Showing 69001 words to 72000 words out of 98260 words

Chapter 24 - BILHAQQI

Start ads

05 Sep 2025

224

Middle Ads

yi kamar ana caccaka mishi kibiya. Kanshi kuwa kamar ana sarawa da guduma.

A daidai wannan lokacin wani yaron fulani ya shiga cikin bukkar hannunshi ɗauke da ƙoƙon da aka shaƙe da damammiyar fura da nono.

Da sauri ya koma ya sanar da Baffansa ganin halin da na kwancen yake ciki. Ba tare da wani ɓata lokaci ba kuwa ya biyo shi da sauri suka koma bukkar.

Suna shiga shi kuma cikin zafin nama ya miƙe tsaye, har lokacin bai sake kansa ba, idanunsa sun kaɗa sunyi jazur saboda azabar da yake ji a jikinsa. A zafafe ya nufi hanyar fita daga bukkar da sauri dattijon ya riƙe shi yana tambayarshi lafiya?

Ya fara kici-kicin ƙwacewa sai kuma ya ƙwalla ihu jikinsa ya sake gaba ɗaya a jikin dattijon da yake riƙe da shi.

"Baffah kamar ya mutu ko?"

"Bai mutu ba Bello. Yi sauri gurin Yafendo ka ce ta baka ruwa mai sanyi da magungunan Tukurere ka kawo min yanzunnan."
Hankalinshi a tashe ya kwantar da shi a kan tabarmar yana mishi firfita. Sai tattaɓa saitin zuciyarsa yake yi da duk inda ya kamata ya taɓa don jin yana raye ko ya mutu?

Manyan samari biyu ne suka biyo bayan Bello suna riƙe da magungunan da ruwan sanyi a kwanon sha na roba mai murfi.

Ba tare da duba yawa ko sanyin ruwan ba yana amsa a hannunsu gaba ɗaya ya sheƙawa wanda ya kira Tukurere a jiki.

Nan take ya ja wani nannauyan ajiyar zuciya alamun ya farfaɗo. Ko kafin ya buɗe ido ya dawo hayyacinshi sun buɗe bakinshi sun ɗura mishi wani magani da yake jiƙe a cikin gora.

Idanunshi a rufe wani ƙaƙƙarfan amai ya taho mishi da sauri Baffa ya tallabe kanshi ya karkata gefe ɗaya yayi ta kwara aman mai haɗe da wasu baƙaƙen gudaji mai kama da jini a ciki. Ko kafin ya gama aman ya galabaita da ƙyar suka samu aman ya tsaya.

Ruwa mai rangwamen zafi aka kai bayan bukka Baffa ya umarci Matasan nan biyu suka taimaka mishi yayi wanka ya canza kaya. Daga haka kuma sai wani nannauyan barci ya kwashe shi.

Bai farka ba sai bayan sallar azahar, har lokacin su Baffa suna zagaye da shi, ganin ya farka yasa duk suka matsa jikinsa suna jera mishi sannu da tambayar yanayin jikinshi.
"Tukurere ka tashi? Sannu! ya jikin naka?"

Wawwaigawa shi ma ya fara yi don ganin wanene suke kira Tukurere sai yaga shi ɗin dai suke kallo. Da mamaki a fuskarsa ya kalli tsohon
"Ni ? Sunana Mustapha. Babana sunanshi Abdulfah! Babana ne sarkin garin Bauchi. Ina ne nan? ku kuma su waye?"



BILHAƘƘI


Da mamaki matasan suka bi shi da kallo. Duk tunaninsu ɗaya
'Ko dai ya samu taɓin hankali ne daga farkawarsa?"

Shi kuwa Baffa sai dariya yake yi yana godewa Allah.
"Ma sha Allahu! Yau dai Allah yayi Tukurere tunaninka ya dawo bayan tsawon shekaru goma sha tara da kayi tsakanin mare hankali da mai hankali. Kwantar da hankalinka, mu ba masu cutarwa bane a gare ka. Muna nufinka da alkhairi ne a ko wane lokaci. Yanzu dai kafin inyi maka bayanin komai bari a kawo maka abinci ka ci."

Da idanu ya raka su yana ta jujjuya maganganun tsohon a ransa har suka fice daga ɗakin.
'Shi Mustapha ya ga ta kansa! shi ne yayi shekaru goma sha tara tsakanin hauka da hankali?'

Babu jimawa dattijon ya koma cikin bukkar matasan suna biye da shi. Tuwon dawa ne mai zafi-zafi da alamun ba a daɗe da kwashewa ba da miyar busassar kuɓewa.

A hannun Baffa kuma kofin ruwa ne. Ruwan ya karɓa ya fita bakin bukkar don kuskure baki da wanke hannu. Nan ya tsaya yana ƙarewa rugar kallo. Bukkoki tsilli tsilli ne daga inda yake tsaye, sai can nesa ya hangi wasu tarin bukko ki, a gefe guda kuma akwai tarin dabbobi.

"Tukurere me kake yi? kazo ka ci tuwon mana kada ya huce."

Ya ji muryar Baffa daga cikin ɗakin yana mishi magana, wani ƙunci ne ya tsunguli zuciyarsa.
'Tukurere'
Ya maimaita sunan a ransa cike da ƙyamar sunan, jin sunan yake yi yana neman saka shi amai. Da sauri ya wanke bakin ya koma cikin bukkar.

Tunda ya yanki lomar farko na tuwon ya dangwali miya ya kai baki bai sake marmarin ci ba. Tun basu fahimta ba har suka gane bazai iya ci ba.

Ko kaɗan hakan bai ƙona zuciyarsu ba
"Ko a kawo maka fura da nono?"

Da sauri ya ɗaga kai alamar eh.

Nan da nan aka amso mishi gurin Yafendo uwargidan Baffah. Ya sha sosai kaɗan ya rage ya ajiye ƙwaryar ya ce ya ƙoshi.

Tsohon ya ƙara kallonsa da tattausan murmushi a fuskarsa.
"Kana buƙatar ƙara hutawa ne kafin ka ba mu tarihinka ko za ka iya ba mu yanzu?"

A nutse ya buɗe bakinsa ya fara warware musu labarin tarihin rayuwarsa, tun daga kan nasabarsa, zuwa yadda ya bar masarautarsu a ranar ake murna da bikin cikarsa shekaru goma sha biyar. Da yadda yaita gararambar rayuwa da buga-buga a sassan jihohi daban-daban har Allah ya aje shi a Jihar kaduna, ƙaramar hukumar kajuru, a ƙauyen kasuwar magani. Da yake gari ne mai arzikin noma da kasuwanci sai Allah ya haɗa shi da abokai na gari, iyayensu suka riƙe shi kamar su suka haife shi ba tare da tuhumar waye shi ko kuma daga ina yake ba.

Babbar kasuwar ƙauyen da take ci duk ranar alhamis a can ya haɗu da Rebecca tana kai tallen dafaffiyar doya da kunun zaƙi. Shi kuma a lokacin baro yake turawa, saboda tsaftarta da nutsuwarta yasa suke siyan abinci a gurinta daga bisani kamar wasa Allah ya sarƙa soyayya mai tsanani a tsakanin zuciyoyinsu.

Babban abinda ke damun ƙauyen kasuwar magani yawan rikici a tsakanin arna da musulman garin, duk wadataccen zaman lafiyar da yake tsakaninsu akwai mummunan ƙabilanci a zukatan cristian ɗin ƙauyen. A ko wane lokaci idan rikici ya tashi yunƙurinsu su kori duk wani bahaushe da yake ƙauyen da ƙananun ƙauyukan da ke kusa dasu, irinsu Kallah, Rimau, Gefe, Dutsen gayya, da sauran ƙauyaku.

Wata rana afujajan wasu ƴan mata biyu mazauna kasuwar magani da suke soyayya da yaran hausawa abokan Mustapha suka je masallaci da cewa za su musulunta. Saboda samarinsu sun yi alkawarin za su aure su matuƙar suka musulunta.

Wannan shi ne abinda ya tada mummunan rikici a garin bayan an musuluntar da su. Da yake ko wani lokaci musulunci sama yake da kafurci kuma Allah yayi alƙawarin zai ka re addininshi a faɗin duniya musulmai ne suka yi nasara, cristian sun yi asarar rayuka sosai kuma basu ci nasarar dawo da ƴaƴansu ba. Da wannan damar Mustapha yayi amfani ya gudu da Rebeccah Cikin kaduna aka shiga da su gidan Musuluntattu ita da sauran ƴanmatan. Wani Alhaji mai yawan taimakon addini ya ce idan aurensu ya tashi a faɗa mishi zai yi musu kayan ɗaki na kece raini.

Wata uku bayan rikicin aka ɗaura musu aure a masallacin musabaƙa da ke Kinkinau. Sauran samari biyun suka ɗauki matansu da suka musulunta ɗaya ya zauna a garin kujama da ke ƙaramar hukumar Chikun, ɗayan ya koma kasuwar magani da zama, shi kuwa Mustapha da matarsa Rebeccah da har lokacin bata mususulunta ba nan cikin garin kaduna ya zauna. Hayan ɗaki mai sauƙi ya nema a tudun wada, sai ya shiga kasuwar bacci gurin abokansa ƴan gwanjo da ya saba da su tun a kasuwar magani ya basu ƴan kuɗaɗen hannunshi suka tallafa mishi ya fara buɗe dilar gwanjo na kayan yara.

Da yake yana da nasibi a harkar nan da nan ya fara samun ƴan kuɗaɗe suka ci gaba da rayuwarsu cikin rufin asiri shi da matarsa Rebeccah.

Duk bayan sati biyu yana leƙawa kasuwar magani ya gaisa da abokan arziki ya kaiwa waɗanda suka riƙe shi a matsayin ɗansu ihsani. Bai je garin da Rebeccah ba sai da suka shekara ɗaya da rabi da yin aure, lokacin tana ɗauke da tsohon cikin haihuwa yau ko gobe. A lokacin kuma gari yayi lafiya kamar ba a yi wani rikici ba, da wannan ƙwaƙƙwaran dalilin ya sa yaje da ita garin don ta gaida iyayenta. A tunaninshi komai ya wuce, kuma tunda bata musulunta ba zai sa su rungumeta su rungumeshi a matsayin suruki ba tare da ƙyama ko tsangwama ba.

Da suka kwana biyu a Kasuwan magani ya ce su je ƙauyenta ta ce a'a tana jin tsoro. Yayi yayi ta ce ita dai baza ta ba, sai da yayi fushi sosai sannan ta amince suka tafi ƙauyen tana cike da taraddadi.

Wani tsohon ɗan ƙaramin gida da yake can ta bayan gari ginin ƙasa da ta gada a gurin Mahaifiyarta kafin ta mutu a nan suka sauka. Sai da suka huta sosai sannan ta je da mijinta suka gaida Babanta da ɗanuwanta. Yadda suka karɓe ta a wulaƙance ne ya ƙara sanyayar mata da jiki, har suka koma gidan da suka sauka tana mita da ƙorafin ita ba dan shi ba wallahi baza ta je garin ba. Yana murmushi yake tausarta da rarrashinta, basu daɗe da zama ba gaf da magriba sai ga ɗan aike wai Mustapha ya je. Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma, cikin rashin nutsuwa ta ce kar ya je, dan tana tunanin akwai wani abu na mugunta da ɗan'uwanta Zidane da mahaifinta suke ƙullawa.

Bai saurareta ba ya fice ya bi bayan ɗan aiken har zuwa ɓoyayyen gurin da Zidane da abokansa suke maƙale.

Tashin hankalin fitarshi da tunanin abinda ka iya zuwa ya dawo yasa naƙuda ya taso mata gadan-gadan bayan fitarsa. Cikin hikima ta Ubangiji sai ya dube ta ya kawo mata haihuwar da matuƙar sauƙi, da yake a gidan da suke haya a kaduna su uku ne, ita, wata tsohuwar ma'aikaciyar unguwar zoma, sai wata matashiyar mata mai ƴaƴa biyu. Tsohuwar ta sha kwatanta mata yadda za ta gyara kanta idan ta haihu babu kowa a kusa da ita, wannan ɗayar matar ma da ta ƙara haihuwa kusan komai a gabanta aka yi ta ga yadda ake yanke cibi da goge jikin jariri. Nan da nan ta yanke cibi ta goge jikin jaririyar ta naɗe da jallabiya, ta gyara jikinta ta tsaya jiran ganin da yanayin da Mustapha zai koma gidan.

Tsawon awa biyu da rabi suka ɓoye shi a gurin, sai da dare ya fara shiga sosai babu wani musayar ra'ayi a tsakani Zidane ya soka mishi wata kakkaifar wuƙa a cikinshi, suka sake shi bayan sun ce mishi idan zai iya ya koma gida za su zo har gidan su haɗa shi da tsinanniyar matarshi su ƙona su da ransu. Idan kuma ya mutu a hanya za su kaiwa Rebeccah gawarshi su ƙona shi tare da ita. (Idan baku manta ba daga inda ya koma gida a wahalce muka fara labarin littafin)

Mustapha ya gyara zama ya ci gaba da cewa
"Babban abinda yake bani mamaki a rayuwata tun bayan barowata masautarmu sam na kasa faɗawa kowa daga inda na fito. Kuma da farko-farkon barowata duk sadda na fara tunanin ya kamata in koma gida sai inji wani masifaffen ciwon kai da tsananin son in sake lulawa can cikin duniya. Da wannan dalilin yasa na daina tunanin komawa masautarmu.
Lokacin da na tarar Rebecca ta haihu ne naji a raina ko ni ban koma gida ba ya kamata gudan jinina ta san asalin Ubanta. Musuluntar matata Rebeccah a wannan daren shi ne abinda ya ƙara tabbatar min lallai zan mutu da farin-ciki. Da na yi yunƙurin faɗawa matata daga inda nake sai naji kamar an naɗe min harshe da wani mugun ƙulli, dole sai masarautar Maru ta jihar zamfara na iya faɗi saboda mahaifiyata tana da danganta da can masarautar. A wahalce na samu na yiwa ƴata alamar da idan an gani a masarautarmu za a yadda ita ɗin gudan jinin Mustapha ne. Daga sama-sama na ke jin abinda yake faruwa har zuwa lokacin da na fice a hayyacina gaba ɗaya ban ƙara sanin me yake faruwa ba."
Ya tuɓe rigarsa ya nuna musu ta shi alamar a ƙirji sak irin wacce yayi wa Bilhaƙƙi. Daga nan yayi shiru alamun ya gama basu labarin.

Ko da Baffa Yalleru ya fahimci ya gama basu labarinsa mai cike da al'ajabi sai ya gyara zama shi kuma ya ci gaba da cewa
"To kaga a daidai wannan lokacin da tunaninka ya ɗauke ka suma? A daidai lokacin Allah ya nufi ɗan'uwa Ilyassa'u ya kai maka ɗauki da taimakon gaggawa. Mutum ne da tun kafin a haifeshi aljannu suka shafe shi a cikin mahaifiyarmu. A bayan haihuwarsa kuma bayan tsananin wahalar da Innarmu da suka yi gurin nema mishi magani sai kwatsam suka buɗe mishi idanu yana ganin abubuwa da yawa da mu mutane ba ma gani.

Tun yana ɗan shekaru ashirin ya bar gida ya koma bin jeji daga wannan zuwa wancan, rayuwarsa a cikin daji yake gudanar da ita. Sam ba ya kaunar zaman cikin gari, tun mahaifiyarmu tana ƙorafi akan ya dawo gida har ta haƙura ta ƙyale shi.

Wata rana a hanyarsa ta wucewa ne ya ganka kwance a cikin wani ƙaramin gida, a waje kuma ga wasu matasa nan suna ta watsawa gidan kalanzir da alamun ƙona gidan za suyi. Ko da ya tattaɓa ka ya fahimci mummunan halin da kake ciki ba tare da tunanin komai ba ya ɗauke ka ɓat kuka ɓace daga gurin.

Shi ya fara maka maganin sukar wuƙan da yake cikinka, daga baya kuma ya kawo min kai, ya ja min kunne akan lallai duk runtsi in kasance tare da kai. Ya faɗa min mummunan sammu da jifa ne a jikinka amma in Allah ya yarda lokacin warware asirin ya kusa zuwa.

Haka na ci gaba da yi maka magani ina kula da kai ni da iyalina har ka warke. Ko da ka warke kuma sai ka zama wani irin mutum ba mai hankali ba ba mahaukaci ba, ba ruwanka da kowa. A haka ka rayu har zuwa yau da ka dawo haiyacinka. Kusan shekaru goma sha tara ke nan kana tare da mu."

Tunanin irin gararamba da yawon da yayi guri-guri tun yana da ƙananun shekaru har zuwa yau da ya fara manyanta, tunanin a wane hali yanzu iyayensa da ƴan'uwansa suke ciki? tunanin a wane hali matarsa da tilon ƴarsa suke ciki? Waɗannan tunane-tunanen su suka haɗu suka dagula duniyar nutsuwa da ɗan guntun walwalarsa. Da ya rasa me zaiyi kawai sai ya fashe da wani ƙaƙƙarfar kuka kamar ƙaramin yaro.

Basu dakatar da shi ba, sun san ya cancanta yayi kukan ko dan ya rage damuwar da ke cin zuciyarsa. Matasan nan da suke masu shekaru ashirin da ƴaƴaye su kansu girma suka yi suka ganshi a rugar, basu taɓa tsammanin babban al'amari ne haka a tattare da shi ba. Sai sharar ƙwallah suke yi cike da tausayinsa.

Baffah ne ya dafa kafaɗunsa ya ce
"Tukurere kukan ya isa haka. A ganina godiya ya kamata ka yi wa Allah da ya sa ka dawo cikin hankalinka, kuma har yanzu kana raye. Ka ga waɗannan manyan damarmaki ne da zasu sa ka sake haɗuwa da duk ababen da ka rasa a rayuwarka. In Allah ya yarda.

Ka huta zuwa gobe, ayi maka aski a yanke maka akaifa, ka samu nutsuwa jibi idan mai duka ya kaimu sai mu ɗauki hanyar tafiya can garin naku. Domin daga nan tafiya ce mai tsawo da tsananin nisa."


******** *******


Ba tare da tsoron tsalawar da dare yayi ba ta ci gaba da zagaye duk wani lungu da saƙo na cikin babban gidan sarautar. Sai mamaki take yi ganin gida gari guda amma saboda tsananin mulki a ce duk na Sarki guda ɗaya ne. Duk daɗewarta tana bin lungu da saƙo da duk wata hanya da ta gani ba tare da sanin inda za a ɓulle da ita ba har yanzu bata gama zagaye cikin gidan ba. Haske tar ko ina a cikin gidan, da yake daren ya tsala sosai har lokacin bata haɗu da kowa ba.

Wani irin kunne ne da ita kamar na maciji, tana da tsananin ƙarfin jin sautin magana matuƙar dai ab buɗe baki an furta. Daga can nesa take jiyo muryar wata mace tana magana cikin kuka.
"Yarima dan girman Allah dan darajar iyayenka ka yi haƙuri yau ka ɗaga min ƙafa. Wallahi da gaske nake yi ina al'ada ka gani ma."

Can kuma sai ta ji muryar namiji cikin fushi yana cewa
"Babu ruwana da al'adarki. Wallahi Murja idan kika bari raina ya gama ɓaci sai na yi biji-biji da ke a cikin ɗakin nan sannan inyi abinda naga dama da ke. Ke da kike wulaƙantacciyar baiwa har kin isa ince ga abinda zanyi ki musa min?"

Hankalinta a tashe da gaggawa ta ƙarasa inda take jiyo tashin sautin muryoyin, ganin babbar ƙofar a datse yasa ta yi turus a tsaye. A sanyaye ta murɗa hannun ƙofar ba tare da tunanin a buɗe take ba kawai sai ta ga ƙofar ta buɗe. Ta sauke ajiyar zuciya tare da godewa Allah ta cusa kanta ciki da sauri dan ganin abinda yake faruwa, ba su a tafkeken falon don haka kai tsaye ta cusa kai ɗaya daga cikin ɗakunan da ta tabbatar daga ciki muryoyin suke fitowa.

Banka ƙofar da tayi da ƙarfi yasa duk suka ɗaga ido suna kallonta, Shi yana tsaye daga shi sai gajeren wando. Murja kuma tana tsugunne a gabanshi hannunta riƙe da tsumman ƙunzugunta a hannu tana kuka, ganin wacce ta shiga yasa a tsorace ta maida tsummar bayanta ta ɓoye.

Shi kuwa ɗaure fuska yayi tamau yana kallonta a wulaƙance.
"Ke kuma wace banzar ce? kinsan ina ne nan? kinsan ko ni waye da za ki shigo ɓangare na gaba gaɗi ba tare da neman izini ba?"

Bata saurare shi ba kai tsaye ta nufi gurin Murja da niyyar ta ɗaga ta tsaye. Ko da ya fahimci abinda take da niyyar yi hannu ya kai da nufin ya fincikota ya watsar da sauri ta kauce ya kama iska. Kafin ya dawo cikin nutsuwarshi ta ɗaga hannu ta zabga mishi wani ƙaƙƙarfar mari a kuncinshi na hagu, kafin

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login