Showing 3001 words to 6000 words out of 108894 words
tareda dashi Yana taimakawa gurin hidamar kulawa dashi,
Kusan duk wasu hidimar asibiti madai shine yake jagoran saidai Laylah tabisa abaya.
Ganinsu kowanne fuska ba wani walwala yasata juyawa Takoma ahankali bayan tagaida Dr Abbakar din cikin nustuwa.
Bayanta dukkaninsu sukabi da kallo har Dr Abbakar din Wanda yariga yasan damuwar Abba ba akan rashin kyawun results dinsa dasuka fito na asibiti akan yarsa ne wadda yakejin ko yayane idan Yana Raye tana abun kallo da dogaro Koda Baida wata moriya agareta dagashi har ita suna debewa juna kewa da baqin ciki.
Ajiyar zuciya Dr Abbakar yayi shima cikeda tausayin Abban dama laylan
Ya dago ya kalli abdullahi ya miqa Masa wasu takardu yace"
Malam Abdullahi karba wannan Dan Allah kaimun mota Ina fitowa.
Karba yayi cikin girmamawa jiki a sanyaye ya fice.
Bayan fitar Abdullahi sake sauke numfashi Dr Abbakar yayi tareda kallon Abba da yayi nisa cikin tunani fuskarsa Babu wani alama dayake bayyanarda yanayin da zuciyarsa take ciki,
Zuwa yanzu zuciyarsa tafara riqewa da tawakkalin tabbas komai kaddarowar ubangijine,
Duk kaunar dayakewa 'yarsa yasan idan lokacinsa yayi Allah bazai barsaba,
Hakama Babu wata qaddarar da Allah ya sauko Mata dazai iya sauya Mata,
Results dinsa sun nuna infection daya shiga qashinsa tun farko farkon hadarin da ba'a yanke qafafunba sunyi yawanda harsun fara shiga jininsa,
Tabbas yasan yanda yakeji ajikinsa lokacinsa yakusa zuwa
Saidai duk ya kalli Layla da rayuwarda zai barta aciki hankalinsa tashi yakeyi yabar jikinsa,
Tsoro da fargaba tareda kukane suke lullubesa aduk lokacinda yayi tunanin hakan.
Alhaji MAHMOUD tabbas rikicewar lafiyarka a Yan lokutan Nan sunada babbar nasaba da damuwa da kuncin dakake Tarawa aranka,
Da zaga sassauta damuwa da tunani kasamu hutun zuciya Dana qwaqwalwa ko yayane za'a ringa samun sauki ko yayane.
Sunkuyar da Kai Abban yayi ahankali cikin irin yanayinsa na masu ciwo irin nasa batareda ya iya ko dago idanuwansa ya kalli Dr Abbakar din ba.
Shiru sukai tsawon mintuna kafin Dr Abbakar din ya miqe tsaye Yana kallon abban cikin kulawa yace"
Zan tafi gobe zandawo zamu sake dibar sample ajikinka Inshallah saimu gwada wani awon mugani,
Allah yaqaro lfy.
Juyawa yayi ya fice daga dakin har lokacin Abban Bai motsaba Yana yanda yake.
Ahankali idanuwansa suka sauya zuwa ja jikinsa na daukan zafi na wani irin zazzabi Mai qarfi daya saukar Masa atake saidai zuciyarsa ta riqe yakasa tunanin komai saina Mutum daya daya fado Masa a Rai wato babban Amininsa Wanda shikadaine zai iya magance babban abunda yazo ya tokare ransa tsawon shekaru wato damuwar Laylah.
#MAMUH#
πππKuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete ππ
Mamuhgee @Arewabooks
*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin?_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne_
_Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi_
*_NoorAlbi#MAMUH_*
Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biyaππΌ
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
[6/2, 11:19 PM] MGπ: *_NOOR ALBI_*
*_Mamuhgee_*
3
Tana zaune tsakar gidan tsaye bakin kicin tana wanke hannu a fanfo Dr Abbakar yafito ya fice Tai Masa asauka lfya cikin biyayyarta
Ya amsa Mata cikin kulawa shima ya fice.
Qarasa wanke hannayenta tayi sbd miyar abincin da anty Sa'adah ta zubar a Palo batareda sani ba tagama kashewa shine take wanke hannun,
Kofar palon abban ta nufa Kai tsaye tashiga da sallama
Har lokacin Yana yanda Dr Abbakar yafita yabarsa cikin zurfin tunanin abinda ke addabar zuciyarsa da shawarar dayake nanatawa kansa akan ya yanke Dan inganta rayuwar yarsa ko baya Raye ko Yana raye
Tabbas idan tana qarqashin inuwar Amininsa Kuma Aminin mahaifiyarta zata samu gata da kulawa tareda samun Amintacciyar rayuwar kwanciyar hankali.
Kai tsaye gurinda flask din abincinsa yake ta nufa tafara daukan flask din ta bude wani tiririn zafi da qamshin kunun alkama da gyada ya ringa fitowa daga ciki
Ta dauki dauki cup daya cikin cups din Dake gurin wainda aka Ware musu aka Bata na Abban
Ta tsiyaya kunun Mai Dan yawa aciki kafin ta maida sauran ta rufe ta dauki kofin ta baro gurin bayan ta jefa cokali aciki tana juyawa ahankali ahankali Dan ya huce ta nufi gurin Abban tana kallon yanayinsa da a fili qarara yake nuna yayi nisa a tunani.
Aje kofin tayi tafara tura kujerarsa zuwa bakin windo bayan tasake yaye musu labule sbd iska Dan yanzu tana basa kunun zufa zai taso Masa.
Janyo tata kujerar tayi ta zauna gabansa tareda aje tissue gefensu ta dago fararen idanuwanta ta kallesa cikin kulawa shima ita yake kallo
Ahankali tasaki wani irin murmushin dayasa Abban rufe idanuwansa ahankali sbd murmushinta bakomai yake bayyanawa ba sai zallar tausayinta.
Saida ta tabbatarda ya huce ba zafi kunun ta dauka tafara basa ahankali da spoon ta nufa bakinsa,
Sam bayajin yunwar Shan komai ayanzu sbd damuwar dayake cikinta sosai,
Jin inda lafiyarsa ta dosa ya wargaza duk wani Dan sauran qwarin gwiwarsa da dukkanin jarumtarsa
Tunaninsa 'daya yanzu yanda zai Fadawa *_TURAKI_* buqatarsa Dan kuwa wannan babban abune Mai girma zai roqa agurinsa duk da girman banbanci masu tarin yawa dasuke cike a tsakani.
Sbd kawar da sabuwar damuwar da hanata shiga wani sabon halin yasa hakanan take basa abincin Yana sha tanayi tana goge Masa da tissue
ahaka yakesha har sukai nisa yakusa shanyewa.
Cikin nutsuwa ta Dan kallesa kafin ta bude Baki kamar ko yaushe da taqaitaccen sauti tace"
Koma menene sakamakon asibitinka
Bana cire Rai ga falalan ubangiji akan samun sauki da lafiyarka.
Karka saka sabuwan damuwa
Ko ahakan Ina godiya ga ubangiji daya bani ikon tasowa nayi rayi rayuwa da mahaifina.
Kallonta yake da idanuwansa dasuke jajir har lokacin zuciyarsa na sake zurfafa da tunani.
Tas tagama basa kunun ta dauko maganinsa shima tabasa kafin ta goge Masa ta dauko wani Dan turarensa da baya yanke musu Abdullahi ke siyowa ta 'dan fesa Masa kadan sbd abdullahi din yamasa wanka kafin zuwan dr Abbakar
Tana gamawa ta fice Dan yau tana Dan da ayyuka
Ga wankin Momy ma ta Tara gwara na anty Sa'adah ta rage Mata jiya tayi abunta da kanta.
Harta fita Jin zafi a garin yasa tadawo ta turo kujerarsa ta fito dashi tsakar gidan Dan Tasha iska musamman dayake yamma tafarayi ba rana.
Wankin kayan Momy tafara a natse sai kayan anty Sa'adah kadan Wanda anty Sa'adah din Bata qarasa ba jiyan tana cikin Yi anty Sa'adah ta fito ta zaune gefen Abban daukeda takardunta na makarantar jami'a datakeyi tana karatu Dan tanada test a satin.
Sama sama take karatun tanayi tana Jan laylan da surutu duk da tasaba Laylah ba wani surutun zataiba musamman ma datake aiki Amma dai Haka sukeyin surutun sama sama tana yiwa Laylan bayanin wasu abubuwan dake cikin handout dinta tunda ita Layla Bata karatu tunda tagama secondary School last year shikenan iya inda nata karatun zai tsay kenan Kuma
Dan Momy tariga tafadawa Sa'adah da Abban hakan,
Bazata iya qarawa daga Nan
Tayi iya abinda taji zata iya
Idan akwai Wanda zai iya daukan karantun nata acikinsu biyun bismillarsu zasu iya dorawa daga Nan,
Shi dai Abba yasan baqar maganace tafada Masa Amma ko ahakan ya gode Mata Dan Koda laylan makarantar datai ta gwamnati ce yaga alamar tasamu ilimin Dan Haka shi ahakanma ya gode matuqa.
Sallamar momyn ce data dawo daga fitar datai tasaka Anty Sa'adah kallon kofa ita Kuma Laylah sauke kanta tayi qasa tana cigaba da wankin sbd sanin fuskartace abinda yafi komai tada zafi da ciwon Dake qunshe cikin ran momyn na shekaru yasa so da dama ita da kanta take dauke kanta da duk inda momyn zata kalleta din.
Kallon abban Dake zaune zugum idanuwansa a rufe yanajinsu sbd ganin yanda rayuwar yaransa biyu takeda banbanci Mai girma.
Direct Palo take neman shigewa Sa'adah tace Mata"
Momy zafi ake sosai fa gashi kin dawo kilama kin gaji.
Matuqar Laylah ko abba na guri bakajin muryarta cikin sakewa ko walwala Dan Haka batareda ta juyoba ta qarasa ciki tana cewa"
Bari nayi sallar la'asar saina fito ai.
Tana shigewa ciki Laylah ta tsame hannuwanta daga ruwan wankin ta dauraye tareda gogewa ta miqe taje ta dauko babbar daddumar da momyn ke zama akai ta dawo ta Kama kujeran abbanta ta matsar dashi gefe kusada ita sosai kafin ta shimfidawa momyn daddumar ta dauko Mata ruwa da abincinta duk ta aje Mata akai kafin ta koma ta juyarda kayan wankinta dayan gefen tana fuskantar abbanta sbd bawa momyn baya kamar yanda yake tun yarinta.
Wankinta taci gaba dayi har lokacin Sa'adah na janta da labari Amma tunda momy ta fito tayi tsit bayan motsin wankinta Babu abinda ke tashi sai qarar cokalinda momyn kecin abinci
Sa'adah ma datasan Laylah bazata Kuma maganaba Kuma saitayi shiru tamaida firarta gurin momyn.
Kusa rayuwar gidan gabaki dayansu Sa'adah ce kawai wadda Allah yabawa ikon gudanar da rayuwarta cikin walwala da sakewa tareda wadataccen kwanciyar hankali da nutsuwa harma da farin ciki sbd Sam bata dauka komai tasakawa rantaba,
Abban nema so da dama batada shaquwa dashi Sam Sam sbd farko datana yarinya abunda yafaru yaso cusa Mata tsanar mahaifin nata Amma Kuma qaunarta da 'yar uwarta da batada kowa saishi dakuma yanda shima Bai boye qaunar Laylah din ba ko a idanuwansa yasa takasa riqe komai aranta saima Suka dawo tausayinsu yayi rinjaye akan Jin zafin cin amanar da yayiwa momynta da mahaifiyar Laylah din Dan Haka tana qaunarsa saidai ba wani shaquwa a tsakaninsu musamman dayake Mata kallon wadda sbd itane mahaifiyarta take taimakonsu take riqe dasu duk da hakan ta wani bangaren itama Yana farin ciki da ingantacciyar rayuwar farin ciki da kwanciyar hankalin datake.
Sai gab da magriba tagama wankin lokacin tuni Momy tayi baquwa suka shige ciki Dan hakama wankin nata yayi sauri cikin tayita tashi kaiwa baquwar momyn ruwa da abinci.
Jin anfara Kiran sallar magriba yasa ta aje shanyar datake ta goge hannuwanta dasukai sanyi ta nufi gurin Abban da idanuwansa suke zuru dan dama hakan suke rayuwar kullum.
Maidasa ciki tayi tasaki labulai sbd sauro tana kokarin fitowa saiga abdullahi yashigo tace"
Anyi sallah Yaya abdullahi shima Abban sai yayi.
Eh dama shine nashigo Dan dubawa.
Ficewa tayi shikuma ya qarasa ciki yaja Abban zuwa toilet din dake dakinsa Dan Koda Abban na buqatan toilet.
Har aka gama sallah Bata Gama shanyarba Saida aka sallame tagama ta tattara gurin ta share ta tsaftacesa ta watsa ruwa tayo tata alwalar ta nufi ciki ta wuce dakinta direct tasaka wata baqar jallabiya ta tada sallah.
Bayan tagama sallar dakin Anty Sa'adah taje ta dauka Qur'an ta nufi palon abbansu ta zauna gefensa tafara karatun al qur'an din cikin zuciyarta har akai sallar ishai anan palon tayi sallah bayan tagama taga alamar shima sallar yakeyi Dan Haka Kai tsaye ta nufa abincinsa ta zubo ta tareda zuba Masa ruwa a wani kofin ta daukosu tareda magani tadawo gabansa.
Tana Gama basa komai ta gyara Masa koina abdullahi yazo ya daukesa daga kan kujera ya maidasa Kan gadonsa Tai Masa addua ta fice shima abdullahin tare suka fito taja Masa kofa.
gurin Anty Sa'adah ta nufa Dan karatun dare datake koya Mata na littafan addini.
Acan takai kusan karfe goma na dare suna karatun kafin ta harhadawa anty Sa'adah dakin ta gyara Mata shimfidar gadonta dasuka zauna Baki taje ta dauko Mata ruwan dare datake yawan tashi Sha ta aje Mata kafin ta fito taje ta rufe gidan da koina ta nufi nata dakin tayi Shirin kwanciya tayi addua ta kwanta.
πππKuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete ππ
Mamuhgee @Arewabooks
*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin?_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne_
_Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi_
*_NoorAlbi#MAMUH_*
Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biyaππΌ
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
[6/2, 11:19 PM] MGπ: https://arewabooks.com/book?id=628264fab77ff582983da456
*_NOOR ALBI_*
_*Mamuhgee*_
4
Washe gari tunda safe da hadari Mai qarfi aka tashi da iska
Da sauri ta fito palon ta nufa windunan dake palon guda biyu ta rufe ta nufi dakin momyn da sauri ta bude ahankali sbd karta dameta da motsinta
bakinta daukesa sallama ta shiga
Momyn na kwance kan gadon ta nufa windon dakin ta rufe ahankali ta fito ta nufa dakin anty Sa'adah itama ta rufe Mata nata windon kafin ta fito tsakar gidan lokacin iskan yaqara qarfi da gudu ta qarasa dakin abbanta ta rufe Masa koina duk da idonsa biyu bata tsayaba sbd aikin gabanta ta fito da hanzari tafara kwashe shanyar wankin momyn datai jiyan duk wasu har zun fado sunyi qura tahau kwashewa zuwa lokacin tuni ruwa masu qarfi suka sauko ta shiga ciki da sauri ta aje kayan palon Kan kujera duk da tasanma saita Kuma wanke wasu
Ta fito tsakar gidan ruwan na dukanta tahau tattara kayan dake tsakar gidan takai na kaiwa cikin takai na kaiwa Palo tasake fitowa ta taje ta bude gida sbd Kar suna ciki Abdullahi yazo basuji bugun gidansaba.
Kofar kicin ta tsaya ta kakkama gefenΒ kayan jikinta ta Dan matsesu tarage musu ruwan dake tsayaya ta zame Dan kwalin kanta shima ta matse daga waje ta shanyasa Kan kofar kicin din sbd Kan yasha iska Dan kuwa ta barsa da dankwalin sanyin Kan Dana dankwalin suka hadu sanyi zai shigeta ya kwantar da ita
Babu ciwon Dake tsananin azabtar da ita kamar sanyi idan yashigeta
Gashi kwantawarta ciwo ba kyau
Wuya takeci Mai tsanani Dan duk rintsi saitayi aikin dake kanta ga abbanta idan ta kwanta batada Mai kulawa dashi Dan hakan nema take dannewa duk girman ciwo sai idan yafi qarfinta Dan Haka takeda kiyayewa akan lafiyarta.
Risho ta kunna ta Dora ruwan zafi ta hada qullun kunun alkamar dazatawa Abban Takoma ta zauna Kan kujera tana jiran su tafada wani irin sanyin ruwan da ake Yana ratsata tanaji.
Ba jimawa ruwan suka tafasa ta hada kunun ta zuba Masa a flask dinsa ta rufe ta juyewa Anty Sa'adah sauran a flask itama sbd tanashan kunu sosai itama musamman nata dayake da Madara take shansa sbd lafiyar fata Inji momy.
Cikin ruwan takuma fitowa takaiwa bbanta ta basa Tasha tabasa magani ta goggoge Masa jiki ta fito Yana binta da kallo yanda take jiqe sharkaf sai Kama jiki take karta jiqa Masa daki Takoma kicin tahau aikin abincin karin kumallonsu momy.
Dakin Sa'adah taje cikin rashin son takurata daga baccin datake tace"
Anty Sa'adah me za'a dafa na Karin?
Cikin bacci Sa'adah ta juya tana sake shigewa Dan madaidaicin bargonta tace"
Laylah duk abinda kikai Amma dai karki manta da kunu na.
Anty Sa'adah jiya Momy bataci abincin dareba sosai Naga abincin yayi saura ko ulcer dinta ya tashine saina dafa Mata ruwan tea da faten dankali kawai.
Kimata duk yanda kikai kaina na ciwo bacci nakeji sosai.
Juyawa tayi Takoma kicin din tahau aiki.
Wani maganin ulcer din momyn tafara dafawa Mai wuyar dahuwa Haka taita jira har yayi kafin ta dafa taliya Mara yaji ko kadan sbd momyn ta juye a kula ta zuba Mata maganin a babban kofi ta saka Mata a fridge duk da Babu wuta zaiyi sanyi sbd ruwan sanyin Dake ciki.
Tana gamawa anan kicin din taci abincin sama sama tagama tai wanke wanke ta sharesa tsaf ta fito lokacin ruwan sun Dan rage sosai sai Dan yayyafi ta nufi dakinta tacire kayan jikinta ta watsa ruwa ta sauya zuwa wata atampar tafara gyara nata dakin fes ta fito tafara aikin gyaran palon tana gamawa tashiga na mum tayi Takoma na anty Sa'adah tayo tafito tsakar gidan shima Tai Masa tas kafin ta fita tasamo garwashi maqota tazo tayi turaren wutarda momyn qaidane sai anmata shi Dan tanason qamshi.
Gurin abbanta ta nufa ta gyare Masa koina taje ta dauko Dan sauran burbushin hayaqin turaren daga palon Momy takawo Nan dakinsa shima yasamu Dan qamshin ko yayane,
sai alokacin ta zauna gabansa bayan ta aje kaskon turaren cikin kulawa a natse Tai Masa Ina kwana tana kallon idanuwansa dasuka qanqance Suka sauya launi da alama Bai samu bacci ba ta dauko ruwa tasake bashi yasa cikin kulawa a natse tabude Baki tace"
Abba?
Akwai wani matsala da kakeji ne?
Saida ya Dan hadiye yawun dayake hadiyewa da dabara daqyar shiyasa shi nasa ciwon baya zubarda yawu ta gefen Baki Allah ya taimakesa saboda saukin dayake samun Yana iya hadiye yawu.
Dan rintse idanuwansa dasukai laushi yayi ahankali alamar yanada damuwa.
Faduwa gabanta yayi da qarfi saidai fuskar Bata nuna hakan
Ta zuba Masa fararen idanuwanta batareda ta iya cewa komaiba.
Hannunsa Dake rawa da gyangyadi yadan daga yayi Mana alamar karta damu bayajin ciwon komai.
Shiru kawai tayi Dan batasan Mai zataceba bayan jurewa ta boye damuwarta sbd ko nacewa tayi tasan abinda yake damun nasa Babu abinda zata iya Masa bayan tashiga qunci da damuwa sai addu'a da take Masa.
Shiru sukai daga ita harshi Dan ko Dan zancen datake Masa wasu lokutan takasa sbd mutuwa da jikinta yayi dakuma damuwar datashiga yanzu din akan yanayin nasa tasan Dole Kam akwai abinda yake damunsa tsakanin jiya zuwa yau din.
Ganin gwara ya kwanta kozai samu baccin yazo Masa yasa ta tashi ta tura kujerarsa har bakin gadonsa da kanta ta mirginasa zuwa Kan gadon ta gyara Masa kansa akan pillow ta rufe Masa Rabin jikinsa sbd akwai sauran sanyi sosai na ruwan saman da aka gama ta bude Masa windows Dan iska da Sanyi na shigo Masa ta fice Takoma dakinta itama ta zauna jigum sbd Haka tata rayuwar take.
Sai qarfe kusan goma Sha daya saura momy da anty Sa'adah suka fito dayake komai takawo musu palon na Kari suka zauna karyawa
Ita Momy tuni tayi wanka kafin ta fito.
Motsinsu yasata aje littafin datake karatu na koyan wasu abubuwan addini da anty Sa'adah tabata ta aje gefe tareda miqewa ta fito.
Bata tsaya ba kicin ta nufa