Showing 33001 words to 36000 words out of 108894 words
Siddika ta hada Mata komai na ruwan wanka masu dumi sosai tayi wanka ta fito sanyesa white bathrobe wadda Zata shiga toilet din aka kawo matasu sabbabi ajere kusan guda biyar kala daban daban saidai dukansu ba wasu masu tsayi bane Dole ta Sanya ta fito har lokacin siddika na dakin tana qarasa jera Mata kayanta a closet Wanda Basu wani da yawa Dan Ms Na'ima Bata barta tazo da wasu kayan ba sai anzo Nan.
Koina dakin yadauka qamshin Untrasonic Humidifier dake aiki sai sanyin AC da siddika ta rage Mata sanin akwai zazzabi tareda ita.
Kan couch ta zauna ta jira siddika tagama jera kayan ta fice kafin ta miqe jiki amace ya dauki wata doguwar English gown da siddikar tabar Mata Kan gado tasaka sai qaramar hula Mara nauyi
Cikin qarfin hali tayi sallolinta da aka nunar da ita gabas tana gamawa zazzabin yaci qarfinta sosai ta kwanta agurin kenan saiga saqon zuwan dr Dole ahaka saddika ta kamata suka fito zuwa main hall na gidan ma'ana babban palon farko.
Kallonta Dr Noah yayi anatse kafin yafara mgna da ita saidai ganin maganar bazata yiyuba sbd Bata Gane abinda yake fada sai kawai ya taba duba temperature dinta da sauran abinda yakamata ya Bata magunan dasuka kamata ya tafiyarsa.
Bedroom dinta aka maidata tareda Kai Mata black tea Mai zafi Tasha sosai kafin Tasha magani take bacci ya dauketa siddika ta rufeta da abun rufa Mai tsakanin taushi aka rufo Mata dakin ta nufi nasu dakin na maids tana sauke ajiyar zuciya a gajiye Dan tunda suka iso Bata zaunaba sai yanzu zataje ta huta tayi nata sallolin.
Dayake baccin zazzabi ne sai yamma sosai ta tashi da Rashin qwarin jiki Amma dai zazzabin ya saketa Dan Haka tana farkawa dmta tashi zaune cikin sanyi tareda zuro qafafuwanta qasa ta sauko ta miqe tana nufar toilet ta shige.
Wani wankan da alwala tayo ta fito jikinta na sakewa da samun qwari Dan Haka Kai tsaye sallah tafara Yi kafin ta saka wata doguwar rigar Mai hannuwa Dan ta dazun qaramin hannune da ita Takoma ta zauna Kan couch tana jingina tareda rufe idanuwanta tanajin kewar mutanen data Saba dasu a rayuwarta Wanda ayanzu Anne tana ciki sbd ko ahalin data shiga na yanayin lafiyarta ta shaidar da girman kaunar Anne gareta Dan Haka take sake Jin girman Anty Sa'adah a zuciyarta sbd duk itace ta Bata wannan kyakkyawar rayuwar tunda gidan Aurenta ne ita Anty Sa'adah din.
Tana zaune agurin cikin tunani har tsawon lokaci saiga siddika tashigo dauke da manyan varieties na turarukan Zubawa a humidifier Dake dakin ta jeresu tsaf a inda ake jerawa ta fice Bayan ta sanar da ita anjima zata fito cin abincin dare tareda su Ms Na'ima Dan Haka saita shirya,.
Wasu turarukan tafita takuma shigowa dasu kala daban daban masu tsananin tsada ta jere agaban makeken madubin dakin tana sake sanar da ita koina na gidan basa Wasa da qamshi sbd Mai gidan da zasu zauna guri daya dashi anan gidan.
Sai alokacin ta Dan dago fararen idanuwansa daga zaunen ta kalli siddika da farar baturiyar Dake tayata shigowa da kayan dasuketa shigowa dasu wainda online shopping ne akai Mata masu delivery suka kawo.
Anty Sa'adah na can mijinta na Nan daban
Dama Haka zasuyi rayuwar auren? Kokuwa Dan antyn tana karatu ne
Dan Kam zaman kishi da irin Ms Na'ima Dole a taimakesu anty Sa'adah tayi karatu Mai zurfi sbd samun damar nutsuwa dako wane irin al'amari zaman zai kawo duk da tana jinjinawa Ms Na'ima wani bangaren da batada Kishi ko fitina har tana iya daukar riqon qanwar kishiyarta da zuciya daya Dan Bata taba nuna mata wata fuskar ba bayan ta kulawa da kauna saidai duk girmanta da mutuncinta data gani har abada bazata Kai Mata 'yar uwarta agurinta ba.
Da daddare bayan tagama sallar ishai tana kokarin kwantawa duk da yunwar datake ji saiga knocking kofar dakin ahankali cikin nutsuwa dake nunin ba'a son damunta da bugawar.
Batace komaiba Saida aka Kuma bugawa ta sauko gadon ta nufi kofar ta bude a natse tareda kallon farar baturiyar dasuketa aikin hidimarta dazu da Siddika.
Kallonta tayi da fararen idanuwanta kafin ta Dan sauke idanuwanta tana sauraren abinda take fada Wanda bayan come da waiting in dining room Babu abinda ta fahimta acikin kalmomin Dan turancin yamata tsauri musamman dayake turancin na asalin baturiya ne Dan Haka tunda Bata da wani abun cewa a natse ta saki kofar tabi bayanta cikin nutsuwa.
Doguwar rigace ajikinta Mara nauyi Mai Fadi sosai wadda fadin nata da rashin nauyin material din rigar yasara kwantawa ajikinta sai hular kanta ta bacci mara girma sosai da Bata rufe gaban gashintaba dayake kwance cikin zallan gyaran dayakesha a Abuja Dan kuwa anty Sa'adah da qarfi da yaji Takoma Kamar Mai saloon dinta.
Suka nufi hanyar dining room din Dake palon kurya na hanyar hayewa sama asalin palonsa da master bedroom din Mai gidan.
Daga bakin kofar shiga Cindy ta Dan dakata tareda bata hanya tana nuna Mata tashiga,
Kallonta Laylah tayi kafin takalli kofar data iya jiyo qamshi na musamman na tarbonsu tun daga Nan din,
Jin tayi zuciya na neman shiga rawa sbd ita daza'a barta dakin dayafi Mata
Sam Bata Saba da irin wannan rayuwar ba.
Sake nuna Mata kofa Cindy tayi Wanda yasata daga qafafunta ahankali ta shiga tana kokarin sauke kanta Dan kuwa tana saka Kai akan farar kamilalliyar fuskarsa Data cika palon da kwarjini idanuwanta suka fara sauka.
Zaune yake Kan dining din Kan kujerar Dake saiti da kofar shigowa wadda itace asalin kujerarsa dayake zama cin abinci,
Sanye yake cikin wata black jallabiya da farar hular sallah gabaki daya qamshinsa na _Bois Elite_ ya cike dakin cin abincin
Ms Na'ima na zaune Kan daya daga cikin kujerun dining din itama sanyeda doguwar Riga mara dogon hannu fuskarta ba kwalliyar komai sai lipstick data Dan lura so da dama kamar Yana burge Turakin tunda dadewa sbd duk ranar datasha lipstick Yana Dan yawan kallonta saita dauka hakan da duk suna guri daya lipstick baya rabuwa da bakinta sai idan bacci zatai kokuma tashinta da safe kenan batai wankaba.
Qamshin body mist dinta na _Perry Ellis_ ne yasa Ms Na'ima waiwayowa kofa ta kalleta fuskarta daukeda yanayin damuwa da kulawa tace"
Heyyy Laylah qaraso zo ki zauna
Yaya jikinki?
Kinji sauki da kikasha magani kuwa? Kodai asake Kiran Dr yadawo?
Dagowa yayi ya zuba Mata idanuwansa akaro na farko daya fara ganinta gabansa Dan kuwa tun tana jaririyarta rabon daya Kuma ganinta,
Dogon hancinta zuwa idanuwanta da yanayin jikinta gabaki dayanta yake kalla Wanda tsaf tanajin kallon na yawo akanta Dan Haka sai takasa daga qafafuwanta ta qaraso taja ta tsaya da inda take tsaye zuciyarta na Dan bugawa da rashin sakewa dakuma tsoro harma da shakkar kallo Dan duk abubuwane wainnan gabaki daya da Bata Saba da subaba.
Tasowa Ms Na'ima tayi ta qaraso inda take tareda Kama hannunta ta qaraso da ita tana kallon Turaki Wanda ya maida hankalinsa Kan abincin da aka gama zuba Masa ya saka spoon yafara ci cikin nutsuwa da kamewa tace"
Laylah ki gaida dadynki kafin ki zauna muci abinci ko.
Turaki dama Suprice naso baka shiyasa ban fada maka tareda Laylah zanzo ba
Karatu nakeson tayi anan Dan inason tasamu ilimin dayafi na makarantannin Nigeria sbd gaba idan zata riqe matsayi masu girma a companies dinka"" taqasa fada fuskarta daukeda farin ciki da murmushi Mai yalwa.
Dan dagowa yayi yayi mata kallon seconds biyar na mamakinta Yana tabbatarwa da kansa tabbas batasan matsayin Laylah ba agurinta Amma dai koma tasani ko batasaninba baya tunanin hakan nada amfani Dan kuwa ayanzune ya sake tabbarwa da wannan auren Kamar wani riqone agaresa Dan kuwa Babu ta yanda zai iya kallon 'yar cikin Mahmoud da Zainab amatsayin Mata,
Alaqar aure da ita Kamar abune daya Riga ya haramtawa kansa
Zamanta a matsayin Yar riqo garesa kamar yanda Na'ima tadauka
Da kansa zai aurar da ita Inshallah idan lokacin hakan yayi.
Cikin wata irin sanyin murya da nutsuwar dake bayyanarda rashin sakewarta agurin ta furta"
Ina wuni.
Gyada Kai yayi Kai tsaye Yana cewa"
Seat.
Zaunawa tayi a darare tanajin duk girmansa ya cika gurin Dan Haka sama sama taci abincin Wanda dama Bata iya cinsaba Dan macaroni salad ne sai baked potato da fresh fruits masu sanyi kadan.
Ita tafara gamawa Amma takasa barin gurin Saida yagama ya miqe yabar dining din Yana yimusu Saida safe cikin sautin girma da kulawa.
Yana fita Ms Na'ima tasake zuba Mata abincin Wanda tasata ci Dole ahakan kuwa cikinta ya cika ba laifi kafin suka baro dinning din zuwa Palo Ms Na'ima na janta da zantukan yanayin qasar da rayuwar gidan
Dayake zuwa yanxu tasaba da yanayin Laylan sai rashin tankawarta sosai baya damunta tunda tasan hakan Laylahn take.
Saida bacci yazowa Laylah sosai kafin Ms Na'ima tabarta ta nufi bedroom dinta tayi Shirin bacci ta kwanta
Take bacci ya dauketa sbd koshi da gajiya.
Washe gari da safe data Gama tabbatarda sake kiranta za'ai gurin Cin abincin safe Dan Haka saita lafe taqi nuna ta farka duk yawon kiranta da Cindy taringa Yi Dole aka barta sbd lokacin Turaki ya sauko harya zauna cin abinci
Yana gamawa ya fice.
Sai qarfe goma Sha daya ta nuna ta farka ta tashi tayo wanka tuni akai Mata nata abincin aka Kai dining ta fito Dole sanye da farar chiffon lace blouse da blue palazzo kanta daureda qaramar veil fari fuskarta ba komai bayan glowing na savor beauty moisturizer Babu abinda takeyi
Kai tsaye dining room din Cindy ta nufa da ita agaba tana binta.
Ba laifi abincin da akai ta iya cinsa sbd pancakes ne da Black tea sai soyayyan kwai da potato chips.
Tana gamawa daki Takoma tayi zamanta cikin kadaici da kewa.
Da yamma Dr Noah yasake dawowa yaduba yanayin jikinta ya tabbatarda tasamu lafiya saiya tafiyarsa.
Haka ta wuni ba wani abin Yi ko abokin Hira har dare takuma dojewa fita cin abincin Amma da Rana dayake akwai Dan sani da sabo tsakaninta da Ms Na'ima taje sunci abincin Rana tare a dining din.
Washe gari Bayan fitar Turaki A Abdoul yasakawa Ms Na'ima wasu irin maqudan kudi na siyayyar Laylah da har anshigar da maganar sakata makaranta,
Dadin duniyane yafara cika Kan Ms Na'ima ganin tafara morewa riqon Laylah tun baaje koinaba Dan kudin da aka batan idan siyayyar haukar me zataiwa Laylah bazasu cinyesu Dan Haka Laylah Nagama breakfast Ms Na'ima na jiranta cikin Shirin doguwar Ashape gown ta chiffon Mai tsadar gaske suka fita cikin daya daga cikin manyan motocin gidan.
#MAMUH#
Follow me at Arewabook @mamuhgee Dan samun complete books Dina dama sauran pages na Noor Albi Dake fara sauka acan.
ðð
Eznah
Tarayya
Deen Marshal
Ubayd maleek
Min qalb
Buri daya
Kaunarmu
Noor Albi
Dacewa
Dawood
Zucuyarmu daya
Auren raba gardama
Taura biyu
[6/8, 9:57 AM] MGð: _*Mamuhgee 19*_
Siyayya sosai Ms Na'ima tayiwa Laylan ta kayan Yan Mata 'yayan gata,
Komai da aka siyo Mata designers na yayan gayu tun daga kan handbags da shoes da kayan sawar dasu agago,da perfumes da undies ma da aka siyo Mata Kaya guda harma da nightwears.
Harda sabuwar waya Mai tsada sosai ta aka siya Mata tun acan aka saka Mata komai tasaka Mata Numbern Anne wadda takejin buqatar su dawo gida takira ta gaisa dasu musamman anty Sa'adah datakejinta tamkar uwa.
Sai yamma suka dawo gida sbd Saida suka biya spa.
Suna dawowa sallah kawai Laylah tayi ta saka Kiran Anne wadda Kamar tasan Laylah ce Bata qi daga Kiran ba kamar yanda take wasu lokutan na qin daga baquwar numbern Amma ganin international number saita daga.
Cikin sanyi da nutsuwa Kamar koyaushe Laylah tace"
Assalamualaikum Anne Ina wuni.
Da mamaki Mai tattareda farin ciki Anne ta amsa sallamar tana cewa"
Masha Allah Laylah tasamu Kira kenan.
Ahankali Laylan tasaki murmushi Mai qaramin sauti tana cewa"
Dazu ne aka bani wayar,
Ya gida Anne?
Inasu halima duk suna lafiya?
Dariyar manya Annen tayi tana cewa"
Duk lafiya kalau Sa'adah ma da kike Jin nauyin fara tambayarta kafin kowa lafiyarta kalau
Tana daki tareda baqi datai dangin mahaifiyartane sukazo Zan Bata numbrnki saita kiraki,
Yaya kike?
Ya qasar kina Jin Dadi kuwa?
Zaki iya zama kokuwa nasa Turaki ya dawo Dake Nan?
Murmushi kawai ta iya saki ahankali tana cewa"
Lafiyarta kalau.
Kin tabbata Zaki iya zama dasu anan din dai ko?
Kasa cewa komai tayi sbd itakam duk yanda sukai da ita Yi zatai Dan Haka batajin tanada zabin inda zata zauna acikinsu koina zata iya zama ayanzu tunda Bata tareda mahaifinta.
Ga dangin Momy da Annen tace sunzo kilama tafiya zasuyi da ita kamar yanda dama sukace bazata zauna dindindin hannun Sa'adah ba zasu dauketa Takoma gida,
Yanzu da Momy Bata Nan idan Suka dauketa tasan gidan umma Jamila za'a tafi da ita direct Dan Haka ita batada zabi aduk inda za'a kaita
Me gata ne yakeda zabin gurin dazai iya zama.
Sosai Anne ta tambayeta lafiyarta dakuma tambayoyi akan idan batada matsala da komai na gidan
Hardai suka gangaro akan karatu da Laylan zata fara ta Bata qwarin gwiwa da tabbacin zata iya sosai idan tabada himma kafin suka aje wayar tanajin nutsuwa da kwanciyar hankali akan maganar datai da Annen Dan kuwa magana da Anne na Bata nutsuwa shine abinda tasabu dashi a zamansu.
Wanka tayi kafin ta fito komai na dakinta da siyayyar da akayo Mata angama tsarasu ako Ina take dakin yazama na cikakkiyar budurwa
Tana fitowa Cindy data Gama aikin tana ficewa tabar siddika datake qarasa kunna Mata humidifier itama tana gamawa ta fice.
Zama tayi gaban mirror tana kallon fuskarta akaro na farko data zauna tana qurewa kanta kallo tareda Shiga tunanin wannan wace irin rayuwace tasamu kanta aciki kuma wadda take ga Kamar Jin dadin yayiwa marainiyar kamarta yawa.
Mai tashafa da body mist ta miqe ta duba closet dinta da aka gama gyarawa shaqe da Kaya saidai abin sanyin jikin shine yawanci ba kayan mutunci bane Dan mafi yawansu wanduna ne da skirt na Yan gayu da batasan yazatai sabo da sakawa
Dogayen rigunan ciki qalilan ne Suma duk ba masu mayafai bane saidai idan ka saka ka daura qaramin scarf akai.
Batada zabi Bayan saka wando da Riga Takoma bakin gado ta zauna tana daukar sabuwar wayarta da har cikin ranta tayi farin cikin samun wayar sbd waya dasu anty Sa'adah duk da tanajin tanason kira taji abbanta Amma tasan Momy bazata taba iya magana da itaba Dan Haka ta hakura da hakan tunda anty Sa'adah na waya da ita tanajin komai tana fada Mata hakanma yayi zataci gaba da Masa addua ta jira hukuncin ubangiji akan ranar haduwarta da Mahaifinta.
Da daddare ba dalilin rashin fitowarta cin abinci Dan Haka Dole ta fito sanye cikin Riga da wando masu Fadi kalar Ash kanta daure cikin qaramin scarf saidai gashinta ya fito kadan
Tana shigowa dining room din taga ba kowa aciki tasaki boyayyar Ajiyar zuciya tana Shirin juyawa saiga Turakin ya doso dining room din sanye cikin Ash Armani's da slippers baqaqe da Suka bayyanarda Hasken qafafuwansa
Kyakkyawar fuskarsa a sake saidai bakuma Wai Yana murmushi bane ko dariya
Tana ganin hakan ta dawo tana matsawa daga hanya Yana kawowa ya dago fararen idanuwansa yayi Mata kallo daya ya dauke Yana amsa siririyar gaisuwarta datai Masa itama bayan ta sauke idanuwanta daga kallonsa.
Ms Na'ima Dake gefensa ta miqa Mata hannu ta Kama suka qarasa dining din tana cewa"
You look fresh my girl.
Sunkuyar da Kai kawai Laylan tayi suna zaunawa.
Bayan sun Gama cin abincin Kai tsaye kallon Laylah yayi bayan ya miqe yace ta samesa Palo idan tagama.
Kasa hadiye ruwan dake bakinta Tai sbd wata irin fargaba data sameta ta dago ahankali ta kalli Ms Na'ima Dake Mata murmushi tace"
Take it easy Girl ba komai bane zaiji abubuwan dakike buqata ne da Kuma raayinki Akan abinda kikeson karanta.
Kallon Ms Na'ima din tayi tareda bude Baki cikin sanyi da nutsuwa tace"
Me zance?
Wata dariyar Jin Dadi Ms Na'ima tayi ta Jin dadin Laylah tafara zama tafin hannunta akan sai abinda tace.
Ta Kama hannunta suka miqe zuwa gurin Turakin tana cewa"
Daddynki ne kibar Masa zabi da kansa ya zaba miki kawai dai ki dage kiyi karatu sbd akwai yiyuwar rayuwa Mai kyau agaba idan kikai karatu zamuji Dadi Sosai agaba.
Gyada Kai kawai tayi batareda tana fahimtar komai da Ms Na'ima din ke fada ba Dan duk Bata nutsuwarta.
Zaune yake gabaki daya yagama sauya iskar palon da qamshin jikinsa Wanda Babu Wanda zaiyi haduwa biyu zuwa uku dashi batareda ya Gama sanin wannan qamshin nasane na musamman.
Saida suka kawo tsakiyar palon kafin ya dago daga wayar daya keyi ya zuba musu idanuwansa take Laylah ta Dan rage takunta ta danyi bayan Ms Na'ima itama kanta Ms Na'ima din idanuwan Turaki kasheta sukeyi Dan Haka ita qafafuwanta sauri suka qara Kamar ansaka musu batir ta qaraso gefensa ta zauna tanajin a duniya batajin akwai ranar dazata iya barin Turakin ya iya kallon wata macen da sunan so ko makamancin hakanba Dan kila Aron hauka zatai ta halaka koma wace da danginta gabaki daya.
Dauke kallonsa yayi daga kan Laylan wadda duk tabi ta rikice Tama Rasa gurin zama saitayo gurin Ms Na'ima din tana kokarin zama a qasa.
Muryarsa dake sake rudar da ita sbd kamewa da Rabin Wasa ko kadan acikinta ya furta"
Gobe za'a fara fita Dake zuwa harkar makaranta Dan Haka ki ringa kula Nan ba Nigeria bane karkiyi qawayen banza ok??
Bata Gama gane meyace ba kawai dai ta gyada kanta cikin biyayya tareda furta "nagoge" ahankali.
Daga Haka Ms Na'ima ce ta ringa tsarowa Laylan zance da nasiha akan ta dage tayi karatu.
Ita dai Kai kawai take gyadawa Bata iya bude Baki.
Sai kusan goman dare tadawo bedroom dinta ta sauke numfashi tareda Ajiyar zuciya tana zare kayan jikinta ta nufi toilet tayo alwala ta fito ta Sanya kayan bacci Kamar yanda Ms Na'ima ta Gama Bata tsari da yanda zata ringa gudanar da komai.
Face cleanser ta Gama goge fuskarta kafin ta kwanta Wanda shikuma a spa din dasukaje aka karbo Mata shi akace ta ringa shafawa kullum kafin kwanciya shima duk aikin Ms Na'ima ne.
Washe gari qarfe goma A Abdoul yazo ya dauketa a motar Turakin yakaita Emory inda dama tun zuwanta washe gari aka fara process na shigar da ita Dan Haka Koda A Abdoul yakaita har process da payment nata na extra classes anyi komai tareda da daukar Mata wata Sofia Yar asalin nijar da zata ringa koyar da ita wasu abubuwan da Hausa kafin tagama iya turancin da wasu abubuwan.
Dan Haka washe gari tun safe tafara zuwa makaranta
Da farko hankalinta ya tashi sbd kasa Shiga cikin mutane tayi Saida