Showing 21001 words to 24000 words out of 108894 words
zasu tafi Dake jibi Kuma meyene na zuwa yanzu?
Sunkuyar dakai tayi cikin tsananin kunyar kanta da baqin cikin halin dangin mahaifiyarta.
Anne ce tayi murmushin manyanci tace"
Zuwa sukayi gaidani
Bakuma illa bane hakan, tare suke da Yar gurin Zainab wato zainab.
Gyada Kai yayi Yana jinjina al'amarin dangin Zainab da basuda lissafi ko daya.
Dan dagowa Sa'adah tayi cikin zurfafa kalami da nutsuwa ta kalli Kawun tace"
Kawu inada maganar fada akan....cikin wani Irin sauri da waskewa Kawun ya katseta da cewa"
To Ina suka tafi da bazasu taho ku koma Haka ba tunda Kun Mata barka da zuwan.
Kallon mamaki Sa'adah takewa Kawun ganin ya da yayi saurin katseta kamar yasan abunda zata fada,
Kokuwa shima su umma Jamila sun siyesa an shafa Masa kudi?
Shikuwa Kawun sanin rashin Arziki irin na dangin Zainab yasashi katse Sa'adah din Dan baisan mezata fadaba agaban sirikar da ba'a ringa andaura aurenba taje ta zubarwa da kanta dashi da Dan uwansa mutunci tunda su dangin uwarta Akan kwadayi yaga alamar ba kalar mutuncin da bazasu zubarba.
Sake yunqurin magana tayi ya banko Mata wata irin mugun kallo yna kokarin miqewa Yana yiwa Anne sai anjima shi zai tafi.
Kallon Sa'adah da idanuwanta suka sauya tayi dakyau taga alamar da akawai damuwa saita kalli Kawun a natse tace"
Kaga malam saidu koma ka zauna
Yarinyar Nan magana zatai dakai
Da alama Kuma akan auren Nan
ALLAH yasa ba Dole acikin al'amarin??
Ajiyar zuciya ya sauke yana komawa ya zauna zuciyarsa fal da takaici Dan kuwa idan har yarinyar Nan ta bude Baki gaban Anne tace batason auren Turaki wlh saiya Mata dukan mutuwa tabi sahun mahaifinta asibiti
Dan iyakar zubarda girma da mutunci ta zubar masa idan hakan tafaru
Kuma agaban Anne yarinyar Nan zata shimfida wannan rashin da'ar.
Kallon Sa'adah Anne Tayi hankali kwance a natse tace"
Menene Damuwar Sa'adah?
Auren ne bakyaso zasuyi Miki Dole kokuwa?
Zazzaro idanuwa Kawu saidu yayi Yana kallon Sa'adah Dan ta kallosa yasamu damar Mata gargadi Kota idone Amma taqi kallonsa Kai tsaye ta gyada Kai tareda sauke Kai daga kallon da Anne ke Mata tace"
Bani Abba yaceba
Laylah yace....
Dan shiru tayi na minti daya kafin ta hadiye hawayen dasuka ciko idanuwanta tana qara bawa kanta qwarin gwiwar magana tace"
Su umma Jamila ne sukeson sauyawa Dani Amma Abba Laylah yakes.....kasa qarasawa tayi sbd siririn kukan dayazo Mata na karyewar zuciya Dan kuwa harga Allah da ita din aka bada datayi farin ciki Amma Kuma bazata iya auren Wanda ba ita din aka basa aurenba Kamar haramci take kallon kanta a auren shiyasa ta Kori shedan ta danne komai ta fada gskia.
Wasu manya manyan Ajiyar zuciya Kawu saidu ya ringa jerowa a boye Yana Dan goge zufan daya tsatsafo Masa a goshi cikin dubara
Dan duk yagama katsewa da bijrewa auren Sa'adah zatai ta wulaqanta zumuncin da mutunci da Anne ke gani
Shi Turakin ba'a maganarsa sbd yasan ko ahaka Matar da auren ba lallai suna gabansaba.
Anne kuwa wani irin kyakkwan murmushi Mai sanyi tasaki tana kallon Sa'adah din cikin tsananin burgewa da yabawa da hankalinta datai saima taji Sa'adah din tashiga ranta itama Dan Haka ta kalli Sa'adah din a natse tace"
Meyasa zasu sauya Laylah bayan da ita din Dake duk Abu dayane?
Shiru Sa'adah tayi Bata iya cewa komaiba sbd a bayyane yake basai anfadaba ansan Laylah batada gata batada Wanda ya tsaya Mata sai Allah.
Wani murmushin Anne takuma saki kafin ta kalli Kawu saidu tace"
Malam saidu kaji abindayake faruwa.
Cikin takaici da baqin cikin Hali irin na zuriarsu umma Jamila yace"
Tabbas dama Zainab da danginta bazasu taba Bari Laylah tayi rayuwarda kowane 'da mai yanci zaiyiba,
So suke yanda ta taso a wahala ta qare a wahala shiyasa gashinan masifarsu da rashin imaninsu ya haukatar da ita kwakwalwarta Bata cikakkiyar lafiya
Yarinya Takoma Kamar mutum mutumi
To gwara danaji wannan zancen Dan kuwa wallahi ita Zan daurawa aure dukkaninsu sun Dade kwadayi Bai Gama kashesuba Dan nasan manufarsu ta auren
Kema nafasa tafiyar bazan tafiba saina aurar Dake ga duk Wanda nasamu zanga uban dayafini iko akanku cikinsu.
Daga fada da maganganun Kawun Anne tafahimci abindayake faruwa a rayuwar iyalin Mahmoud din take taji wani irin rashin Jin Dadi da tsananin qauna da tausayin Laylah
Yarinyar data taso cikin maraicin uwa da uba duk da Yana Raye,
Tabbas kuwa Kamar yanda Kawun Yafada aure Kam da Laylah Kamar ba fashi saidai Kuma fushinsa na aurarda Sa'adah din daketa kuka Mai tsima Rai bataga DACEWA da adalci a hakan ba Dan kuwa itama Sa'adah ta cancanta rayuwa Mai kyau tunda har tanada kyakkwan zuciya Dan Haka Kai tsaye tace"
Malam saidu kayi hkr karka yanke hukunci cikin fushi akan Sa'adah da Babu ruwanta a wanna al'amarin
Idan har batada wani tsayayyan mijin Zan tafi da ita kodan Yanayi na rayuwar Laylah daba lafiya isashiyaba
Tunda harkace ta mental health Dole zaaje da Wanda tasaba dashi harta warware tafito daga depression din datake ciki kafin ma ayi maganar sanar da ita auren Dake kanta daga
Kuma best solution anan shine tafiya da Sa'adah,
Dan karatu da komai na rayuwar Sa'adah na dauka Inshallah Dan dama tuni yakamata muyi hakan mu dauki 'yayan Mahmoud Dan inganta rayuwarsu da ilimi Mai kyau da tarbiya
Amma tunda yanzu komai yazo da hakan Inshallah idan ka amince Zan daukesu duka su biyun
Laylah Amatsayin Matar Turaki Sa'adah Amatsayin Amanata Inshallah.
Sosai ran Kawu yake quna da Daci sbd har kunyar kansa yaringa ji daya biyewasu Alhaji Atiku Ashe yaudararsa akeyi Dan ya cutatar da 'yar marainiyar 'yar Dan uwansa duk da Sa'adah dinma daya suke agunsa Amma ita tanada gata tako Ina tunda gashi sunso cin amanarsa su tura tasu Yar gurin arzki,
To kuwa zasusan yanda asalin mugunta da yaudara take Dan yanda sukai Masa Haka zai musu bazai fada musu gskiyarba shima shiru zaiyi sai ranarda Allah ya nufa susani.
Sanin daga Laylah din har Sa'adah suna buqatar rayuwar da Anne ke fatar Basu yasa ya amince da tafiya dasu duka biyun tunda koba komai Abba ma wata qasar za'a kaisa dan Haka zamansu cikin zuriar Zainab da basuda Imanin na sanin komai bayan kudi akwai matsala gwara su tafi gurin Annen har Allah yabawa Abban nasu lfy.
Bayan ya amince rokon Anne yayi akan abar zancen auren ayanda yake abar dangin Zainab da sanin da Sa'adah za'a daura sbd karsu cutatar da Laylah.
Momy kuwa dayake da ita za'a tafi qasar daza'akai Abban itama yace abari sai bayan daurin auren zai sanar Mata a sirrance ko zatai hankali tabar rakiyar danginta taje tayi jinyar mijinta tasamu lada ko zunubanta na shekaru sa kakkabe.
Da wannan Ya tafi yabar Sa'adah din wadda Anne keyiwa nasiha cikin hikima da tambayayi akan Laylah datake iya amsa wasu
Wasu Kam bazata iya amsawa sbd basuda dadin saurare Kuma hakan tamkar zubarda mutuncin mahaifiyarta ne zatai.
Anne da kanta da Yan bayanin data samu daga Sa'adah din tasake fahimtar rayuwarda Laylah ta taso aciki Dan Haka ta yanke shawarar hadawa har Laylah din ta riqesu da Sa'adah bazatai saurin sakata a rayuwar aureba sai Laylan tadawo kamar kowane 'da mai walwala da rayuwar yanci,
Bama za'a nuna Mata tanada aurenba a yanzu tana buqatar Abubuwan sauyin rayuwa harma da ilimi duk bayan tadawo cikakkiyar lafiyayyarta kenan idan depression yabarta Dan Haka zata barta Akan riqo ta daukosu kokuma akan biyo Sa'adah datai gidan Aurenta.
Tafiyar Kawu ba jimawa Haj Karima tadawo tareda Laylah dake bayanta kamar Mara lafiya tana tafiya a sulale
Kallon qauna Mai girma Anne ke Mata tana Jero adduar samun tsaftatacciyar zuria daga gareta.
Kasa boye kulawarta tayi tasa aka dauko kyauta ta musamman na kayan Alfarma da aka dinko masu tsadar gske da sunan Amaryar Turakin tabawa Laylah tace"
Gashinan kema gobe ranar daurin auren kiyi ado.
Saida takalli anty Sa'adah kafin tasaka hannu biyu ta karba tana godiya kanta aqasa.
A hanya ba kalar fada da masifar zuwa da ita da Sa'adah tasa sukai Wanda Haj Karima din bataiba kamar ta rufe laylan da duka duk da yau Sa'adah dinma tafi qular da ita Haka suka koma gida masu gyaranta na jiranta ayi za'ai Mata qunshi.
umma Jamila taso karbar kayan ta sauyawa Laylah da wasu Momy ta Hana da cewan Kar ayi abunda zai zubarda mutuncin ko wani kallon daban daga Anne.
Hakan yasa ta hakura ta barwa laylan Amma Kam mugun kallo Babu kalar Wanda ba'a bita dashiba ta sulale tashige daki ta zaunawarta anata hidima da hayaniya sbd gidan acike yake tap da dankin Momy anata bidiri cikinma an hanasu bikin komai da Allah kadai yasan irin shagalin dazasuyi.
Qunshi akaiwa Sa'adah sai bayan magriba aka kammala tasamu ta wanke tayi wanka tayi sallah har lokacin Laylah na daki Bata fitoba dan yau fitowa daki tafi qarfinta a gidan sbd dangin Momy duk Babu Wanda yake qaunar ganin ko giftawarta.
Duk yanda taso janta da zance akan ta sake kasa sakewa Laylah tayi dan itadai matuqar dangin momyn na gidan batada sauran nutsuwa ko sukuni.
Haka Sa'adah ta qyaleta har lokacin kwanciya yayi Laylan tayi bacci tabar Sa'adah na binta da kallon gobe Kamar wannan lokacin ra igiyoyin Turaki uku cif na Aure akan Laylahn,
Wannan shine babbar nasara sbd batada masaniya,
Lokacinda zatasan da aurensa akanta kilama lokaci yaja lokacin zatafi Jin zancen auren Al'amari Mai girma.
##MAMUH#
Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
[6/2, 11:21 PM] MG💋: *_Mamuhgee 12_*
*_SAKINA VENDABLES_*
*_Ina ma'abota son qamshi da gyara? Ina masoya qamshi dasuka San darajar qamshi da gyara irin na qamshi?_*
*_To kuzo ga SAKINA VENDABLES Tasake zuwar muku da ingantattu Kuma tsararrin kayan qamshi masu kyau da qarko,_*
*_Ga wainda suke buqatan turarukan gaske masu kyau na asalin qamshi da Kama jiki da Kaya suzo ga inda aka tabbatarda kyau da qarfinsu a gurin SAKINA VENDABLES_*
*Turaren wuta list*
Queens special
Kajiji mix
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous
Khumra White & Black
*Kulaccam* Black(for hair) white (for body)
Handles *Instagram* @sakina_vendibles *Facebook* @Sakina vendible *Tiktok* @Sakina vendibkes
08106974073
******
Kamar yanda Haj Anne ta sanar Masa da bayanin komai da Kawu saidu yayi Mata shiru yayi Yana sake juya zancen Dan kuwa Babu wani sauran abinda zai iya fada ayanzu tunda Anne tariga ta karba Auren Amma Kuma duk da hakan zai karba auren ne Dan taqaita maganar,
Zai karba auren Amma badan ya karbeta a matsayin Mataba,
Zai karba auren Dan inganta rayuwarta ta hanyar Bata ilimi Mai kyau da tsadarda zai iya bawa 'yayan cikinsa da yanada,
Kar karbeta ne tamkar 'yar riqo har zuwa lokacinda Allah zai bawa Amininsa nasa lafiya saiya sawwaqe Mata ayi Mata auren daya kamaceta,
Wannan shine abinda ya yankewa kansa da maganar auren
Dan kuwa bayajin har abada zai iya kallon 'yar da Mahmoud da Zainab suka Haifa Amatsayin matarsa,
Macen da zai iya muamala ta daban da ita bayan ta uba da 'ya.
Da wannan ya rufe maganar aka fara Shirin auren Wanda Babu Bata lokaci aka Sanya sati Mai zagayo ranar juma'a.
Wasu irin kudin gaske Aka aikowa Momy da Kawu saidu na hidimar Wanda yakusa haukata kawunan dangin momyn suka so cinye kudin
Dayake Kawu saidu shima idanuwansa a bude suke yace Babu wannan maganar shima Dole a fitarda na dangin uba abasa idan bahakaba zai fasa bada auren.
Wani irin murmushin bakada lafiya su Haj Karima sukai Masa
Alhaji Atiku kuwa Jin abinda Kawun Yafada yasashi kallonsa da kyau da hasaso irin dukan mutuwar dazasu saka Yan dabansu na shiyasa suyi Masa idan har ya kwatanta abinda Yafada din,
Umma Jamila kuwa cikin ranta fatar saukar masifar datafi ta Dan uwansa Mahmoud tai Masa.
Momy da har lokacin zuciyarta najin wani iri a al'amarin kallonsu tayi jiki a Dan mace ta rokesu akan subawa kawun haqqinsa na matsayin uba ko Dan asamu albarka a wannan auren.
Haka suka bawa Kawun saidu kudin dabai taba riqe irinsuba arayuwarsa hakama takamaimai baisan me zaiyi dasuba kawai dai yafison ya karba din Dan kuwa yagama ganin zallar kwadayin abun duniya da son zuciya a al'amarin dangin Zainab din.
(WAINDA SUKE RUDEWA DA SUNAN ZAINAB DANAKE FADA SHINE DA MOMY DA MAHAIFIYAR LAYLAH DA LAYLAH DUK SUNANSU ZAINAB,ITA LAYLAH SUNAN MAHAIFIYARTA AKA SANYA MATA BAYAN RASUWAR MAHAIFIYAR).
Sabuwar rayuwa Kawu ya bude a garin Dan kuwa tuni yasaka Abdullahi agaba akayo Masa manyan dinkunan bikin tareda huluna masu tsada da takarma harma dasu turaruka Kawun ya siya,
Dayake baida rowa har Abdullahi yabawa nasa kason kudi masu 'yar tsoka wanda yasa Jikin abdullahi din yakuma sanyi da al'amarin yaji bazai iya boyewaba Dan Haka Ana saura kwana biyu daurin auren da daddare ya nufi gidan umma Jamila Dan ganin Sa'adah wadda ita kadai yasan zata fahimcesa sbd kaf kowa dukiyar tagama rufe idonsa
Shikuma yakasa danne al'amarin sbd sanin Auren Laylah da Turaki Kamar wani boyayyan burine Kuma Alqawarin Abba Wanda duk ranarda ya tashi yaga wannan sauyin bazaiji dadiba duk da itama Sa'adah din 'yarsa ce Amma kamar sbd mahaifiyar Laylah yakeson Lallai laylance zata aura Turaki.
Babbar Sa'ar dayaci a zuwa gidan umma Jamila Bata Nan suna gurin hidimar bikin da aketayi duk da Turakin yasanar da cewan basason Ayada Dan kada Yan Media suji Amma zancen ya Dan firfita sbd sukam su Alhaji Qarami sunason asan Wanda suka bawa auren yarsu,sunason duniya tasan sun hada alaqa da ABUTURAB TURAKI Ko Dan matsayinsu da girmansu yaqaru a idon jama'a.
Lokacinda Anty Sa'adah taga Abdullahin ne Mai neman ta gabanta Saida yayi mummunan faduwa
Take jikinta yayi Sanyi sbd tasan tabbas kodai abbansu kokuma Laylah akwai Wanda wani Abu yasama.
Shigowa tayi dashi palon baqin gidan suka zauna takawo Masa ruwa tana kallonsa jiki mace muryarta na bayyanarda damuwarta tace"
Yaya Abdullahi Allah yasa lfy dai Dan nikam ganinka yasa jikina mutuwa.
Ruwan data kawo Masa ya Dan Sha Yana dauke idanuwansa daga kallonta ganin irin yanda ta sauya sbd zallar gyara da ake mata tayi haske sosai tayi fresh duk da ta rame Amma duk da hakan a idanuwansa ko ahakan batakai Laylah kyawu da haske ba.
Aje ruwan yayi tareda Dan kallonta kadan cikin nutsuwa yace"
Abba dai yananan yanda take hakama Laylah tananan da dama itama saidai Kam duk tayi wani iri sbd kadaici da rashinki ahakan ma dai aikin gidan yadawo kanta,
Saidai ba wannan ne yakawoniba.
Kallonsa Anty Sa'adah din tayi batareda ta iya cewa komaiba tana sauraron abunda zai fada.
Ya fuskanceta dakyau Yana tattaro nutsuwa yace"
Maganar auren Nan ne da za'a daura jibi nazo nafada Miki sbd naso daurewa nayi shiru nakasa hakan sbd Abba da Laylah dama ke din.
Ahankali ya zayyano Mata burin Abba da babban qudurin nasa na Bawa Turaki auren Laylah tareda sanar da ita asalin abindaya faru ranarda ciwon na Abban ya rikice sbd shima Kamar yanda Momy taji komai yaji komai ganin momyn zata juyo tabar gurin yasashi barin gurin tun kafin tagansa ya fice daga gidan
Dan Haka ya Dora da cewa"
Sa'adah ke kadaice gatan Laylah ayanzu tunda Babu Wanda take nuna yasanda ita bare damuwa da rayuwarta,
Kece gatanta ayanzu da Abban yake kwance,
Kece uwa Kuma uba gareta hakama 'yar uwa,
Idan kikayi auren Nan Kika tafi Amatsayin Laylah da wace daraja Turakin da Mahaifiyarsa zasu kalleki?
Hakama Abban duk ranarda ya tashi da wace darajar zai kalleki da Momy,
Hakama babban abindayake faruwa shine Turaki yasa ahada takardu da komai na lafiyar Abban za'a daukesa daga Nan zuwa wata qasar Kuma ansanar da Momy ta aminta da atafi dashi din Dan Haka bayan aurenki bana tunanin Laylah tanada wani sauran abinda yarage anan bayan kunci.
Nidai abindayasa nazo nafada Miki gaskiyar lamarin sbd kome Zakiyi karki manta da 'yar uwarki Dan Allah,
Kamar yanda Kika dauko tallafar rayuwar marainiyar Allah kici gaba da tallafa Mata Dan Allah karki Bari ta Shiga wani mummanan halin dayafi Wanda take ciki sbd nidai da antafi da Abba zuwana gidan nasan yaqare tunda dama dawainiyar Abban ke kaini.....
Dogon numfashin data saukene yasashi dakatawa Yana sauke nasa numfashin shima kafin ya kalleta ganin yanayinta ya sanyashi miqewa Yana kallon Agogo
Gwara ya tafi kafin umma Jamila tadawo ta taddasa gidan
Hardai idan tasan abin daya kawosa da Babu shakka saita Ari hauka ta Masa mummunan wulaqanci.
Bayan tafiyar Abdullahi Sa'adah na shiga gida tafara hada kayanta Dan kuwa ta yanke shawarar komawa gida ayau din,
Gwara Takoma gida kawai aqarasa komaima acan.
Koda umma Jamila tadawo agajiye take shiyasa Koda Sa'adah din Tai maganar komawa gida Bata kawo komai arantaba tasa driver yakaita Dan dama gobe za'a maida Sa'adahn gida sbd gobe su Haj Anne zasu iso
Dan Haka Kai tsaye tasa aka maida Sa'adahn gida da maraicen ta bugawa Mai hajiyar dasuka dauko ta musamman Dan gyaran Amarya waya cewa subi Sa'adah din can gida aqarasa acan na yau da goben.
Ko data iso gidan tsit kamar ba hidimar biki akeba Momy na Palo da baqi suna magana tashigo a natse fuskarta daukeda murmushi taqaraso gabansu cikin girmamawa ta gaidasu tana kallon Momy datake kallonta tana yaba kyawun datayi tace"
Momy kinata kallona
Na sauya Miki ne?
Murmushi momyn tayi tana cewa"
Dan sauyi kin sauya Kam kamar ba Sa'adah ba
Wannan hajiya Sa'adah shuwa Arab ce.
Dariya baqin momyn sukayi suna yaba gyaran na Sa'adah dake bayyane afili Dayar tace"
Momy ko Zaki bani numbern me gyaran Nan sbd auren sanah da zaizo qarshen watan Nan Dan Naga ta iya gyaran amare Kam gashi Sa'adah sai wani irin qamshi takeyi Mai Dadi.
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902_* itace Mai wannan aikin na gyaran Amare tareda kayan qamshinda ko a anguwa za'a San ankawo Amarya,
Turarukanta na musamman ne Dan kuwa daga Chad suke zuwa ga kayan Mata na gyara masu kyau da inganci
08067558902.
Kai tsaye daki Sa'adah ta wuce inda ta tararda Laylah a dakinta zaune tana ninke kayan wanki datai na tarin tsoffin kayan Sa'adah da aka Bata akace gashinan ta ringa sakawa can gidan idan Sa'adah din taje da ita Dan karta ringa saka tsoffin kayanta dasuka Gama kodewa.
Tana ganin Sa'adah taji wani irin sanyin farin ciki harsaida fuskarta ta bayyanarda hakan
Fararen idanuwanta akan Sa'adah din tabude baki tace"
Anty Sa'adah kindawo tun yau ne?
Qarasowa Sa'adah tayi gabanta fuskarta daukeda murmushi tana kallon kayan da Laylah din ke linkewa tace"
Meyasa zakiyi wankin kayana tunda banananma ba sakawa nayi ba.
Kallon kayan tayi tana qarasa Nade rigar Dake hannunta tace"
Jiya Umma Jamila datazo suka bani itada Momy sunce Dani zakije na ringa sakawa acan.
Shiru tayi tareda sauke Kai tana jiran abinda anty Sa'adah din zatace ko tana buqatarsa kayan nata.
Shiru anty Sa'adah tayi