗin ya fara jera mishi kenan bayan ya idar da sallar.
"Lafiya ƙalau Malam. Barka da dare."
"Yauwa barkanmu dai Magaji. Me yake faruwa?"
Ya sake tambayarshi cikin zaƙuwa, dan ya ga alamun maganganu ne a bakin Maheer ɗin.
"Malam daman kira ne mai muhimmanci aka yi min daga gurin aikinmu. Sun buƙaci lallai idan zai yiwu in koma kaduna gobe. Shi yasa daman na zo inji yaushe ne ka shirya za mu koma gida?"
"Eh to nima da a niyyata mu koma gida gobe ko don saboda aikin naka. Amma a darennan Mai martaba ya zo min da buƙatar da bazan iya musa mishi ba. Ya ce akwai muhimmin al'amari dangane da Yarima Mustapha da zai kaisu can wani ƙauye a jihar kaduna. Ya buƙaci ko zan koma gida in bari muyi wannan tafiyar mu dawo, in yaso ma ni sai in tsaya a kaduna idan sun gama su sai su dawo nan ɗin."
Shiru suka yi duk suna saƙe-saƙe, sai Malam ɗin ya ci gaba da cewa
"Ina ga abinda za a yi gobe idan Allah ya kaimu kai ka koma gurin aikinka. Ni sai na iso kawai. Daman tun kafin bayyanar Mustapha Innah ta buƙaci in bar Salamatu da Bilhaƙƙi a nan har sai bayan an gama shagalin suna sai su bi tawagar masu zuwa daga maru su sauka a kaduna. Idan duk hakanma bai yiwu ba za ta sa a mayar da su har gida."
Da 'To' kawai ya amsawa Malam wacce bahaushe yake kira da ba ta karya wuya. Amma ya san tafiyarshi ya bar Bilhaƙƙi a nan ko da lafiya ƙalau ne ba abinda ke faruwa ba abu ne da zai iya jurewa ba.
Balle kuma ga gaggarumin tashin hankalin da ya ɓullo musu. Ya san ko ya hana Bilhaƙƙi tafiya ga mahaifiyarta tabbas za ta tafi, shi yasa da ta bi motar haya ba tare da saninsa ba gara shi ya kaita da kanshi.
Ya zaɓi ya ɓoyewa Malam gaskiyar halin da ake ciki ne saboda ya san yana iya shiga cikin matsanancin tashin hankali da damuwa. Sallama yayi mishi da fatan tashi lafiya bayan ya sanar da shi gobe ana idar da sallar asubah zai ɗauki hanya. Ya fice daga ɗakin ya koma ɗakinsa gurinta. Ya tarar da ita har lokacin tana barci, shirin bacci yayi ya hau gadon ya janyota jikinsa ya rungume, yayi musu addu'ar barci gaba ɗaya ya shafe musu jiki ya ja musu bargo.
A wannan ranar nan gurinsa ta kwana, kiran sallar farko ya tashe ta tayi wanka. Tana fitowa shi ma ya shiga ko kafin ya fito har ta maida kayan jikinta, har lokacin fuskarta danƙare take da damuwa. Shi ma bai yi ƙoƙarin damunta ba saboda ya san lamarin babu sauƙi, addu'a ya umarci tayi sosai idan ta idar da sallah sannan ya fice zuwa masallaci.
Ana idar da sallah kafin jama'a su fara fitowa ya fice daga masallacin, sauri-sauri ya kira ta ta shige motar ya ja a sukwane suka fice daga gidan. Suna hawa titi ya ƙure ƙarar karatun alƙur'ani mai girma ƙira'ar Sudais. Sosai yake ba motar wuta duk da nisan tafiyar so yake su isa kaduna a cikin taƙaitaccen lokaci.
****** *******
Duk zamanta a gidan baifi a ƙirga ba da ta taɓa haɗuwa da shi, tunda shi ba mazaunin jihar kaduna bane.
Tsananin ƙwazo da himmar aiki haɗe da tsage gaskiya yasa a cikin ƙananun shekarunsa aka ba shi muƙamin D.P.O na ƴan sanda. Shi yasa yau a cilla shi wannan jihar gobe a cilla shi wancan jihar don share tsagerun da suka addabi garuruwa.
Bai fi sati biyu ba baya da aka yi mishi transfer zuwa jiharshi ta kaduna, yana tsaka da aiki Maheer ya kira shi yana faɗa mishi wannan sarƙaƙƙen al'amarin na Bilhaƙƙi. Shi ya bada shawarar duk yadda ya kamata suyi kuma Maheer ya gamsu ɗari bisa ɗari.
A karo na barkatai ya sake kallonta da manyan idanunsa, shi mamaki ma yake yi ƴar ƙanƙanuwar yarinya kamar ita da babban al'amari. Da gaske in banda Yayanshi ne ya tare shi da case ɗin kai tsaye zai ƙaryata duk wanda ya faɗa mishi labarinta.
"Amma ƙanwata kina ga mu barki ki tafi gurinsu ke ɗaya shi ne abinda ya fi? Ko dai in haɗa ki da jami'an da zasu taimaka miki a tarwatsa ƙungiyar..."
"A'a! A'a Ya Luƙman. Dan Allah kar kayi haka."
Ta katse shi da sauri jikinta na rawa, sai kuma hawaye shar... ta ci gaba da magana cikin kuka
"Wallahi ba imani ne da su ba idan aka bi bayana na tabbata za su iya kashe min mahaifiyata. Idan kuwa hakan ta faru bazan taɓa yafewa kaina ba."
Ɗage kafaɗa yayi alamun shi kenan tunda hakan ta zaɓa, ya sake tura kwalin lemun exotic da kofi a gabanta. Kisha kafin Yayan ya dawo sai ku wuce..."
Buɗe ƙofar da aka yi tare da shigowar Maheer yasa shi yayi shiru, kallon juna suka yi, Maheer yayi wa Lukman wani alama da ido da na rasa gane ko me yake nufi.
Gyaɗa kai yayi tare da ce masa
"Ka dawo?"
"Eh na dawo."
Ya ajiye wani leda a gabanta ya ɗago haɓarta da hannunsa yana kallonta cikin ido. Kujera ya janyo ya zauna a kusa da ita har gwuiwoyinsu na gogar na juna
"Babe kukan ne har yanzu?"
Kafin ta yi magana Luƙman ya ce
"Ina ga idan ta sha lemun za ku iya wucewa. Ta ce bata buƙatar mu bi ta, za ta iya zuwa ita kaɗai."
Yana gama maganar ya fice daga Ofis ɗin sannan ya ja musu ƙofar. Hannayenta ya rirriƙe duk biyun fuskarsa baibaye da damuwa
"Kin tabbata barinki ki tafi ke kaɗai shi zai sa su sake ta lafiya ba tare da sun cutar da ita ba?"
Ɗaga mishi kai kawai ta yi alamun eh!
"Babe kiyi min alƙawarin kema za ki dawo gare ni, wallahi ina tsananin sonki. Bazan iya rayuwa idan baki a kusa da ni ba."
"Gaskiya banyi maka alƙawari ba Sevglim. Amma zanyi ƙoƙarin dawowa idan na samu dama in Allah ya yarda."
Ta amsa tana ƙoƙarin ƙara ƙarfafa ma kanta gwuiwa.
Janyo ta jikinsa yayi ya riƙe ta tsam a ƙirjinsa, sai sassauke ajiyar zuciya suke yi a tare, tsawon lokaci sannan ya kai hannu ya buɗe kwalin lemun ya tsiyaya a kofi. Ya ɗauko kofin ya nufo bakinta da shi, kauda kai ta yi, murya ƙasa-ƙasa ta ce
"Bana jin zan iya shan wani abu yanzu."
Shiru yayi bai amsa ta ba, ko da ta kalli fuskarsa sai ta ga yanayinsa ya canza, kamar bai ji daɗin ƙin shan da tayi ba. Kawai sai ta karɓi kofin ta kafa a baki ta fara sha, saboda sanyinshi yasa ta shanye gaba ɗaya ta aje kofin a kan tebur.
Ajiyar zuciyar da ya sauke yasa ta kalle shi, sai ya sakar mata murmushi kaɗan.
Miƙewa tayi daga jikinshi
"Ya kamata in tafi, lokaci yana ƙara tafiya."
"Tam! Ɗan jira ni minti biyu bari inga Luƙman a waje."
Ko kafin ta amsa har ya fice daga ofis ɗin.
Minti biyu, huɗu bai dawo ba, nauyin da ta ji kanta yayi mata yasa ta ɗan kifa kai a kan tebur ɗin kafin ya dawo. Nan fa wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita.
Minti takwas yayi da fita sannan ya koma cikin Ofis ɗin, ganin ta yi barci yasa shi sakin murmushi ya koma ya sanar da Luƙman, sannan ya kira Dr. Bilyaminu da yake zaune a wani ɗan ƙaramin Ofis suka koma ofishin Luƙman duk su ukun.
******** ********
"Madam ! kamar yadda na sanar da ku a shirye nake in koma cikin ƙungiya dan in cece rayuwar Mahaifiyata. Lokacin yayi, ga ni yanzu na fito daga gidan Malam. A ina zamu haɗu...?"
"Ki rufe min baki Bibi!"
Ta daka mata tsawa daga can ɓangaren, cikin masifa ta ci gaba da cewa
"Me kika maida ni? Wacce ba ta da wayau ko me? karki manta duk iskancinki da wayon da kike ganin kina da shi a ƙarƙashi na kike. Ko kin manta kina ƴar ƙanƙanuwar yarinya na tsince ki? Ki ajiye wayar hannunki da duk wani abu da kike riƙe da shi a ƙofar gidan ki hawo titi ki ci gaba da tafiya kawai."
Wani dogon tsaki ta ja sannan ta katse wayar.
Daman wayar ce kawai a hannunta, jikinta a sanyaye ta aje wayar a ƙofar gidan ta ci gaba da tafiya cikin sauri tana waige-waige. Ko da ta isa kan titin tsayawa tayi tana tunani don bata san ina ya kamata ta bi ba. Gabas ko yamma, kudu ko arewa? kawai sai tayi shahadar ƙuda ta miƙe titin yamma samɓal tana ta tafiya.
Ta jigata ƙwarai, domin ta shafe minti arba'in tana tafe da sassarfa kafin wata baƙar mota ta ci burki mai ƙarfi a gefenta, ko kafin ta waiwaya ta gama gane kalar motan an buɗe ƙofar da sauri aka fincike ta zuwa cikin motar, aka ƙara figar motar a guje aka harba titi.
Basu barta ta gama nutsuwa daga firgitan janye ta da suka yi ba aka shaƙa mata wani hoda a hancinta. Daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba har suka isa wani babban gida a sabon tasha.
Wani ƙato a cikinsu ne ya saɓa ta a kafaɗa kamar ya ɗauki sillan kara ya shige gidan da ita, wani ɗaki ya kaita ya shimfiɗar a kan gado.
Minti biyu tsakani wasu ƴan mata biyu suka shiga ɗakin suka caje ta gaba ɗaya bayan sun cire kayan jikinta tas! ɗaya daga cikinsu ce ta kira Madam a waya ta yi mata bayani
"Madam! babu komai a jikinta. Sosai mun duba ta ko ina a jikinta bamu samu komai ba."
"Ok! ku saka mata kayan nan da na ba Moses ya kawo muku."
"Ok ma!"
Wani doguwar riga shuɗi suka saka mata a jikinta saɓanin riga da zane na atamfar da suka cire mata. Suka ɗaure gashin kanta da wani jan ƙyalle mai ɗan faɗi.
Garjejen ƙaton nan ne ya sake ɗaukarta ya kai mota, saɓanin motar da suka zo da ita a ciki yanzu wata ƙaramar mota suka ɗauke ta a ciki, a hankali suke tafiya har suka isa gidan Aunty Mercy da yake Kamazou, inda a can suke tare da Madam Mary.
Bata farfaɗo ta dawo cikin hayyacinta ba sai ƙarfe biyu da minti biyar na dare, tana farkawa ta ga su Madam a tsaye a kanta cikin shigarsu ta ƙungiya, ko kafin ta ce komai sun dafa kafaɗunta sun ɓace ɓat! basu baiyana a ko ina ba sai a gaban Oga da sauran ƴan ƙungiya.
"Barka da dawowa gare mu Bibi... Bibi barka da zuwa... kinzo ke nan ba komawa Bibi..."
Sautin maganganu mabanbanta da ɗakin taron ya fara amsa kuwwa kenan ana yi wa Bilhaƙƙi murna da barka da komawa cikinsu.
Tana zaune a hakimce kan kujera, idanunta jajur, gashin kanta a mimmiƙe, a kallo ɗaya za a yi mata a fahimci wannan ba Bilhaƙƙin Maheer ba ce, wata ce can daban wacce aka tsuma ta kuma aka rene ta da manyan kayayyakin tsafi tun tana jaririya.
Fuskantar juna suke yi ita da Oga kowa fuskarshi a ɗaure. Ita ta fara katse shirun tayi magana da wani irin murya mare daɗin sauraro
"Na dawo gare ku kamar yadda kuke so, ina Rebeccah?"
Daga can ɓangaren a gigice Maheer ya ɗaga kai ya kalli Luƙman, shi ma luƙman ɗin ya kalle sa. Amma sai ya ɗaga mishi hannu alamun yayi shiru kar yayi magana, ya ƙara ƙure ƙarar maganganun da suke saurare ta jikin na'urar da suka jona da abinda yake maƙale a kunnensa.
A can cikin ƙungiya kuma wani ƙaƙƙarfan dariya Oga ya fashe da shi yana nuna ta da dungulmin hannunsa.
"Da kina tsammanin za ki iya guje mana mu barki ki rayu a wata duniya ba tare da mu ba? Bari in faɗa miki abinda baki sani ba. Tun ranar da Mary ta kawo ki cikin ƙungiyar nan Garkuwa ya bani daman ganin manyan sirrukan tsafe-tsafen da Veronika ta jiƙa ki da su. Amma kuma ke kanki baza ki san ke shahararriyar matsafiya bace sai ranar da kika cika shekaru ashirin a duniya, duk wani abu da za kiga kinyi ya faru ƙarami ne a cikin tsafin da aka raine ki da shi tunda baki kai shekaru ashirin ba. Da wannan dalilin yasa muka umarci Mary ta kula da ke ta raineki cikin gata, ta baki duk abinda kike so. Saboda ranar da za ki cika shekaru ashirin a gaban Garkuwa za mu kwana ni da ke muna bauta mishi. Idan muka yi hakan wannan ƙungiyar tamu za ta ɗaukaka, za muyi gogayya da duk wata ƙungiya ta tsafi da take ji da kanta a duniya.
Sai da lokacin ya kusa kuma za ki barmu? Da farko mun barki kin huta a gidan wancan malamin ne saboda babu halin mu ɗaukoki daga gurinshi, amma aurar da ke da yayi abu ne da zai rusa mana abinda muke jira shekara da shekaru. Idan muka yi kuskuren barin wani namiji ya kusanceki duk wani tsafi da aka rene ki da shi zai gudu ya barki ke kaɗai da baiwar da aka haife ki da shi, wannan kuma ba komai bane fa ce wani abu da Hausawa suke kira KAMBUN BAKA.
Idan kika cika shekaru ashirin ɗinnan za ki samu mulki, za a miki biyayya a duniya, duk girman ƙungiyarnan ke za ki zama mataimakiyar Oga. Bibi..."
"Alheri."
Ta faɗa da wata siririyar murya cikin tsawa tare da miƙewa tsaye a fusace, wani walƙiya mai tsananin haske tare da rugugi kamar aradu yayi fitan burgu daga idanunta ya maka Oga da jikin bango.
Daga can ɓangaren su Maheer kuma wani ma'aikaci da yake gaban wasu na'urori da kwamfuta a gabanshi yana aiki ya waiga yana kallon Lukman
"Yallaɓai! A halin yanzu mun gano dai-dai inda suke meeting ɗin."
"Good!"
Da mugun gudu Luƙman da Maheer da sauran ma'aikatan da ya shirya zai tafi da su suka fice daga babban ofishin suka shiga motoci biyun da suka zuzzuba kayan aikin da za su tafi da su, ba tare da ɓata lokaci ba direban da su Maheer suke ciki ya ja motar da gudu ɗayan direban ya bi bayanshi, kunnen direban maƙale da abin sauraren magana wancan ma'aikacin da ya gano inda su Bilhaƙƙi suke yana mishi kwatancen gurin.
BILHAƘƘI
Duk da mugun buguwan da yayi bai hana ya miƙe yana tangaɗi ba, kafin ta ankara ya nuna mata dungulmin hannunshi ya runtse idanu yana wasu irin maganganu na tsafi, nan take aka ɗaga ta sama cak! aka fara hajijiya da ita tsakankanin tulunan da suka yiwa saman ɗakin ƙawanya, ita ba a sama ba a ƙasa ba.
Kanta ne ya fara juyawa a saman, duk yadda ta so ta sauka ƙasa da nata ƙarfin tsafin ta kasa, tana zuwa kusa da wani ƙaton tulu da yafi ko wanne girma yana tsaye cak a saman ɗakin kawai sai ta dunƙule hannu ta dake shi da mugun ƙarfi ranta a ɓace. Tush! ƙarar fashewar tulun da sakin wata siririyar ƙara da ya karaɗe ɗakin duk a tare suka fito daga cikin tulun.
Cikin sauri Oga ya buɗe idanunsa a tsorace, ganin abinda ta yi yasa shi ƙwalla wani gigitaccen ƙara ya zube a tsakar gurin yana kururuwa da birgima kamar wani makaho, zuciyarsa cike da tunanin amfanin tulun a gare su.
'Wannan tulun da ta fasa shi ne babban turaku ko kuma murhun da yake riƙe da ƙungiyarsu, Garkuwa ya taɓa faɗa mishi duk ranar da aka fasa wannan tulu to tabbas ƙarshen ƙungiyarsu ne ya zo, kuma daga lokacin da tulun ya fashe baza su sake jin motsinshi ko kuma ya biya musu wata buƙata tasu ba.'
Ita kuma Bilhaƙƙi ganin hakan da yake yi yasa ta gane lallai tayi musu babban ɓarna. Don haka cikin masifaffen sauri kamar walƙiya ta ci gaba da bin tulukan tana farfasawa, duk tulun da ta fasa da kalar