Showing 9001 words to 12000 words out of 98260 words
cikin jakar da ya ratayo a kafaɗa.
Sulallan gwal masu yawan gaske ta sallame shi da su zuciyarta cike da matsanancin farinciki.
Ya maida kayan matan jikinsa suka fice shi da Jakadiya Babba ba tare da ya bata ko tsinke tayi amfani da shi a matsayin magani ba.
Da yake an san girman matsayinta na Babbar Jakadiyar sarki babu wanda yake tare ta ko tambayar da wa take tare? ko da zasu shigo tun daga can ƙofar fada duk ce ma masu gadi tayi ƴar'uwarta ce, kuma ta sanar da Fulani kafin ta bata damar zuwa da ita, shi yasa ko gurin fita duk inda ta wuce sai dai a miƙa musu gaisuwa cikin girmamawa.
Sarauniya ta kalli Jakadiya bayan ta fitar da shi har can bayan gari ta koma cikin gidan sarki.
"Ni fa na fara gajiya da gafara sa banga ƙaho ba, amma Jakadiya kina ga shi wannan ɗin zai iya...?"
"A kul! kul Ranki ya daɗe. Hattara dai, ki iya bakinki. Ba a saka kokwanto ko shakka a cikin aikin Na shuri, idan kika yi haka ke da kanki zaki ɓata aikinki, ki zuba ido kawai ki yi kallon biyan buƙata."
Wani dariya tayi na jin daɗi tana ƙara ƙarfafawa zuciyarta yarda da aikin sabon bokan da Jakadiya ta kawo mata.
"Madallah da ke Jakadiya. Lallai kuwa idan buƙatarmu ta biya kamar yadda ya alƙarwarta mana baza mu taɓa mantawa da alkhairanki ba, zamu ɗaukaka darajarki a cikin gidannan, za ki kwankwaɗi romo da daɗin mulki irin wanda baki taɓa tsammani ba."
"Godiya nake ranki ya daɗe, Allah ya ida nufi. Ubangiji ya ja kwananki da na Yarima Muzaffar sarkin gobe a Bauchi bi'izinillahi. Alkhairi a jininki yake, kyauta halinki ne. Maƙiyanki sune fadawanki kina tafe kina take su a baya."
Kanta sai ƙara kumbura yake yi yana neman fashewa dan tsananin jin daɗin wannan kirarin na Jakadiya. Sai murmushi take yi tana huhhura hanci ita a dole ta fi su.
"Jakadiya a duba min wane hali Haye take ciki, a tambayi Raliya da fatan aikin da muka ɗora ta a kai tana gudanar da shi yadda ya kamata?"
"An gama Ranki ya daɗe"
Ta miƙe da zafin nama ta nufi sashen Sarauniya Safiyya, Amaryar sarki Abdulfatah, abokiyar zaman Sarauniya Safara'u.
***** ***** *****
HAYIN RIGASA, LAYIN MAI DUBUN TSUMMA. 19/6/2012
Tun daga nesa Maman Ushe ta zubawa buhun da take hange daga can nesa idanu, idan ba gizo idanunta suke mata ba sai taga kamar motsi buhun yake yi.
A hankali cike da takatsantsan da rashin tsoro ta sake gyara riƙon addar hannunta, ta ci gaba da tunkaran buhun gadan-gadan.
Ko da ta ƙarasa sai taga tabbas motsi buhun yake yi, alamun wani abu mai rai ne a ciki. Da sauri ta tsuguna ta fara kici-kicin kwance bakin buhun dan ceto rayuwar abinda yake ciki, ta fi tunanin wata dabbar ce.
Fara kyakkyawar yarinyar da tayi arba da ita an ɗaure bakinta tamau da tsumma an kulle idanunta yasa ta ja da baya a tsorace.
"Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahirrahmanirraheem"
Ta faɗa da ƙarfi tana sake kallon yarinyar da har lokacin bata bar juye-juye ba. Nan ta ci gaba da jan duk addu'oin da suka zo bakinta tana tofawa da nufin idan aljana ce ma ta ɓace amma taga ko gezau bata yi ba.
'Ina ga mutum ce'
Ta ayyana hakan a ranta sannan ta ƙarasa da sauri ta zaro ta daga cikin buhu ta fara ƙoƙarin kwance mugun ɗaurin da aka mata.
Yarinyar ta riga ta galabaita dan haka ta sunkuceta da sauri ta saɓa ta a baya, a maimakon ta ƙarasa cikin daji dan ɗiban ganyayyakin magunguna kamar yadda ta saba sai ta koma cikin gari ta nufi gidansu.
Wani matashi da bai wuce shekaru ashirin da biyu ba yana tsungunne yana wanki a tsakar gidan ya kalleta fuskarsa cike da fara'a bayan ya amsa sallamarta.
"Maman Ushe barka da dawowa, yau dai kin dawo da wuri. Allah yasa kin samo min sassaƙen gamjin..."
"Amma dai Musa baka ji daɗin halinka ba, kai kam anyi ɗan banzan yaro mai kunnen ƙashi. Ban hana ka shiga harkar ƴar mai ganyen nan ba?"
Mahaifiyarshi Indo ta katse shi cikin masifa tana bankawa Maman Ushe harara kamar idanunta zasu faɗo ƙasa.
Ita ma ba kanwar lasa bace, ba a taɓa ta ta ƙyale, ba a nuna mata yatsa bata karya ba. Amma da yake tana cikin wani sha'anin ko kallonsu bata yi ba, kai tsaye ɗakinta ta nufa ta kwantar da yarinyar a kan yaloluwar katifar da take shimfiɗe a tsakar ɗakin.
Shi kuwa Musa tura baki yayi yana ƙunƙuni kamar ƙaramin yaro ya ci gaba da jiƙa-jiƙan wankin da yake yi, daman ba kayanshi bane, kayan Indo ne.
Waje ta fito ta girgije tokan abin girkin gawayinta ta ɗora ruwan zafi dan ta yi ma yarinyar wanka.
"Musa kallamu saƙonka bai samu ba, Allah cikin ikonsa ko cikin dajin sosai ban shiga ba nayi gam da katar da kyautar Allah. In taƙaice maka dai rabo na minallahi ƴa daga sama nutsattsiya..."
"Ahayye nanaye. Ƴa dai Karimatu?"
Indo ta katse ta da shewa dan tana ganin surutan banza kawai take yi, dan ta share wa kanta tantama kawai sai ta bankaɗe labulen ɗakin dan gane wa idanunta.
"Na shiga uku ni ƴar gidan mutum biyu jikar mutum huɗu. Karimatu wani bala'in ne kika kwaso mana haka?"
Tayi mata tambayar bayan ta ja da baya a tsorace ta ɗora hannunta bibbiyu a ƙirjinta tana zazzare idanu.
Ita dai Maman Ushe bata ce komai ba ta cigaba da haɗa wuta tana ƴan waƙe-waƙenta zuciyarta cike da nishaɗi.
Musa ma ɗauraye kumfar hannunsa yayi yaje zai shiga ɗakin dan ganewa idanunsa da sauri Indo ta janyo shi baya, ta fara zazzaga mishi bala'i ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.
"Dan ubanka baka da hankali ne? kana ganin yarinyar da kamannin aljanu kake ƙoƙarin shiga inda take? yi sauri ka kira Malam yazo ya kashe wannan gobarar dan wallahi bazan zauna da aljana a gida ɗaya ba"
Ta ƙarasa maganar haɗe da fyalla mishi mari a ƙeya.
"Wai ke Indo sai ki ringa dukan mutum kiyi ta mishi masifa bai yi miki komai ba."
Ya faɗa cikin ƙunƙuni lokacin da ya kama hanyar ficewa daga gidan.
Cikin minti talatin Maman Ushe tayi wa yarinyar wanka da ruwa mai tsananin zafi ta gargasa mata jiki. Duk inda ta bi a tsakar gidan Indo sake mata habaici da baƙaƙen maganganu take yi amma ita ko a jikinta wai an tsikari kakkausa, a ƙarshe ma Indon gajiya tayi ta shige ɗaki tana jiran isowar Malam.
Ita kuwa ta ɗauki sabon kayan Ushe guda ɗaya da ta ajiye dan ta ringa tunawa da ita tasa mata, kayan suka zauna mata cas a jikinta kamar dan ita aka ɗinka su. Riga da sket na ƴan kantin da ta cire mata kuma ta tsoma a ruwan wankan ta wanke su tas ta shanya.
Ragowar kamu ta ɗauko a ɗakinta ta dama kunu tasa suger kaɗan ta fara ba yarinyar da har lokacin bata gama farfaɗewa ta dawo cikin haiyacinta ba, tana rungume da ita a jikinta take bata kunun tana jifanta da murmushi lokaci bayan lokaci, ta karɓa ɗaya biyu kawai sai ta fara kwara amai.
A dai-dai lokacin kuma mai gidansu Malam Tanimu ya sawo kai cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama.
Daga cikin ɗakinta ta amsa sallamar tana yi ma Malam sannu da zuwa, cike da ƙauna yake kallonta da yarinyar, bai matsanta da jin komai ba kawai sai ya ɗauki buta ya zagaya banɗaki.
Ita kuwa ba tare da damuwa ba ta sako ragowar ruwan zafin ta ɗauraye mata jiki ta canza mata kaya, ta kwance kuɗi a haɓar zaninta taba Musa saƙon kayan shayi.
Ta sha shayin kaɗan kafin wani wahalallen barci ya ɗauketa a jikin Maman Ushe, ganin haka ta kwantar da ita a kan katifar ta nufi gurin Malam da ya ce idan ta gama yana jiranta.
Cikin nutsuwa da balagar iya furta tausasan kalamai ta gama kora musu bayanin duk yadda aka yi ta tsince ta, ta ƙara da cewa.
"Waɗanda suka yasar da ita da alamun hallakata suka so suyi, domin irin mugun ɗaurin da suka yi mata ba na wasa bane. Amma da yake tana da sauran kwana da shan ruwa a gaba cikin hikima ta Ubangiji ya tserar da rayuwarta ta hanyar haɗani da ita.
Da wannan nake roƙon alfarmarka Malam in dai babu damuwa dan girman Allah ka barni in riƙe ta, Allah ya sani a kallon farko da na yi mata naji nutsuwa, ƙauna, matsanancin tausayinta duk sun mamayi zuciyata. Idan kuma kana ganin akwai damuwa a riƙonta da zanyi sai in haƙura, umarninka abin bi ne a gurina."
Tun ɗazu take yunƙurin yin magana Malam yake dakatar da ita, daga ƙarshe ma har sai da yayi mata ƙwaƙƙwaran jan kunne ta hanyar ce wa idan ta sake yunƙurin cewa uffan ba tare da karima ta gama magana ba zaiyi mugun saɓa mata, dole ta haɗiye maganganunta, domin kura ta san gidan mai babban sanda, Malam ɗin tsayayyen namiji ne a gidansa da sam baya ɗaukar wargi daga gurin ko waccensu.
"Gaskiya bazai yiwu ba, taɓɗijan! ta ya daga tsinto yarinya a dawa baki san mutum ce ko aljana ce ta fito da siffar mutane ki ce zaki riƙe ta a gidannan? sam hakan bazai yuwu ba gaskiya. Ko dai ki san nayi da ita ko kuma ki maida ta inda kika ɗaukota..."
"Saboda nan gidanki ne?"
Ya katse ta yana bin ta da kallon mamaki.
Ta zunmɓuro baki gaba kamar shantu, ranta a ɓace, zuciyarta a ƙuntace ta ce.
"Amma Malam..."
"Amma me? Aisha ki fita daga idona in rufe. Tun kafin in saɓa miki ki fita daga batun yarinyar nan"
Ya faɗa yana nuna mata ƴar yatsarsa manuniya alamar gargaɗi. Sai kuma ya maida hankalinsa kan Karima ya cigaba da magana.
"Allah yayi miki albarka Karima, haƙiƙa taimako ko da niyyar aikata shi kika yi Allah zai baki lada balle kuma ki aikata taimakon, Allah ya miki albarka."
Cike da jin daɗi ta amsa da
"Ameen Malam"
Kyakkyawar fahimta ke a tsakaninta da mijinta, shi yasa ko da Indo take ta zage-zage da habaici bata maida kai ta kalle ta ba. Ta san in kowa a gidan zai ƙi fahimtarta Malam zai fahimceta, kuma zai goya mata baya ya ƙarfafa mata gwiwa idan har tana da gaskiya.
"A halin yanzu dai bani da ikon yarje miki ki ci gaba da riƙon yarinyar nan har sai munje da ita gurin mai unguwa, duk abinda ya zartar a kanta dole zamu yi haƙuri.
Domin ba abin mamaki bane yarinyar sato ta aka yi, iyayenta suna can cikin tashin hankali da damuwar rashin sanin inda take, kinga idan muka riƙe ta ba tare da cigiya ba munyi zalunci. Kin fahimce ni?"
Ta ɗaga kai a sanyaye alamar eh ta fahimce shi.
"Dan haka ki shirya bayan an idar da sallar magriba muje gidan mai unguwa, in Allah ya yarda ma zuwa lokacin ta dawo cikin haiyacinta, ƙila baza mu rasa bayanin inda iyayenta suke ba, dan naga a ƙiyasce zata iya kaiwa shekaru goma sha biyu."
BILHAƘƘI
"To Malam, duk yadda ka ce haka za a yi. Allah yasa mu dace."
Ta faɗa a ladabce, kanta a ƙasa.
"Ameen Karima"
"Gaskiya Malam idan ka ce a gidannan za a riƙe tsintacciyar nan zaka haddasa mummunar bala'i da masifan da idan ta taso duk unguwar nan baza su iya kashe wa ba. Ehe ! haka kawai ina da ƙananun ƴaƴa mata baza a jajubo tsintacciya a haɗa su min da su ba, yo wa ya sani ma ko ƴar gaba da fatiha ce? Wallahi bazai yiwu ba, maganin kar a yi kar a kuskura a fara."
"Kin gama?"
Ya tambayeta yana kallonta da mamakin tsabar rashin kunyar da take mishi ganin yadda ta miƙe tana masifa tana girgiza kafaɗu a gabanshi.
"Eh na gama, fatan za a bi abinda na ce dan a zauna lafiya."
"Indo?"
Ya kira ta yana sake gyara zamanshi.
Bata amsa ba sai ta waiga ta kalle shi alamar tana jinshi.
"Nan gidan waye?"
"Gidanka ne gadon ƴaƴana nan gaba kaɗan"
Ta amsa kai tsaye ba tare da damuwar abinda zaije ya zo ba.
Ya miƙe tsaye ya tsaya daf da ita
"Da kyau! To tunda sai can gaba ne gidan zai zama gadon ƴaƴan naki har yanzu yana matsayin gida na ne ko? to kashaidi na farko kuma na ƙarshe muddin kika ƙara kuskuren furta baki yarda a riƙe yarinyar nan a gidannan ba wallahi zaki koma gidan iyayenki. ƴaƴan da kike faƙaƙa da su kuma in tattarasu in ba Karima ta riƙe da tsintacciyar da kike magana, sai inga yadda zaki yi da ni"
Yana gama faɗin haka ya zura takalmanshi ya ɗauki buta ya shige cikin bayi, ya barta a gurin tsaye baki buɗe kamar mutum-mutumi.
Maman Ushe ma ɗakinta ta shige ta ƙyale ta a tsaye a gurin.
Kamar yadda Malam ya faɗa suna idar da sallar magariba ya tasa ta a gaba ta goya yarinyar suka nufi gidan mai unguwa, da yake tafiyar babu nisa nan da nan suka isa gidan.
"Mu ga yarinyar?"
Mai unguwa Mukhtar ya faɗa bayan Malam Ali ya gama kora mishi bayanin duk yadda aka yi mai ɗakinsa ta tsintota, nan da nan Maman Ushe ta kwanceta daga baya ta riƙo ta a hannu, sai ta miƙawa Malam ita shi kuma yayi niyyar miƙa ta ga mai unguwa, shi kuma ya dallare ta da tocilan hannunshi.
Kuka ta sanya mai ƙarfi ta maƙale a jikin Malam alamun ita baza ta je ba, sai ma fara ƙoƙarin zillewa a jikinsa za ta koma gurin Maman Ushe har lokacin bata daina kukan ba, da sauri ta karɓe ta tana rarrashinta.
"Ma sha Allahu, ga yarinyar tubarkallah da ita. Ta faɗa muku sunanta ne?"
"A'a! Tunda ta dawo cikin hayyacinta bata yi magana ba, sai dai kuka kamar yadda ka ga tana yi yanzu."
Malam Ali ya bashi wannan bayanin.
"Ubangiji Allah ya baiyana iyayenta"
"Ameen ya Allah"
Malam da Maman Ushe suka amsa addu'ar cikin haɗin baki.
"Kuna sha'awar riƙe ta ne kafin Allah ya baiyana iyayenta ko zaku barta a nan gurin iyali na?"
Ya sake tambayarsu yana kallon yadda tayi luf a jikin Maman Ushe kamar ƴar kyanwa.
"Karimatu tayi niyyar riƙe ta tsakani da Allah har zuwa lokacin da iyayenta zasu bayyana."
"To madallah! hakan yayi kyau, ba laifi."
Ya amsa yana sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, domin tunda suka fara bayanin sun tsinto ƴa abinda ya fara tunani
'cikin matansa uku da bataliyar ƴaƴansu ashirin da ɗaya a wani ɗaki zai jefa ta? Zaman gidan nasa da ake yi ta kai ta kai ko wace uwa ƴaƴanta ta sani, 35% ya ɗauke a batun duk hidindimun da Allah ya ɗora mishi matan a dole suka ɗauki 65% na hidimarsu da ƴaƴansu, da wannan babban dalilin yasa sam bashi da ta cewa a gidanshi.'
"Yanzu abinda za a yi ku koma da ita, gobe idan mai duka ya kaimu zan turo yaro mai ɗaukar hoto ya ɗauki hotonta, da hoton kayan da aka tsinceta da su. Ki kuma bashi taƙaitaccen bayani na dai-dai inda kika tsinto ta dan zamu bada cigiya ne a gidan radio da talabijin ko Allah zai sa a gano iyayenta. Dan Allah Malam Ali ku ji tsoron Allah gurin riƙonta, ku kwatanta adalci tsakaninta da ƴaƴan da kuka haifa, ita amana ce a gurinku."
"In Allah ya yarda Yallaɓai, mun gode ƙwarai. Allah ya ƙara girma."
Suka sake haɗe baki gurin yin godiya. Nan ta sake goyata a baya suka koma gida zukatansu fal da farin ciki, tsananin ƙaunar ƴar tsintuwar da Malam yake gani a idanun karima yasa shima ya ji yana ƙaunar ƴar, da gaske fa son mace yana sa namiji ya so duk abinda take so.
Sun koma gida ana daf da kiran sallar isha'i, a lokacin Indo ta cika tayi tam, dan ranar girkinta ne. Sai tsaki take ja ƙasa ƙasa tana tsoron yin magana a kaɗa ta gidan tsoho.
Maman Ushe ko kallonta bata yi ba ta shige cikin ɗakinta, zuciyarta cike da farin ciki.
****** ******
Sati uku tsakani duk cigiyar da ake yi ko wanda ya san iyayenta ba a samu ba balle iyayenta. A lokacin ta riga ta zama ƴar gida, ta sake sosai tana wasanninta a cikin yara, sai dai har lokacin bata magana, idan abu ya bata dariya sai ta yi, kuka ne bata yi ko da abu ya ɓata mata rai.
"Amira zo muje ki yi alwala, kinji an kira sallar la'asar ko?"
A hankali ta ɗago fararen idanunta ta kalle ta. sai kuma ta miƙe a hankali ta bi bayanta zuwa cikin gidan.
Butoci biyu Maman Ushe ta ɗauko ƙarami da babba, ta bata ƙaramin ta fara alwala da babban.
"Ki ringa yin kamar yadda nake yi kinji?"
Ɗaga kai kawai ta yi alamar ta ji tana wasa da ruwan butan.
Tunda ta lura daga alwala har sallah yarinyar bata iya ba a hankali take koya mata komai na dangane da addini, ƙananun abubuwa waɗanda ya kamata yara su sani, duk da bata iya magana amma hira take yi da ita kamar mai baki, kuma wani abin daɗi duk abinda tace mata tana fahimtar abinda take nufi, amsawa ne kawai bata iya yi.
Wata-rana suna zaune ta haɗa mata tea tana firfita mata da ɗayan kofin
"Amira ƴan matan Mama, ji da ke nake yi kamar tsoka ɗaya a miya, Allah ya buɗa min bakinki Malam ya kaiki makarantar islamiya da boko."
Kamar daga sama ta ji ta ce
"Ma...ma?"
"Laaa... Alhadulillah ! Amira magana kika yi? Mama kika ce min? Allah na gode maka, sake