Showing 75001 words to 78000 words out of 98260 words

Chapter 26 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

226

Middle Ads

da jariran ta yi akan gado ta fita dan ta riga kowa kaiwa Takawa wannan kyakkyawan albishir ɗin, tana da tabbacin za ta samu gwaggwaɓan tukwuicin da zai jijjiga nutsuwarta. Duk wanda ta ci karo da shi a hanya umarni take badawa kan a shiga lungu da saƙo na cikin gidan a sanar da Sarauniya Safiyya ta haifo kyakkyawar Gimbiya da sabon balarabe Yariman Bauchi.

Nan fa labarin ya sake fantsama a lungu da saƙo na cikin gidan.

Haka Allah yake ikonsa, idan ya so sai ya haɗa wa bawa farin-ciki da baƙin ciki duk a lokaci guda. Hakan ce ta kasance ga Takawa, ga farin-cikin haihuwar Safiyya ga baƙin cikin abinda yake faruwa da Muzaffar. Da kanshi yay tattaki har zuwa ɓangaren Safiyya don ganin sanyin idanunsa.

A karo na tara cikin kyarma da rawan jiki Jakadiya ta sake ƙwanƙwasa ƙofar turakar Fulani Taka, amma har lokacin ko alamun za a buɗe mata ƙofar bata ji ba. Kanta ta kwantar a jikin kofar ta buɗe murya sosai yadda za ta iya jiyo ta ta ciki
"Ranki ya daɗe Jakadiya babba ce. Jaje haɗe da gwaggwaɓar albishir na taho inyi miki. Jajen akan abinda ya faru da Yarimanmu ne, albishir ɗin kuwa yanzunnan na samu labarin Fulani ta sauka lafiya, ta haifi ƴaƴa tagwaye lafiyayyu ƙosassu, da ita da jariran duk suna lafiya..."

Ihun da taji an yanka ta can cikin ɗakin tare da jin rijib! alamun faɗuwar wani abu yasa ta kasa ƙarasa maganar da take yi, daga nan kuma ɗif ake ji.



BILHAƘƘI


Duk da jikinta yana bata wannan ƙarar da ta ji daga cikin ɗakin da alamun faɗuwar wani abu ba na lafiya bane. Amma don ta ƙara tabbatarwa sai ta sake kara kanta a jikin ƙofar tana kiranta.

"Ranki ya daɗe Fulani? kina ji na? Allah yaja zamaninki ki daɗe kina yi a masarautar bauchi. Dan girman Allah ki taimake ni ki buɗe ƙofar nan."
Shiru ne nan ma ya sake ba ta amsa. Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma. Tana nan tsaye ita da bayin ɓangaren sunyi cirko-cirko da tunanin waƙar farawa sai ga shigowar Chiroma buguzum-buguzum yana baza babbar riga.

Nan da nan duk suka dare suka bashi guri, kowa ya zube a ƙasa yana kwasar gaisuwa. Ko amsa musu ya kasa yi saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki.

Haihuwar Fulani lafiya ba tare da samun labarin mutuwarta gurin haihuwar ba shi ne babban abinda ya sashi ya zuge ya ƙare a lokaci ɗaya.

Daman ga damuwar ciwon sambatu da ya kama Muzaffar farat ɗaya. Daga samun labarin haihuwar zuwa yanzu ya zaga bayi sau shida. Duk gwuiyawunsa a sake suke saboda rashin ƙarfin jiki.

Fulani Taka yayarsa ce, tonuwar asirinta a masarautar nan tabbas babban tonuwar asirinsa ne. Domin duk wani tuggu da makirci da asire-asire tare da shi take ƙullawa, a taƙaice ma shi ne jakadan amsowa da isar da duk wani saƙo ko magani a gurin malamai da bokayenta. Da wannan dalilin yasa yazo tun da wuri kafin wankin hula ya kaisu dare, gara su san na kwatanci su nemawa kansu mafita da hanya mai ɓullewa.

Ya kalle su shakaka da baki sannan ya daka musu tsawa dan kawo ƙarshen gaishe-gaishen da suke ta mishi.
"Kai dallah ku saurara min! Ina ita Fulanin ta ke?"

Jakadiya ce ta gyara tsuguno ta kora mishi bayanin duk abinda ya faru.

A diririce ya matsa kusa da ƙofar shi ma yayi kirari, yayi magiya, yayi roƙo amma shiru ya ke ji, babu ma alamun za ta amsa balle har ya saka ran za ta buɗe ƙofar.

Hankali a tashe ya kwashi jiki zuwa gurin Mai Martaba don ya sanar da shi halin da ake ciki. Mai soron baƙi ne ta tare shi da cewar baya nan ya shiga cikin gida gurin Mai Babban ɗaki (Mahaifiyar Sarki).

Haka ya sake kwasan jiki zuwa ɓangaren Mai babban ɗaki bayan ya nemi iso anyi mishi izinin shiga ciki, ya tarar da lafiyayyiyar tsohuwar mai kyawun jiki an zuba mata jariran a gabanta tana tottofe su da zafafan addu'o'i.

Takawa yana zaune a gefe yana kallon yaran da mahaifiyarsa fuskarsa cike da farin ciki.
"Chiroma lafiya kuwa? Me yake faruwa da har aka gaza jira mu fito har sai an biyo mu nan gurin Umma?"

Ƙasa ya sake kwantar da kanshi yana neman afuwa
"Tuba nake Ranka ya daɗe. Tuba nake, Allah ya huci zuciyarka. Haƙiƙa ba lafiya ba, tunda Fulani taga halin da Yarima yake ciki ta bar sashen cikin tashin hankali da damuwa har yanzu bamu san a wane hali take ciki ba. Ta kulle kanta a turakarta ko motsinta ba a ji, munyi magana munyi magiya shiru har yanzu bata buɗe ƙofar ba. Tsoro muke ko tana cikin wani mummunan hali shi yasa nayi gaggawar zuwa in sanar da Takawa. Tuba nake Ranka ya daɗe."

"Subhanallahi! Abdulfahi ayi gaggawar ba da umarnin a buɗe ƙofar ko ta wane hali don a ga yanayin da take ciki."

"To Umma. An gama!"
Ya amsa ma umarninta cike da ladabi da biyayya a muryarsa. Sai kuma ya maida idanunsa kan Chiroma.
"Ayi gaggawar sanar da Badaru halin da ake ciki, idan ta kama ma a ɓalla ƙofar. Gamu nan fitowa."

"A fito lafiya Ranka ya daɗe. Allah ya huta gajiya. Ranki ya daɗe a huta lafiya, Allah ya raya mana Gimbiya da Yarima ƙarami, Allah yayi musu albarka."
Haka yayi ta surutai yana satar kallon kyawawan yaran har ya fice daga sasan gaba ɗaya.

Ko da aka ɓalle ƙofar turakar Fulani a sume aka tarar da ita. Shi yasa ba tare da wani ɓata lokaci ba itama aka kwashe ta zuwa babban asibitin cikin gari, inda a can ne aka kwantar da Shalelenta.


****** ********


An kira babbar likita har gida ta duba Sarauniya Safiyya da jariran ta tabbatar da lafiyarsu ta ba Safiyya magunguna, Mai martaba yayi mata sha tara na arziki sannan ya sallameta.

A wannan ranar Takawa kyaututtuka yake ta yi na bajinta da nuna godiyarsa ga Allah. Mai soron baƙi da ta kai albishir ɗin haihuwar jariran kyautar Raƙumi da doki aka yi mata. Malam da iyalansa kuwa anyi musu kyaututtuka na ban girma, ciki har da wani tamfatsetsen gida na Mai martaba da yake cikin garin kaduna.

An ƴanta bayi talatin da biyu a cikin gidan. A wannan ranar dai duk wanda yake cikin masarautar zai shaida wannan gaggarumin abin farin ciki da ake ciki. Masu girke sai dafe-dafe suke yi kala-kala ana sadakar da shi. A wannan ranar ko zaman fada cikin farin ciki da walwala Takawa yake yinsa. Jariran har fada an fitar da su naɗe a gadajensu na jarirai, Hakimai, Galadima, Wambai da duk sauran masu mukami a masarautan sai leƙa fuskokinsu suke yi ana saka musu albarka.

Da yamma lis ana gaf da tashi daga zaman fada wani firgitaccen labari da ya firgita duk wani mai rai da ke cikin fadar ya isa kunnensu. Wai ga wani tsohon bafullatani nan da wani matashin dattijo da ya ce shi ne Mustapha ɗan Sarki Abdulfatah. Kafin a ce kwabo Sarki ya bada umarnin ayi gaggawar isa da su cikin fadar don ya ganewa idonsa shin da gaske ne ko ƙarya ne mahassadansa suka yi mishi ture? Don yana da tabbacin in dai Mustapha ɗansa ne duk tsawon shekaru ko da komai na jikinsa ya canza akwai abubuwa da dama da zai iya gane shi da su.

"Hattara Matashin dattijo! Nutsu!! shiga cikin taitayinka!!! Gaban Sarkin duniya kake Abdulfatahi na biyu wanda sam baya ɗaukar wargi."
Wani Bafade ne ya dakawa Mustapha tsawa ganin yadda ake janshi yana ta turje-turje.

Jin an ce a gaban mahaifinshi yake ya sa shi ya ɗaga idanunshi da suke ciccike da hawaye ya zuba a kan fuskar Takawa. Nan take sai hawayen suka gangaro shar... bisa kuncinsa don tsananin ƙunci, kewa, damuwar rashin ahalinsa na tsawon shekarun da bashi da tabbacin iyakarsu.
"Abbbuu... bar...ka... da... yamma..."
Ya faɗa a rarrabe bakinshi na rawa.

Tsam Takawa ya miƙe tsaye daga kan karagar mulkinsa yana nuna Mustapha da ɗan yatsarsa manuniya.
'Tabbas duk da cika da alamun girma da muryar ta ƙara bazai taɓa manta muryar Shalelen ɗansa Mustapha ba. Muryar da ko da basa tare tsawon shekaru kusan kullum sai yayi mafarkinsa yana ce mishi duk daren daɗewa zai koma gare su.? Ta ya zai kasa tantance muryar masoyinsa?'
Yana wannan tunanin har ya ƙarasa kusa da Mustapha ya cire hannunsa daga cikin alkyabbar jikinsa ya kama fuskarsa ya ɗaga ya ƙura mishi ido.

Har lokacin hawayen idanun Mustapha basu daina zuba ba. Ya saki fuskar ya kamo hannunsa na dama ya ja hannun rigarsa har saman damtsensa. Wani ƙaton tawadar Allah ce da girma yasa ita ma ta ƙara buɗewa a damtsen hannun, yasa yatsarsa ya murje da ƙarfi ta ƙi goguwa. Zuwa wannan lokacin jikin Takawa ya fara kyarma, a hankali ya kama rigar jikin Mustaphan da niyyar cire mishi ita, ganin yadda jikinsa ke rawa yasa Mustaphan ya ƙarasa zare rigar da kansa. Sai ga wannan tambarin na ƙirjinsa wanda alama ce da ake yiwa duk wani jinin sarautar gidan da zai iya hawa karagar mulki.

Taga-taga Sarki ya tafi zai faɗi da saurin gaske su Liman da waziri suka tare shi kafin ya kai ƙasa.
"Mustapha na ne. Tabbas shi ne wannan..."
Kafin ya ƙarasa jijiyoyin sadar da saƙonnin jikinsa suka tsaya ƙyam, ya suma a jikinsu.


******** ********


Zuwa dare gaggarumin abin farin-cikin da ya ƙara samuwa yayi tambari a duk wani lungu da saƙo na cikin garin Bauchi.
"Babban ɗan Mai martaba Sarki Abdulfatahi na biyu Yarima Mustapha ya koma gida yau bayan ɓatarsa da shekaru ashirin da takwas."

Wannan babban labari ne kuma abin farin ciki ne da ya jijjiga duk wani mai rai da yake rayuwa a cikin garin Bauchi da kewayenta. Ƙawayen masarautar ma sai kiraye-kiraye suke yi suna taya masautar murna.

Ga Takawa, Sarauniya Safiyya, Uwar soro, mai babban ɗaki, Mal Abdulganiyyu da iyalansa na barwa masu karatu ku kwatantawa kanku irin kogin farin-cikin da aka tsunduma su a ciki🤣🥰👌🏽. Ƙarfe goma da rabi na dare Mustapha da Yalleru sun gama samun nutsuwa, sunci lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Mustapha yayi wanka ya shirya cikin kaya na alfarma da sarauta. Kasa haƙuri iyayen suka yi suka kulle kansu a turakar Mai martaba aka tasa Mustapha da Baffa Yalleru a gaba yana basu labarin irin gararambar rayuwar da yayi a cikin duniya. Masu saurin kuka a cikin ɗakin sai sharar hawaye suke yi.

Tun bayan bayyanar labarin dawowar ɓataccen ɗan Sarki take jinta a cikin wani irin yanayi na faɗuwar gaba da sanyin jiki. Duk da bata samu ganin baƙon ba amma yadda ta ga Sarauniya tana ta murna da kuka tana godiya ga Allah da ya dawo musu da shi yasa ta tabbatar ba ƙaramin ƙauna suke yiwa Mustaphan ba.

Shiru tayi a kan gado tana saƙe-saƙe da tunani. Mummy yau da wuri tayi bacci saboda gajiya, don yini suka yi zurga-zurga da hidiman jarirai, tunda ba kowa ake yarda ya ɗauke su saboda gudun abinda ka je ya zo na sharrin mutane.

Wani matsanancin kewar Sevgilim ɗinta ne yake ta taso mata tana dannewa. Tun jiya da suka iso gidan bata sake haɗuwa da shi ba sai dai suyi magana ta waya. Da wannan tunanin yasa ta lalubo wayarta a jaka da nufin kiranshi sai ta ga an tura mata saƙonni biyu a fuskar wayar.

Ko da ta buɗe saƙonnin ɗaya daga gurinshi ne, ɗayan kuma daga wani baƙon lamba ne da bata san ko ta waye ba.

Saƙonshi ta fara buɗewa, zaƙaƙan kalamai ne yana faɗa mata yadda yake tsanani sonta da yadda yake kewarta, har yana ƙorafin shi fa shi yasa a rayuwarsa sam baya son harkar al'amarin gidan sarauta. Ace kai da iyalinka ba halin ku sake kuga juna a lokacin da kuke so? Da yadda ya ƙosa su koma gida a yi bikinsu ta tare a kusa da shi.

Yalwataccen murmushin jin daɗi ne kwance a fuskarta, har za ta danna kiranshi sai kuma ta yanke shawarar fara duba ɗayan saƙon da aka tura mata, dan haka ta buɗe. Sunan da ta gani ne da abinda saƙon ya ƙunsa yasa ƙirjinta yayi wani mugun bugawa, kayan cikinta suka cure guri guda.
"Bibi. Madam Mary ce. Duba whatsapp ɗinki ki ga wani babban abin mamaki da na tura miki."

Da sauri ta wuce saƙon ta shiga whatsapp ɗin da kwata-kwata kwananta huɗu ne da buɗewa. Duk hange da tunaninta ya tafi ne ga tuhumar a ina Madam ta samu sabon lambar wayarta?

Saƙon vidio ne Madam ɗin ta tura mata. Kafin ya buɗe sai jan tsaki take yi ƙasa-ƙasa cike da ƙosawa da son ganin abinda vidion ya ƙunsa.

Yana buɗewa ta fara cin karo da fuskar wata tsohuwar mace, tana zaune cikin mawuyacin hali. An ɗaure ta tamau a jikin kujera, kanta fari fat! furfura ce ko wahala ce oho. Wani hannu da bata san ko na waye ba ya damƙi gashin kan matar aka ɗaga fuskarta yadda mai kallon vidion zai iya ganinta sosai. Sautin muryar Madam da ta ji ya biyo bayan ɗaga fuskar yasa ta miƙe tsaye a zabure, hankalinta a tashe, tsananin tashin hankali yasa idanunta ya fara canza launi daga fari da baƙi zuwa ja da kore
"Bibi kinga wannan matar? ita ce Mahaifiyarki Rebeccah. Tsawon shekaru goma sha tara tayi a kulle a Coci ana gana mata azaba. Yau mun je mun ƙwato ta a hannun waɗancan da suke tsare da ita, idan kin damu da ita kina son ganinta a raye ki miƙo kanki gare mu, ki dawo cikin ƙungiya ki karɓi muƙaminki. Idan kika yi haka mu kuma munyi miki alƙawarin za mu sake ta lafiya ba tare da wani abu ya faru da ita ba. Kuma kafin ki taho ki tabbatar kin kashe wannan ɗan iskan auren da kika yi, domin a muƙaminki na ƙungiya sam babu aure a rayuwarki."
Sai ta sake fashewa da dariya mai tsananin ƙarfi tana ta ƙyaƙyatawa har zuwa ƙarshen vidion.

Tsigar jikinta ne ya fara wani irin mimmiƙewa kamar ƙayoyi don tsananin tashin hankali, bata san lokacin da hannunta ya danna amsa kiran wayar da Mustapha yai mata ba sai muryarsa kawai ta ji yana ta
"Hello... helloo... Tatlim kina ji na?"

"Ka fito yanzun nan ina so mu haɗu."
Tayi maganar da wani irin murya da a can ɓangarensa sai da ya cire wayar a kunnensa ya sake kallon sunan da tunanin ko dai ba ita ya kira ba? ganin tabbas sunanta ne kuma lambarta ce yasa ya miƙe zaune da sauri, da jin muryar nan ya tabbatar ba lafiya take ba.

Kamar walƙiya tunanin abinda ya faru da ita jiya a hanyarsu ta zuwa ya faɗo masa a rai.
"La haula wala ƙuwwata illa billahil aliyyul azeem. Tatlim kiyi ta maimaitawa gani nan zuwa, ki fito mu haɗu yanzu. La haula wala ƙuwwata illa billahil aliyyul azeem."
Haka yayi ta maimaitawa a wayar tun yana jinta shiru bata amsa shi har ya ji ita ma tana maimaitawa, cikin sauri ya zura rigarsa wayar na maƙale a kunnensa ya fice daga ɓangaren baƙin da aka sauke su.

Kai tsaye cikin gidan ya nufa hanyar da zai sada shi da ɓangaren Sarauniya Safiyya. Saboda dare da ya fara yi don lokacin sha ɗaya ta gota jefi-jefi yake haɗuwa da bayi har yayi kiciɓus da ita a hanya, da sanyin jiki take tafe kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Hannunta ya ja da mugun sauri suka koma inda ya fito.

Suna shiga cikin ɗakin ya maida ƙofar ya rufe, sannan ya janyo ta tsam ya rungume a ƙirjinsa yana tottofeta da duk wata addu'a da ta zo bakinshi.

Ita kuwa sai ƙara riƙe shi take yi a tsorace tana ta sassauke ajiyar zuciya mai nauyi sauri-sauri. Sai da yaga ta ɗan samu nutsuwa ya riƙe ta a jikinsa suka zauna a gefen gadon, sannan ya ɗago fuskarta a tausashe ya fara tambayarta abinda ya ɗaga mata hankali.
"Tatlim! kinsan bana son damuwarki ko? Ummm?! Faɗa min! Wa ya taɓa min ke? Menene abinda ya ɗaga miki hankali?"

Sai a lokacin ta ji wani ƙaƙƙarfan kuka ya taho mata, karo na biyu ta sake kwantar da kanta a ƙirjinsa ta fara rera kukan a nutse kamar karatu. Shi kuwa bai katse ta ba sai shafa bayanta yake yi yana ɗan bubbuga ta alamar rarrashi har saida ta samu nutsuwa don kanta ta ɗago tana kallonsa ta fara magana a muryarta baiyane ƙarara da tashin hankali.

"Sevgilim! Sun kama Mahaifiyata... ashe duk wannan gararambar da nake yi a duniya mahaifiyar da ta haifeni tana raye a can tsare a hannun wasu azzaluman mutane. Yanzu su Oga sun kamo ta, sun ce in dai ban koma cikinsu ba za su kashe min ita. Sevgilim ita Ummata ce wacce ta tsugunna ta haife ni, ya zama dole in miƙa musu tawa rayuwar don in cece tata rayuwar. Duk da ban taɓa ganinta a ido biyu ba na ji a raina ina tsananin son ta, sun faɗa min shekarunta goma sha tara tana cikin uƙuba a hannun waɗancan mutanen. Don tabbatuwar cika ta ƴar halas ya zama dole in zame mata silar jin daɗi. Ko bayan ba raina kai da Malam dan Allah ku riƙe min ita Sevgilim, ka jiyar da ita daɗin duniyan da ta daɗe ba ta ji ba. Idan kayi min haka ka gama min komai Masoyi."
A karo na uku ta sake kwantar da kanta a ƙirjinsa wasu zafafan hawaye suna tsiyaya daga idanunta.


BILHAƘƘI


Shiru yayi yana saƙe-saƙe da jujjuya maganganunta. Kamar ya fahimta amma kuma bai gama fahimtar inda maganganunta suka dosa ba. Har sai da ya tambaye ta
"Babe nutsu pls, ta ina ne suka faɗa miki sun kamo Mahaifiyarki?"

Wayarta ta nuna mishi da take yashe a can gefen gadon. Zai tashi ya ɗauko ta hana shi ta hanyar sake ƙanƙame shi. Dole ya koma ya zauna ya ci gaba da shafa bayanta.

Tsawon lokaci suna

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login