Showing 84001 words to 87000 words out of 98260 words

Chapter 29 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

219

Middle Ads

nan da Dr. Bilyaminu ya tabbatar mishi da cewa a ko wane lokaci za ta iya farfaɗowa. Amma har lokacin shiru kake ji, babu ma wani alamu na za ta farfaɗo.

Hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, ga noses sai shigowa suke suna tambayarshi bata farfaɗo ba? tun yana iya amsa musu da baki har ya koma sai dai ya ɗaga musu kai. Daga ƙarshe ma shiru yayi musu yayi tagumi ya zuba mata idanu.

Yana zaune ne a kan wani kujera gaf da gaf da gadon da take kwance. Ta rame ta yi fiyau a yini biyu kawai da faruwar komai. Sashin hannun Oga ne ɓaro-ɓaro a wuyanta, ita kaɗai ta san mugun azaban da ta sha a hannunshi kafin Allah ya kai su gurin su ceceta.

Hannunta da babu ƙarin ruwan ya kamo ya riƙe ya zubawa hannun ido, gefen gadon da take kwance ya raɓa ya zauna yana ƙara kallonta. Bisa ga mamakinshi sai ga hawaye shar daga idanunshi, kifa kanshi yayi a kan gadon gefen cikinta yana jan wani irin nishi sauri-sauri mai kama da shessheƙan kuka. Duk tunani da addu'arshi ya tattara ne ga roƙon kada Allah yasa ta mutu ta barshi ba tare da ya gwada mata lagwadar soyayyar da ya daɗe yana mata tanadi ba.

"Sev gilim..."
Ya ji ta kira sunanshi kamar a mafarki. Da sauri ya ɗaga kai yana kallonta idanunshi jajur, fuskarsa ƙarara bayyane da mugun tashin hankali.

Lura da yayi bakinta yana ɗan motsawa amma bata buɗe idanunta ba yasa ya matsa da kunnensa sosai kusa da bakinta. Ya ɗan matsa hannunta da ɗan ƙarfi yadda za ta ji a jikinta
"Tatlim ga ni kusa da ke! Me kike so uuumm?"

"Ina... son... ka...!"
Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa, jimlar kalaman suka fito a rarrabe kamar mai koyon magana.

"Nima ina son ki Tatlim. Dan Allah ki tashi kin ji? kar ki mutu ki barni kin ji? Ga Ummanmu can ita ma tun ɗazu take ta son ganinki..."

Buɗe ƙofar ɗakin da shigan Dr. Bilyaminu cikin ɗakin hankalinsa a tashe yasa shi ɗaga kanshi daga gurin fuskarta ya kalle shi, shi kuwa likitan ganin alamun ta farfaɗo yasa shi sauke ajiyar zuciya.
"Alhamdulillahi. Ai ni kira na suka yi wai har yanzu bata farfaɗo ba. Wallahi hankalina ya tashi Maheer..."

"Ni naga tashin hankali ba kai ba Dr. Alhamdulillahi dai tunda ta farfaɗo."

"Allah shi ne abin godiya."
Gurin ruwan da ake ƙara mata ya je ya fasa wani ruwan allura ya zuƙa a sirinji ya tsira a cikin ruwan.
"Lafiya in Allah ya yarda, za ta ƙara farfaɗewa yanzu. Sauƙi gaba ɗaya kuma ka san dai sai a hankali. Bari in koma gida, sai zuwa dare. Daman rashin farfaɗowar da suka ce min bata yi ba shi ya dawo da ni yanzu."
Sallama suka yi likitan ya fice daga ɗakin, shi kuma ya koma bakin gadon ya zauna a kusa da ita.

Cikin hukuncin Allah kuwa minti ashirin tsakani ta farko sosai, amma a hankali take iya magana. Sosai take mishi kuka saman gurin kafaɗanta na dama yana mata ciwo, da ta yi yunƙurin taɓawa ma sai taji kamar babban ciwo ne a gurin.
"Ki yi haƙuri Babe, ciwo ne da nasa aka ji miki jiya yau kuma na sa aka ƙara farke ɗinkin. Baki yi mamakin yadda aka yi muka bibiye ki har gurin su Oga ba?"

Kallonshi ta yi da mamaki, sai yanzu ma wannan tunanin ya faɗo mata a ranta, yunƙurawa tayi za ta tashi zaune da sauri ta koma ta kwanta tana runtse ido.

"Sannu Tatlim!"
Ya faɗa mata a tausashe, ita kuma ta gyaɗa kai tana yunƙurin yin murmushi.

Tarairayarta yayi a jikinsa yasa fuloli biyu a bayanta sannan ya jinginata yadda baza ta ji zafin sosai ba.
"Kinga shekaran jiya tun kafin mu dawo daga bauchi na yi ma Lukman bayanin duk irin abubuwan da suke faruwa, shi kuma ya sama mana mafitar da na amince da shi. Jiya da na baki lemon nan kika sha maganin bacci ne a ciki, da wannan daman muka yi amfani Lukman ya ba Dr. Bilyamin wani ɗan ƙaramin na'ura ya tsaga kafadarki yasa a ciki sannan ya maida gurin ya ɗinke. Allurai yayi miki guda biyu da ko da kin tashi sosai zai kashe miki zafin ciwon.

Sai kuma muka yi sa'a ma ko da kika farka tashin hankalin da kike ciki na son ki miƙa kanki gurin su Madam Mary don ki cece Mahaifiyarki bai barki kin ankare da wani ciwo a jikinki ba.

Amfanin wanna na'urar shi ne duk inda kika za a iya gano wa, sannan kuma duk maganganun da kike yi ke da wasu za a iya jin duk abinda kuke cewa. Sosai munji tsoro da muka ji wasu suna cewa za a caje ki don ganin ko kin taho da wani abu a jikinki.

Cikin hukuncin Allah kuma masu cajewar har suka gama basu yiwa Madam maganar ciwo da ɗinkin da ke kafaɗarki ba. Da wannan damar muka yi amfani gurin bin diddiginki da kai miki ɗauki."

Ƙuri tayi masa da idanunta, fuskanta ɗauke da murmushi, zuciyarta cike da jin daɗin wannan tsananin ƙaunar da mijinta yake mata. Ta sakar mishi murmushi kawai, wani godiyar ya fi ƙarfin baki ya baiyana sai dai a bar kaza cikin gashinta.
"Ina ita mahaifiyar tawa? ko su... su kashe..."

"Tana wancan ɗakin tare da Ummee, ita ma a galabaice aka ɗaukota a inda suka ɓoye ta. Amma dai yanzu sosai jikinta da sauƙi, tun ɗazu ma take ta tambayar ina kike..."

"Da gaske? shi ne baka kai ni gurinta ba tun ɗazu?"
Tayi rau-rau da idanu kamar za ta fashe da kuka, nan fa jikinta ya fara rawa tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon don zuwa gurin mahaifiyarta.

Abin dariya abin tausayi ƙarfen ƙarin ruwan ya sunguma da hannu ɗaya ya tallafe ta a kafaɗarsa na dama bayan ya saka mata hijabi suka fice daga ɗakin don zuwa ɗakin da aka kwantar da Rebeccah. A kofar ɗakin suka ci karo da Luƙman shi kuma yana ƙoƙarin buɗe ƙofar, baki buɗe yake kallonsu da mamaki a fuskarsa ya ce
"Ina zuwa haka?"

"Ta matsa ita sai na kaita ta ga Mum ɗinta."

"To madallah! kawo ƙarfen ƙarin ruwan in riƙe maka"
Ba musu kuwa ya mika mishi. Duk inda suka wuce haka ake binsu da kallon mamaki baki buɗe har suka isa ɗakin Rebeccah...


******* ********

A wannan ranar, a wannan lokacin, a wannan tsakankanin, duk wadda ya ga yadda UWA da ƳAR suka yi da haɗuwar juna bayan tsawon shekaru goma sha tara da rabuwarsu dole mai imani da tausayi ya zubda hawaye.

Gaba-ɗaya jikkunansu rawa yake yi, bakunansu kyarma yake, hawayen idanunsu bulbulowa suke yi, da suka kasa cewa komai ga junansu sai shafa fuskokin juna suke yi don jin da gaske wai yau Allah ya ƙaddara haɗuwarsu ne??? kamar haɗin baki sai suka fara sharce wa juna hawaye, a gare su gaba ɗaya haɗuwarsu ta kasance abu ne da basu taɓa tsammani ba.

Ummee da take gefe sai sharce hawayen tausayinsu take yi, Lukman da Maheer kam ficewa suka yi daga ɗakin saboda raunin da zukatansu ta fara yi, a ƙarshe Ummee ma bin bayansu ta yi.

Kaman jira take yi a fice a basu guri ta buɗe bakinta a raunane tana kuka tana dariya haɗe da tattaɓa jikinta da yatsa, ta fara magana da turanci
"Da gaske ke ce? Babyn da na haifa a cikina na kaiwa Mama Vero? ina kika shige duk tsawon wannan lokacin???"

Bilhaƙƙi dai ba baka sai kunne, hawaye sunki tsayawa ga murmushi ya ƙi ɗaukewa daga fuskarta, ƙarshe ma kwanciya tayi a jikin mahaifiyar tana ta sassauke ajiyar zuciya masu sanyi, mintuna kaɗan wani daddaɗan barci da tun da take bata taɓa yin irinsa ba ya kwashe ta a jikin Inna uwa mai bada mama😂🥰🥰

A haka su Maheer suka koma ciki suka same su, duk sai suka yi murmushi. Shi kuwa Maheer har da wani ɗan sosa kai alamun ya ji kunya.

"Kun ganta ko? Haka kawai ta yi barci."
Rebeccah ta faɗa tana kallonsu da murmushi, hannunta na gefen fuskar Bilhaƙƙi sai shafa mata kumatu take yi kamar wata baby.


******* *******


Ta kasa zaune ta kasa tsaye, tun da duhun dare ya fara shiga sai safa da marwa take yi tana jiran ganin ta inda su Jakadiya za su ɓullo.

Jefi-jefi ƙirjinta yake bugawa ɗas! ɗas!! kamar alamun wani mummunan abu yana shirin faruwa da ita. Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma, hannu biyu ta ɗaga sama idanunta ciccike da hawaye take roƙon Allah ya tsare ta da sharrin Mai wutsiya, babban burinta da fatanta bai wuce Na shuri ya samu shiga lafiya ta karɓi magunguna ba tare da wani mummunan abu ya sake faruwa da ita ba.

Ƙarar buɗe ƙofar yasa ta juya a sukwane da burin haɗa idanu da Jakadiya, saɓanin ita sai ta haɗa idanu da ɗaya daga cikin bayinta. Kafin baiwar ta ce komai ta daka mata wani gigitaccen tsawa
"Lafiya? Ban ce kar wacce ta shigo min nan idan ba Jakadiya ba?"

"Afuwan Ranki ya daɗe. Tuba nake. Daman Takawa ne ya aiko yana son ganinki da gaggawa a ƙaramin falon ganawa."
Baiwar ta faɗi haka cikin rawan jiki da rawan murya.

Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi! Ta zazzare ido a tsorace.
"Takawa kuma? Me zai sa Takawa ya neme ni a darennan?"

"E Ranki ya daɗe, nima ban sani ba."

Tsananin ruɗewa yasa bata san a fili tayi maganar ba sai da ta ji baiwar ta amsa mata.

Alkyabbarta ta janyo ta sanya a jikinta, da muryar dakewa tana ƙoƙarin daidaita nutsuwarta ta ce da Baiwar
"Kar a bar kowa ya shigo min nan in dai ba Jakadiya da ƴar'uwarta ba. Ku faɗawa Jakadiyar na je gurin Mai martaba yanzu zan dawo."

"To Ranki ya daɗe, an gama.!"

"Tana tafe tana saƙe-saƙe har ta isa kusa da ɓangaren Uwar Soro dan a yi mata ison shiga ciki, irin kallon da ta ga tana bin ta da shi da irin amsar da ta bata ne ya ƙara kaɗa mata ƴaƴan hanji, ta tabbatar ba lafiya ba.
"Hakima mundiya ai yau ke kam ba kya buƙatar wani iso, ki shiga kawai Takawa yana can yana jiran isarki."

A ɗarare take har ta shiga cikin falon bayan anyi mata izinin shiga ciki. Gabanta ya yanke yayi wani mugun faɗuwa da ta ga Takawa da Liman a zaune, fuskokinsu duk babu walwala.

Yadda suka amsa mata gaisuwa wani sasakai yasa jikinta ya gama yin sanyi gaba-ɗaya, kawai sai ta sadda kai ƙasa cike da shahadar ƙuda.

"Safra'u! A gidannan muna sane da abinda kika daɗe kina aikatawa fa, da kuma abinda kike yunƙurin aikatawa a yanzu. Kina ga har yanzu bai kamata ki nutsu ki san Annabi ya faku ba duk bayan ababen da kika aikata marassa daɗi da kuma abubuwan da suka biyo baya?"

Ɗif ta ɗauke wuta tayi suman wucin gadi. Shi ke nan! Ta faru ta ƙare wai anyi wa mai dami ɗaya sata. Daga jin irin maganganun da Takawa yake yi ta san Mai wutsiya ta ƙarasa lalata komai.

Da Takawa ya ji shirun yayi yawa ranshi a ɓace ya ci gaba da magana
"Kinyi shiru baki ce komai ba Safra'u? ko da yake ba musu muka kira ki muyi da ke ba. Muna da ƙwararan hujja a hannunmu kan abinda kika daɗe kina aikatawa.

Safra'u bazan hana ki ba, sannan bazan ce ki yi hakuri ki rungumi komai a yadda Allah ya ƙaddara miki ba. Amma ina so ki tuna da wani abu guda ɗaya.

A cikin masarautar nan mun ɗaukaka ki, mun gwada miki ƙauna mai yawa. Mun baki duk wani girma a matsayinki ta matar fari a gare mu. Mun mallaka miki mulki da yin duk abinda kike so dukda a wasu lokutan munsan kuskure kike aikatawa. Bamu taɓa dakatar da ke ko mu kunyata ki a cikin mutane ba.

Duk wannan gatan da muke gwada miki ashe kin daɗe kina burin tozarta mu da son ganin bayanmu? Safara'u mulki hauka ne da za ki dinga gwada son zuciya da zalunci irin wannan? Ko kinsan mun san ke kike da alhakin ɓatan El-mustapha daga masarautannan? Ashe ke ce da alhakin sa wa a hana Safiyya haihuwa duk tsawon lokacinnan?Ashe duk munanan abubuwan da suke ta faruwa da mu ke ce a bayan aikata su?"
Ya haɗiye wani zazzafan miyau idanunshi a ƙanƙance, ya ci gaba da magana ranshi na ƙuna.

Daman kunsan mai haƙuri bai iya fushi ba
"A bayan duk abubuwannan nan kuma Allah ya nuna miki iyakarki ta hanyar kawo ƙarshen duk wani mummunan abu da kika taɓa aikatawa a baya shi ne kike ƙoƙarin sake aikata wani mummunan abun? To bari in faɗa miki wata magana da baki sani ba, Jakadiya, bokan da kika tura ta taho da shi, ƙaninki Chiroma da ya kasance abokin cin mushenki duk suna nan a tsare a hannunmu. Kici gaba da yin abinda kika ga shi ne miki dai-dai kuma shi zai sama miki ci gaba Safra'u. Ki ci gaba da yi!Allah yana ji kuma yana gani, shi zai ci gaba da kare mu daga duk wani mummunan jifa da sharri da kike nufinmu da shi.
A yanzu arzikin Mal Liman kika ci da yake da matsayin kamar mahaifi a gare ki, a karo na gaba muddin kika bari muka sake karon batta wallahi za ki sha mamakin irin mummunan matakin da za mu ɗauka a kanki."

Yana gama faɗin maganganun da suke cikinshi ya gyara kishingiɗa idanunsa a runtse, sai jan inna lillahi yake yi saboda tsananin ɓacin ran da zuciyarsa take ciki.

Daga nan Liman ya fara magana shi ma ransa a ɓace, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba saboda ɓacin rai. Ya rantse mata da Allah wallahi muddin ta sake aikata wani abu na son zuciya ko ɗan ƙiris ne a masarautar nan shi da kanshi zayyi tattaki har can masarautarsu ya faɗawa Mahaifinta duk abinda take aikatawa.

Daga ƙarshe kuma ya ɓuge da yi mata nasiha tare da nusar da ita muhimmancin yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau.

Ita dai Fulani Taka kuka da majina kawai ta ke sharɓa tana gogewa da gefen alkyabbar jikinta, ta ji kunya ƙwarai, kunya ba kaɗan ba. Da wasa bata taɓa tsammanin asirinta zai iya mummunan tonuwa a cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka ba. Tsamo-tsamo tayi a gabansu kamar kazar da aka sheƙawa ruwan zafi.

Daga ƙarshe cikin tsawa da murya mai cike da tozarci da muzantawa Takawa ya ce ta ɓace masa da gani. Kuma ya kafa mata sharaɗin kar ta kuskura ya sake ganin gilmawarta a idanunsa matuƙar ba shi ne ya neme ta ba. Duk abinda za ta yi ta tsaya a can iya sashenta.

Bata san yadda aka yi ta kai kanta ɓangarenta ba, kawai tsintar kanta tayi a turakarta, da mugun sauri ta danne ƙofar ta kulle da bayanta, nan ta zube a gurin tana sharɓan kuka kamar wata sabuwar kamu.

Tattausan kalamai na rarrashi da ban baki Mal Liman ya ƙara faɗawa Mai martaba, sannan yayi mishi sallama shi ma ya fice daga falon ya nufi gidansa.

Shiru Takawa yayi yana tunani, sai mamaki yake yi na yadda yayi saken da Safra'u ta daɗe tana cin karenta babu babbaka ba tare da saninshi ba. Ko jiya Allah ne yasa zai san abinda ke faruwa ta hanya Baffa Ilyassa'u (Dan'uwan Baffa Yalleru).

'Shi ya je har fada ya nemi ganawa da shi bayan ya sanar da ko shi waye. A wannan ganawar ne fa ya faɗa mishi duk munanan abubuwan da suke faruwa Uwargidansa ke da alhakin aikata su, da taimakon Jakadiyarshi, da kuma ƙaninta Chiroma. Yace mishi yasa idanu sosai dan har lokacin bata haƙura ba. Sai kuma ya kawo wasu magunguna ya bashi ya faɗa mishi yadda zaiy amfani da su shi da iyalansa gaba daya. Ya ƙara da cewa in dai suka yi amfani da maganin dai-dai kamar yadda ya ce in Allah ya yarda ba dai mutum ba sai dai Allah.

Da wannan bayanin yayi amfani yasa aka titsiye Jakadiya da Chiroma, ya rantse da Allah idan basu faɗa mishi gaskiya ba zai sa Hauni ya tsire su a gaban jama'a. Tsoron mutuwa yasa cikin kuka da matsanancin tashin hankali duk suka warware mishi tuggun da suka daɗe suna ƙullawa a tsakaninsu.'


******* *******

Ido waje yake kallonta bayan ta gama basu labarin tarihin ko ita wacece. Ya nuna ta da yatsarsa manuniya bakinshi na rawa
"Da gaske kike yi? ke ce Rebeccah matar Mustapha? kuma wannan ita ce Bilhaƙƙin da ya barki da ita tun tana jaririya?"

Gyaɗa kai ta yi tana mamaki, ita ma sai jikinta ya fara tsuma bayan ta yi tunanin ko dai ya san Mustapha ne.
"Eh! wallahi da gaske nake yi. Babu ƙarya ko ɗaya a cikin labarin da na baku."

Gemai-gemai da shi sai ga hawaye sun zubo masa shar! nan yasa gwuiwoyinshi a ƙasa yana sujudush-shukur.

Iyalanshi dai sai binshi da kallon mamaki suke yi har ya ɗago daga sujudar. Hannun Bilhaƙƙi ya ja ta koma kusa da shi
"Ashe shi yasa tun da na fara ganinki nake jin tsananin ƙaunarki kamar ƴar da na haifa a cikina? ke ƴata ce Bilhaƙƙi. Da gaske ke ƴata ce ta tashin alƙiyama. Mahaifiyata Hajja matar wazirin Sarkin Maru ita ce tasha nono ta sake wa mahaifiyar Mustapha Inna Safiyyah matar sarkin Bauchi da muka je gurinta da ke kwanakin baya."
Cikin rawan jiki da tsuma ya shige turakarsa ya ɗauko wasu tsaffin hotuna guda uku, Bilhaƙƙi ya miƙawa ɗaya kafin ta amsa da sauri Rebeccah ta fisge

"Wannan ɗan yaron da yake riƙe da hannuna shi ne Mustapha."

Hoton take ta kallo, ta gane Malam ne

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login