Showing 60001 words to 63000 words out of 98260 words

Chapter 21 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

216

Middle Ads

a sanyaye yanayin fuskarsa yana ƙara canzawa zuwa cikin damuwa da taraddadi.

"Ina jinka. Faɗa min me ya ce?"
Ta tambaye shi cike da nutsuwa, wani bahagon murmushi da yake fuskarta yasa shi kasa tantance a wani yanayi zuciyarta take ciki.

Har ya buɗe baki zaiyi magana aka buɗo ƙofar turakar aka shiga ciki ba tare da sallama ko neman izini ba. Duk su biyun ɗaga kai suka yi suna kallon ƙofar.
Yarima Muzaffar ne, babban ɗan sarki Abdulfatah na biyu. Yarima mai jiran gado a babbar masarautan Bauchi da kewayenta.

"Yaya Safara'u na rasa dalilin da yasa har yanzu Muzaffar baiyi hankali ba. Fisabilillahi ta ya zai shigo mana nan kai tsaye ba tare da neman izinin shigowa ba...?"

"Dakata Hamisu! Dakata Ciroma!!"
Ta daka mishi tsawa har sau biyu, nan da nan ta ɗaure fuska ta haɗe girar sama da ƙasa ta yi murtuk. In da abinda ta tsana a rayuwarta bai wuce a kawo wani cikas ɗin halin Muzaffar ba, shi yasa ko Mai martaba suke yawan haurawa sama da shi akan tilon ɗan nata da ta kafa ta tsare gaba da baya sama da ƙasa a kanshi.
"Ta ya dan zai shigo turakar Mahaifiyarsa ka ce sai ya nemi izini kamar sauran gama-garin mutane? Yo ko Mai martaba ya isa ya faɗi haka balle kai karan kaɗa miya? Ina ƙara jan kunnenka ka kama bakinka da kushe shi Ciroma. Ka san dai shi ne Sarkin gobe a masarautar nan ko? Ina maka tunin ana wanke ƙwarya ko dan gobe ne idan ba haka ba wallahi lokacin da ya samu dama a hannunsa bazan hana shi aikata duk abinda yake so akan ko wane shege a masauratar nan ba. Ba ruwana da kusancin da ke tsakanina da ko Uban waye."

Ta maida hankalinta kan Muzaffar da yayi ɗai-ɗai a kan makeken gadonta can nesa da su, kamar ma baisan akan me suke magana ba.
"Yarima? Lafiya kake kuwa? ina fatan dai yau ka sha maganinka?"

"Na sha."
Ya amsa da ƙyar a gaulance tare da dalalar da wani yayyauƙar miyau a bakinsa. Ba tare da duba tsadar zanin gadon da yake kwance a kai ba yasa hannu ya tattaro zanin gadon ya goge bakinsa, ya juyo ya kalle su duk su biyun.
"Umma... Ki sanar da mai martaba aure nake so. Ya nema min auren Aisha ƴar gidan Waziri Lawal, sau shida ina aikawa gurinta amma sam ta ƙi saurarena. Da na sake aikawa jiya ma sai ta ce a faɗa min ita tafi ƙarfin ta auri Gaula iri na..."

"Kan Ubancan!"
Ta lailayo wani makeken ashar ta maka kamar ba Sarauniya Safara'u ba.
"Inji ta ne ta ce maka Gaula? waye ma ubanta a garinnan balle ita banzan banza dillalin kashi? Tsiyan matsiyatan ƴaƴan talakawa masu haye a sarauta kenan basu iya girman kai ba. Amma Yarima ba na ce ka bari in gama tunanin wace ƴar sarki ce ta da ce da kai a cikin ƴaƴan manyan sarakuna sa'annin mahaifinka ba? ka san fa nan gaba kaɗan kaine Sarki a masaurautannan ta ya za ka fara da neman auren ƴar gidan waziri? ƙasƙantacce da yake a ƙarƙashinka...?"

"Ni dai gaskiya ita nake so Umma."
Yayi maganar yana bubbuga ƙafafunshi cike da shagwaɓa a kan gadon kamar wani ƙaramin yaro.

Chiroma dai baki sake yake kallon wannan ya kalli wancan ranshi a dagule.
'Tsananin tsana da haushin Muzaffar da yake ji a ransa kamar ya tashi ya shaƙo shi har sai ya daina numfashi. Ya rasa dalilin da yasa ya tsani yaron tsana mai tsananin gaske. Ko don saboda iyakarshi da Yayarshi take gwada mishi a kan yaron ne? oho!'
Tunaninsa ya katse lokacin da ya ji ta fara rarrashinsa da kalaman kwantar da hankali.

"To shi kenan. Kwantar da hankalinka. Ai dole mu so duk abinda kake so ko da ranmu baya so. Anjima zanje in samu Mai martaba da maganar . Ka kwantar da hankalinka ka ji ko?"

"Yauwa Ummata. Haka nake son ji."
Dira yayi daga kan gadon ya nufi hanyar fita daga ɗakin, duk suka bi shi da kallo har ya fice ya ɓacewa ganinsu.

"Ke Murja."
Ya ƙwalawa ɗaya daga cikin bayin da suke ta kara-kaina a falon kira.

Gabanta ne ya yanke ya faɗi, nan ta ke ta fara rawar ɗari idanunta ciccike da hawaye ta zube a gabansa.
"Allah yaja zamanin Yarima. Ga ni! kiranka abin amsawa ne a gare ni Yarima mai jiran gado. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana."

Wani mugun kallo da ya auna mata yasa kayan cikinta suka haɗe a dunƙule guri guda. Ya buɗe baki zayyi magana wani yayyauƙar miyau ya taho mishi da sauri ya kama rigar alkhabbarsa ya goge miyan da ita. Sai zazzare idanu yake yi yana ciccin magani a gaban Bayi dan kar su kawo mishi wargi ko kuma su ga wallenshi.
"Anjima da daddare ki samu Bala zai baki saƙo ki kawo ma Umma."

"To Ranka ya daɗe. Angama in Allah ya yarda."
Ta amsa a sanyaye idanunta ciccike da hawaye.

Wucewa yayi ya barta tsugune a gurin tana sharar ƙwalla, zuciyarta a ƙuntace. Kiran Yarima ba komai bane a gurinta fa ce masifa, ga shi yayi mugun matsa mata a cikin kwana biyunnan.

"Chiroma ina saurarenka."

Sosai ya ƙara ƙasa da muryarsa, ya fara magana fuskarsa cike da damuwa.
"Yaya Safara'u wai kina nufin har yau Yarima bai daina taɓe-taɓen Bayin nan ba? kinsan kuwa ko jiya sai da Malam ya ƙara ja min kunne akan haka? ya kuma ce in faɗa miki muddin bai daina ba idan tauraruwa mai wutsiya ta gitto ƙasarnan cikin ƙanƙanin lokaci alkadarinki zai karye..."

"Ƙarya ne wallahi."
Ta katse shi cikin tsawa fuskarta na bayyana tsananin ɓacin rai da tashin hankali. A zabure ta miƙe tsaye ta fara kai kawo a tsakar ɗakin tana buga tafukan hannayenta ɗaya cikin ɗaya.
"Chiroma kalle ni nan!"
Ta nuna ƙirjinta da yatsarta manuniya, ta ci gaba da magana cikin fushi da isa mai bayyana tsananin izzar da take taƙama da ita.
"Ni Safara'u na ci dubu sai ceto. Ƙarya ne a ce wata ƴar ƙanƙanuwar tauraruwa za ta kawo ƙarshen tsananin haskawar da na daɗe ina yi kuma har gobe ina kan yi a masaurautar nan da duk inda nasa ƙafa a faɗin duniyarnan. Wannan ƙarya ne. Ko babu aikin Malam akwai aikin tsafi. Idan kuma tsafin Boka yaƙi ci akwai tsananin makircin da na yi tsawon shekaru biyu ina tsotsa a nonon gyatumarmu Mai babban ɗaki. Karka kuskura ka sake faɗa min banzar magana makamanciyar wannan? kana ji na?"

"Tuba nake Ranki ya daɗe. Allah ya huci zuciyarki Yaya. Zan kiyaye gaba."

Tsawon lokaci tana ƙasa tana sama haɗe da gwama numfashi kamar wata kububuwa, a ƙasaice ta koma ta zauna a inda take tun kafin shigowarsa. Kishingiɗa tayi akan tumtum ɗin sarauta da suke ajiye jefi-jefi a kan kafet ɗin da ya malaye uwar ɗakin.
"Ka sanar da Malam ya bar aikin tauraruwa mai wutsiya a hannuna. Na ga alamun bazai iya ba, zan nemi wanda zai iya yi kamar yadda nake so. Amma a wannan karon ina so yayi min aiki mai tsananin zafi a kan Safiyya. A yi mata mai gaba ɗaya, tunda dai sun dage ita da Mai martaba suna son ganin abinda yake cikinta ya tako duniya. Ka sanar da shi wannan karon biyu babu nake so ya tabbata da zarar likitoci sun ɗaura wuƙar tiyata a jikinta. Ka fahimce ni?"

"Ƙwarai na fahimci abinda kike nufi Yaya, yadda kika ce haka za a yi. Angama."
Ya amsa a tsorace, yadda ya ga ta fusata shi yasa ya haɗiye sauran maganganun tauraruwa mai wutsiya a cikinshi ya ƙi sanar da ita. Ya san fushinta ba kyau, yanzu sai ta nemi gwada sauke fushinta a kanshi duk da ba shi ya kar zomon ba.

"Ɓace min da gani. Na sallame ka."

Yana fita ta maida kanta ƙasa tana sakin wani murmushi, zuciyarta cike da muggan saƙe-saƙe.
Ɗaya daga cikin amintattun bayinta ta aika aka yi mata kiran Jakadiya suka ƙule a can ƙuryar turakarta.
"Ya zama dole Jakadiya ki koma gurin Ci dubu a wannan karon. Tauraruwar nan shi kaɗai ne zai iya min maganinta yadda baza ma ta taɓa tunanin giftowa yankin jiharnan ba. Idan kuwa ta kuskura ta yi yunkurin shigowa yasa hadimansa su hallaka ta tun kafin ta iso. Zan ba shi duk abinda yake buƙata a faɗin duniyar nan matuƙar aikinshi yayi kyau kamar yadda ya saba."


******* *******

"Bir tanem gaskiya ni dai A'a...! kunya nake ji ni dai gaskiya... Haka kawai sai inje in ce wa Ummee zan raka ka unguwa...? Kawai su ga kamar bani da kunya ina so inbi mijina ne...? ni dai a'a..."

Sake ƙanƙame wayar yayi a kunnensa yana jin saukar daddaɗan muryarta, shauƙin da muryar yake saukar masa a jikinsa kamar misalin saukar sassanyar ruwan sama ne a jikin bil'adama lokacin tsananin zafi. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana jin wani yam-yam kamar tana mishi tafiyar tsutsa, har ta gama zuba mishi shagwaɓa da ƙorafin ita baza ta iya cewa su Ummee za ta raka shi ba.

"Tatlim."
Ya kira ta da sabon sunan soyayyar da shi ma ya raɗa mata, a muryarsa cike da wani irin zazzaƙar salon da ya sa ta kusa shiɗewa a kan gado. Ƙara ƙanƙame filo tayi a ƙirjinta tana lullumshe idanu kamar yana gabanta. Ta sake ƙasa da muryarta sosai ta amsa da.
"Na'am Bir tanem."

"Ki shirya zuwa ƙarfe uku. Ni da kaina zan tambaya mana Ummee izinin fita. Sosai nake kewar lallausar fatarki fa. Cikin kwana biyun nan kuma na lura gaba ɗaya Ummee ta kasa ta tsare kamar zan wani cinye ki."

Sassanyar dariya ta sakar mishi a kunne, dole tasa shi ma ya murmusa yana sosa keya.
"Dariyar ta mecece?"

"Dan Allah ba ka jin kunya Bir tanem?"

"Tatlim kunyar wa zanji? ke ɗin fa matata ce. Mallakina ce. Halaliyata ce. To bayan waɗannan ƙwararan dalilan da suka haɗu suka damƙa min ke kunyar wa zanji gurin fita da ke?."

"Hakane Bir tanem. Yauwa na tuna, faɗa min"

"Me zan faɗa miki?"
Ya tambaye ta cikin shaukin son da ya gagara ɓoyuwa har a muryarsa.

"Yadda aka yi ka gano fassarar sunan da na raɗa maka mana? na ji kai ma har ka raɗa min daddaɗan suna. Amma da gaske ni Sweetheart ɗinka ce?"

"Kina shakka ne? Bari anjima idan mun fito zan tabbatar miki, zan share miki duk wani tantama da kike yi. A google na nemi fassarar Bir tanem, sai suka bani amsar My one and only in Turkish. Sai na nemi yadda ake kiran Sweetheart a Turkish suka bani amsa Tatlim. Kinji yadda na samu amsoshin.
Amma a ina kika san yaren Tukish?"

"A makaranta suka koya mana."

"Ashe kinyi karatu..."

"Kai...! kyakkyawan sakamakon da ba kowa ke iya samu ba na fito da shi a jarabawar waec da neco. Kawai dan dai komai na barshi a can gidan Madam ne."

"Ma sha Allah. Kina sha'awar ci gaba da karatu?"

"E in dai za ka barni ina so."

Shigar Rabi cikin ɗakin yasa yayi ɗif a wayar bai amsa mata ba. Ya bi ta da kallo ganin yadda ta ɗanɗasa kwalliya cikin ƙananun kaya, ta yi kyau sosai kam. Duk wasu albarkatun jikinta ta matso su sun bayyana a fili. Ya ɗanyi murmushi.
"Tatlim. Will call you letter."
Bai jira amsawarta ba ya katse wayar.

A can ɓangarenta kuma sake da baki ta bi wayar da kallo, ta danna dan ganin lokaci. Karfe tara da kwata na safe ne, tunanin ko matarsa ne ta shiga cikin ɗakin yasa ta ja tsaki ta ajiye wayar a gefe taja bargo ta lullaɓa har kanta. Ko da Saudat ta shiga ma ganin kamar tana bacci yasa ta fita a hankali dan kar ta tashe ta.


******** ******

Cike da zakwaɗi da masifar ɗoki take komai da sauri-sauri har ta gama shiryawa cikin riga da sket na lesi mare nauyi. Duk da haka sai da yayi zaman jiranta na minti ashirin.

Mummy da Ummee sai tsokanarta suke yi ita kuma tana dariya da sunne kai. Bayan tsawon watanni shida da wasu kwanaki da tayi a gida tana zaune ba tare da ta leƙa ko ƙofar gida ba sai yau za ta fita. Lallai wannan babban abin farinciki ne a gurinta.

Ga Malam kam da ƙyar ya barta tayi rakiyar bayan ya keɓe Maheer yayi mishi ƙwaƙƙwaran jan kunnen ya kula da ita. Ya ƙara da tunasar da shi har yanzu waɗanda ke bibiyar rayuwarta ba wai sun haƙura bane, akwai muhimmin abun da suke so a tare da ita. Ya ce yaji ya gani in Allah ya yarda zai kula da ita har su koma gidan.

"Babe duk wannan farincikin na menene...?"
Ya tambaye ta yana murmushi bayan ya riƙo hannunta ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma yana murza sitiyari.

"Sai yau fa na fito. Darling sai yau na fito waje tun da na zo gidan Malam fa. Wawwww! Dubi unguwarnan ashe tana da kyau sosai har haka? Can ne masallacin Malam ko?"
Ta nuna masallacin da yatsa.

"Eh nan ne."
Ya amsa yana dariya.

Daƙyar ya samu ta nutsu har suka ƙarasa kasuwan central inda shagunansu yake. Duk da ba zaman kasuwar yake yi sosai ba sai a weekend yake leƙawa yana da babban ofis ɗinshi, a gefen nashi Ofis ɗin ne na Yusuf yake. Haɗaɗɗen Ofis ne har da A.C a ciki saboda tsabar son hutu. A ciki ya zaunar da ita.

Ko da Yusuf ya shiga dan su gaisa da Amarya duk su biyun sun shiga matsanancin mamakin da ya gaza ɓoyuwa a fuskokinsu.
"Laaaaa Ya Yusuf? Ashe rai kan ga rai?"

"Bibi ke zan tambaya ai, bani labarin ta inda aka haihu a ragaya."
Ya tambayeta yana dariya. Sosai ya ji daɗin sake ganinta da kuma kasancewarta matar Yallaɓai.

Shima yayi mamakin sanin juna da suka yi, ganin ta gyara zama za ta fara zuba mishi labari da sauri Maheer ya katse ta, fuskarsa a ɗaure.
"Ke me kike shirin yi?"

Galala ta bishi da kallo baki buɗe, mamaki take yi fushin kuma na miye? Bai sake kallonta ba ya maida hankalinshi kan Yusuf.
"Hirarku mai tsawo ne Yusuf, kuma yanzu sauri muke yi akwai inda za mu je."

Dariya kawai yayi, dan ya gane Maheer kishi yake yi. Bai ji haushin shi ba, sosai ya ji daɗin kasancewarsu ma'aurata. Daman tun a ganin farko da yayi mata ya hango dacewarsu ta ko wane ɓangare.

Wani babban jaka troley da yake ajiye a Ofis ɗin ya umarci yaran shagon suka ɗauka mishi zuwa mota, tana shiga ya ja motar fuuu suka tafi bayan Yusuf ya cika ta kyautan kuɗi.

"A ina kika san Yusuf?"

Ya jefa mata tambayar a bazata, ko da ta kalle shi ba ita yake kallo ba, hankalinshi na kan tuƙin da yake yi. Kyaɓe baki ta yi alamun can ta matse mishi.
"A kachia. Tun wancan lokacin da nake ta nacin sonka kai kuma baka so na..."

"Wa ya ce miki tun a wancan lokacin ba na sonki?"

"Kai ka faɗa min da bakinka. Ko ka manta in tuna maka a mabanbantan lokutan da ka ce baka so na? har ma ka ce baza ka taɓa ƙaunata ba."
Wani mugun ɓacin rai da ya taso mata dole ta gimtse sauran maganganun, ta ɗaure tamau ta maida kanta can gefen titin tana kalle-kalle. Shima sai yayi shiru kawai ya ci gaba da tuƙi har suka isa hotel ɗin.

Gurin zama ya nuna mata a gefe ya ajiye jakan a kusa da ita ya ƙarasa ciki ya gama duk abinda zayyi sannan ya dawo gurinta ya ce ta bishi, bisa ga mamakinta ciki suka shiga maimakon gida da tayi tsammanin za su koma. Wani ma'aikacin hotel ɗin na gaba riƙe da jakar su kuma suna binshi a baya har ya kaisu wani ɗaki yasa makulli ya buɗe ƙofar. Har ciki ya shiga da jakar yayi wa Maheer sallama ya fice daga ɗakin.

"Ki shigo ciki mana."
Yayi maganar fuskarsa da murmushi ganin yadda ta doge a bakin ƙofar ɗakin.

Kaɗan ta shiga ciki shi kuma ya maida ƙofar ya rufe har da murza key.
"Me zamu yi a nan ɗin?"
Ta tambaye shi har lokacin fuskarta babu walwala.

"Sallah kawai za muyi mu huta zuwa ɗan anjima sai in maida ke gida."

Bai saurari amsarta ba ya shige banɗaki don ɗauro alwala. Dole ta yi wa kanta mazauni akan kujeran ɗakin tana jiran ya fito.

*****

"Fushi-fushin me kike ta yi haka Tatlim? zo kiji wani labari."
Ya ƙarasa maganar haɗe da janyo ta gaba ɗaya zuwa jikinsa. Hijabin jikinta ya zare a hankali ya ƙara gyara zama akan daddumar da suka idar da sallan. Sosai ya kwantar da ita a jikinshi, ya zame ɗankwalinta yana shafa kwantaccen gashin kanta da hannu ɗaya.
"Kinsan Allah ɗaya ne ko Babe? Tun ranar da na fara haɗuwa da ke a asibiti har muka gabza karo wallahi na ji wani abu na musamman yana tsattsarge zuciyata game ke. Sosai na shiga wani irin yanayi da a wancan lokacin na gaza gane ko menene. Da na fahimci munyi canjen waya ba ƙaramin murna nayi ba dan nasan wannan dama ce da zaisa in ƙara tozali da kyakkyawar fuskarki. To abinda ya sagar min da gwuiwa a kanki kuma yasa ƙarfi da yaji na ke ta ƙoƙarin yakice ki a raina har na ringa miki wulakanci ina faɗa miki bana sonki bai wuce abubuwa biyu zuwa uku ba. Kinga na farko yadda na fahimci sam ba ki da wani babba

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login