Showing 93001 words to 96000 words out of 98260 words
duk wanda ya sanki a jiya da wuya idan ya ganki zai gane ki. Gyara yanzu muka fara, ke dai ki ci gaba da bada haɗin kai. Ga ruwan wanka can an gama haɗa miki. Ungo wannan sabulun"
Ta ɗauko mata wani sabulu na daban ba waɗanda suka yi amfani da su cikin dare ba
"Yanzu kiyi amfani da wannan, shi wannan amfaninshi a cikin kwanaki uku kacal za ki ga fatarki ta fara sheƙi tana ɗaukar idanun mai kallonki. Asalin hasken fatar jikinki zai fito cikin ƙanƙanin lokaci."
"To Aunty. Na gode."
Ko da ta fito wankan sai da aka sake turare ta da wasu kala-kalan turaruka masu tsananin ƙamshi, aka mulke jikinta da wani haɗaɗɗen humra, sannan aka bata kwalakca ta shafa.
Wani haɗaɗɗen lesi da a kallon farko ta gane zayyi mugun tsada ɗinkin Buba da bata san lokacin da aka shiga da shi ɗakin ba Hajiyar ta bata ta ce ta saka.
Da yake Hajiyar a cikin yaranta akwai ƙwararru a wajen makeover nan da nan su kuma suka fara aikinsu bayan ta saka kaya. Sai da aka gama shirya ta tsaf aka naɗa mata ɗaurin ɗankwali sannan aka ba Bilhaƙƙi daman shiga ɗakin.
Lokacin da tayi arba da Mahaifiyarta ƙam tayi poster a tsaye saboda kaɗuwa da yadda aka cancare ta da gyara, sai da Khadeejan ta je ta kamo hannunta tana dariya sannan ta dawo hayyacinta.
"Mamana...? Ke ce haka? Aradu idan Babana ya ganki da wuya zai gane ki. Wallahi kinyi kyau sosai kamar wata amarya."
Duk sai taba mazauna ɗakin dariya, haka taita sambatu tana dariya tare da zuzuta kyawun da uwar ta yi. Ta juya ta dinga godiya ga Hajiyar na irin kyakkywar gyaran da tayi wa Mamanta.
"Oya common Baby, godiyar ta isa haka. Yanzu saura ke. Kakarki ta ce in gyara ki sosai yadda za ki fito a TAURARUWARKI. Ta ce so take ki fi kowa tsananin haskawa a gurin taron nan."
"Haba Hajjaju. Yau ai fagen na Mamana da Babana ne. Su suke lokaci. Ni irin wannan gyaran ki bari sai gaf da bikina."
Dariya suka sake sakawa ganin yadda ta haƙiƙance tana maganar babu ko kunya, tunda suka isa jiya sai a lokacin ta ɗauko wayarta ta kunna, tana ganin saƙonnin Maheer kawai ta danna musu delete gaba ɗaya don bata buƙatar karanta su. Tayi ta ɗaukar uwar hotuna kala daban-daban. Sai da ƙyar ta samu nutsuwa ita ma aka fara mata gyaran jikin.
Da gaske dojewa ta dinga yi dole aka yi mata gyaran jikin sama-sama kamar yadda ta buƙata. Ita ma bayan ta yi wanka wani doguwar rigan material less mare nauyi aka bata ta sanya, rigar cas tayi a jikinta kaman an gwada ta kafin a ɗinka. Aka yi mata taƙaitaccen kwalliya sannan aka naɗa mata ɗaurin ɗankwali.
Sosai ta yi masifaffen kyau kamar a sure ta a gudu. Ta matsa kusa da Mamanta sukai ta ɗaukar hoto tana ƙyalƙyala dariya, a lokacin tana ganin kiran Maheer yana ta shigo mata ita kuma tana ta rejecting.
Har saida Mamanta ta ce
"Baby ki ɗauki wayar mana. Wa ke ta kiranki haka?"
"Manta kawai Mamana, bana son a dame ni yanzu. Bari inje gurinsu Ummeena. Yanzu zan dawo."
Da sauri ta fice daga ɗakin tana murmushi, har yanzu zuciyarta cike ta ke da haushin Maheer, bata shirya sauraren ban haƙurinsa ba.
'Har ita zai gwadawa yana da mata biyu bayan ita? Bai faɗa mata tare da su za ayi tafiyar ba kawai ya wani taso su a gaba da wani kwalliyarsu dan su haɗu su nuna mata iyakarta? a gabanshi matarsa ta wulaƙantata amma ya kasa tsawatarwa balle ya ɗauki mataki?'
Ƙwafa kawai ta yi ta jinjina kai, duk inda ta gilma bayi zubewa suke yi suna kwasar gaisuwa har ta isa ɗakin da aka sauki Rabi, Surayya, Aisha.
Da ƴar fara'a ta shiga ɗakin tana wani shan ƙamshi haɗe da basarwa kawai dan ta guma musu takaici, ta ci nasarar hakan kuwa. Kishiyoyin nata zugudi suka yi suna kallonta duk jikinsu a sanyaye, sai suka raina kwalliya da suturar da suka sa duk da ƙure adaka suka yi.
"Sas-sannunku da hutawa Auntys ɗina. Akwai wani abu da kuke buƙata ne in ba da umarnin a kawo muku?"
Bata jira cewarsu ba ta maida idanunta kan Surayya fuskarta da wani lalataccen murmushi ta ce
"Aunty yau ma ko kina buƙatar in ɗauke kofin daga gabanki ne?"
Su biyun tsu suka yi a tsure, ba ma kamar Surayya da take ta zazzare idanu kamar ƙwai a ledan burodi. Aisha ce tayi dariya, ta matsa tare da dafa kafaɗar Bilhaƙƙi tana kallonta cike da sha'awa da yabawa
"Ƙanwata ba ma buƙatar komai. An bamu komai a wadace har ma da abinda bamu buƙata ba. Har yanzu maganar jiya bata wuce ba?"
Da dariya ta amsa tana wani karkaɗa ƙwayoyin idanunta.
"A'a ta wuce fa Aunty. Da gaske ta wuce har abada. Bari in je gurinsu Ummeena."
"Kinyi kyau sosai ƙanwata."
Ta faɗa mata a daidai lokacin da take gaf da ficewa daga ɗakin.
"Na gode Aunty Aisha. Na gode"
Ta amsa da dariya tare da ficewa daga ɗakin.
Sai da ta tabbatar tayi nisa sannan ta juya ta kalle su, kamar baza ta tanka musu ba sai kuma ta ce
"Kunsan Allah? Idan kunso tsaf za ku zauna lafiya da yarinyar nan. Kune manya idan kun kame girmanku ba ta yadda za a yi ta raina ku. Amma wallahi idan kuka ce za ku riƙe ta a sakalce kuna gwada mata wani izza ko makirci wallahi za ku sha mamakin abinda zai biyo baya.
Kun dai ga yadda reshe ya juye da mujiya ko? Ba gori ba kuma ban cire kaina ba duk ta fimu zuzzurfar nasaba da kusanci da mazajen da muke tunƙaho da su.
Idan kun daure zuciyarku kuma kun kauda kai gare ta da Maheer komai mai zuwa da wucewa ne. Daman kuma kun san Amarya ko ta buzuzu ce dole miji sai yayi ɗokinta. Gaskiyar da zaku gwada mata gurin zama da ita shi zai sa ta saki jikinta da ku ta rungume ku kamar yayyinta na gaske. Kuci arziki ku bar arziki a inda yake.
Idan kunƙi kuma sai ta kame dangin mijinku tayi hurɗa da su daman kuma yayyinta ne. Miji kuwa bayan aure ɗanuwanta ne makusanci. Idan kunne ya ji gangar jiki ya tsira da mutunci."
Daga haka bata sake cewa komai ba ta shige banɗaki.
Su kuwa shiru suka yi kowacce tana jujjuya maganganun a ranta. Da alamun dai duk sun gamsu kuma sun amince da shawarwarinta.
******* ********
Anyi gaggarumin taron lafiya an tashi lafiya. An gudanar da komai cikin farinciki, walwala, nutsuwa haɗe da kwanciyar hankali.
Anci, ansha, anyi hani'an! Yara sunci sunan Yarima Fareed Abdulfatah da Gimbiya Fareedah Abdulfatah😝🤣 Wasanni kala-kala aka yi na sarauta sannan naɗin Yarima Mustapha a matsayin tabbataccen Yarima mai jiran gado ya biyo baya.
A gaban dubban jama'a manyan mutane daga masarautu daban-daban da masu ƙumban susa aka gabatar da Gimbiya Nana Khadeeja Mustapha da Gimbiya Bilhaƙƙi Mustapha a matsayin iyalan Yarima mai jiran gado.
Ƴan jarida, ma'aikatan gidan radio, ma'aikatan gidan T.v daga sassa daban daban na jihohin ƙasarnan sai ɗauka ake ana nunawa kai tsaye a gidan T.v.
Can na hangi gungun haɗaɗɗun matan Rumbilhaƙ comment section, sun sha haɗaɗɗiyar kwalliya cikin ankon kyakkyawar atamfofinsu, ko waccensu ta ɗora alkyabba a kan kayan jikinta.😍😍😍 Da na matsa kusa da su don ɗaukar labari yanyame ni suka yi ko wacce tana tofa albarkacin bakinta. Jimla ɗaya da duk suka fi haɗuwa a kai dai shi ne
"Muma baza a barmu a baya gurin taya Bilhaƙƙi, Rebeccah, Mustapha murnar kawo ƙarshen matsalolinsu ba. Alhamdulillah. Allah ya zaunar da su lafiya da mazajensu."
Sai a gurin taron Maheer ya samu ganin Bilhaƙƙi, sosai tayi mishi mugun kyau a cikin alkyabbar da ta ɗora a saman kayan jikinta. Ba tare da kunyar idanun jama'a ba ya matsa kusa da ita ya ɗaɗɗaukesu hotuna kala-kala da wayarsa.
An raba manyan kyaututtuka da dama a wurin. Taro dai yayi taro Alhamdulillahi. Komai an yi shi lafiya kuma an watse taro lafiya. Sai fatan Allah ya maida kowa gidanshi lafiya.
******* ********
"Wa nake gani haka a gabana kamar Safara'u. Lafiya kike kuwa? ko har yanzu jikin naki ne bai gama warwarewa ba..."
Zubewa ƙasa da tayi cikin kuka tare da kama ƙafafun Umman shi yasa tayi shiru tana jiran jin da wacce ta zo.
Cikin kuka ta fara magana har lokacin bata sake ƙafafunta ba. Cike da da na sani ta warwarewa Umma duk wani mugun ƙulli da ta daɗe tana tufkawa a masarautar, har zuwa kan tonuwar asirinta da kuma irin matakin da Mai martaba ya ɗauka a kanta. Tare da rantsewa da girman Allah kan cewa ita yanzu ta tuba ta gane kuskurenta, dan girman Allah a roƙa mata Takawa da Safiyya su yafe mata. In Allah ya yarda baza ta sake aikata wani kuskure makamancin wannan ba.
Shiru Umma tayi zuciyarta cike da mamaki, duk da Mai martaba ya faɗa mata komai da ya faru amma ƙara jin labarin daga bakin Safara'un da kanta ya ƙara girgizata.
Shiru tayi bata ce komai ba, sai da taji kukan Safra'un ya ki ƙarewa sannan ta ɗaga kai ta kalle ta
"To ni yanzu me kike so inyi miki Safara? bayan sadda kika ƙulla irin wannan mugun aikin baki taɓa tunanin rana mai kaman ta yau zai iya zuwa miki ba?"
"Umma dan girman Allah ku yafe min. Na tuba, na bi Allah na bi ku. Ki saka baki dan ya rasulillahi Takawa ya yafe min. Wallahi tallahi na yi nadama, na gane kuskure na. Ku taimaka ku bani dama a karo na biyu, na yarda na ɗauki alƙawari idan aka sake kamani da laifi makamancin wannan a jefe ni."
Yadda take ta neman gafara tare da cin alwashin baza ta sake aikatawa ba cikin mahaukacin kuka yasa tayi masifan ba Umma tausayi.
"Ya isa haka Safara'u. Allah ya yafe mana gaba ɗaya. Je ki sasanki sai na neme ki. Allah ya tsare mu da son zuciya."
"Aameen. Na gode kwarai Umma. Na gode. Allah ya kara girma. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana. Na gode."
Bayan ta bar ɓangaren Umma haka ta dinga raɓe raɓe a cikin daren tana rurrufe fuska don gudun haɗuwa da waɗanda ta sani har ta ƙarasa ɓangarenta.
Bayan faruwan al'amarin sosai ta muzanta ta wulaƙanta a cikin mutane, ko cikin barorinta gani take yi kamar asirinta ya gama tonuwa. Sosai take kunyar fita cikin mutane. Duk abinda yake faruwa a gidan tana da labarinsa amma tsananin kunyan abinda ta aikata da tsoron kashaidin Mai martaba na karta kuskura ya sake ganinta yasa take lafewa cikin turakarta.
Yanzu duk wani izza, isa, mulki, tunƙaho, taƙama babu shi a tare da ita. Wani tsoron Allah ne yayi matukar kamata, istigfari take ta yi tana neman yafiyar Allah. Tare da wani matsanancin tsoron mutuwa ya risketa a wannan halin ba tare da ta nemi yafiyar waɗanda ta zalunta ba.
Da wannan dalilin yasa tayi ƙundubalar zuwa ta tari Umma da zancen a daren da aka gama taron nan, ta san ita ne kaɗai za ta iya tanƙwara Takawa ya dube ta da idanun rahama ya yafe mata kura-kuranta ko da bazai maida ita kamar da ba. Bata sake jin labarin halin da Chiroma da Jakadiya suke ciki ba, kuma ita ma ba ta ko marmarin sanin wane hali suke ciki.
Washe gari tun da wuri duk baƙi suka fara watsewa bayan an cika kowa da abin arziki. Su Malam ma da iyalansa ƙarfe goma sha biyu suka gama shirin tafiya, sunyi rana sosai amma in Allah ya yarda a ranar kaduna za su kwana.
Sosai suma an cika su da abin arziki kala-kala. Maheer suka tsaya jira yana can yana sallama da Bilhaƙƙi a falon Babanta.
Wani abin mamaki yanzu duk babu fushin nan, sosai take kukan zai tafi ya barta. Tana riƙe a ƙirjinsa tana ta sharar hawaye.
Shima dai duk zuciyarsa a damalmale ta ke, tsakani har ga Allah in banda dole ta kai dole babu yadda za a yi ya tafi ya barta a nan. Babban tashin hankalinsa ma shi ne har yanzu da zasu tafi ba a tsaida ranar da za a yi biki a kai masa amaryarsa ba.
"Tatlim kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki. Ba ga waya ba? za mu dinga magana ta waya ai. Tuƙi zanyi mai nisa a babbar hanya, da wannan kukan za ki sallame ni?"
Girgiza kai tayi ta sa hannu ta fara goge hawayen, amma wani abin tausayi tana gogewa wasu sabbi suna sake gangaro mata.
Haɗe bakinsu yayi ya fara aika mata da wani zazzaƙar sumba, yana tsotsan bakinta yana ɗauke hawayen da babbar yatsarsa har ya share mata hawayen gaba ɗaya.
Kudi masu yawa ya ɗauko a aljihunsa ya miƙa mata
"Ungo wannan ba yawa. Ki rike a hannunki ko za ki nemi wani abun."
"Ni dai ban so. Babana zai siya min komai..."
"Kin manta yanzu nauyinki a kaina yake?"
Kuɗin ya sake damƙa mata a hannu sannan ya ja ta suka fice daga falon, a hankali suke tafe yana faɗa mata tausasan kalamai na yadda yake tsananin sonta har suka ƙarasa falon Sarauniya Safiyya inda su Ummee suke jiransu. Yau dai saboda damuwa a hanya duk inda bayi suka zube musu ana kai gaisuwan ban girma kasa tankawa ta yi, sai shi ne yake ɗaga musu hannu har suka isa cikin falon.
Shigansu ciki yasa idanun kowa ya koma kansu, sosai suka dace a matsayin miji da mata. Kamar wata da tauraruwa mai tsananin haske.
Rabi da Surayya muƙut suka haɗiye wani dunƙulallen abu suka bi su da dariyar yaƙe.
Kai tsaye jikin Ummee ta shige ta rungumeta
"Ummeena zanyi kewarki."
"Nima haka Bilhaƙƙi. Karki damu kinji? nan da lokaci kaɗan za ki dawo mana."
Ta ɗaga kai kawai cike da damuwa, jikin Mummy ta koma tayi mata kamar yadda ta yi wa Ummee.
A mutunce suka yi sallama da kishiyoyinta da Aisha. Tana ji tana gani dai haka suka tafi suka barta, kuka ta sake fashewa da shi Babanta da Sarauniya Safiyya ne suka tasa ta gaba da rarrashi har ta haƙura tayi shiru.
Yinin ranar a ɗarare cike da sanyin jiki da damuwa ta ƙarasa shi, kuci-kuci kaɗan ta ɗaga waya ta kira Ummee ta ji suna ina? bata samu nutsuwa ba sai da ta samu tabbacin sun isa gida lafiya.
Jin muryar Maheer gar alamun sun isa lafiya yasa hankalinta ya ƙara kwanciya, cike da salon soyayya ta ƙara kashe murya ba tare da jin kunyar kakarta ba ta ce mishi
"Sevgilim ka yi wanka da ruwa mai zafi ka kwanta da wuri ka huta ka ji? kar ka kira ni ka kwanta kayi bacci. Da asubah zan tashe ka inji yadda ka kwana. I love you."
"I love you too Babe. Zanyi hakan in Allah ya yarda."
Ya amsa cike da mazewa tunda har lokacin yana tare da matansa. Ko waccensu haɗiyewa kawai tayi suka yi dariyar yaƙe haɗe da ɗan basarwa kamar basu ji ba.
BAYAN SATI BIYU
Jin dirin motarsa yasa a nutse ko waccensu cike da karairaya da gwalli suka nufi tsakar gidan. Sunsha gayu cikin riga da sket da ya kama ko waccensu ɗam!
Cike da fara'a da soyayya suka tarbe shi suna mishi barka da zuwa. Da yake girkin Rabi ne ita ta maƙale shi a kafaɗa ita kuma Surayya ta ɗauki jakar aikinsa da wayoyinsa ta bisu a baya har zuwa cikin falon.
"Aunty Surayya minti biyar kacal za ki bamu Honey yayi wanka yanzu zamu fito..."
"Ba komai ƙanwata, a fito lafiya. Ki kular min da Sweetat da kyau fa."
Duk su ukun dariya suka yi, ta ja hannun mijin suka nufi ɓangarensa.
Kamar yadda ta alƙarwarta basu daɗe a ciki ba, yana gama shiryawa suka fito falo don cin abinci. Har lokacin tana zaune a inda suka barta, da dariya ta tare su suka nufi dining gaba daya.
"Yau dai Honey mu za mu ciyar da kai gaskiya, hannunka ya huta. Ɗan gata kawai ɗari bisa ɗari. Kasan fa sosai muke ji da kai."
"Haba Honey duk yadda kuke ji da ni ai bai kai yadda nake ji da ku ba. Bari kuma ki gani."
Abincin ya ɗiba a cokali ya nufi bakinta gadan-gadan.
Sai da ta buɗe baki har tana wani lumshe ido kawai ya kautar da cokalin ya kai bakinsa ya cinye abincin. Dariyar da taji sun fashe da shi yasa ta buɗe idanunta, ko da ta ankare da abinda yake faruwa kawai sai ta sa kukan shagwaɓa tana cewa ita bata yarda ba.
"Wannan wayau ne Honey. Allah wannan wayau ne. Ban yadda ba ni dai."
"Ƙyale shi kinji ƙanwata. Buɗe baki ni in baki"
Ko da ta zuba mata abincin sai ta fara dariya tana mishi gwalo, ita ma ta ɗiba a cokali ta ba Surayyan, shi ma ya ɗiba ya ba Rabi sannan ya ba Surayya. Haka suka ci abincin zukatansu cike da farin ciki har suka gama. Falo suka koma suna hira suna kallon T.v
"Sweetat tun shekaran jiya baka kira mana ƙanwarmu ba, yau dai pls ka kira ta mu gaisa."
Babu musu ya ɗaga wayar ya kira ta, daga can ringing biyu ta ɗauka da sauri, daman tana cikin kewarshi.
"Sevgilim"
"Tatlim ga Auntys ɗinki ku gaisa."
Bai jira ta amsa shi ba ya miƙawa Surayya wayar, a mutunce suka gaisa sannan ta ba Rabi wayar ita ma suka gaisa, aka mika mishi wayar a karshe.
Hannu ya ɗaga musu alamun yana zuwa ya nufi ɓangarenshi wayar na maƙale a kunnenshi,
"Babe gaskiya na fara gajiya. Haba sati biyu yau fa. Har yau shirin me kuke yi ne?"
"Yi hakuri Tatlim. I love you..."
Katse wayar yayi ranshi a ɓace, sai