Showing 3001 words to 6000 words out of 98260 words
mike a zuciye tana kallonsa, fuskarta a daure murtuk. Tofar da miyau mai hade da jini tayi ta sake maida idanunta kansa cikin tsananin fushi.
"Zidane ! Live me alone. Ina ruwanka da rayuwata? Me yasa ba za ka barni in sha iska mai sanyi ba? Me mijina yayi muku da za ku kashe shi? Idan bakwa son zamanmu a kauyen nan ku kore mu mana za mu tafi ba dawowa me yasa zaku kashe shi? Are we no brother and sister? Ko Daddy ba mahaifina bane? Idan..."
Wani 6arin makauniya ya kai mata a ciki da yasa dole ta hadiye sauran maganganun, durkushewa tayi a gurin ta kwalla wani mahaukacin k'ara dan tsananin azaban da taji, nan da nan numfashinta ya fara fita sama-sama dole ta kwanta a kasa tana gurmususu.
A wulakance cike da rashin tausayi ya ja ta kamar kayan wanki ya watsar da ita a gaban k'onannen gidan da har lokacin yana ci da wuta, kanta ya bugu da wani dutse, ta saki wani marayan k'ara a hankali kamar wacce aka shak'e wa mak'ogwaro.
Tsugunawa yayi a kusa da ita yana kyalkyala dariya, ya damk'i gashin kanta da k'arfi ya daga ta zaune sukai ido da ido, ya watsa mata wani mummunar kallo kamar zai cinye ta danye.
Saukar da kwayar idanunta kasa tayi a hankali tana ci gaba da maimaita kalmar shahadar da Musty ya biya mata kafin rasuwarsa, irin azabar da take ji a jikinta da zuciyarta ta tabbatar yau zata bi Mustafa, zata je inda ya je...
Katse mata tunani yayi ya fara magana da turanci, (Duk al'ummar kauyen Christian ne, duk da hausawa suna shiga kauyen sosai dan yin cinikayya da sarin kayan abinci hausa bai zauna a bakinshi ba kamar yadda ya zauna a bakin Rebecca, dan ita ta fita daga kauyen, tayi rayuwa a mabanbantan garuruwa na hausawa) fuskarsa na baiyana tsananin tsanar da yake mata.
"Rebecca my sister, let me tell u something, I hate u. Do you know why? Because of your mother. She is a witch, ita ta cinye grandfather, shi yasa aka k'ona ta da ranta a gaban duk mutanen kauyen nan, wannan tsanar da aka yi mata shi ne ya koma kanki.(Rebecca 'yaruwata, bari in fada miki wani abu, na tsane ki. Kin san dalili? Saboda mahaifiyarki. Ita mayya ce.)"
A zafafe ta dago idanunta tana kallonshi, dukda bata san mahaifiyarta ba kuma bata rayu da ita ba ta tsani duk wani kalma na aibatawa a gare ta, duk mutanen kauyen in dai za su fadi magana a kan mahaifiyarta mummunan kalma suke fada amma ba'a ta6a fada mata mai muni da zafin wannan ba, wani karfi da ya ziyarci jikinta yasa ta daga hannu ta zabga mishi wani kakkarfar mari, ta k'ara da tofa mishi miyan bakinta mai hade da jini a mummunar fuskarsa.
"How dare you da zaka fadi mummunar kalma a kan Mum dina?"
Ta tambaye shi cikin tsawa kamar ba ita ne take shesshekar mutuwa ba.
Wani mugun murmushi yayi da ta rasa gane ma'anarsa. Da yake kakkarfa ne marin da tayi mishi girgijewa yayi kawai ya kakka6e, abinda ya fi 6ata mishi rai miyan da ta tofa mishi, faskeken hannunshi yasa ya shafo miyan ya kalla yayi dariya, sai ya goge a jikin burgujejen gajeren wandon da yake sanye a jikinshi.
"Zidane we are westing our time, kawai ka bamu guri mu daddatsa ta"
Daya daga cikinsu ya fada cikin fushi.
"Karka damu Markus, akwai abinda nake jira ne. Lokacin da na ganta dazu na ganta da katon cikin da ta kusa haihuwa, yanzu kuma ka ga babu cikin, thats mean ta haihu kenan.
Ina kika kai Babyn? Bai kamata ki mutu ki barshi ba"
Ya karasa maganar bayan ya damki gashin kanta ya fincika da k'arfi.
"Ahhhh !"
Ta fada cikin kuka ta rike hannunsa da ya rike gashin da hannayenta duk biyu.
Ya sake kwashewa da dariya, ya kalle ta yana cije gefen bakinsa, cikin tsawa ya tambaye ta.
"Ina kika kai Babyn?"
"He is inside, yay... Yay... Yana ciki tare da babansa"
Ta amsa cikin kuka, muryarta na rawa.
"Karya kike yi Rebecca, Markus kuyi searching zagayen nan na tabbata duk inda ta kaishi bata yi nisa da shi ba. So nake in cire liver na shi inci a gaban Rebecca sannan in kashe ta tabi shegen mijinta"
Yana gama fadin haka ya wancakalar da ita gefe d'aya ya bada umarnin sauran su d'aure ta, nan da nan kuwa suka yi mata wani mugun dauri mai kama da na huhun goro a jikin wani bishiyan mangwaro da yake nesa da gidan kad'an.
Sama da mintuna goma sha biyar suna dube-dube amma basu samu jinjiran ba, dole suka koma suka sanar da Zidane basu samu yaron ba, kila da gaske take yi yaron yana ciki tare da Babansa.
Haushi da takaici yasa ya ringa gaura mata mari kamar Allah ya aiko shi, nan da nan ya hada mata jini da majina, tana langa6e kawai a jikin bishiyan tana kallonshi tana jiran ajalinta ya sauka, numfashinta ma dakyar yake fita.
Galan din da suka ciko da fetur ya dauko ya fara zazzaga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa sauran sassan jikinta, yana yi yana kyalkyala dariya kamar mahaukaci.
"Zidane !!!"
Aka kwalla mishi kira daga can nesa a lokacin da yake niyyar kyasta mata ashana, idanunta a lumshe tana kalmar shahada a zuciyarta.
Da mamaki yake kallon wanda ya kwala mishi kiran har ya karasa kusa da su.
"Jocob ?! Mene ya faru?"
Wanda aka kira da Jocob yana ta sauke numfarfashi sauri-sauri saboda gudun da ya yi, ya nuna Rebecca da yatsarsa manuniya.
"Pastor ya ce karku kashe ta, idan kun kashe ta akwai matsala, spirit na Alheri yana yawo a kauyen nan, in dai kun kashe Rebecca spirit din Alheri zai kashe kowa a kauyen nan."
Wani dunkulallen bakin ciki ne ya kawo mishi naushi a kahon zuci, ya so kwarai a ce yau ya shafe babin Rebecca daga doron k'asa. Da ya kalle ta a zuciye sai yaga tana mishi wani murmushi mai kama da na rainin hankali. Ta motsa bakinta a hankali ta ce
*"I'm a Muslim"*
Tsabar rud'ani yasa ya sandare a tsaye a gurin, sauran abokan tafiyarsa kuwa suka fara kwance Rebecca dan cika umarnin Pastor Nuhu.
[12/12, 11:58 PM] Bilhaqqi: *BILHAQQI*
**** ***** ****
Ya kalle ta da wani irin tattausan murmushi, da idanu mai cike da rahama irin wanda tun da aka haife ta bai ta6a kallonta da irinsa ba.
"Rebecca yarinya na"
Ya kira ta a tausashe, bai jira ta amsa ba ya cigaba da jero mata dad'ad'an tausasan kalamai kamar yadda Pastor ya umarce shi.
"Rebecca ! i'm your father. Duk da kike gani kamar mun tsane ki muna son ki sosai, addinin cristianity shi ne asalin addininmu tun iyaye da kakanni. Kina ganin kin kyauta kenan ki bar addininki ki koma wani addini na k'arya? Addininmu shi ne addinin gaskiya, addinin da idan kin mutu Yeso zai daukake ki ki shiga paradise, ki hadu da mahaifiyarki Alheri.
I'm sure ko Alheri yanzu haka da zaki ganta a kabarinta tana fushi da ke, saboda kin bar addininki na cristianity. Ki tuba, ki dawo cikin addininki, ki roki Almasihu ya yafe miki laifukan da kika yi mishi a baya, ki gina sabuwar rayuwa a gaba, Idan kika yi haka mu kuma zamu nuna miki soyayya, za mu baki mukami mai girma a church.
Zidane ma yayi alkawari zai karbe ki as a luvly Sister, zai ji da ke, zai baki kulawa a duk inda kike a kauyen nan.
Pls my dear, ki zàma yarinya mai biyayya, kar kibi zugan wancan shegen mijin naki da ya dad'e da mutuwa, daman bai dace da aurenki ba, he is a muslim, yana kan addinin 6ata ne, shiyasa ko gurin mutuwarsa yayi mummunan mutuwa. Ke kuwa da Yeso yake sonki da shiriya kinga ya tserar da ke, ki dawo kan addinin gaskiya ki bi maganganun littafi mai tsarki."
Yana kaiwa nan a maganarsa yayi shiru yana nazarin yanayinta, zuciyarsa cike da fatan ta amince kuma ta yarda tayi duk abinda ya umarceta. Dukda ba kaunarta yake yi ba sam ba ya fata a ce ta sanadin 'yarshi aka samu gur6acewa a cikin tarihinsu na iyaye da kakanni, dan ko a garin suna daga cikin familyn da aka sansu da tsananin riko da addinin kirista.
A hankali ta dago manyan idanunta da sukai luhu-luhu saboda kuka da tsananin wahala ta kalle shi, ya sake sakar mata wani tattausan murmushi da wafcecen bakinsa.
Ta maida idanunta kan Zidane da yake tsaye a bayan mahaifinsa, idanunsa cike da matsanancin tsanan da yake mata amma yana kokarin boyewa. Fuskarsa dauke da murmushi mai hade da dariya. Gaftara-gaftaran hakoransa suka baiyana a waje kamar zai cinye ta d'anye, amma shi ala dole dariya yake mata.
Ta saukar da idanunta sai suka sauka a kan farantin abincin da suka ajiye mata, farar shinkafa ce k'al da miyan stew, a gefe guda kuma aka zuba mata hadin ganyayyaki da tsokokin nama soyayye manya-manya
"Idan kika bi abinda na ce miki irin wannan delicious din i promise har karshen rayuwarki shi zaki dinga ci..."
"Daddy !"
Ta katse shi cikin zafin rai, runtse ido tayi dan jin wani azababben zafi da ya ziyarci kumburarren bakinta saboda maganar da ta yi. Saida ta d'an numfasa bakin ya rage zafi ta daga kai ta kalle shi ido cikin ido, fuskarshi na baiyana matsanancin fargabar abinda zai fito daga bakinta, ita kuma idanunta ciccike da hawaye.
"Idan zaku bani duk abinda kuke da shi bazan bar musulunci ba. Ni musulma ce, daga yau sunana ba Rebecca ba, sunana Khadeeja Mustapha..."
Wani gigitaccen tsawa da ya daka mata dole ta hadiye sauran maganar a cikinta, ya daga hannu zai zabga mata mari ya ji an rike hannunsa. Cikin fushi da tsananin mamaki ya juya dan ganin mai karfin halin da ya hana shi tattaka Rebecca, sai yayi ido biyu da Pastor Nuhu.
"Luka calm down. Ka manta abinda na fada maka?"
Bai jira ya amsa ba ya ja daya daga cikin kujerar robobin da suka yi wa falon kawanya ya matsa kusa da Rebecca ya zauna.
"Rebecca, dukda mahaifiyarki mayya ce har ta mutu bata bar addininta na Christianity ba. Kin amince zaki dawo cikin addininki?"
Da kai ta amsa mishi alamun a'a, idanunta ciccike da hawaye.
"Ok ! Thats good. Baza mu kashe ki ba. But zaki yi rayuwa ne tsakanin mutuwa da rayuwa har zuwa karshen rayuwarki. Dakin duhu da yake cikin church a nan zaki zauna har karshen rayuwarki. Kullum za mu baki abinci sau daya dan kar yunwa ta kashe ki. But duk lokacin da kika ji a ranki zaki iya dawowa addinjnki na Christianity za mu baki 'yanci."
Daga haka bai sake ce mata komai ba garadan samari suka cicci6eta kamar kayan wanki suka kaita inda ya basu umarni.
Zuciyar Daddy Luka da Zidane cike da matsanancin bakin ciki, sun so kwarai su samu damar karar da rayuwarta a wannan lokacin.
*****
Sai da ta kalle ta da kyau ta tabbatar tana kallonta, ta yi wani murmushi mai kama da na mugunta, ta mike da tak'ama tinkis tinkis ta isa gaban kulolin abincin.
Faranti ta dauka da luddayin diban abincin ta fara bude kulolin abincin, duk da tashin k'amshin da miyar taushen yake yi yamutsa fuska ta fara yi kamar ta shak'i wari. Wainar da yayi kyau shar kuma yayi tashi su6u su6u ta dauki guda biyu kacal ta zuba a farantin, maimakon ta dibi miyar kawai sai ta d'auki jug din tangaran da yake cike da had'in sassanyar jinja, kamar zata tsiyaya a kofi kawai sai ta saki Jug din da gangar ya fadi a k'asa. Nan take kuwa ya tarwatse.
Ta saki wani k'ayataccen murmushi tana kallonta, ta yamutsa baki da fuska ta ce
"Sai ki dau na annabawa, wannan ma ya bi ayarin 'yan uwansa. Ya riga mu gidan gaskiya..."
"Kan uban can! Uban kuturu ma yayi kadan ballantana na makaho, idan kin isa Allah ya tsine min."
Kamar kububuwa ta tura kujeran teburin cin abincin da take zaune ta mike a fusace ta zagaya ta gurinta. Cikin tsananin masifa ta cigaba da magana bakinta har yana tartsatsin miyau, ko tsoron ta taka fasasshen kwalbar Jug din bata yi.
"Ke Suraiya bari in fada miki, shiru-shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne. Na ga alamar sai mun goge raini tsakanina da ke a gidannan, ki bar gani na haka-haka idan zamu kwana mu yini muna ba hammata iska ko kwarzane baki isa ki yi min ba. Wallahi ko ki biya ni dubu biyar din jug dina ko inyi miki magagan dukan kawo wuk'a a gidan nan, in daki banza a banza in daki kud'i na..."
"Ni... Wace ni in had'a jiki da kishiya? Baki da labarin hakan tsiya yake janyo wa? Ke dai da kike matsiyaciya kije can ki nemi dai-dai da ke amma ni na fi karfinki."
Ta fada hankalinta a kwance, sai karkad'e-karkad'en kafad'u take yi kamar tana ji fitsari.
Haushi, takaici, wani dunkulallen bakin ciki da suka hade guri daya suka kawo mata naushi a kahon zuci yasa tayi kukan kura ta mika hannu biyu da nufin ta cakumo Surayyan sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Da mugun sauri ta ja baya, hakan da tayi yasa ta taka wani fasasshen kwalba dukda akwai tattausan silifas a kafafunta saida ya huda takalmin ya ratsa kafafunta.
"Ahhhhh !"
Ta fada cikin jin zafi ta durkushe a gurin tana kokarin kamo kafar ta duba. Ba tare da ta lura ba ta sake dafa hannunta daya a kan wani kwalbar, kwalla kara ta yi ta dago a zuciye ta kalle ta.
"Rabi baki da hankali ko? kina so ki hallakani ne?"
kafin ta amsa mata ta ji shigowar motar mai gidan, kwafa tayi tana murmushin jin zafi,
"Zaki gani, tabbas zaki biya wannan"
Tana jin ya kashe motar ta bude baki da matsanancin sauri ta kwallah ihu mai tsananin karan da yake barazanar fasa dodon kunne.
Ita kuwa Rabi sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, dukda ta san Surayya gwana ce gurin makirci bata zaci abin nata ya kai haka ba, da ta kalli fuskarta sai taga har ta jika shi da ruwan hawaye.
A daidai lokacin ya sanyo kai cikin falon da sassarfa bakinshi dauke da sallama, hankalinshi yana kan Surayya da take durkushe a kasa tana kuka, ko da Rabi ta nufe shi tana kwarkwasa da yi mishi sannu da zuwa sakar mata jaka da ledojin hannunshi kawai yayi bai kalle ta ba ya nufi Surayya.
"Menene? me ya faru?"
Yana ganin fasassun kwalaben yaja da baya da sauri
"Subhanallahi, me ya faru haka?"
Yayi tambayar yana kallon Rabi da manyan idanunsa masu cike da tuhuma.
Ranta a ɓace, fuskarta a cunkushe, zuciyarta a ƙuntace da irin wannan cin mutuncin da yake gwada mata a gaban kishiyarta. Ta dai daure ta cije tayi ƙoƙarin ɓoye ɓacin ranta, ta buɗe baki zata yi magana Surayya ta riga ta fara magana cikin kuka
"Sweetat wai fa kawai dan na ture mata jug ban sani ba ya fashe shi ne tace sai na biya ta. Na fara bata hakuri da gangar ta hankaɗa ni cikin fasassun kwalaben, ka ga har na huda ƙafa da tafin hannuna..."
Ta ƙara fashewa da kuka tana nuna mishi hannun da yake ta tsattsafar jini.
Mugun kallo ya watsa wa Rabi, a hankali cikin takatsantsan ya ƙarasa gurinta ya ɗaga ta tsaye, cikin hila ta langaɓe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa.
"Ki tabbatar kin gyara gurin nan kafin in kaita asibiti in dawo."
Bai ƙara kallonta ba yaja ta a hankali suka nufi dakinta, minti biyu tsakani suka fito yana riƙe da ita a kafaɗunsa a hankali suka nufi hanyar fita daga falon. Ita kuwa poster tayi tana kallonsu fuskarta cike da hawaye, zuciyarta sai lugude take yi kamar zata faso ta fito fili.
Sai da suka kusa fita daga falon ta waigo ta kashe mata ido ɗaya ta yi mata gwalo. Ta sake rukunkume shi tana faɗin
"Wash ! Sweetat zafi"
Nan ya sake tarairayota jikinsa yana jera mata sannu kaman zai ari baki.
Tana jin tashin motarsa ta ɗora hannu biyu a kai ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka, kamar mahaukaciya ta fara watsi da ƙananun kofunan da Surayya ta fasa jug dinsu.
**** **** ****
"Ke ! har kin isa ince ga abinda zanyi ki ce min ga abinda kike ga ya kamata inyi?"
Tayi mata tambayar cikin mamaki tare da zazzare mata idanu. Bata ba ta damar kare kanta ba ta ci gaba da zazzaga mata ruwan masifa tana hakimce akan kujera mazaunin mutum biyu ta dora kafa daya kan daya. Sai jijjiga kafar take yi alamun jira take yi a taɓa ta tayi bindiga.
"Ke wacece ? yaushe kika zo gidannan? to kashaidi na farko kuma na ƙarshe kar in sake yin magana a gidannan ki tsoma min zumɓutun bakinki, a gidannan da kika ganni zaman kaina nake yi. Ko Madam Mary bata isa ince ga abinda nake da ra'ayin yi ta hana ni ba balle ku ƙananun ƴan iska. Idan kunne ya ji rayuwarki ta tsira. Ina fatan kin fahimce ni?"
Da sauri ta dinga ɗaga kai alamar ta ji, da rawar murya ta dinga jera mata kalaman ban hakuri kamar me fadanci.
"Ki yi hakuri Bibi, Allah ya huci zuciyarki.