Showing 24001 words to 27000 words out of 98260 words
ki rasa wanda za ki cinye sai Lidiya da mahaifina?"
Kaɗa kai kawai yayi ya fice daga ɗakin fuskarsa a cunkushe, zuciyarsa ɗauke da zallar takaicinta, baƙin ciki, da da-na sanin aurenta.
Tun daga ranar mutanen ƙauyen da shi kanshi mijin nata suka tsangwame ta, sun ɗauki wannan matakin na tsangwamarta ne a cewarsu idan ka nuna kana tsoron maye shi ne zai bashi damar samun galaba a kanka. Ba ta da halin ta shaƙi iska mai sanyi sai su fara zaginta suna jifanta da baƙaƙen maganganu, idan ta kuskura ta fita waje kuwa da kuka take komawa cikin gida saboda da jifa suke rako ta, ta rame tayi baƙi ta fice daga haiyacinta, Rebecca ma ta fige tayi firit kamar bakwaini saboda rashin samun kyakkyawar kulawa daga mahaifiyarta.
Tun kafin ta haihu ta ɗauke ƙata ɗif daga gurin Mama Vero, ta daina zuwa gaba ɗaya, ita ma ba ta neme ta ba, ba ta da masaniyar abinda yake faruwa a cikin ƙauyen saboda wani muhimmin aiki da take yi, har daga ƙarshe tafiya ta kama ta.
James wan Zidane ne ya kamu da mummunan ciwon da aka rasa gane kansa da gindinsa, da farko ya fara da haɓo ne sai kuma jinin ya ɓalle masa ta hanci ta baki, kwana biyu yana cikin mawuyacin hali kafin ya mutu a daren ranar asabar.
Nan ƙauyen ya sake ɗauka kwam zancen Alheri mayya ko ina shi ake yi, wasu suna cewa a kore ta kafin ta gama musu ɗauki ɗai-ɗai wasu suna cewa a kashe ta. Washe gari lahadi a coci manyan pastocin ƙauyen su huɗu ƙarƙashin jagorancin babbansu pastor Nuhu suka yanke shawarar kashe ta, da yammacin ranar kuwa suka aiwatar da ƙudirinsu bayan an tsige Rebecca daga bakin nono, Alheri tana kuka tana magiyar su barta ta gama shayar da ƴarta suka ja ta bayan gari a wulaƙance suka ɗaure ta a jikin bishiya aka diddila mata fetur Luka ya ƙyasta ashana ya hurga mata.
Ko da Mama Vero ta dawo ta samu labarin abinda ya faru tayi kuka kamar ranta zai fita, da ta saukar da annobar amai da gudawa matasa mata sa'annin Alheri masu aure da marasa aure su talatin ne suka mutu.
Sai da suka shekara huɗu amfanin gonansu yana lalacewa, sun shiga matsanancin hali da yunwa mai tsanani, kuma duk wanda yayi nufin barin ƙauyen sai dai a tsinci gawarsa a hanya. Ko da ƙauyukan kusa da su sunyi niyyar kawo musu tallafi sai dai a ga kayan abincin ya lalace tsutsotsi manya manya masu kama da gwazarma suna safa da marwa a ciki.
Da tashin hankali yayi tashin hankali bala'i yayi bala'i tsofaffin ƙauyen da pastoci ne suka haɗu aka je gurin Mama Vero neman tuba dan sun tabbatar wannan bala'in daga gurinta yake.
Cikin fushi take sanar da su laifin da suka aikata mata ta ƙara da cewa sai sun shekara goma a cikin wannan hali.
Rebecca da aka nuna mata a matsayin ƴar Alheri yasa ta sassauta musu daga fushin da ta yi da su har daga ƙarshe ta barsu suka ci gaba da harkokinsu cikin lumana da zaman lafiya.
A kwan a tashi Rebecca tana girma amma wani abin mamaki ga Mama Vero sam Rebecca ta tsane ta, bata ƙaunarta bata ƙaunar ganinta, shi yasa sai ta shafe wata guda cur bata je gurin Mama Vero ba duk da matsanancin halin da take ciki a ƙauyen a gurin Mahaifinta da ɗan uwanta da wasu daga cikin mutanen gari, tsananin tsanan da aka gwada wa mahaifiyarta ne yake bibiyarta duk da an tabbatar ita ba mayya bace.
Duk yadda Mama Vero take bibiyarta akan idan akwai abinda take so tayi mata ko a kan mutanen garin ta faɗa za ta yi mata amma bata taɓa neman alfarmarta ba sai akan riƙon BILHAƘƘI wacce take kira da sunan kakarta Alheri saboda ta fahimci tana ɗauke da irin baiwar da Alherin take da shi, yanzu ga shi ta ƙara mata da manyan sirrika na tsafin da ta sani kaf rayuwarta. Mama Vero ita ce ta aikawa Pastor Nuhu saƙon gaggawa akan matuƙar suka kashe Rebecca to tabbas zasu ɓallowa kansu masifu da bala'in da basu taɓa tsammani ba, za ta tado ruhin Alheri ta ɗauki fansar kisan da suka yi mata. Da wannan daliin ne yasa yayi gaggawar dakatar da kashe Rebecca.'
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke bayan ta dawo daga duniya mai tsananin nisa na tunanin da ta lula, ta sake kallon Alheri tana sakin tatausan murmushi, har lokacin yarinyar bata san me Mama take yi ba, amma yanzu ba wasa da fararen dutsuna take yi ba, wasu ma'auratan malam buɗe littafi take ta jujjuya su da ƙarfin tsafin idanunta tana ƙyalƙyala dariya cike da matsanancin nishaɗi.
Nan da nan kuma Mama Vero ta ɓata fuska bayan wani tunani ya faɗo mata a rai.
'Ba a halicci Alheri dan ta rayu a ƙuntataccen ƙauyen nan ba, a binciken da tayi cikib sanin ta Alheri za ta zaga sassa daban-daban na jihohin ƙasar nigeria da ma ƙasashen ƙetare, za ta yi gwagwarmaya da mutane mabanbanta, za ta ɗaukaka, kuma ƙarfin baiwa da tsafinta zai kareta daga duk wani abin cutarwa a duk inda ta shiga. Kuma ta gano Alheri za ta zama fitacciya gagara duniya ne a lokacin da ta cika shekaru ashirin da haihuwa, domin a lokacin ne zata iya sarrafa duk wani baiwa na tsafi da yake jikinta... abinda yake bata takaici da saka ta a cikin tunani da ɓacin rai bai wuce ganowar da tayi dole su rabu da juna ko tana so ko bata so, ƙaddarar zamanta da Alheri na shekaru biyu ne kawai...'
"Mama... come and see..."
Alheri ta ƙwalla mata kira daga inda take zaune. Da sauri ta nufi gurinta kamar ba tsohuwa ba idanunta ciccike da hawaye...
****** *******
Daga nan kawai sai hotonta da Mama Vero ya ɓace a idanunta sai wata walƙiya ta baiyana bayan washewar hasken sai Oga ya ganta sanye da kayan fulani a hannun wani dattijon makiyayi. Irin fulanin nan masu zagayawa da dabbobinsu da iyalinsu daga wannan jeji zuwa wancan jeji zuwa wancan jeji.
Da yake dattijon babban malami ne da ba ya sake da ambaton Ubangiji, mai yawaita ibada da addu'o'i hakan ne ya dakushe kaifin tsafin da yake jikinta. Da farko tana yawan firgita da tsorata a lokuta mabanbanta amma da ya tasa ta gaba da manyan addu'o'i sai ta fara komawa dai-dai, sam ba ta iya amfani da tsafin da yake jikinta sai asalin baiwar da Allah ya halicceta da su. Kamar misalin idan ta kalli abu da zafin rai cikin kankanin lokaci abin yake lalacewa, idan ta ji haushin mutum to tabbas wani mummunar abu sai ya faru da wannan mutumin ko da kuwa dabba ce.
Da Baffa ya fahimci yanayin halittarta sai yake ta cusa mata duk maganar da zata yi ta ringa ƙarawa da ambaton Allah hakan ne yake dakushe kaifin baiwarta ba ta lalata abubuwa kuma bata cika cutar da mutane akai akai ba.
A gurin dai wannan dattijo rayuwarta abar sha'awa cike da tarbiyyar musulunci har ta shekara biyar a gurinshi idan aka haɗa da biyun da tayi gurin Mama Vero shekarunta bakwai kenan, suna kiranta da suna Aisha. Nutsattsiyar yarinya mai cike da kamala da kyawawan halaye.
Juyin juya hali irinna ƙaddarar ta kamar yadda Mama Vero ta gano za ta rayu a mabanbantan gurare da mabanbantan mutane.
Wata rana ta raka matar Baffa Inna Danejo siyan ɓahe (kuka) a cikin kasuwa kawai ta sunɓule mata, haka taita garanba a cikin kasuwar daga ƙarshe da ta ji ta gaji ta lallaɓa ta buɗe wata kyakkyawar mota ta shige ciki ta kwanta luf a ƙasan kujerun bayan motar, nan da nan kuwa nannauyan barci ya kwashe ta. Ba tare da sanin akwai wata halitta a cikin motar ba Allex yaja motarsa ya bar cikin kasuwar zuwa gidansa da yake ɗirkaniya cikin garin kaduna.
Da farko sun firgita da ganinta amma a kallon farko Allah ya jefa musu matsanancin ƙaunarta a zukatansu, daman a tsawon aurensu shekaru goma basu taɓa haihuwa.
Dokas da mijinta Allex sunyi murna ƙwarai da wannan kyauta na ƴa sukutum da guda da Ubangiji yayi musu, dan sunyi tambayar duniya har coci sun kaita gurin pastor amma ta kasa faɗen takamaimai inda iyayenta suke. Abu ɗaya kawai suka fahimta, ita yarinyar musulma ce.
Nan fa ƙabilancin addininsu ya motsa, Pastor ya basu shawarar idan suka riƙe yarinyar nan da amana kuma suka yi ƙoƙarin maida ita mabiyiyar addinin kirista suna da gwaggwaɓar lada a gurin Allah, wai kuma Yeso zaiyi alfahari da su.
Da wannan dalilin suka ɗaura ɗamarar riƙe ta gam tare da mantar da ita duk wani harka na musulunci da addinin musulunci da ta sani a baya.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka fara cimma nasarar hakan, dan a lokacin shekarunta bakwai ne bazaiyi wahalar mantar da ita abubuwan da ta sani a baya ba.
Cikin shekara biyu da suka yi na riƙonta babu wata matsala sai ci gaba da suke samu ta ko wane ɓangare da alkhairai da dama, sun tabbatar tsintarta alkhairi ne a gare su. Sun bar ɗan madaidaicin gidan da suke da shi sun gina tamfatsetsen gida duk a nan ɗirkaniyar, sun mallaki danƙara danƙaran motoci na hawa da miyagun kuɗaɗe a asusun bankinsu.
Idan aka ga Alherin Mama Vero, Aishan Baffa Yallero, Happy ɗin Dokas da Allex kamar yadda suke kiranta babu wanda zai gane ta, saboda ta canza gaba ɗaya. Sun maida ita wata hutacciya ƴar gatan yarinya wacce ake mƙatuƙar ji da ita da gwada mata gata ta ko wane ɓangare...
A dai dai wannan lokacin ne kuma ta fara dama musu kunu da kwaɓa musu al'amura bayan ƙannin Dokas mata biyu sun koma hannunta da zama, gori suke mata a fili dan sun san ba yayarsu bace ta haifeta, abu kaɗan sai su sa hannu da nufin make ta.
Wata rana dai da ta zuciya ta kaiwa ɗaya daga cikinsu wani mugun shaƙa bata sake ta ba saida ta shaƙa mata ƙamshin mutuwa sosai sannan ta yarɓar da ita, Dokas kuwa ta zuciya ta yi ma Happy duka da dorina dan ta ladabtar da ita.
Tun daga nan lamuransu ya fara taɓarɓarewa, duk abinda suka taɓa sai ya lalace, duk yawan tattalin arzikinsu cikin ƙanƙanin lokaci ya taɓarɓare gaba ɗaya. A ƙarshe dai suka zauna su biyu suka yanke shawarar rabuwa da ita, shi ne suka ɗaɗɗaure ta suka ƙulle a buhu Allex ya fita da ita a mota ya biya wani yaronshi da cewar ya kaita can cikin musulmi ya hurgar da ita.
Walƙiya ne ya sake baiyana a cikin idanunta da tsananin haske, bayan ɓacewar komai sai ga hoton yadda Maman Ushe ta tsince ta, da irin abubuwan da sukai ta faruwa har zuwa haɗuwarta da Mary har yau da ya buƙaci Mary ta kawo mishi ita. Yana gama ganin komai ya saki hannunta kakkaifar hasken idanunta ya sake maka shi da jikin bango ya watsar da shi a sume a tsakar gurin.
Tana miƙewa tsaye da nufin barin gurin wani jiri mai ƙarfi ya kwashe ta ta zube a gurin kusa da ƙafafun Oga....
BILHAƘƘI
Bibi ce shimfiɗe a ƙasa a gaban gunkin tsafin shi kuma yana tsungune yasa gwuiwoyinshi a ƙasa, idanunshi a rufe, dungulmin hannayenshi duk biyun ya haɗe su guri ɗaya alamar roƙo, wani irin maganganu yake yi na tsafi sam ba a gane me yake cewa.
Can kuma sai yayi sujuda a gaban gunkin tsafin na tsawon daƙiƙu, ya ɗago ya sake gurfana gwuiwoyinsa a ƙasa ya ci gaba da surutan kamar yadda yayi da farko, tsawon wani lokaci yana a wannan hali sannan ya juyar da kansa gefe da gefe kamar wanda ya idar da sallah, cak ya ɗauki Bibi kamar wata ƴar tsana a kafaɗarsa ya fita da ita daga ɗakin tsafe-tsafen ya nufi gurin su Mary.
"Ki tafi da ita, kamar yadda na faɗa miki duk wata ɗaukaka da arziki na duniya da zaki nema yana tattare da wannan yarinyar. Za ki ji daɗinta, za ki sami abinda kike so, amma a tattare da samun abinda kike so akwai tsananin wahalar da za ta baki. Wannan kuma ƙaddararki ce."
Yana gama wannan maganar ya shafi cinyoyinsa ɓat ya ɓace a gurin kamar bai taɓa baiyana ba, su ma basu jira komai ba suka rungume Bibi idanunsu a rufe, nan take suka ɓace basu baiyana a ko ina ba sai a tsakiyar kan gadon Mercy.
Tun daga wannan lokacin duk wani abu da Madam za ta taɓa da niyyar sana'a dan samun kuɗi matuƙar Bibi ta amince da shi sosai yake samun karɓuwa agurin mutane, cikin ƙanƙanin lokaci ita ma aka fara kiranta tana amsawa, ta mallaki manyan kuɗaɗe da manyan gidaje a cikin kaduna da can garinsu kacia, daga ƙarshe sai ta tattara komai nasu ta koma can garinsu bayan Oga ya bata shawarar hakan, ya ƙara da ce mata a can ne Bibi zata haɗu da ƙaddararta.
Tamfatseten gidan rawa, haɗaɗɗen abinci, da kayayyakin shaye-shaye ta gina a fitacciyar unguwar Zame wando, inda ya zama nan ne matattarar duk wani shege da shegiya na cikin garin har ma da baƙi masu zuwa cin kasuwa, da ƴaƴan masu hannu da shuni. Unguwa ce da tayi fice sosai gurin samun duk wani nau'in kayan maye da ake buƙata, cikin ƙanƙanin lokaci GIDAN GALAR MADAM MARY ya samu mugun karɓuwa fiye da yadda tayi tsammani, ta ko wane fanni na sana'ar gidan, abinci, drinks, rawa tana da ma'aikata fiye da mutane goma. Aiki ake zuwa nema a gidan kamar yadda ake zuwa neman aikin gwamnati, dan ita ma sai mutum yana kwalin karatu mai kyau da hanyan na sama a gidan, kuma idan Bibi ta yaba da ƙwazon mutum sannan za ta duba in ka cancanta ta ɗauke ka da kyakkyawan albashi dubu talatin ko sama da haka, ya danganta da yanayin aikin da mutum zaiyi mata.
A daddafe ta sa Bibi makaranta mai shegen tsada ta ci gaba da karatunta har ta kammala Secondry, ta fito da mafi kyawun sakamako. Tun daga nan ta sa almakashi ta datse karatun, ta kaita gurin koyon rawa na musamman aka koya mata zafafan rawa da iya murguɗa duk wani komaɗo da lungu da saƙo na jikinta, a ƙarshe bayan ta ƙware sosai ta maida ita shugabar ƴan matan da suke rawa a gidan, nan da nan kuwa ta ƙara janyo manyan kwastomomi ƴaƴan masu kuɗi da su kansu masu ƙumban susan, dan idan Bibi tana rawa duk wani mai kallonta shagaltuwa yake yi, basa ji basa gani sai ita da tsananin sha'awarta dan tsananin gwanancewarta. Shi yasa duk ranar da zata yi rawa cika da tumbatsar da gidan yake yi daban ne da na kullum.
****** ******
"Oyoyo Madam Mary"
Ta faɗa tana sauke tattausar murmushi kamar ba ita ba.
Wani sabon takaicin ne ya sake ƙume ta, ƙoƙarin murmushi tayi da kumburraren fuskarta ta ci gaba da ɗingishi tana takawa zuwa cikin falon, jikinta babu inda baya ciwo saboda tsamin da jikinta yayi.
"Bibi ta"
Ta faɗa har lokacin murmushin bai bar fuskarta ba.
Gimtse dariyar da ya taho mata tayi, ta ajiye kofin tea da yake hannunta da sassarfa ta ƙarasa gurinsu ta rungume Madam.
"Jiya nayi kewarku, duk gidan ba daɗi saboda rashinku."
"Ayya... muma haka Bibi, bari in watsa ruwan zafi duk jikina ciwo yake min."
Ta zame jikinta a hankali duk zuciyarta a ƙuntace ta nufi saman Benen, suma Liyat babu wacce ta tsaya a gurin, ɗakunansu suka nufa duk suna ɗingishi dan gasa jikkunansu, a zukatansu bama-baman tsinuwa kawai suke saukewa Bibin, dan sun tabbatar duk ita ce silar wannan uwar wahalar da suka sha daga daren jiya zuwa yau.
"Ammm Madam..."
Sai kuma tayi shiru ta ci gaba da takawa a hankali zuwa inda ta ajiye kofin tea ɗin, kamar ba ita ce ta fara maganar ba ta ci gaba da kurɓar tea ɗin a hankali tana ta hurga idanunta a lungu da saƙo na falon ta share Madam da tayi poster a saman benen tana jiran jin me zata ce.
"Uhmm! ina jinki Bibi"
Ta faɗa a ƙagauce bayan ta sauke wani nannauyan numfashi.
"Ummm na ce kafin ki gargasa jikin ko zaki kira ma'aikata su gyara gurin can? na leƙa na ga ɓarnar da aka yi jiya ba kaɗan bane, a taƙaice dai gurin bashi ma da ko kyan gani. A gyara da wuri a tari galar yau ko? Nima na gama shiryawa"
Murmushin yaƙe wanda bahaushe ya ce ya fi kuka ciwo ta yi, ta taka a hankali ta dawo da baya har ta ƙarasa kusa da ita ta tsaya, ta kalle ta fuskarta ɗauke da wani irin yanayi na ƙoƙarin danne ƙuncin da yake danƙare a zuciyarta, a hankali ta fara magana kamar ba ta cikin damuwa.
"Ki huta abinki kawai Bibita. Saboda abinda ya faru jiya da har ya jawo rasa ran mutane biyu da mutane talatin marassa lafiya, DPO ya bada umarnin in dakatar da duk wasu harkoki da nake yi a gidannan har zuwa nan da wata ɗaya. Kuma duk waɗanda aka raunata ni zan ɗauki nauyin maganinsu da duk wani abu da zasu buƙata har zuwa lokacin da za a sallamesu daga asibiti. To duk wannan ba wani abin damuwa bane, Mu ci gaba da jin daɗinmu kawai, kafin wata ɗayan ya cika a hankali zamu ƙara ƙayata wajen fiye da yadda yake a baya, kin gane?"
Ɗaga kai kawai tayi alamun ta fahimta, a sace take kallon Madam ɗin har fara tattaka matattakalar tana ɗingisawa zuwa ɗakinta da yake saman Benen.
"Madam wai sun duke ku ne?"
Ta sake dakatar da ita da tambayar tana dariya ƙasa ƙasa.
Tagwayen tsaki take ta ja a zuciyarta, tayi banza da ita kamar bata ji tambayar ba ta cigaba da nufar inda tasa gaba.
"Madam..."
"Basu dake mu ba Bibi, amma mun kwana a takure a zaune cikin cell, ga azaba ta manyan saurayen da sukai ta bidiri bireɗe akan naman jikinmu, bayan duhu da tsananin sanyin da muka kwana a ciki. Da wannan dalilin yasa duk jikinmu ba inda