Showing 87001 words to 90000 words out of 108894 words

Chapter 30 - NOOR ALBI COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

30

Middle Ads

biyu Bata tako ko kofar fita Dana bangarentaba tana fama da kanta sai data cika kwanan biyu cif tadawo daidai ta nufa Sashen Anne ta gaidata Kamar Dole ta fito Takoma bangarenta tana wayoyinta da Zinat data dagawa hankali akan ita ta tafi Ta binciko musu sbd zaman Nan a baibai bazai kaisu koinaba sai gurin baqin ciki da bacin Rai sbd suna Bata lokaci cikin Yana da uwar cikin suna sake samun qarfi tunda ciki zaina cigaba da girma.

*****
Qarfe 5 na asuba jirginsu ya sauka a Murtala Muhammed International airport dake Lagos,

Sanye take da _Moja majka_ Abaya maroon Mai shaking material
Kanta nade cikin Marron veil qarami na Abayar sai black Gucci suede loafers a qafarta da qaramar _Bottega veneta_ small shoulder bag Dake rataye a kafadarta,fuskarta tayi haske sosai ta yanda ko kafin idonka ya sauka a cikinta zakasan tana daukeda juna biyu dayayi Mata kyau matuqa,

Bata qara wata qiba ba hakama Bata rameba shiyasa cikin ya fito sosai iya watanninsa...

Wani numfashi ta sauke lokacinda ta shaqi iskar Nigeria ta lumshe ido cikin gajiya da Yar yunwar Dake damunta ta fito Ana biyeda ita da luggages dinta.

Tana fitowa Wanda idonta yafara sauka akansa ne tsaye Yana waya cikin black Rugby's Riga da wando da jacket Mai girma datakai Masa har gwiwa...

Duk da Yana sanyeda face mask black da hular sanyi,
kallo daya tayi Masa tagane shine duk koina nasa kusan a rufe yake Kuma Bata taba tunanin zai iya zuwa airport da kansa tarbonta ba
Da haka wani sanyi ne ya mamaye zuciyarta har batasan idonta Yana cikowa da hawayen kewarsa dataiba da farin cikin ganinsa...

Ahankali take takowa idonta cikin nasa daya zuba matasu cikin kallo Mai wuyar fassarawa,

Akan cikinta daya turo Ana ganinsa da kyau ya sauke idanuwansa kafin ya ware Mata hannuwansa ahankali Yana cewa"

Finally.

Ahankali tashige jikinsa tareda rungunmesa da sauri hawayenta suka sauko tana cewa"

Abbahhhh.

Hannunta ya Kama A Abdoul ya wuce gaba tareda kayanta aka shigar mota kafin ya bude motar Turakin da kansa ya bude Mata motar yana riqeda hannunta ta shiga kafin shima ya Shiga A Abdoul yaja motar suka bar airport din.

Hannunta na cikin nasa a sarke yake kallon cikinta Yana kallon fuskarta Dake glowing tana daukan idonsa da hankalinsa..

Wani malalacin murmushi ya saki Mara sauti ko kadan alokacinda idonsa yagama shawagi Kan cikinta Kuma maganar Abbanta ya fada Masa alokaci daya.

Dagowa tayi ta kallesa ganin murmushin daya sake,
a hankali ta bude Baki zatai magana ya Dan rufe Ido Yana girgiza Mata Kai alamar Bata buqatan magana.

Lumshe fararen idanuwanta tayi tareda Dora hannunta daya Kan hannuwansu dake sarqe cikin kulawa da son abun Dake ranta ta bude Baki ba sauti tace"

I love you Abbahh.

Wannan karon murmushinsa sai daya bada sauti kadan sbd shigarsa da kalmar Tayi da dagashi sai itane bazata hadiye yawun datake bakinta lokacinda tafada Masa wannan kalmar saiya shanyesu tas Dan kuwa sauran zaqin kalmar na cikinsu...Dan Haka sai kawai ya sake damqe hannunta cikin nasa cikin kulawa Yana Dan dauke Kai daga kallonta ya maida Kan wayarsa da aka sake Kira.

Lafiyayyan gidansa Dake Lagos din suka Isa Madam sarat Dake gidan tareda sabuwar Mai aiki daya da aka kawo Ruky sungama gyare koina a gidan sai qamshi da Sanyi ke tashi koina
Ga aikin breakfast dasuke Yi cikin qwarewa da mutsuwa...

Hannunta cikin nasa Suka shigo palon bayan A Abdoul ya miqawa Madam sarat akwatinan Lv0 na Laylan ya juya ya nufi sashensa dake gidan dan komawa baccin Dake cinsa.

Madam sarat kallo daya tayiwa hannuwansu dake sarqe ta dauke Kai tana neman Yar rudewa dai kafin ta Kama nutsuwarta sukai ciki da kayan itada ruky tana kyafta idonta Dan tabbatarda cikin Dake gaban Laylan da alama da Turakin ne tunda ga hannuwansu a sarqe...

To kodai Ms Na'ima ta rasu ne?

Da wannan rudadden tunanin Suka kai kayanta duka makeken bedroom dinsa daya Dake palonsa na sama Suka sauko.
##MAMUH#
[6/29, 6:27 PM] MG💋: *_Mamuhgee 47_*
Parking motocinsu sukai a harabar gidan,

A Abdoul ne yafara fitowa motar dayake ciki zaune a gaba sai Ruky a sit din baya,

Motar da Turakin suke ciki ya nufa da niyar bude Masa sai gashi ya bude da kansa tareda zuro qafafunsa Dake sanye da black Camilo Italian leather loafers ya fito motar.

Hannu ya miqa Mata ahankali ta Kama zuciyarta na bugawa ta fito motar sanyeda Ash turkish abaya da light Ash gyale akanta nade.

Handbag dinta ma qarama ce sosai sbd yanzu batason masu girma suna damunta,

Ahankali ta zare hannunta daga nasa Bayan fitowarta motar sbd tasan yanzu Kuma ita dashi sai kallo daga nesa tunda suna gida daya da mum Na'ima gakuma Anne.

Kai tsaye Sashen Annen Suka nufa Ruky da A Abdoul tuni sukai gaba da Suitcases dinta zuwa bangaren Annen,

Ahankali jiki a matuqar sanyaye take tafiya gashi kamarma yanzu tafi ganin girman cikin nata,

Dan Haka duk tabi ta sake shiga halin firgici da damuwa...

Suna gap da Isa su shige babbar kofar dazata sadasu da babban palon bangaren Annen motar Ms Na'ima ta sako Kai harabar gidan ita ke tuqawa da kanta Haj Zinat na gefenta zaune
Kowaccensu cikin Shiga ta alfarmar manyan Mata Kuma matan masu abin duniya...

Motacin Turakin da aka daukosa daga airport dake sarari a pake ta kalla kalla batareda idonta yakai Kan gabansuba hanyar Sashen Annen
Tana kokarin parking tace"

TURAKI ya dawo kenan¿Amma dazu da mukai waya baicemun yau zai dawo din ba,
Zinat shiyasa nake fada Miki Turaki ya......

Haj Zinat da tun shigowarsu idonta ya sauka kansu Laylan dake kokarin Isa kofar bangaren Anne
Batareda ta dauke idontaba akansu cikin zallan mamaki da shakkar abin datake gani a idonta tace"

Na'ima Kamar fa mace Mai ciki ce tareda turakin gasu can zasu shige gurin Anne......

Baammmmm.....wata irin qara Mai qarfi ta tashi na buga motar gabansu da Na'ima tayi ba shiri sbd zancen Zinat...

Ware idonta tayi a bangaren daidai sun sunshige lokaci daya atare....

Bata kashe motarba barewa tsayawar ta bude kofa tana kokarin fita Zinat cikin tashin hankali biyu da biyu ta riqota tana cewa"

Tsayar da motar ki kashe tukuna kafin ki kashemu da sauran kwananmu a gaba..

Tsayar da motar tayi Amma Bata tsaya kashewaba ta fito
Tana cewa"

Zinat wlh itace ya kawo gidan,
Anne ta sane kenan,
Aikuwa yau za'ayi budaddiyar wasika kowa ya dauki sakamonsa....

Gaba tayi har tana tuntube saura kiris ta kife,
Haj Zinat da sauri ta fito tabiyo bayanta batareda itama ta tsaya kashe motarba sbd Ganin ko ganin gabanta Na'iman batayi,

Tasan Sarai Yau mahaukaciyar hauka zata buga idan tayi Ido biyu da Matar Nan,
Yau Babu maganar aro hauka koina original tata din zata buga abarta,

Itakuma bazata yarda ba Na'iman tayi abinda zaisa agane lalurarta gwara ta bita ta danneta duk da itama dazata samu damar idonta idon Matar data rigasu daukan cikin Turaki da hannunta zata halakar da cikin kafin ita Daga baya sayi lokacinta.


Anne ce zaune a Palo tana Amsa wayar Sa'adah cikin kwanciyar hankali nutsuwa,

Palon sai qamshin Turaren wutar YERWA INCENSE yake tashi tareda sanyin Ac da hayaqin Oud Dake fita ahankali daga qatuwar humidifier Dake can gurin hanyar kofar shigowa palon.

Shigowar A Abdoul da ruky Dake janye da set din akwatinan Louis Vuitton guda hudu yasata kallonsu da mamaki akan fuskarta,

Ruky data gefe tana gaidata cikin tsananin girmamawa ta kalla kafin ta kalli A Abdoul din shima tace"

Abdoul-Hameed baqi mukayi ne da Kaya Hakan?

Fara gaidata yayi cikin girmamawa da sakewar Dake tsakaninta dashi yace"

Ms Laylah ce ta dawo..

Da sabon mamaki Mai girma ta Kuma kallonsa murmushi na sauka Kan fuskarta tace"

Laylah Kuma?
Zuwan bazata ba sanarwa....

Shigowar Laylan ne yasa ta dakata da maganarta tana zuba Mata dukkanin idonta da hankalinta saidai har lokacin murmushin fuskarta Bai gusheba saima fadada da yayi
Harma batasan ta zubawa cikin Laylan idoba.

Kunya Mai tsananin girma ta Sanya idanuwan Laylan cikowa da hawaye tana Sunkuyar da Kai qasa a sanyaye take takowa..

Halima ce data fito kitchen tagansu
Aikuwa bakinta yakasa rufuwa da sauri ta ja kayan tana cewa Ruky ta biyota da sauran kayan
Suka nufi dakin Laylan tun na farko dake guri daya Dana Sa'adah
take halima tasa Ruky din ta Kama aiki suka hau gyaran dakin dukda yananan da komai na tsari da buqata acikinsa.

Sir Turakin kuwa qarasowa yayi zai gaida Annen ya wuce nasa bangaren,

Ita Kuma a silale ta nufa inda Annen take zaune tana kokarin Nemo muryarta data maqale a maqoshinta zata gaidata Ms Na'ima ta shigo palon Kai tsaye ta sallamar da kwata kwata batamasan Yaya ta fito abakintaba..

Yana ganin Na'ima ya dakata daga inda yake tsaye Bai qarasa gurin Annenba ya tsaya kallonta fuska a kame hankalinsa kwance.

Anne kuwa tashi daga zaunen datake tayi Tana qarasawa gaban Laylan Kai tsaye tace"

Wuce ciki kifara hutawa tukuna.

Duk yanda take tunanin tashin hankalin fuskantar mum dinta abin ya wuce hakan a zuciyarta sbd daukewa numfashinta yayi Jin muryar mum din  daga bayanta,

Yanda zuciyarta ke harbawane yasa takasa juyowa ta tsaya cak a inda take tareda rufe idanuwanta hawayen dasuke ciki suka gangaro har sai dataji saukan muryan Anne datace ta wuce ciki.

Daga kafa tayi zata wuce batareda ta juyoba har lokacin,
Cikin tsananin bacin Rai Mai girma daya sake rufe Ran Ms Na'ima tace"

Laylah? Tsaya agurin,
Yaushe Kika dawo?
Meyasa Baki fadamun ba?
Wacece kuka dawo da ita tareda Turaki??

Cak Laylan ta tsaya agurin cikeda mamaki da fargaban yanda mum din tagane itace zuciyarta na karyewa da abubuwa da dama,

Har cikin ranta tasan Bata kyautawa riqon da Mum tayi Mataba,

Ta wani bangaren ta yarda da tabbas taci Amanar mum sbd koma yayane tayi Mata riqon 'ya ba irin Wanda ta taso acikinsaba Amma ace itace take dauke da cikin mijin Mum.,

Da wane idon zata kallo mum data kamu da tsananin son Turakinta Mai tsananin datake Jin rabata dashi shine mafi Munin illar da zaaiwa rayuwarta....

Cikin fushi Ms Na'ima ta tinkari Laylan idonta rufe da bacin ran wadda suke boyewa da Turaki yazo da ita tana cewa"

Magana nake Miki amsa Zaki juyo kibani Raina abace yake
karki dora wani laifi akan wannan na zuwan da kikai batareda kin sanar dani b......

Hannunta Turaki ya riqo akaro na farko tun shigowarsu gidan daya bude Baki Yana kallon cikin idonta Kai tsaye murya a kame yace"

Ki nutsu banason hayaniya Anan,

Wuce,koma kije bangarenki....

Qwace hannunta tayi da qarfi tana kallon Anne idonta jajir tace"

Anne gwara ayi komai a gabanki tunda da alama kinsan komai,
Turaki Wlh nasan yanada wata macen daban bayan Ni da waccar dayar,

Najima da Dani Dan Haka gwara a fadamun meyasa za'a rufeni akan wani auren daya Kuma.....

Just shut up Na'ima,
Ki fita kibar Nan nace...

Gurin Laylah takuma nufa gadan gadan tana cewa"

Wallahi bazan fita ba sai nayi magana da Laylah kokuma tabiyoni muje ai dama nice mum dinta,
Nice nake riqonta,
Ta wuce muje da kaina zanyi magana da ita.

Kallonta Anne tayi cikin kulawa kafin tayi mgn
Baice komaiba ya Kama hannun Na'iman ya juya da ita
yana ganin Haj Zinat bayansu ya sakar Mata ita Kai tsaye yace"

Jata ku tafi.

Kama hannun Na'ima Zinat tayi dukkanin wutarta na daukewa da zallan mamaki da firgici harma da tashin hankali dan kuwa kallon tsaf dataiwa Laylah daga bayanta sbd a hangi ciki a jikinta wallahi.....

Kokarin Jan Na'ima takeyi Amma ta fizge da qarfi kafin kowa ya Ankara ta Isa gurin Laylah Dake tafiya zuwa daki Tasha gabanta....
##MAMUH#
[6/30, 10:57 AM] MG💋: *_Mamuhgee 48_*
Cak ta tsaya gaban Laylah tareda mutuwar tsaye tana fiddo dukkanin girman idanuwanta afili tana kallon ciki dayake gaban Laylan,

Kallonta ta maida Kan Turaki da sauri Dan batada lokacin Anne ita ba yanzu ba,

Ganin yanda fuskarsa take a hade tsaf yasata maida kallonta Kan Laylah cikin wata muryar tashin hankali tace"

Laylah,ciki kikayi?
A Ina?
Waye yayi Miki?
Shiyasa ake mun boyo?Kokuwa kinada wata uwar data fini da baza'a sakani cikin masana ba.

Hawaye Laylah takeyi sosai takasa ko kwakwaran motsi sbd gabaki daya neman fita take hayyacinta sbd firgicen datake..

Hannu Ms Na'ima takai ta damqo hannunta tana cewa"

Muje can bangaren zamuyi magana a tsanake Dan kinada laifi Mai girma agurina,
Gabaki daya an sauyamin ke
Komaima Dake ake boyemin..

Bangare hannunta daga na Layla yayi zuwa Lokacin fuskarsa na bayyanarda bacin ransa sosai ya jata tana kokarin qwacewa bataji Bata gani idan ba Laylah aka Bata ba ta zaunar da ita sukai budaddiyar wasika Dan koma menene Laylah tasan komai,

Ita ba cikin jikin Laylah ya dameta ba Maganar wacece a rayuwar Turaki takeson ji
Dan akan hakan yau tafison ta cinnawa gidan wuta Har Turakin da ita su mutu hankalinta ya kwanta.

Haj Zinat ta fita tana waiwayen Laylah hankalinta tashe saidai itama takasa yadda da tunanin abinda suke gani da Wanda suke Shirin ji ma,

Bin bayansu Na'ima da Turakin tayi Bata daina waiwayeba har tana kifewa da sauri ta tashi tabi bayansu qafafunta na rawa....

Bakin Kofar bangaren Na'iman ya dakata tareda sake hannunta
fuska daure ya kalli gefenda Haj Zinat ta iso da sauri ta riqe Na'iman Kai Tsaye yace"

Ta zauna aciki idan ta fito ta tafi gurinta Zan dauka matakin hakan,
Ta dawo hankalinta wannan zallan rashin Kama Kaine ga masu aiki suna kallonta,
Ki nutsar da ita zaifi Mata mutunci..

Juyawa yayi yabar gurin sbd yasan duk hakurinsa da kamewarsa bazai iya tankwafar da Na'iman ba,
Sbd Bata ganin kowa idan tana rashin Jin ta,
zubar Masa ma da mutunci zatai a gaban securities da masu aikin gidansa idan ya biyewa tankwafar da ita din.

Yana barin gurin bangarensa ya nufa ya shige batareda ko waiwayensu yayi ba saidai yasan duk fashinsa da fadansa bazai Hana Na'ima tashin hankali ba idan tagama sanin ZAINAB da cikinta duka nasa ne Dan Haka Dole zai rabasu,
Bazasu zaunu guri dayaba,

Laylah tunda tazo bazata komaba saita haihu Dan Haka Na'iman zai tura Takoma Lagos kokuma US.

Da karfi fa yaji a haukace Haj Zinat ke janta tana kokarin qwacewa
Tayi ciki da ita suna Shiga babban palonta ta qwalawa siddika Kira da qarfi tana cewa"

Yi sauri saka key ki rufemin kofar ki zare keys din..

A rude da mamaki siddika ta qaraso ta dannawa kofar key tareda zaresu tayi saurin miqawa Haj Zinat din kafin Ms Na'iman tayo kanta.

Damqe keys din Haj Zinat tayi kafin ta saki Ms Na'iman cikin tashin hankali Mai girma da itama yau haukar takusa kamata ta nufi kujera ta zauna tana zare mayafinta tayi wurgi dashi,

Danwkalinta takuma zarewa ta jefar Kan kujera tana kallon siddika cikin tsawa tace"

Kawo Mana ruwa ko zuciyata zata dawo Kan aiki.

Kallon Na'ima Dake safa da marwa cikin masifar Dake cin koina jikinta tace"

Ki zauna wlh akawi babbar matsala Mai girma.,
Ke bama matsala bace wannan akwai masifa da bala'i masu girma a cikin wannan zancen...

Kasa zama Ms Na'ima tayi taci gaba da safa da marwa cikin masifa da takaicin Mai tsananin gaske tace"

Sai naci uwar Laylah,
Zan koya Mata darasi Mai girman gaske idan munkoma ta yanda bazata Kuma ya yarda a munafurceni da ita ba,

Banyimata riqon dazaisa taji Ina cutartaba Dan me zatamun mufurci,
Yanzu gashi Nan duk yanda nake kaffa kaffa Kar tayi saurayi Ashe ciki tayo ta rufeni baibai,

Har Anne da Turakin sun sani tunda sune jininta gashinan an daukota da saidai naga 'dan shege a gidana,

Ni tsabar masifa da bala'i Banda Allah yayita asararrar duniya wlh data Bari nasan da cikin bazan Bari Turaki da Anne su saniba haifemun shi zatai taban nasamu magaji gurin Turakin tunda yanzu yasamu lafiya hakurinsa na haihuwa ya gaza Sai bin Mata yake....

Wallahi Laylah taci Amanata Kuma wlh zatasan bacin Raina baida kyau ko gaba ance tasake min irin Haka bazata kumaba........


Ruwan da siddika takawo masu Dan sanyi Haj Zinat tagama shansu tayi wurgi da robar ruwan da sauran Dake ciki
Siddika tabi robar ta dauke tareda zuwa ta dauko abun gogewa...

Na'ima ki dawo hankalinki ki fuskanci gaskiyar da idonmu ya ganar Mana,
Idan Baki dawo hayyacinki Kika kalli komai a bude ba za'a cigaba da rufemu ne Muna bulayi cikin hauka...

Cikin jikin Laylah na waye?
Sbd kariyar danaga Turaki da Anne sun bayyanarda Shirin Bata ta gaske ce bana tunanin 'ya zatai cikin shege ayi Shirin Bata wannan kariyar.....

Zama Ms Na'ima tayi a kujera tana yiwa Haj Zinat din wani kallo tace"

Bangane wannan bayanin ba...

Na'ima wlh nafara tunanin Mai cikin da muke nema Laylah ce,

Ranarda yace Miki karki kuskura ki Isa gidansa idan kin koma US,

Maganarsa ta tabbatarda abinda yake son hanaki Isa garesa Yana cikin gidansa kenan sbd tun aurenki dashi Bai taba hanaki tafiyaba ko wace irice sai lokacin,

Kuma muka kira Laylah Dan neman sanin abin dayake faruwa cikin gidan tabamu tabbacin Babu kowa a gidan bayan ita da Cindy...
Yanzu Kuma ga ciki a gaban idonmu mungani,

Gata Babu sanarwa yaje ya daukota mungani,

Gashi suna kokarin Bata kariya daga gareki,
Idan har tayi cikin shege da Bai shafeki ba meyesa za'a Bata kariya daga gareki bayan kece yakamata ki Bata kariya daga garesu sbd fusatar da zasuyi idan tayi cikin shege.......

Zuru Ms Na'ima tayiwa Zinat da Ido tana kallonta tamkar wuwuya,

Kiran sunanta Zinat tayi tana girgizata tace"

Kinaji kuwa???

Girgiza Kai Ms Na'ima tayi tana cire hannun Zinat din daga jikinta tana cewa"

So kike kicemun cikin Turaki ne a jikinta?

Da mamakin tambayar Zinat ke kallon Na'iman tace"

Bazaki bude qwaqwalwanki ki fahimta ba kenan...?

Sake girgiza Kai tayi tana dauke kallonta daga Zinat din tace"

Zancen ne bamai taba yiyuwaba,
TURAKI fa kikace da cikin jikinta?
Kinsan me kike fada kuwa?
Abbantane fa,
Aminin Mahaifinta daya hada auren uwarta da ubanta,

Tayaya kike kawo wannan rikitaccen bayanin?
'yar uwarta dasuke uba 'daya yake Aure shi Turakin idan kin manta,
Hakama tamkar 'yar cikinmu muke riqonta,
Wannan tunanin babusa a cikin duniyar mutane..wallahi bazai yiyuba.

A rikice Zinat ke kallonta tace"

Abokin uba nawane yayi lalata da Yar abokinsa?
Qanwar Mata nawa ta kwana da mijin yayarta,
Hakama ke da kike kallonta matsayin 'ya ta riqo wlh akwai 'yayan dasuka kwana da mazajen uwayensu Mata da suka haifesu bare ke 'yar riqo kike magana anan,

Yarinya kyakkyawar gaske da ita ga saka kayan banza anyhow
Tayaya kike mamakin hakan bazata iya faruwaba???

Cikin zafi ta katse Zinat din tana sake win yarda ko kunnuwanta suci gaba da Jin wannan balain Dan wlh bazai yiyuba,
Tashin duniyar Laylah da Turakin za'ayi idan Suka Bari shedan ya rude su sukai Mata wannan Cin amanar da Bata karbu ba,

Batason ko tunanin hakan na shiga kanta shiyasa ta katse zancen da cewa"

Kidaina kawo wannan tunanin wllhi ko dauka kaina bazai iya ba,
Buqa kaina kike neman Yi da wannan tunanin Dan komai zai iya faruwa kinsani.

Hmm Turaki ba Haka yakeba,
Duk neman matansa daya sakawa kansa yanzu wlh bazai taba ko kallon Laylah da wani yanayinba,
Ataqaice ko kallon fes baya Mata bare wani abun daban yazo

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login