Showing 30001 words to 33000 words out of 108894 words

Chapter 11 - NOOR ALBI COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

19

Middle Ads

anriga an daura aure Kuma saboda 'yar riqonsu da suka dauko aka aurota Dan ta kula da ita ace hannun matarsa take Kuma duk Dan sbd basuda magajin gidan ne yanzu itace magajiyar Anne da Turaki......

A haukace Ms Na'ima tace"

Da  dafarko ubanwa ya Hana ki fadan komai Kai tsaye kike fadamun Baki tabbatarba?
Siddika Allah ya kwashe Miki da wannan mugun labarin naki
Wallahi bazan yarda ba
Da anbani rikon ne ban karba ba daza'a auro wata kawai sbd riqo
Dan ita datai riqon ta riqe harda tarin dukiyar da za'a bawa yarinyar kenan
To idan hakan ne ai nice nasan taren Mahmoud din da Turaki..

Miqewa tayi ranta na tsananin Kuna zata give daga palon saiga Kiran Haj Zinat wadda siddika takira daga Nan inda take tsaye Dan itace kawai Mai iya dakatar da Ms Na'ima idan ranta ya baci idanuwanta rufewa sukeyi.

A matuqar hasalce ta daga wayar
Haj Zinat tace"

Karkije koina yanzu Yi zamanki gobe da wuri zanzo gidan musan abin Yi
Kinsan siddika munafuka ce karki hau zancenta duka kiyi abunda Zaki qarasa Bata kanki agurin Anne tunda dama ba wani Yinki takeyiba,
Idanma duka gaskiya ne ai a ruwan sanyi Zaki qwace riqon yarinyar Mahmoud din tadawo hannunki mu taru mu ringa nuna Mata gata da kauna
Kinga a sauki ga babbar damar mamaye zuciyar Annen dakuma ogan Mai gaba daya
Idanma tafiyarki tayi USA gurin Turakin sakata gaba Zakiyi kije da ita can danma yagani da idonsa yanda kike tsananin kauna da kulawa akan 'yar tasu.

Haka Zinat tayita lallaba Ms Na'ima din harta fasa zuwa Sashen Amaryar bawai Dan ta sauko ko taji sassauci ko kadanba a ranta saima wani sabon zafi da tiririn datake ji tayi hanyar bedroom dinta tashige tabar siddika na Mata Saida safe cikin girmamawa.

Saida tashige siddikan ta juya ta nufi dining tafara kwashe kayan Kai tana gyarawa saiga Kiran Haj Zinat
A ladabce ta dauka tana cewa"

Eh tashige Bata tafin ba.

Siddika abinda Kika fada kin tabbatar dashi?
Idan kikai qarin zance Dan ki Kare kanki daga Na'ima Ni karkimun qarya  fadan gskia.

Sanin daga Haj Zinat har Ms Na'ima halinsu daya sbd Aminin gske ne yasa takuma fadar abinda tafadawa Ms Na'ima din Dan ko gskiyar tafada musu cewa batasan komai akaiba ba yarda zasuyiba karshema Mara amfani zasu kirata Kuma tsaf zasu iya korarta su sauyata duk da dadewar datai Mai tsayi ataredasu shiyasa duk lokacinda taga gskiyar zance Bata fiddataba abinda tasan shi sukeson rahotonsa take hadawa ta fada shiyasama takawo har tsawon lokacin ataredasu sirrinsu Babu Wanda bada Bata saniba Dan itace Yar aiken sirrinsu.

Washe gari qarfe goma Sha daya Haj Zinat ta iso gidan Nan suka Gama Yan sirrance su suka fito zuwa Sashen Annen Dan gaidata.

Zaune Annen take a babban palonta tana waya da Turaki Wanda yatafi Zurich wani aikin Yana waya da Annen cikin nutsuwa da kamewarsa duk da Mahaifiyarsa sosai take mutunta Dan nata so da Dama sbd mutum ne Mai haibar cika ido har nata ita Annen nasa.

Cikin girmamawa suka qaraso Suka zauna masu Aikin Sashen Annen suna gaida Ms Na'ima din a matuqar girmame tana amsawa batareda ta kallesu.

Saida Annen tagama wayar ta ajiye gefe ta kallesu fuska a sake tace"

Zinat kina gidan kenan?

Eh Anne yanzune shigowata nace kafin nashige gurinta Bari nazo nafara gaidake,
Barka da Rana Anne?

Barka Zinat ya iyali?

Alhmdlh Anne.

Cikin girmamawa Ms Na'ima tana kallon Annen a ladafce tace"

Anne barka da Rana?
Jiya cikin dare na iso shiyasa ban shigoba sbd lokacin nasan kin shige bakya fitowa.

Murmushi Annen tayi irin nasu na manya tace"

Bakomai ai
Ga gajiyan tafiya dama kin debo
Allah a muku albarka duka to.

Firar rashin makama Ms Na'ima ke Dan yiwa Annen cikin girmamawa
Annen na tankawa ahankali tana duba sakon wayarta na Admission din Sa'adah daya fara samuwa kafin na Laylah da sai anhada da Mai sake koya mata wasu abubuwan.

Ms Na'ima na cikin magana Laylah tashigo palon sanye cikin Riga da skirt na Grand super red data fitar da yanayin shafaffen cikinta da tudun kirjinta sai hips dinta dasuka Dan fito
Dayake dinkunansu kaf a anan Abujar ake musu komai daidai jikinsu ake musu fuskarta fayau sai Hasken fatarta Dake qaruwa kanta red turban hula ce da Bata rufe duka ba sai qamshin turaren _Valentino Donna_ takeyi Mai sanyin dadi...

Wuta Ms Na'ima ta dauke tana hadiye wani mugun yawu tareda Dan rikicewa da abinda take fada idanuwanta gabaki daya Babu wani basarwa ta zubasu akan Laylah wadda Bata lura dasu ba hanyar kicin ta nufa gurin aikin abincin ranar data barwa halima ta duba Mata.

Haj Zinat kanta sakin Baki tayi tana kallon Laylan mamaki na neman kashesu,
Duk kyau da wayewa tareda budewar ido irin nasu na tsoffin Yan duniyar dasuka Gama bude ido a yawan Jin Dadi da daula Saida Suka tabbatar ba kushe yarinyar kyakkyawace.

Zuciyar Ms Na'ima bugawa take neman Yi ba shiri ta bude Baki Yana rawa zatai magana cikin yanayinta duk ya sauya zuwa firgici Haj Zinat tayi saurin Kai hannu zata dafeta sai Anne ta rigata da Kiran sunan Laylan Kai tsaye.

Da sauri suka waiwayo suka kalla Annen atare lokaci daya suna sake maida kallonsu Kan Laylah
Take wata boyayyar Ajiyar zuciya tazo musu Ms Na'ima na sake maimaita sunan Laylan a fili
Haj Zinat kuwa sakin fuska tayi sosai tareda sakin wani faffadan murmushi tana cewa"

Masha Allah yarinya kyakkyawa
Anne baquwa kikai n....
Bata qarasaba Ms Laylah ta saki zancen dayasa Anne kallonsu da idanuwanta cikin boye mamakinta Jin Ms Na'ima na cewa"

Itace Laylah Yar Mahmoud da aka dauko Mana sbd ba yara gidan....

Tsit Haj Zinat tayi cikin tsananin takaicin Aminiyar tata da koyaushe Bata iya danne zance ko boyewa shiyasa komai nata yake gashinan idan badan itabama da yanzu ba sauran labarin Na'ima a gidan Turakin wlh.

Boyayyan tsoki taja cikin ranta na takaicin Na'ima Amma a fili washe Baki tayi tana sake Kiran Laylah cikin bayyanarda kauna afili tace"

Masha Allah
Sannu da kokari Anne wlh Kam anyi dabara gida da yara yanada Dadi
Gashi dama Na'ima nata tunanin samun Dan dazata riqe ai shikenan an huta.

Murmushi Anne tayi sai kawai tace"

Eh ai yanzu gashinan mun samu qarin yarinya cikin gidan
Saikuyi addua daga kan yarinyar Allah yabude Mana haihuwa a gidan yara suyita zuwa masu albarka.

Amin suka amsa bakunansu daukeda murmushi kafin cikin kulawa Anne ta kalli Laylah data qaraso gurin tace"

Laylah ki gaida manyanki,
Matar Turaki ce da kawarta.

Cikin ladabi ta bude Baki da muryarta Mai sanyi ta gaidasu.

Ms Na'ima tayi saurin cewa"

Anne Laylah nada nutsuwa gskia
Amma dai gurina zata zauna ko?

Murmushi Annen tayi tana cewa"

Zaki iya rikon nata ne?

Anne akwai Wanda yakamata yayi riqon wanda yake matsayin 'da tamkar 'Dan da Turaki ya Haifa Kamar ni?
Inshallah Zan kula da ita nabata gata tamkar nida Turakin ne muka haifeta.

Cikin wani yanayi na ganin wautar Na'ima Anne tasaki murmushi tana basar da zancen da kallon kofar da Sa'adah ta fito tana sanye da doguwar rigar lace din daya kwanta baida nauyi ko kadan sbd kudinsa pink kala
Dayake tafi Laylah son kyale kyale harda siririyar sarqa a wuyanta Mai kyau gashi girmanta akan Laylah Ana Dan ganewa sbd jiki datafi Laylah.

Kallon Sa'adah Ms Na'ima tayi dakyau ta tabbatarda itace kishiyar tata wadda ta kutso rayuwarta da abinda tafi so da kauna a rayuwarta wato kudi da Turaki,
Itace wadda takawo kanta acikin masifar da batasan kalar hadari da girmanta.
Dauke Kai tayi tai kamar bata ga Sa'adah din ba Dan kuwa wannan Koda Bata Isa haihuwarta ba ta Isa yin qanwar qarshe sosai da ita,
Dan wannan ma tasan auren Anne ne tayisa Amma Turaki ko ita datake macen data Gama zama mace tako Ina ga kyau ga jiki Mai Kyau da ilimi da wayewa da komai Bata Gama zama shi yazama itaba bare wannan da da ita da wannan Yar Laylah bawani banbanci.

Haj Zinat ma Yi tayi kamar bataga Sa'adah din ba wadda ganinta yasa sukaji duk zafinsu ya rage sbd Dan wannan ba abun daga hankali bane Dan kuwa ba lallai ma Turakin ya dauketa mace ba saidai 'ya ko Yar riko.

Anne dataga basarwar dasukaiwa Sa'adah data gaishesu cikin mutuntawa tana satar kallon Ms Na'ima da akace Matar Turaki duk sai jikinta yake neman mutuwa Dan kuwa a kallo daya tasan Ms Na'ima ba qaramar mace bace ga kyau ba laifi ga gayu da komaima.

Laylah dama ta wuce kicin tuni Dan Haka itama tana gaishesu kicin din ta nufa
Ko bayanta Babu Wanda yasamu damar bi da kallo sai Anne data kalli Ms Na'ima tace"

Dukkaninsu tamkar 'yaya suke gareni
Zasu zauna damu har abada Inshallah 'yar riqona da aure kawai zai rabani da ita Amma dayar kamar yanda Naga alamu sun nuna kinsamu labarin Matar mijinki ce
Turaki Bai fada Miki bane sbd shima Kai tsaye auren yaxo
Kuma ninace yabari Zan sanar Dake saigashi Kikai zamanki Lagos sai yanxu da Kika dawo
Dan Haka Kamar yanda Kika gani yarinyace qarama akanki sosai
Ina fatar bazaki wani damuba Zaki zauna lafiya da ita kamar yanda na tabbatarda zata Baki girmanki sosai.

Zinat tasake fadawa tasake yiwa qawar tata nasihar zama da kishiya musamman Miji irin nata da baya kaunar fitina ko kadan.

Murmushi Haj Zinat ta nuna bakomai ai tunda ma yarinyace Kuma ma ai kamar ba guri daya suke zauneba.

Da wannan suka tashi suka baro Sashen Annen harda Kiran Laylah Haj Zinat tayi sukai sallama cikin kulawa
Anne dai Bata sake bi takansu ba.

Bayan futarsu Ms Na'ima wasu hawayen baqin ciki da takaici ne suka silalo Mata dan tagama tabbata dai Kishiya akai Mata
Turakin da Bata taba dandana kayantaba shine za'a kawo Mata Kishiya Dan Yana samun lafiya arasa waye zai fara samun rabon dashi.
Wlh bazata taba yarda da wannan dakon wahalar datai ba
Ba Sa'adah ba ko uwar Sa'adah ce bazata Bari ko inda inuwar Turaki take ta kusanta ba bare harya ringa tunawa da ita da wani aurenta.
#MAMUH#
pay 300 @+234 903 234 5899


Mamuhgee's complete books

Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Kaunarmu
Buri daya
Tarayya
Eznah
Dawood
Zucuyarmu daya
Daiman
Auren raba gardama
Dacewa

Duka completes dinsu suna AREWABOOKS @Mamuhgee
[6/7, 7:56 AM] MG💋: *_Mamuhgee 17_*
Duk yanda Ms Na'ima taso Kar tayi kishin Sa'adah kasawa takeyi saidai kamar yanda Haj Zinat ta fada Mata dannewa kawai takeyi Bata wani nunawa saidai ko inda Sa'adah take Bata kalla sbd duk iya qanqantawa tagama daukan Sa'adahn a qasqance ganin harda ilimin boko Mai qarfi sosai Bata dashi Dan Haka sai sukafi maida hankali akan Laylah wadda cikin kwanaki kadan Ms Na'ima din tagama fahimtar irin kaunar da Anne ke yiwa Laylah ga laylan nada wuyar sakin jiki da mutane Dan Haka tuni ba itaba ba Haj Zinat ba suka maida hankali sosai Kan nunawa Laylah kulawa Sosai,
Musamman Ms Na'ima ke janta ajikinta tana Mata siyayyar kayan Yan gayun 'yan Mata 'yayan manyan duk da Anne Babu abinda Bata siya musu na duk Wani abun buqata Amma dayake Ms Na'ima wayayyar Yar gayun gaske ce sai siyayyar datakewa laylan yana sake wanke Laylan
Anne said kawai takawo ido tasake sakawa Na'ima Dan tagama gane manufarta ta son abata Laylan Dan samun damar data fi wadda take da ita yanzu Alan dukiyar Turaki,
Murmushi kawai takeyi na ganin wautar Na'ima so da dama idan taga yanda suka taqarqare akan Dole qaunar Laylah sukeyi ba
Kuma ganin rashin sanin zaisa bazata taba cutatar da Laylahn ba ayanzu Dan Haka saita bar komai ahakan yanzu saima tabada fuskan da Ms Na'ima din ke daukan Laylah tana fita da ita.

Laylah Bata sakewa da Ms Na'ima Sam ko kadan sbd sanin matsayinta na kishiyar Sa'adah batason jawowa Sa'adah matsala sai Anty Sa'adah din ta nuna Mata bakomai ai hakan shizaisa azauna lfy kowa da kowa,
Da Haka Ms Na'ima taja Laylah sosai jikinta har Dan Dole Laylah tafara sakewa da ita Dan har cikin ranta so take ta cusa qaunarta Mai qarfi a zuciyar Layla ta yanda zata dauketa tamkar uwa tako Ina yanda Turaki zai sake musu komai yanda yakamata tunda ta rungumi 'yar Kamar ita ta Haifa.



Sa'adah tafara zuwa makaranta tuni a one hundred level takuma farawa tana karantar Biology
Kuma ba laifi tafara sabo da makarantar da 'yan friends din data fara tsirarru ga uwa uba surutu da manyan designers Kaya data duka
Ga hankalinta tuni yagama kwanciya Dan Laylah tasamu lafiyarta cikakkiya itama karatun zata fara Amma Ms Na'ima ta dage akan ita baza'a sakata anan Abuja ba da ita zata tafi USA acan zata sakata karatun kafin su tashi dawowa Laylan tagama Inshallah idanma harta tashi dawowan Laylah Bata kammala karatun ba zata jirata ta kammala kokuma tabarta acan tadawo tunda Turaki na can ga maids a gidan Kuma.

Da wanna ba musu Anne ta Amincewa tafiya da Laylan wadda da farko ta daga hankalinta Amma Sa'adah ta lallasheta tareda sanar da ita Anne tace acan kusa suke da gurinsa Abba zaa ringa kaita tana dubo Abba da Momy tarea Bata qwarin gwiwar karatun shine zai tallafi rayuwarsu data iyayensu Inshallah Dan Haka badan tasoba Haka ta amince musamman da Anne ta zaunar da ita ta rarrasheta Akan Turaki nacan Dan Haka kartaji tunda yasan matsayinta akansa na dolenta.
Hakama dai maganar ganin abbanta shine yafi komai Bata nutsuwa da tafiyar wadda takasa gane dalilin dayasa Ms Na'ima ke sonta Haka Bayan ita din qanwar kishiyarta ce Amma idan ta tuna wasu daga nasihun Anne sai tana yadda da akwai sauyin da Allah ke kawo maka na rayuwa da basai ka tsaya wani tunaninba Bayan gode Masa.


Da wannan aka hau Shirin tafiyarsu USA, Ms Na'ima farin cikin tafiyar takeji sosai musamman ta kalli Haj Zinat tana zare siririyar sarqar white gold din Dake wuyanta dasuka dawo daga Gama harhada bayanan komai na manyan stores data barwa babban 'dan Haj Zinat ragamar cigaba da kulawa da komai tace"

Zinat kisake yiwa siddika sabuwar huduba sbd tana min hauka acan ko kudin ticket din dawowa bazan siya Mata ba Zan korota
Dan kuwa banason duk wani abun damuwa ko ciwon Rai acan
Hutawa najeyi da mijina.

Murmushi Haj Zinat tayi tana aje wayarta data Gama amsawa tace"

Idan hankalinki Bai kwantaba da haukarta ki barta Mana a samo wata kije da ita.

No zuwa da itan zaifi sbd Laylah da ita tasani zatafi Jin dadi idan akaje da Mai Mata hidimar data sani tun anan sbd Kinga turancin ba wani jinsa takeba Dan Haka masu aikin can zasuyi Mata wuyar muamala shiyasa sbd ita kawai zanje da siddikar.
Dan Haka idan tamun abinda zai sakamun ciwon zuciya ratayeta zanyi kowama ya huta" taqarasa fada da Dan takaicin halayen siddikar duk da sune suka sakata ta gwane a munurfin da gulmar Dan kawai dauko musu kowane irin zance.

Dan gyara zama Haj Zinat tayi cikin Isa tana cewa"

Laylahn ma sai anyiwa Siddikar fadan kiyaye abinda takeso da Wanda bataso Dan zata iya kwafsawa tunda munafurci kawai tafi gwanewa akai.

Wani lafiyayyan murmushi Ms Na'ima tayi tana daukar face wipes taqara da Neutrogena makeup remover akai tafara goge fuskarta tana cewa"

Duk halinta zatai tabari ne Dan kuwa amfanin dagewa da tafiya da Laylah shine Zan fake da karatun nata naqi dawowa Dole yanzu zamu zauna Kamar kowanne ma'aurata gani gashi a gida daya qari ga 'yar riqo duk ihun Anne da damuwarta Akan rashin haihuwa dai yanzu Zan huta tunda burinta yacika ta aura Masa gagari
Dan kuwa ko ganinsa ita Annen bazataiba bare juyayyar Matar da aka aura masan saidai taqaraci karatun bokonta tagama tayi gaba tasamu bokon koshi taqaru dashi taje tasamu wani mijin Turaki Kam bana yara bane
Ita kanta dataji komai ta Isa Bata Gama saninsaba bare wadda ya Isa haihuwa.

Dama duk tsanani Kam karkiyi sake yadawo Baki Gama sakashi a kwana ba da kisisina da komai
Tunda gaki da 'yar Mahmoud a hannu kowa yasan irin Aminci da qaunar Dake tsakaninsu Dan Haka kinsan tunda suka dauko yarsa duk Wanda ya sota shine nasu
Tunda gashi yanzu Anne Tadawo tana sake Miki sosai sbd Laylan Dan Haka Turakin ma karkiyi sake
Gwara ki nuna Masa da gaske kike kece uwarta yanzu.

Wani murmushin tayi kawai batareda tace komaiba Dan kuwa kamar anyi komai angama ne.


Bayan dogon shiri da tsare tsare dai jirginsu ya daga zuwa USA inda Laylah take zazzabi da mutuwar jiki suka sameta na yanayin data samu kanta a jirgi doguwar tafiya duk da wannan shine karonta na biyu Hawa jirgi Bayan Wanda suka shiga zuwansu Abuja tareda Anne.


_AMB & Alt perm rep AB TURAKI north Buckhead Atlanta Georgia_

Cikin wata black Audi A8 aka daukosu daga airport zuwa gidan Wanda Laylah Bata wani damu da yanayin tsananin tsaruwarsa da sabuwar duniyar dasuzoba sbd yanayinta batajin Dadi zazzabi sosai ne ajikinta dukda tana daurewa
Dan Haka suna shigowa gidan aka nufi lafiyayyan dakinta da Ms Na'ima tasa aka gyara Mata shi daga shigowar tasu aka ja luggages dinta zuwa can tace saddika ta kula da ita itama zata huta tana Jin gajiya
Tadaga wayarta da tun a mota tasaka layinta na qasar takira numbern A Abdul dasuke tareda Turaki a office Yana Masa bayanin wasu takardu ya sati kallon Turaki Dake zaune yayi crossing dogayen qafafunsa cikin wasu irin Ash Alexander amosu vanquish ii suit fuskarsa da fararen idanuwansa na kallon screen na Apple iPad Air Dake gabansa na bayanin da A Abdoul ke Masa.

Wani Kiran ne yakuma shigowa yakuma kallon Turaki da tun Kiran farko Bai dagoba bare na biyun
A natse A Abdoul din ya dakata da fadin"

Ms Na'imah ne take Kiran shud I take the call ko naci gaba??

Agogon _jaguar executive_ dake daure a hannunsa yafara kalla yaga lokaci yasan ta isa isowane a yanda Anne ta fada Masa Na'ima din Hanya
Kafin ya dago ya kalli A Abdoul din dake Kiran umarninsa yace ya amsa Kiran.

Juyawa yayi ya fice daga office din tareda daukar wayar cikin Bata nata girman yace"

Barka da isowa.

Kai tsaye ko gaisuwarsa Bata amsaba tace yaturo Mata likita tazo da yarinya ba lafiya.

Tana Gama fadar hakan ta kashe wayarta.

Saida yafara Kiran Dr Noah ya sanar Masa kafin ya kashe Yana mamakin inda tasamu yarinyar zuwa da ita
Ya koma gurin Turaki Yana barin tunanin zancen.
##MAMUH#



pay 300 @+234 903 234 5899

Mamuhgee's complete books

Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Kaunarmu
Buri daya
Tarayya
Eznah
Dawood
Zucuyarmu daya
Daiman
Auren raba gardama
Dacewa

Duka completes dinsu suna AREWABOOKS @Mamuhgee
[6/8, 9:57 AM] MG💋: *_Mamuhgee 18_*
Duk yanda takeda sani ba laifi akan kayan gidajen masu kudi yanzu sbd rayuwarsu ta Abuja Nan Saida ta Raina kanta dan komai na gidan wata rayuwace daban,
Toilet din komai nasa tsarinsa daban yake Dan Haka Saida

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login