Showing 66001 words to 69000 words out of 98260 words

Chapter 23 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

216

Middle Ads

gidan sai mu fara zuwa asibiti a duba su ita da Salamatu."

Plate ɗin karatun Alƙur'ani ya kunna ya buɗe volume sosai sannan yayi addu'a ya zauna a mazaunin direba ya ja motar suka bar gurin.

Tunda ta zube a jikin Maheer bayan wasu daƙiƙu ta fara dawowa cikin hayyacinta. Ƙam ta rirriƙe shi zuciyarta cike da tsoro tana tunanin ababen da ta gaggani su ba a mafarki ba kuma ba a ido biyu ba.

A haka dai har Allah yasa suka isa cikin garin Bauchi lafiya. Za su nemi asibiti Mummy ta ce in dai don ita ne su wuce masauta kawai, ta ji sauƙi. Ita ma Bilhaƙƙi ta ce ba ta buƙatar wani likita, ta ji sauƙi gajiya kawai yake damunta. Don haka kai tsaye suka nufi masautar bauchi fadar mai martaba Sarki Abdulfatahi na biyu.


******* ********

Tana hakimce a kishingiɗe tana zuba mulki a tsakiyar bayi da kuyangin da suke mata hidima kawai ta ji ƙirjinta yayi wani mummunan bugawa. Rabon da tayi irin wannan faɗuwar gaban tun shekaru aru-aru da suka gabata, lokacin da Jakadiya ta zo mata da labarin Safiyya amaryar mai martaba tayi ɓatan wata. Masokiya ce mai tsini kamar mashi ta sake taso mata tun daga tsakiyar ƙwaƙwalwarta ta cake ta har zuwa kan babban ɗan yatsar ƙafarta.

Da saurin gaske ta runtse idanu saboda zafin jiki da na zuciya, nan wani zazzafan gumi ya fara antayo mata daga duk wani kafan gashi na jikinta, duk da A.C har uku ne suke fidda daddaɗan iska daga ko wace kusurwa na tafkeken falon. Ƙarin hutu da mulki kuma wasu bayi har biyu ne tsaye ƙiƙam a kanta kamar dogarai suna yi mata firfita da mafici irin na Sarakai.

Ko da ta yunƙura za ta miƙe zaune sai taji kamar an saka wani nannauyan dutse an danne ta.
'Tauraruwa mai wutsiya...'
Kamar walƙiya wannan tunanin ya gilma a duk wani lungu da saƙo na zuciyarta sai kuma ya ɓace ɓat! A tsorace ta fara waige-waige kamar za ta ganta a gabanta, sai kuma ta sauke idanunta a kan ɗaya daga cikin bayin da suke gurfane a gabanta suna bata daɗaɗan labarai don saka ta cikin nishaɗi.
"Laraba anyi wasu baƙi yanzu a masaurautar nan ne?"

"Baƙi kuma Ranki ya daɗe? Gaskiya ba ni da labarin haka. Sai dai kuma a fita a tattambaya ko wane sassa na gidan nan."

"A je ayi hakan. Daga nan a isarwa da Jakadiya Babba saƙon ina son ganinta da gaggawa."

"An gama Ranki ya daɗe."
Ta tashi da hanzari don cika umarni.

Ko da Jakadiya ta isa ta sake tabbatar mata lallai fa babu wasu baƙi da aka yi da magaribar farin nan.
"Lafiya kuwa Fulani Taka?"

Wani zazzafan huci ta ja ta fesar, ta kalli Jakadiyan a ɗimauce
"Me yasa kika tambaye ni haka Jakadiya?"

"Allah ya huci zuciyar Fulani ni ganinki nayi duk a ɗimauce kamar wacce ta haɗiyi kunama. Yo ba ma ni ba ai duk wanda ya kalle ki a yanayin da kike ciki yanzu kallo ɗaya zai fahimci kina cikin gaggarumin tashin hankali."

Gefe da gefe ta waiga ta tabbatar duk baƙin da ta sallama sun fice daga falon sannan ta sake gwada yunƙurawa ta tashi zaune karo na biyu. Wani abin mamaki gare ta yanzu duk nauyin nan babu lafiya kalau ta zauna. Ta yafito Jakadiyar ta matsa sosai kusa da ita, sai ta fara mata magana cikin raɗa muryarta baiyane da tashin hankali.
"Ta iso Jakadiya. Tauraruwa mai wutsiya ta iso. Wallahi na ji isowarta a jikina kamar yadda Na shuri ya tabbatar min zan ji da zarar ta iso. Amma nayi mamaki, rannan da kika ziyarce shi ba kin ce min ya ce zai hallaka ta kafin ta iso nan ba...?"

"A'a Ranki ya daɗe mantawa dai kika yi. Ce miki nayi ya ce zayyi duk mai yiwuwa ya dakatar ita kafin ta iso. Idan tayi taurin kai ma zai iya hallaka ta in ya samu dama a kanta. Yo tunda kika ji ta iso kila shi ma tafi ƙarfinsa ne. Yanzu dai sai ki san mai yiwuwa daman tun farko ya sanar da ke wannan yaƙin naki ne ke kaɗai."

Shiru suka yi duk su biyun, kowa da irin saƙa da tunanin da yake yi a ransa. Jakadiya ce ta sake katse shirun da cewa
"Ni kam Ranki ya daɗe wai tauraruwar nan mutum ce ko aljana?"

"Nima bani da masaniyar daga wane jinsin halittu ta fito Jakadiya. In kika bibiya ma dabba ce, dan na kwana biyu ina mafarkin gani a tsakiyar dokar jeje ina tiƙar dambe da wata ƙatuwar zakanya."
Ta ƙarasa maganar a sanyaye.

Laraba ce ta ƙwanƙwasa ƙofar ta jira aka bata izinin shiga sannan ta shiga ta zube a gaban duk su biyun.
"Ranki ya daɗe Raliya ce ta iso, ta ce a sanar miki akwai labari da ɗumi-ɗumi."

Jin haka da sauri ta bada umarnin a shigo da ita, daga ita har Jakadiyar fatansu Allah yasa labarin ya shafi zancen da suke son ji na game da Tauraruwa.

"Ranki ya daɗe barka da hutawa. Baƙin Fulani sun iso daga kaduna, maza biyu mata biyu. A halin da ake ciki ma har an kaisu masauki suna hutawa..."

Wani dogon tsaki da ta ja shi ya gwaɓarwa da Raliyan gwuiyawu. Ta fara magana cikin fushi.
"Saboda ke dabba ce wannan ne wani labari mai muhimmanci da har za ki raɗa mishi da ɗumi-ɗumi? maza ki koma bakin aikinki karki sake zuwar min da banzan labari irin wannan."

"Tuba nake Ranki ya daɗe, godiya nake. Allah ya huci zuciyarki."
A sace ta fice daga falon cikin sauri tana haɗa hanya.

Jakadiya ta buɗe baki za tayi magana da sauri ta ɗaga mata hannu alamar ta dakata.
"Jakadiya bana son jin komai daga gare ki. Je ki sai na neme ki."


BILHAƘƘI


A fakaice ta kyaɓe baki, alamun ko a jikinta. Ciki-ciki ta yi magana.
"Shi ke nan! Allah ya huci zuciyarki mai babban ɗaki ta gobe a masaurautar Bauchi, ki huta lafiya."

"Jakadiya?"
Ta kira sunanta a lokacin har ta kai bakin ƙofa za ta fita.

Waiwayowa kawai ta yi ba tare da ta dawo ba ta amsa kiran
"Na'am Ranki ya daɗe."

"A nema min ison ganawa da Mai martaba a gurin mai Soron baƙi. Yanzu!"

"To Ranki ya daɗe. Angama!"
Tana hanyar zuwa gurin mai soron baƙi take dariya a zuciyarta.
'Lallai al'amarin mai wutsiya ba ƙaramin girgiza Sarauniya yayi ba. Da da ne yadda ta amsa kiran nan daga ƙofa kuma ta tsaya ƙiƙam a gurin bata koma ta zube a gabanta ba ƙaramin masifa za ta sha akan hakan ba. A hakan ma don dai Jakadiyar ce da a ɗaya daga cikin bayi ne tayi hakan sai tasa an hukunta ta. A ƙalla ta karɓi hukuncin zafafan bulalai talatin. Amsa kira daga tsaye ba tare da zubewa a ƙasa ba babban alama ce ta raini da fitsara ga duk wanda/wacce aka yiwa a Masautar.'

Tana wannan tunanin har ta ƙarasa ɓangaren Mai soron baƙi da yake kusa da ɓangaren Mai martaba. Ƙara shiga cikin nutsuwarta tayi bayan ta nemi iso a ɓangaren an yi mata umarnin shiga.

Tana shiga ta zube a gabanta cike da ladabi ta fara zuba mata kirari. Ita kuwa Mai soron baƙi babbar mace hakima tana zaune ta mimmiƙe ƙafafunta aka lallausan kafet ɗin da ya malaye tsakar ɗakin tana ta sakin murmushi, kanta sai ƙara kumbura yake yi da jin irin kirari da yabon da Jakadiya take jera mata.

"Ranki ya daɗe. Barka da dare, sannu da hutawa. Allah ya ja zamanin tsani kuma ja gaba wajen neman izinin ganin Takawa. Sai kin so ake ganinshi idan baki so ba duk masarautar nan babu wanda ya isa ya ga Takawa. Allah ya ƙara wa Takawa lafiya da nisan kwana."

"Ameen ya Rahmanu. Jakadiya? Me ke tafe da ke a daren nan?"
Ta jefa mata tambayar har lokacin murmushi bai bar kan fuskarta ba.

"Ranki ya daɗe Fulani Taka ce ta turo ni in faɗa miki tana neman iso za ta gana da Mai martaba akan wani muhimmin al'amari yanzu..."

"A sanar da ita bazai yiwu ba Jakadiya. Yau ba ita ce da Mai martaba ba, a bayan haka ma Takawa yana da manyan baƙin da zai gana da su a darennan daga Birnin kaduna."
Ta katse ta tun kafin ta ƙarasa aje numfashin maganarta.

A sace Jakadiya ta ɗaga kai ta kalle ta sai taga wannan murmushin ya ɓace daga fuskarta, fuskarta ɗaure tamau. Cike da mamaki tayi mata sallama ta fice daga gurinta ta nufi gurin Sarauniya don isar mata da saƙo, tunani take ta yi a zuciyarta.
'Ta rasa dalilin da yasa tsakanin Mai soron baƙi da Fulani Taka sam basa ga maciji. Abinda ta lura da shi kamar duk sun zamewa juna dole ne, ga ko wannensu sun zama ƙadangarun bakin tulu. Ita Sarauniya Safara'u uwargidan Sarki ce. Ita kuwa Mai Soron baƙi Inna Laminde ƙanwar gyatumar Mai martaba ce. Tana tsananin ƙaunar Takawa tana ƙaunar duk abinda yake so, ita da kanta ta nemi ya bata wannan muƙamin yadda duk wani abu da zai isa gurin Takawa sai ya fara isa gurinta ta tantance tsaftarsa da halaccinsa saboda gudun a kai mishi abinda zai cutar da shi. Hatta matansa biyu sai sun bi ta gurinta suke samun isa gare shi ko da kuwa ranar girkin mace ne. Ta matsa lamba sosai a masarautar, ta tare gaba ta tare baya. Jajurtacciya ce kuma tsayayyiyar mace da sam bata ɗaukar wargi ko raini ga kowa a masarautar. Wani abin mamaki a yanzu Mai Soron baƙi tana tsananin ƙaunar Safiyya da duk abinda ya shafe ta, saɓanin da da tafi ƙaunar Safara'u akan Safiyya.'
"Ina ga akwai wani ƙwaƙƙwaran dalili da ya juyar da akalar wannan ƙauna da ƙiyayyar, ko ma menene dai ma ji ma gani."
Tayi maganar a fili da murya ƙasa-ƙasa tana murmushi.

A hanya ta ci karo da Sarauniya Safiyya tare da baƙinta biyu (Mummy da Bilhaƙƙi) bayi da kuyangi suna take musu baya. Da alamun kai tsaye ɓangaren gurin Mai martaba suka nufa.

Har ƙasa ta zube cike da ladabi da girmamawa ta fara kwasar gaisuwa ga Sarauniya. A mutunce ta amsa mata suka wuce zuwa inda suka nufa, sai da suka ɓacewa ganinta sannan ta daina kallonsu ta nufi ɓangaren Fulani Taka cikin sauri kamar za ta kifa.

"Inji ita Mai soron baƙin ne ta ce a faɗa min yau ba kwana na bane?"
Ta sake maimaita tambayar cikin tsananin fushi.

"Ƙwarai kuwa Ranki ya daɗe. Ta ce yana da manyan baƙi kuma ni da idanuna naga Fulani da baƙinta mata biyu sun nufi ɓangarensa. Kinga ke nan su ne manyan baƙin."

Ƙwafa tayi, ta cije gefen bakinta na dama alamun mugunta, ta ci gaba da ƙanƙance idanu cike da masifa.
"Safiyya da wasu banzayen baƙinta har sun isa su fini muƙamin ganawa da Takawa?"

"E to ga zahiri kin gani? ai ke kuma kin saka ƙafa a jarka tunda kika yi saken da mai wutsiya ta shigo masautar nan."
Jakadiya ta faɗa ƙasa-ƙasa yadda baza ta abinda ta ce ba.

"Magana kike Jakadiya?"

"A'a cewa nayi Allah ya huci zuciyarki. Amma fa ke kika yi saken da Mai soron baƙi take kawo miki wargi."

"Gaskiya kika faɗa Jakadiya. Bari inje da kaina in gani idan ta isa ta hana ni shiga gurin Takawa in gani."
Ta miƙe a fusace za ta fita da sauri Jakadiya ta dakatar da ita.

Ta rage murya ƙasa-ƙasa ta ce
"Ranki ya daɗe a halin da ake ciki faɗa ko tayar da jijiyar wuya ba naki bane. Ki kawo sulallan gwal a kaita gurin Na shuri ya cika mata aiki kawai."

"Shi kenan Jakadiya. Ya kamata saisaita mata hankali tabbas. Ki faɗa mishi a ganar da ita kuskurenta ta yadda gobe baza ta iya ɗaga idanu ta kalle ni ba balle har ta nemi musawa umarni na. Raini yana neman ya fara shiga tsakanina da ita. Amma abinda bata sani ba ni Safara'u wallahi na sha gabanta, ni ce fa uwar sarkin gobe a masarautar nan. Jakadiya ko akwai wani ɗan da zai gaji Sarki ne bayan Yarima Muzaffar?"

"Ina..! Sam babu!! Wane mutum?!!! Yo ko akwai ma ai saidai ya biyo baya a kira shi ƙanin Mai martaba sarki Muzaffar..."

"Ba ma zan taɓa bari a samu wani ƙani a masarautar nan ba Jakadiya. Muzaffar ɗin dai shi ne. Duk wanda ya ce ba haka ba kuma mu zuba mu gani. Shege ka fasa tsakanina da ko waye"

Jakadiya dai ficewa tayi zuciyarta cike da matsanancin farin ciki. Ta fara gajiya da ganin baƙin hadarin da har yau ya kasa ɓallewa da ruwa, a wannan karon babu wani Na shuri da za ta kaiwa sunan Mai soron baƙi. Ita za ta maye gurbin Na shurin ta hanyar adana sulallan gwala-gwalanta. Yo miye a ciki? ta fara gajiya ne da gafara san da har yau ƙahonshi ya ƙi ya baiyana.


****** ******


Hannu ya miƙa a hankali cikin kejin tattabarun bakinshi cike da addu'o'i ya damƙo fuka-fukanta. Wani tattausan murmushi ne ya suɓuce masa, bakinsa ɗauke da kyawawan kalamai na godiya ga Allah da ya bashi nasarar kama ta.

A yau dai bayan shekaru masu yawa da yayi yana yunƙurin kama baƙuwar tattabaran tana guduwa yau dai ya samu nasarar damƙe ta.

Can gefe guda ya samu guri ya zauna a kan benci yana ƙare mata kallo. Duk yawan kiwon tattabarunshi bai taɓa ganin kalar irinta ba, ita ta fita daban a komai ma nata da sauran tattabaru. Shi yasa tayi ta ɗaukar hankalinshi, duk lokacin da yayi yunƙurin kama ta kuma sai ya neme ta sama ko ƙasa ya rasa a cikin tattabarunshi.

Zazzaro idanu yayi cike da mamaki lokacin da ya buɗe gashin kanta, wani baƙin mayani ɗan ƙanƙani mai ɗauke da wani irin jagwalgwalon rubutu da jan alƙalami aka shimfiɗa a kanta. Sannan aka kawo wasu ƙananun allurai aka caccaka guri guri a jikin mayanin.

Alluran za su kai guda goma.
"La shakka wannan tattabara da gani mummunan sihiri aka yi mata."
Yayi maganar a fili tare da ci gaba da bubbuɗe gashin jikinta, a hammatanta na hagu da dama ya ga allurai bibbiyu, sai kuma a gadon bayanta ya sake ganin alurai huɗu. Abinda yasa ya ƙara tabbatarwa da duk wanda yayi wannan sihirin babban matsafi ne ganin yadda aka shisshigar da alluran cikin fatar jikinta da tsananin ƙarfin tsafi ba tare da an aske gashin jikinta ba. Azabar zamansu a jikinta kuma baisa ta hallaka ba.

"Innah zo ki gani."
Ya ƙwallawa wata dattijuwa da take zaune can nesa da shi a kan tabarma tana murza zaren kaɗi.

"Gidalle lafiya?"
Ta tambaye shi tana zaune a inda take.

Tattabarar ya ɗaga sama yadda za ta iya ganinta.
"Kinga yau dai Allah ya bani sa'ar kama ta. Bayan tsawon shekaru huɗu da tayi tana shawagi da ɓacewa a cikin tantabarun gidannan."

Da sauri ta miƙe ta nufo gurinshi dan ganin tattabarar ya dakatar da ita
"Ɗan taho min da Jakar Baffa na magunguna, da kuma garwashi a cikin kasko."

Ƙasa da mintuna uku ta gama aje duk abinda yake buƙata a gabanshi. Wani garin magani ya umarci Inna ta ɗauko a cikin jakar ta kwance mishi ya damƙi kaɗan ya watsa da ƙarfi a cikin rushin wutar. Nan da nan wani baƙin hayaƙi ya turnuƙe gurin har basa iya ganin junansu.

Kan tattabar ya duƙar yadda za ta shaƙi hayaƙin sosai tsawon minti biyu, lokacin hayaƙin ya fara rage wa da sauri ya fara zazzare alluran da duk wani abu mai baiyana alamun na sihiri ne bakinshi ɗauke da addu'o'i, duk abinda ya cire kai tsaye a wutan yake hurgawa har ya gama zare komai daga jikinta.

Wani irin kuka mai ƙarfi tayi kamar ba tattabara ba ta yunƙura za ta tashi daga hannunsa ya ƙara damƙe ta da kyau. Garin maganin ya umarci Inna ta jiƙa mishi kaɗan ya buɗe bakinta da ƙarfi suka ɗura mata maganin sannan ya saketa ta tashi sama.

Ya zaci tafiya za ta yi kamar yadda ta saba sai yaga ta tsaya akan katangar gidan tana ƙure shi da kallo.

Maganin ya damƙa ya ƙara watsawa a wuta, saidai saɓanin ɗazu da baƙin hayaƙi ya tashi yanzu wani farin hayaƙi ne ya taso ya lulluɓe gurin, sai daga baya kuma a hankali ya washe komai ya koma daidai.

"Alhamdulillah !"
Ya faɗa yana kallon Inna da dariya.

"Sannu da ƙoƙari Gidalle. Wato dalilin wannan aikin ne yasa tsawon shekaru tana bibiyarka sai yau Allah yasa lokacin warware duk wani ƙulli daga jikinta yayi."

"Ƙwarai kuwa Inna. Da yawan mutane yanzu sam tsoron Allah yayi ƙaranci a zukatanmu. An maida tsafe-tsafe ba komai ba. Allah ya tsare mana zuciyoyinmu. Da zaki ji irin ƙaƙƙarfar sihirin da aka haɗa da Baiwar Allahn nan za kiyi mamaki."
Ya ƙarasa maganar yana nuna tattabarar da yatsarsa manuniya.

"Wannan rayuwa sai a hankali. Allah ka iya mana da iyawarka."

"Ameen ba don halayenmu ba."

Kaskon wutan ta ɗauke daga gabanshi ta mayar cikin kicin. Ta koma kan tabarma ta ci gaba da kaɗin da take yi.

Shi kuma Gidalle kayayyakin jakar ya fara cirowa ɗaya-ɗaya bayan yana ajiyewa a gefensa, da alamun wani maganin yake nema.


******** *******

RUGAN BAFFA YALLERU

A cikin wani ɗan madaidaicin bukka da yake cikin rugar. Wani matashin dattijo ne kwance a kan wata yaloluwar tabarma. Yasa hannuwansa biyu ya tallabe kansa, da farko ya ƙurawa silin idanu ne jikinsa a matuƙar sanyaye kamar yana karantar wani abu.

Daga baya kuma sai ya fara juye-juye yana rirriƙe kansa, domin jin ko ina a jikinsa yake

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login