Showing 90001 words to 93000 words out of 98260 words
yi ba.
Kusa da ita ya sake matsawa ya riƙe hannunta, yana ƙoƙarin kallon cikin idanunta
"Idan babu komai shi kuma ɓacin ran na menene?"
"Ba komai!"
Cikin fushi ta amsa tare da watsa mishi wani birkitaccen kallo. Ta fisge hannunta ta haɗa hannu biyu alamar roƙo.
"Dan girman Allah Malam ka fita daga harkata."
Hanyar fita daga kicin ɗin ta nufa, shi kuwa a sukwane ya janyo gefen rigarta.
"Idan za mu tafi fa motata za ki hau..."
"Baza ta hau motarka ba."
Ya ji muryar Ummee kwatsam ba tare da ya ga sadda ta shiga kicin ɗin ba.
Sansarai yayi a tsaye, jikinsa yayi mugun sanyi.
Fuskanta a ɗaure ta ƙarasa shiga kicin ɗin, hannunshi ta nuna da yake riƙe da gefen rigar Bilhaƙƙi.
"Sakar mata riga ka fice min a nan."
Da sauri ya sake ta ya nufi hanyar fita, yana zuwa daf da ita cikin murya mai baiyana ƙwaƙƙwaran kashaidi da jan kunne ta ce
"Ka jawa fitsararriyar matarka kunne. Idan kai wasa daga kai har matan naka babu inda za kuje Wallahi."
"Ummee dan girman Allah kiyi haƙuri..."
"Ka ɓace min da gani na ce ko?"
Da sauri ya cikawa rigarsa iska zuciyarsa cike da takaicin Surayya. Daman ya san tunda ta tada ballin sai ya je da su tabbas sai ta jaza mishi wani tsiyar. A maimakon ya koma cikin falon kawai sai ya fita waje.
Ta kalli Bilhaƙƙi ta yi murmushi, ta ja hannunta suka matsa gaban kayan tea ta fara haɗa mata
"Wai kishiyar kike wa hawaye? Wannan fa alamun jin tsoronta ne tun kafin ki shiga gidan?"
Ta tura baki tana murmushi
"Ba fa tsoro bane Ummee, kawai ni bana son a disgani a cikin mutane ne."
"Eh lallai ba daɗi kam! Amma ki manta da ita kawai, ko ba yau ba kar ki ƙara yadda suyi miki wani abu ki nuna musu ranki ya ɓaci kinji ko?"
"To Ummee na, in Allah ya yarda."
"Yauwa Baben Yayanta, ungo maza je ki zauna ki cinye tas kuma ki shanye tea ɗin. Ki cewa Saudat idan bata fito ba da alama za a tafi a barta. Ni ma bari inje mu ƙarasa shiryawa ni da Mamanki."
"To Ummeena."
Da murmushi a fuskarta ta bar kicin ɗin. Ta ma manta da babin wata Suraiya.
Ummee tana shiga falon ta kalli surukan da ɗaurarriyar fuska, irin kallon da take watsawa Surayyan yasa duk ta ji ta muzanta.
"Ku zo ku gaida Mahaifiyar Bilhaƙƙi."
A sanyaye duk suka bi bayanta zuwa ɗakin. Zukatansu cike da mamakin ko yaushe mahaifiyarta taje gidan? Haka dai suka gaishe ta a ladabce suka fice daga ɗakin.
A wannan ranar dai haka aka yi tafiyar zuciyar Maheer babu daɗi, yana ji yana gani Bilhaƙƙi ta hau ƙatuwar jeap ɗin Luƙman, Malam ne a gaba, ita, Ummee, Mamanta a bayan motar.
Shi kuma matansa biyu ya ɗauka, Aisha matar Lukman, sai Saudat. A gidan Malam dai ƴan samarin ƴaƴansa kawai aka bari da jiran gida.
******* *******
A can Masarautar Bauchi kuwa gaggarumin taro uku ne ake shiryawa, bikin sunan Ƴan biyun Gimbiya Safiyya, bikin murnar baiyanar Mustapha da iyalansa (Don Malam ya sanar da su ganin Rebeccah da ƴarta) Sai bikin naɗin Mustapha a matsayin tabbataccen Yarima mai jiran gado.
Shi Takawa ma tun lokacin ya so yayi murabus ya sauka a naɗa Mustaphan amma yaƙi yarda, shi Mustaphan ya nemi alfarmar a ɗaga mishi ƙafa ya ƙara hutawa ya koma cikin nutsuwarsa sosai, kuma ya samu damar karantar harkar mulki da yadda ake gudanar da shi.
Ta ko ina manyan baƙi masu sarauta, ƴan uwa da abokan arziki na nesa da na kusa sai tuttuɗawa masarauta suke yi. Tun ana gobe sunan algaita da bushe-bushe suka fara tashi a masarautar.
Gaggarumin biki ne da aka daɗe ba'ayi irinsa ba a masarautar, kowa so yake ya kashe ƙwarƙwatan idanunsa.
BILHAƘƘI
Da yake a wannan karon an kawar da matsalar su Oga, Na shuri ma babu maganarshi. Lafiyar Allah suka yi tafiyar cike da kwanciyar hankali da nutsuwa ba tare da wani mummunan abu ya faru da Bilhaƙƙi ba.
Ta daɗe tana sharɓan bacci a jikin Mamanta, sallah da cin abinci kawai ke tada ita. Sai da suka kusa shiga cikin garin sannan Rebeccah ta tashe ta, ta ce ta zauna da kyau ta wartsake an ce sun kusa isa gurin Babanta.
Da yake wannan karon gudu suke yi ba na wasa ba, kuma basuyi tsaye tsaye a hanya ba, ƙarfe biyar saura suka isa cikin masarauta.
Nan fa aka sake kacamewa da gaggarumin murna na bayyanar iyalan Yarima Mustapha, Jakadiya ƙarama da aka mayar da ita matsayin Jakadiya Babba tattakura ta yi ta kama hanci ta rangaɗa zazzaƙar guɗa mai tsananin ƙara da fitar sauti, ko minti biyu bata yi ba Uwar Soro ta karɓe da nata zazzaƙar guɗan.
Wannan watan gaba ɗaya sun raɗa mishi suna WATAN FARIN CIKI.
Sarauniya Safiyya da ta ga Bilhaƙƙi tsaye a gabanta matsayin jikanyarta, halastacciyar ƴa ga gudan jininta na farko suman zaune ta yi, kafin daga baya ta fashe da ƙaƙƙarfar kuka mai baiyana tsananin farin cikin da zuciyarta take ciki.
Rebeccah sai ina za'a saka da ita ake yi. Babu kunya ba kara Sarauniya ta rungume ta a cikin mutane, uwar Soro da Umma sai tsokanarta suke yi irin na jika da kaka, wai ta tafi da zuciyar mai gidansu Mustapha gaba ɗaya ta hana shi nutsuwa saboda rashinta (idan baku manta ba su kakannin Mustapha ne). Ita dai ba baka sai kunne, sai sussunne kai ƙasa take yi saboda kunya da rashin sabo.
A wani babban falo na musamman da yake ɓangaren Sarauniya Safiyya aka tarbe su da kalolin abinci na gani na faɗa na alfarma, sunci sunsha sunyi hani'an sai godiya ga Allah suke yi. Nama kala-kala sunci sun ture ciki har da na ɗawisu. Kai wani kalan naman ma basu san ko na wace dabbar bace su dai kawai ci suke yi suna tanɗe hannu, kunnuwansu kamar zai tsinke saboda tsananin daɗi.
Tun daga nan su Surayya suka fara zubar da makaman yaƙinsu bayan sun fahimci abinda yake faruwa. Tsananin takaici da bakin cikin wannan al'amari na ɗaukakar Bilhaƙƙi lokaci ɗaya Surayya sai da ta shige banɗaki ta shaƙi kuka kamar ranta zai fita.
'Yanzu duk matan Maheer ita ce koma baya kenan? Daga ƴar sarki sai ƴar Alhaji ita ce ƴar Ladani? Ita wallahi da ta ma san abinda za ta gani kenan da bata zo ba.'
Tana zuwa nan a tunaninta wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle mata shar! shar!! kamar an buɗe famfo.
Haka ta shaƙi kukanta ta fita tana yaƙe a cikin mutane. Ga dangin Maheer daga Maru sunje sosai, saboda sha'ani ne da aka daɗe ana cin burin lokacin zuwanshi.
Duk ƙwaƙwar Musty da yadda ya ci burin son ganin Rebeccah da yadda ita ma ta ci burin ganinsa a karon farko da isarsu basu samu damar haɗuwa da juna ba sai da aka idar da sallar magrib.
A lokacin ne Takawa ya bada umarnin a kira duk wasu dangi makusanta na jiki-jiki don a gabatar da Bilhaƙƙi da Mahaifiyarta.
A wannan lokacin ne haɗuwar masoyan biyu ta kasance, dukda an raba su da juna na tsawon shekaru goma sha tara zuciyoyinsu na tare da juna. Sun ba kowa na cikin falon tausayi, duk wani mai rai da yake cikin falon nan sai da ya zubar da ƙwallar tausayin waɗannan masoya biyu.
Lallai da gaske ne soyayya ba ta tsufa sai dai masoyan su tsufa, haɗuwa ce da duk su biyun suka daɗe da fitarda tsammanin yin irinta, idanunsu rufewa yayi ruf! basa ji basa ganin kowa a falon sai su biyun nan.
A tsakiyar falon suka haɗe idanunsu na cikin na juna suna zubar da hawaye, hannuwansu na riƙe da na juna. Jikkunansu sai kyarma suke yi, lallaɓansu sai mazari suke yi. Kamar haɗin baki a tare suka kai gwuiyawunsu ƙasa har lokacin basu daina kallon juna ba.
Rebeccah ce ta fara katse shirun da suka yi da magana cikin muryar matsanancin kuka da ciwon zuciya
"Musty nah... Tsawon shekarun nan suna gana min azaba... kullum sai Zidane ya zane ni saboda na ƙi sakin kalmar da ka laƙaba min a baki kafin ka tafi... sun alƙawarta min dukiya mai yawa amma na ƙi ƙarɓa... sunyi min alƙawarin muƙami mai girma a coci na ce bana so... har Jerusalam sun ce za su kaini na ce bana so... Ka san saboda menene suka yi min haka? wai in bar musuluncin da na shiga a gurinka. Wai in daina kiran la'ilaha illallahu muhammadur rasulillah... Amma har yau ban bar Musuluncin ba Musty, ban bari ba. Na rantse maka ban bari ba... kullum sai na ce La'ilaha illallah atleast sau talatin... Amma duk tsawon lokacin nan bana yin sallah Musty, basu bani damar da zan fita cikin musulmai ba balle in koya yadda zanyi... har yau ban canza sunana daga Rebeccah zuwa sunan musulmai ba Musty... kana ganin musuluncina har yanzu yana nan Musty???"
Jikinsa ne ya ƙara sanyi da ɗaukar matsanancin rawa kaman bugun zazzaɓi, hannuwanta duk biyun ya damƙe a ƙirjinsa kamar mai ƙoƙarin janta ta shige cikin jikinsa, cikin kuka shi ma ya fara magana da ya fahimci amsoshinshi take jira
"Musuluncinki yana nan Rebeccah... Tabbas har yanzu ke cikakkiyar musulma Ummu Bilhaƙƙi... Addininmu mai adalci ne. Ubangijinmu mai jin ƙan bayinsa ne. Bazai taɓa kama ki da laifin da aka tilastaki gurin aikata shi ba... idan kuma kina tantama zo kiji daga bakin babban limaminmu."
Tsananin tashin hankali yasa da rarrafe ya ja ta har gaban Malam Liman da shi ma ya sadda kai ƙasa yana ta sharan ƙwallah
"Liman dan Allah ka faɗa mata. Ina ce har yanzu ita musulma ce ko? ka faɗa mata ko hankalinta zai kwanta. Matata ce ita da har yanzu nake tsananin son ta, ta sadaukar da abubuwa masu girma saboda ni da farinciki na. Don Allah ka faɗa mata, sam bana son tashin hankalinta. Har yanzu ita musulma ce ko?"
"Ƙwarai kuwa Mustapha. Har yanzu ita musulma ce."
A tare suka sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, suka haɗa idanu ga kuka ga murmushin farin-ciki.
A wannan lokacin dai sam sun kasa nutsuwa, tsananin tausayinsu kuma da ya cika zukatan mazauna gurin duk sun kasa magana.
Liman ne kawai yayi dogon nasiha mai ratsa zuciya, a ciki ya nusar da kowa wannan tafiya da Mustapha yayi dukda akwai sila rubutaccen ƙaddara ne da aka rubuta zayyi tun kafin a haifesa. Ya ƙara da cewa ta wani fannin tafiyar ta haifar da alkhairai da dama, ciki har da jihadi na musuluntar da wata Ahlul kitabi. Wannan babban abin farin ciki da godiya ga Allah ne.
Sannan ya maida akalar nasihan kan Rebeccah yana faɗa mata irin gwaggwaɓar lagwadar da duk bawan da ya mutu a matsayin cikakken musulmi mai imani zai sharɓa a gurin Allah SWT. Ya kuma gode haɗe da shi mata albarka na yadda tsananin wahalan da tasha a hannun ƴan'uwanta bai sa ta fita a musulunci ba.
Ya sake janyo hankalin duk dangi da iyayen Mustapha kan su tsananta kyautata kamar yadda addininmu ya koyar da mu, ta yadda ko a mummunan tunani baza ta taɓa yin dana sanin shigowa musulunci ba.
Daga nan ya bata damar zaɓen sunan da take so na musulunci ita kuma ta ce ta ba Mustapha wannan daman, yana daga cikin abinda take jira idan sun haɗu a aljannah ya raɗa mata.
A nan kam sai da taba kowa dariya da tausayi.
"Nana Khadeeja. Malam Liman na raɗa mata sunan Nana Khadeeja."
Mustapha ya faɗa da sanyin murya.
Nan gaba ɗaya falon ya kaure da kabbara.
A nan sai Malam Abdulganiyyu ya karɓi bayanin, inda ya bada taƙaitacce tarihin Nana khadeeja da irin gudummuwarta ga addinin musulunci.
Nanma wata kabbarar aka sake ɓarkewa da ita.
A nutse ya ci gaba da bada labarin duk yadda aka yi Bilhakki taje hannunshi, har zuwa ɗaura mata aure da yayi, da yadda su Maheer suka samu nasarar karɓo Rebeccah. Bai ɓoye komai ba ci ke da nutsuwa ya gama warware musu duk bakin zaren.
A nan ma dai wani jimamin aka sake yi, tare da godiya ga Allah da ya kawo ƙarshen komai duk da tsawon lokacin da aka ɗauka ana shan wahalhalu da gwagwarmaya iri-iri.
Yarima Mustapha sai kallon kyakkyawar budurwar da aka kira a matsayin ƴarshi yake yi. Babu abinda yake tunani sai yadda ya rabu da ita tana jaririya ranar da aka haife ta.
Lallai komai yayi farko yana da ƙarshe amma banda ikon Allah. Har lokacin bai daina share hawaye ba.
Takawa ya kira Bilhaƙƙi ta je ta durƙusa a gabanshi, hannunta bibiyu ya riƙe fuskarsa yalwace da farin ciki. Shi mata albarka yayi sannan ya ƙara da yi mata addu'ar Allah ya ci gaba da tsare ta daga sharrin duk wani abin halitta.
Haka ta ci gaba da zagawa tana gaisar da iyaye da kakanninta su kuma suna saka mata albarka, daga mai rike hannu ya shafa kanta a cikin maza, sai masu rungume ta a cikin mata.
A haka dai har ta gaisa da kowa ta zube a gaban Babanta, lokacin ne wasu hawayen suka sake ɓalle musu duk su biyun
"Ba...ba...na..."
Ta kira shi da rawar murya.
"Na'am Bilhaƙƙi"
Ya amsa kiran a raunane tare da janyota jikinsa ya haɗa ita da Nana Khadeeja(Rebeccah) ya rungume a kirjinsa. Nan suka ƙara karyarwa da kowa zuciya.
Sai da aka natsa, hankali ya kwanta Takawa da iyaye da ƴan'uwansa suka miƙa godiya ta misamman ga Malam da iyalansa.
Ya kuma yanke bayan wannan taron na gobe in Allah ya yarda za a yanke ranar da za a yi bikin Bilhaƙƙi a kaita gidan mijinta. Jin hakan ba ƙaramin farantawa Maheer rai yayi ba.
Sai wani sussunne kai yake yi cike da kunya lokacin da yake miƙa gaisuwa gurin Takawa, Umma, Yarima Mustapha. Mai soron baƙi kuwa sai tsokanarshi take yi yana murmushi kawai.
Nan falon Takawa Liman ya ja su sallar isha'i zukatansu cike da farin ciki. Su kuma matan suka yi nasu sallar a cikin gida.
******* *******
"Ammi"
"Na'am! ya aka yi El-mustapha? Baka yi bacci ba?"
Sosa kanshi yayi cikin kunya, duk da ya fara girma a gaban iyayen jinshi yake yi kamar wani karamin yaro.
"Ammi na zaci za ki turo Nana Khadeeja ta tayani hira...?"
Ido warwaje take kallonshi da mamaki. Sai kuma tayi murmushi.
"El-Mustapha ka fita daga idona. Ko za a baka matarka sai nan da sati uku. Lokacin ta gama hutawa kuma an gyara mata ɓangaren da zata zauna. Kar in sake jin wannan maganar ka ji ko?"
"To Ammi"
Ya amsa da alamun ba haka ranshi yaso ba.
"To Ammi ki turo min ita inyi mata sai da safe."
"Ai ta daɗe da yin bacci, faɗa min gobe idan ta tashi sai Balaraba ta faɗa mata saƙonka."
Duk ta inda ya ɓullo mata sai da ta ɓille haka nan dai dole ya haƙura ya tafi ɓangarensa, ta bishi da kallo kawai har ya ɓacewa ganinta tana dariya a zuciyarta.
"Ranki ya daɗe ke da waye a nan?"
Ta jiyo muryar Bilhaƙƙi daga can nesa.
Hannu tasa ta yafitota alamun tazo.
Da sauri ta ƙarasa ta zauna a ƙasa kan kafet kusa da ƙafafunta.
"Karki sake ce min Ranki ya daɗe kinji ko?"
"Tom! Kakus, Kakaty, Sweet Kakas, Kakalliya, wanne sunan kike so a cikin waɗannan?"
A tare suka kwashe da dariya duk su biyun. Hannunta ta kamo ta riƙe a cikin nata tana kallon fuskarta cike da tsananin ƙauna.
"Wallah tun ranar da na fara ganin wannan doguwar kyakkyawar fuskar taki na ji ina tsananin ƙaunarki. Allah ya ci gaba da tsare mana ke kinji Ƴar jikalle?"
"Ameen Sweet Kakaty"
Ta amsa tana murmushi.
"Amma yau a turakata za ki kwana ko...?"
"A'a gurin Mamana dai. Ina zan ga Babana inyi mishi sai da safe?"
"Iyyeee... abin ƴar hakane? Yarinya ƴar gatan Mamanta da Babanta. Mamanki tana can ita da Hajiya Yagana ana gyara mata jiki, yau kusan kwana za suyi ana mata gyaran saiɓee. Shi kuma Babanki yanzun nan ya tafi ɓangarensa. Dolenki yau a gurina za ki kwana, akwai maganar da nake so muyi."
"Tam! an gama Sweet kakaty"
Dariya duk suka sake yi gaba ɗaya.
BILHAƘƘI
ƘARSHE 💃🏽💃🏽💃🏽
A cikin dare ɗaya kacal Hajiya Yagana ƙwararriyar mai gyaran jiki daga maiduguri, aminiyar Sarauniya Safiyya ta gyara Nana Khadeeja ta yi kyau sosai fiye da tunanin mai tunani.
Duk wani loko-lokon tsufa, da wani tudu da kwari da tabban duka a jikin Nana Khadeeja ta fara dirje shi da haɗaɗɗun kayanta na gyaran Saiɓi. Gashin kanta an wanke, an cuɗe, hallau aka sake wanke shi da haɗaɗɗun maya-mayan wankin kai, daga bisani aka sake cuɗe shi da wani haɗaɗɗen sabon salo na wankin kalkashi.
Tattausan Ƙamshi mai tsananin daɗi ake ji a jikinta ga duk wanda ya kusanceta, sosai ƙamshin har ya fara kama jikinta. Lallai da gaske sayen na gari maida kuɗi gida, kuma idan kina da kyau ki ƙara da wanka.
Ita kanta sai kallon kanta take yi a madubi tana sake murmushi, tunani take yi
'Ashe dai har yanzu da sauranta? lallai da sauran kallo a rayuwar aurensu ita da rabin ranta Mustapha. Soyayya za ta gwada mishi sosai irinta bugawa a jarida.' Zuciyarta cike da farin-ciki ta ke cewa ga Yagana
"Aunty na gode na gode sosai. Allah ya saka miki da alkhairi. Daman ina ta tunanin wasu irin mayuka zanyi amfani da su don gyaran jiki na sosai in dawo yarinya."
Ta ƙarasa maganar haɗe da rufe fuskarta da tafukan hannunta biyu tana dariya.
Murmushi kawai Hajiyar tayi, sosai Khadeejar ta burgeta, saboda duk abinda ta ce tayi tana yi babu musu ko tambayar amfanin abinda tasa ta yi. Sosai ta ke son zura idanu da biyayya a tsarin aikinta.
"Karki damu Khadeeja. Alƙawarin da na ɗaukarwa Safiyya cikin sati ɗaya in Allah ya yarda