Showing 63001 words to 66000 words out of 108894 words

Chapter 22 - NOOR ALBI COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

29

Middle Ads

top sai printed Blazer blue data Dora akai da scarf da qatuwar cold jacket sbd hakanan takejin sanyi sosai cikin jikinta.

Lipstick din bakinta yanda ya zauna daram da eyeliner dinta zaka dauka ahakan zasu zauna bazasu gogeba musamman yanda fuskarta ke glowing kamar wadda Tai makeup Amma Sam Bata wani makeup iyakacinta lipstick da eyeliner Suma Dan kamar tasan sunfi komai yimata kyau.

Qamshinta yasa Cindy dake kitchen tana aiki dagowa Suka hada Ido ta lumshe ido tareda sakin Ajiyar zuciya sbd bazata iya goge abin daya riga yafaruba Dan Haka ta kalli Cindyn Kai tsaye tace"

Thank you.

Gyada Kai Cindy tayi kawai tareda nunawa Laylan breakfast data kusa kammalawa tace"

The breakfast will be ready in 10min.

No Cindy I can't wait, am late for my school already...

Madara kawai ta karba Tasha ta fice tana fiddo key din motarta daga handbag dinta ta fice.

Sai yamma tadawo gida tashige ta tube tayi wanka a daki Cindy takawo Mata noodles data sakata tadafa Mata taci takwanta sbd bacci datake masifar ji.

Da daddare harsun fara cin abinci ta fito ta nufi dakin cin abincin sanyeda Riga da wandon masu kauri na bacci sbd sanyi takeji harda socks ta Sanya.

Kallon fuskarta mum tayi lokacinda take gaidasu taja kujera ta zauna.

Cikin kulawa tace"

Laylah lafiyarki kuwa kayan sanyi da Daren Nan harda socks?

Lumshe ido tayi Ahankali tace"

Sanyi nakeji mum.

To lafiya kalau kike kuwa?

Yes mum kawai gajiyan school ne.

Yanajinsu Amma Bai dagoba Bai Kuma daina cin abincinba qarshe dai miqewa yayi ya fice daga dakin yabarsu.

Sun Jima gurin Cin abincin itada mum daketa Mata zance dabam dabam har suka Gama Suka fito mum din ta wuce dakinta itama ta wuce nata.

Tana Shiga dakinta ta rufo kofar tareda nufar toilet Dan yin brush.

Tana cikin yin brush sai jin tayi anrungumota ta Bata tareda Dora kansa Kan kafagarta Yana kallon fuskarta ta cikin madubi da idanuwansa dasuka kashe jikinta daga brush din datake ta zuba Masa ido tacikin madubin itama tana kallon yanda shima yake kallonta.

Ahankali ya dago hannunsa daya yakai Kan hannunta data tsaya daga brush din tana kallonsa yafara yimata brush din ahankali Yana magana cikin kunnenta wadda ita kadai tasan meyake fada saidai wani irin murmushi da kunyane Suka rufeta lokaci daya tareda wata muguwar qaunarsa data Gama cikata tun kwanaki.

Yanda yake cigaba da magana cikin kunnenta da qaramin sauti Mai tafe da wani sanyayyan numfashi Mai dumi zuwa cikin kunnenta yasata juyowa gabaki daya tana kallonsa ya dobo ruwa Yana wanke Mata Baki Yana binta da kallo.

Yanda take wanke bakin cikin wani salo kamar batason Yi yasashi janyota ya matse jikinsa Yana kallon fuskarta yace"

Are you testing my patience??

Wani murmushi tasake tana Masa wani irin kallo tace"

Why wll I do that??

Dan juyar da Kai yayi Yana sake wani qayataccen murmushi yakai hannu ya fara zare band din Dake daure da gashinta ya jefar Yana nufar kunnenta da wata sabuwar murya ya furta"

Bansaniba Zan gwadane na gani.

Maganarsa tasata juyar da kanta ahankali gefen fuskarta ya shafa wuyansa ya sake matseta jikin bangon toilet din Yana shinshinar gashin kanta dake qamshin Aveda zuwa wuyanta da qamshin _All over body spray_ na Tom Ford..

Yanda yake shinshinata yasa duk tsigan jikinta tashi ta qanqamesa tana kokarin kallonsa ya cirata ya Dora akan inda tagama Gama brush yafara yamutsata.
Dakin Suka dawo inda Suka cigaba da abinda suka faro toilet din...
Wannan karon dayake sunriga sunyi sabo da yanda suke gurzan juna ba qaramin dumi komai ya daukaba kafin suka samu nutsuwa.

Tana yin wanka takwanta bacci ya dauketa ajikinsa take.
Saida bacccinta yayi nisa sosai kafin yayi wankan shima lokacin dare yayi sosai ya nufi office dinsa na cikin gidan ya dauko iPad dinsa da wasu abubuwan dazaiyi aiki dasu bayan asuba ya dawo ciki ya Haye sama Yana shiga bedroom dinsa ya tadda Ms Na'ima kwance kan gadonsa tuni tayi bacci saidai shigowarsa yasata farkawa sbd da tunanin inda yaje baccin ya dauketa..

Kallonsa take cikin dan mamaki da bacci a idonta sai idonta ya sauka a hannunsa,
Ganin abin dake hannunsa yasata komawa ta kwanta batareda tace komaiba sbd iPad da takardun hannunsa sun nuna daga office dinsa na cikin gida take.

Aje kayan hannunasa yayi ya dauko redbull drink yazauna a sofa Yana Sha anatse idanuwansa a lumshe.

Washe gari daqyar tayi Shirin makaranta ta fice Dan kamar harda zazzabi takeji na gajiya Haka dai ta lallaba ta wuni a school din dagacan ta wuce gidansu Sofia acan Suka qarasa wunin sai dare tadawo gida tana dawowa wanka kawai tayi ta kwanta sai bacci.

Washe gari da safe tana tashi taga text dinsa yayi tafiya.
Daga school yauma spa Suka wuce da Sofia sbd mum Yana tafiya itama tayi tafiya zuwa Dubai zasu hadu da Haj Zinat acan suyi wani siyayyan kayan kasuwancinsu Dan Haka gidan ita kadai ke kadaici saisu Cindy dake debe Mata kewa dasu Anne da Babu ranar da basa waya
Anty Sa'adah kuwa sun saka Rana zasu sake zuwa dubo abbansu ance ya samu sauki sosai Ana tadashi ya zauna Yana ganin kowa magana da sauran motsa jiki sosai ya rage Dan Haka ta matsu taje tagansa Dan Haka tana waya da abba Turakin bayan isarsa Australia ta sanar Masa tanason zuwa dubo abbanta zata siya ticket yace ta jira kwana biyu zaiyi yadawo.

Mum kuwa data buga ta sanar Mata zata dubo abbanta hanawa tayi Kai tsaye sbd Bata kaunar yawan tafiyar Laylan yanzu dan kada tasamu Wanda zata fara soyayya dashi batareda manufarta akanta tagama cikaba,
Nacewa Laylan tayi da rokonta Amma mum din taqi Haka ta hakura washe ba zato sai gashi A Abdoul yazo ya dauketa suka nufa airport basu Bata ko awa biyu ba sukabi flight.

Koda suka Isa tayi mamakin samun Turakin ma garin already Dan Haka ranar Basu samu zuw asibiti dubo abbanta sbd zafin jiki na zazzabin tafiya dakeson kamata sai washe gari Suka tafi lokacin Abban na bacci momy kuwa tun kafin su iso tabar asibitin dataji labarin zuwansu daga Sa'adah wadda Bata isoba tkuna sai gobe ko jibi Inshallah.

Suna dawowa tun a mota jikinta da yayi Sanyi rashin ganin Momy yaqara daukan zafi Dan Haka suna dawowa gida abincima daqyar taci tayi sallah ta kwanta bacci ya dauketa.
##MAMUH#
[6/22, 9:28 AM] MG💋: *_Mamuhgee 34_*
Washe gari lafiya kalau ta tashi da qarfinta ba zazzabi ko wani ciwon jiki Dan Haka wanka tafara Yi ta fito sanyeda bathrobe kanta a daure da qaramin towel jikinta daya qara haske sosai sai wani daukan ido yake musamman 'yar kyakkawar fuskarta,

Zaune yake Yana amsa waya sanye da fararen Armani's tafito tana tafiya cikin wani yanayi na daukan hankalinsa
Ya miqa Mata hannu daya Yana kallon gaban rigar wankan da Bata rufe dukaba..
Maimakon ta Kama hannun nasa qaqarin wucesa takeyi ya kamo hannunta tareda janyota kansa da dan qarfi harsaida ta saki wani siririn ihu cikin kunnensa daya sanyashi kusan dauke wuta daga wayar dayake,
acan bangaren Anne kuwa Dake waya dashi kunnuwanta Suka jiyo Mata ihun duk da Babu sauti sosai.
Shiru tayi tsawon seconds tana nazarin tasan Na'ima na Dubai,
Kasa shiru tayi sbd zuciya irin ta uwa zatafi kowa baqin ciki da takaicin ace Turakin na wata hulda da Mata bayan ta aiki Kuma adaidai wannan lokacin tasan Bai Isa fita aikiba Dan Haka cikin nutsuwa taso tambayarsa muryar wadda taji sai Laylan tayi wani juyo ajikinsa tana kokarin tashi kirjinta ya mannu da nasa sosai take ya kashe wayar Dan kuwa Annen zata iya Jin abinda Bai kamataba.

Yana kashe wayar yayi switching nata off gabaki daya ya ajiye gefe Yana Kama tafukan hannayenta dakeda Dan sanyi ya matsa Ahankali tareda dagowa ya kalli fuskarta da tamkar fuskar Zainab ce aka zaro aka Dora Mata saidai kuruciya da haske tareda kyan fata ta hutu da Laylan tafi mahaifiyarta ya lumshe ido ahankali tareda kwantarda kansa cikin wuyanta ya sauke qaramin numfashi yana sake rufe ido cikin nutsuy Yana tuno lokacinda ya Ciro sadakin mahaifiyarta daya biyawa Aminsa ranarda aka daura auren Mahmoud da Zainab.

Hannu yakai ahankali ya rungumeta tsam tsam jikinsa wani irin sabon dumin shigarta jininsa nabinsa koina,
Dan kuwa ita kadaice takeda matsayi dabam dabam fiyeda daya agunsa kaf rayuwarsa,
Tana matsayin kyakkwan rabo na alaqar aure daya qulla tsakanin Aminsa da 'yar uwarsa dayakeda aminci sosai da ita,

Tanada matsayi na 'yar daya biya sadakin mahaifiyarta da hannunsa,

Sanadin haihuwarta ya Rasa lafiyarsa ta zamtowarsa namiji,

Akanta ya warke Wanda Allah ya yanke hukuncin akanta zai fara sanin mace shiyasa aranarda tazo duniya ranar ya Rasa lafiyarsa harsai data girma ta zama cikakkiyar mace a qarqashinsa,

Ga matsayi na Matar da igiyoyinsa uku na aure suke kanta,

Itace macen data fara saninsa Kuma mace daya data fara daukan cikinsa duk da ya bare ko ahakan yasamu tarihin yasamu rabo a duniya na ciki....

Kwantar da kanta datai a kansa Dake wuyanta ya sanyashi bude idanuwansa ya zuba Mata Yana kallon bakinta Dake saiti da nasa suna shaqar numfashin juna light kiss yabata Kan lips dinta kafin ya tayarda ita cikin nutsuwa yace"

Zamu fita,
ki shirya.

Gaban mirror suka nufa Yana tsaye bayanta ta shirya cikin doguwar _Annah Hariri_ Abaya wadda shine yayi Mata odarsu jiya ganin duka kayanta qananune Babu na zuwa gurin abbanta.

Makeup tayi daidai yanda ta saba bakin Nan yadauki hot red lipstick qamshinta Dake tashi ajikinta shi kadaine yake jinsa sbd ya hanata sanyawa da yawa matuqar zata fita sbd jiyan a asibiti duk inda ta motsa qamshinta kawai ke tashi yana birkita kansa.

Fitowa sukai ga breakfast Nan jere a dining Wanda A Abdoul yayi ordar
Suka zauna taje ta dauko duk wani abun buqata sukai breakfast din suka fito suka nufa asibiti.

Shiru sukai a motar hannunsa na riqe da nata kowa na tunanin yanda zai hadu da Abban musamman a yanayin dasuke ciki kallo daya Abban zai musu zai iya gano abinda yake faruwa da ita da Abba Turakin..

Tunanin hakan ya hanata nutsuwa da sukuni,
Tsananin kunyar Abban da momyn ma takeyi tanajin Kamar zasu Gama gano abinda yake faruwa da ita.

Ahankali cikin nutsuwa ya waiwayo ya Dan kalleta Yana maida hankalinsa Kan wayar dayake tabawa da hannu daya cikin muryarsa mai nutsuwa da kamewa yace"

All ok???

Numfashi ta Dan sauke jikinta na mutuwa tace"

Tare zamu shiga gurin Abban?

Tambayarta ta sanyashi Dan kallonta kadan tareda basarda yanayin yace"

No,zamu ajeki idan nadawo Zan shigo.

Ajiyar zuciya tasauke ahankali Jin abinda yace shima Daman bazai iya Shiga da itan ba kunyar Amininsa yakeji,
Bazai iya kallon cikin idonsa ba bayan abunda ya tsakaninsa da 'yarsa yanzu duk da bazaiji komaiba idan shikadai zai tunkari Mahmoud dinba,
Da ita dinne bazai iya fuskantar Amininsa ba da baya iya boyewa kowane sirrinsa Amma yanzu Kam Banda wani.

Parking driver yayi A Abdoul Dake gaba gefen driver ya fita yabasu guri.

Hannunta Dake cikin nasa yayi kissing ahankali tareda furta"

Take care.

Gyada masa Kai tayi Ahankali tareda budewa ta fito suka wuce ta qarasa ciki fuskarta sanyeda sunglasses na Prada sai heels Dake qafarta da handbag din LV.

Kai tsaye dakin abbanta ta nufa cikin sa'a tana knocking kofar ahankali ta Murda ta tura Momy Dake zaune tana Masa waya shigowarta kenan ta dago Suka hada Ido.

Faduwa gabanta yayi ganin Momy
Ta sauke idanuwanta qasa dama ta zare glass Dake idonta tun data iso kofar dakin.

Ahankali taqaraso gefen momyn tareda sunkuyawa cikin tsananin girmamawa anatse tace"

Momy Ina kwana?

Wayar datake kashe batada ikon fita tabar dakin tunda Laylan tariga tashigo Kuma ga Abban idonsa biyu tun shigowar Laylah ya zuba Mata idanuwansa Dake bayyanarda tsananin farin cikin da zuciyarsa take ciki na ganinta gabansa ayau din,
Hannu yakeson miqa Mata Amma ba Hali Dan Haka wani sanyayyan murmushi ne mamaye Kan fuskarsa datai haske sosai na ciwo dakuma hutawa da fatarsa keyi.

Batareda Momy ta juyo da kyauba ta kalleta ta amsa gaisuwarta tana koma gefe ta zauna Kan lafiyayyar sofa Dake dakin ta dauki news paper tana dubawa sbd itama zamanta a turai tasamu cigaba na wayewar Kai da zurfafa Dan iliminta sosai ba laifi duk da matsi da takurawar dasu umma Jamila dasu Haj Karima sukai Mata Akan tadawowarta Nigeria sbd suna buqatan Shiga jikin Sa'adah sosai Amma ba dama sbd koyaushe cewa ake Bata qasar itama duk sukai waya da ita Bata Nan koyaushe cikin tafiye tafiye take Dan Haka sunsan ko zata Bari sushiga arzkin gidan AB TURAKI sai uwarta data haifeta tadawo Nigeria tunda ita sunada dama da ikon juyata son ransu,
Ita kanta momyn ta matsu a sallami Abban su tattara sukoma Nigeria ayita aqare su umma Jamilan Susan bada Sa'adah aka daura aurenba.

Jikinta sanyi yayi da yanayin momyn Dan kuwa har gobe har ranarda numfashinta zai barta bazata daina Jin kauna ga girman Momy a rantaba,

Idanuwanta ta maida Kan abbanta Dake sakar Mata murmushi taji wasu hawayen farin ciki na cikowa idanuwanta ta qarasa gurinsa ta rumgumesa Yana zaune
Ahankali hawayen idonta Suka gangaro takira sunansa cikin wata murya dake bayyanarda irin kewarsa datai tace"

Abba nayi kewarka,
Abban kullum da kewarka na tashi na wuni na kwana.

Murmushinsa qara fadada kawai yakeyi yanajin inama zai iya rungumarta shima,
Wani irin kauna yakewa Laylah fiyeda kansa da duk abin dayakeda a duniya,
Qaunarta daban take a Zuciya da rayuwarsa,
Bazai taba kaunar laylansa da kowaba sai Sa'adah wadda yake kaunarta sosai saidai tausayin maraicin Layla da rayuwar data taso ciki yasa qaunarta ta dara ta Sa'adahn cikin ransa bawai Dan fifikon ganin damaba kawai.

Sun Jima ahakan cikin tsananin kewan junansu kafin ta sakesa ahankali ta dago tana kallonsa idonta har lokacin da sauran hawaye tasaka fararen yatsun hannunta Dake sanye da zoben white gold guda biyu marasa hayaniya ta share hawayenta tareda sakin murmushi tana sake kallonsa tace"

Abba Allah yabaka lafiya naji muryanka kaman yanda kowa ke ji muryan mahaifinsa,
Naji ka Kira sunana da bakinka ka sanyani wani aikin.

Kyakkyawan murmushi yasake Mata Yana Dan rufe ido alamar ranar na zuwa Inshallah.

Momy na zaune har lokacin tana jinsu Bata waiwayo ta kallesu ba,
Haka ta wuni tana zaune maqale kusada abbanta har yamma,
Abinci ma aranar itace ta basa sbd tayi tsananin kewar hakan sai gap da magriba Anty Sa'adah ta iso Kuma daga airport direct asibiti tazo Dan Haka tana shigowa da tsananin murna na farin ciki taso tarbanta saidai ganin Momy na zaune Kuma ita ta tarba Yar tata shiyasata dakatawa Bata Isa gurin Sa'adah din ba saidai daga inda take cikin takaita bayyanarda farin cikinta sbd gudun batawa Momy Rai tayiwa anty Sa'adah din barka da zuwa tareda miqewa ta janyo Dan qaramin akwatinta na lv guda daya data zo dashi takai gefe ta aje.

Gurin Abba Sa'adahn tazo cikin nutsuwa da farin cikin ganinsa ta zauna gefensa tana gaidasa tareda Masa ya jiki.z

Zuba Mata idanuwansa yayi Yana kallonta cikin farin ciki tareda tausayinta Mai girma cikin ransa,
Tabbas Sa'adah Mai hakuri da tawakkali ce tunda Bata Bari son abun duniya ya hanata barin Yar uwarta ta auri Wanda akace dinba,
Kawu saidu ya sanar dashi komai Dan Haka har abada bazai daina sakawa Sa'adah albarka ba gode Mata.

Tunda Anty Sa'adah ta iso Momy take Nan Nan da ita sai jikin Laylan yasake yin sanyi tanason sakewa da anty Sa'adahn Amma ta Kama kanta sbd gudun bacin ran momyn.

Ana Gama sallar magriba saiga A Abdoul yayi knocking ahankali yashigo dakin sanye cikin white Balenciaga sleeves da blue Armani trousers sai jacket din sanyi Mai tsayi datakai gwiwarsa,
Qamshin turarensa na D&G na tashi ahankali ya kalli Momy cikin tsananin girmamawa ya gaidata...

Dayake ta Saba dashi sosai sbd komai na dawainiyarsu shi yake zuwa yayi shiyasa sukeda sabo cikin sakewar fuska da kulawa tace"

Lafiya kalau Abdoul, Jiya saika tafi baka Bari nadawo ba.

Murmushi yayi Yana cewa"

Nakira wayanki naji akashe shiyasa na wuce din kawai...

Zatai magana sukaji shigowar Turaki Wanda qamshin turarensa yafara shigowa dakin kafin shi din yashigo Yana sanye cikin navy blue Ralph Lauren Kaftan St, Hasken fatarsa yafito sosai sbd duhun kayan jikin nasa hannunsa dake sanyeda agogon diamond Rolex riqeda wata paper bag da tsadadden turaren dayasan Amininsa Yana amfani dashi tun lokacin Yana lafiyarsa cikin arzkikinsa yasaba duk zaizo gurinsa saiya zo Masa dashi Dan Haka cikin nutsuwarsa da kamewarsa ya qarasa shigowa dakin duk sukai tsit suna Dan rage kallonsu daga kansa,

Sa'adah kallo daya tayi Masa ta Dan sauke Kai tareda bude Baki ta gaidasa cikin girmamawa,
A hankali ya amsa tareda Dan kallon gefen Momy suka gaisa Yana tambayarta jikin Abban Dake kallonsa da dukkanin kauna irin ta Dan uwa na jini dayake jinsa.

Daga inda take zaune ta saci kallon abbanta da Momy harma da anty Sa'adah kafin ta Dan saci kallon gefensa taga yanda kwarjininsa duk yabi ya cika idon dukkanin wainda ke dakin sai Taji kunyar da Babu dalili ta kamata Dan Haka ahankali itama cikin nutsuwa kanta a qasa tace"

Abba barka da shigowa.

Bai waiwayoba ya amsa Mata a gajarce cikin kamewa sbd idan yayi gangancin waiwayowa ya kalleta gurin amsawa za'a iya gane halinda suke ciki Dan Haka gabaki daya hankalinsa na Kan Mahmoud dayake magana dashi.

Miqewa tayi ta sulale ta fito Momy ma dama duk fita zasuyi Dan Haka gabaki dayansu Suka fito dakin aka barsa daga shi sai Abban.
##MAMUH#
[6/23, 9:37 AM] MG💋: *_Mamuhgee 35_*
Suna fitowa waje Momy taja Sa'adah suka nufa inda zasu zauna taje ta siyo Mata ginger drink Mai zafi suka zauna suna magana.

Itama zama tayi a can gefe tareda fidda wayarta jiki amace ta Rasa wa zata Kira saiga Kiran Anne ya shigo wayarta wani sanyayyan murmushi ne ya sauka Kan kyakkyawar fuskarta ta dauki wayar anatse cikin farin cikin Jin Annen tafara sauke nannauyan numfashi tace"

Nagode Anne.

Murmushi Annen tasake Jin irin numfashin da Laylan tasake na samun saukin damuwa kafin tace"

Kina asibitin ne haryanzu tareda Momynku kenan?

Sunkuyar da Kai tayi takuma sauke wani numfashin kafin ta dago ta saci kallonsu anty Sa'adahn yanda Momy ke magana da ita cikin tsananin kauna da kulawa irin ta mahaifiya zuwa ga yarta,
Jin tayi idanuwanta suna kokarin cikowa da hawaye akaro na farko dataji kewa da maraicin rashin uwa,

A da rayuwarta batasan Jin Dadi,yanci ko walwalaba,
Batasan wani kwanciyar hankaliba ko wata yancinda har zatai kewar uwa,
Batada lokacin kanta batada na mahaifinta koyaushe rayuwarta acikin hidima da dawainiyar Momy da Anty Sa'adah da dangin Momy take,
Bata samu yancin kewan tata mahaifiyarba sai yanzu datai rayuwar yanci,
gata,
Jin dadi da kwanciyar hankali,
Tabbas itadin marainiyace badan Anne da Abba turakiba harma da mum Na'ima dake kishiyarta sun Bata kauna da kulawar da Bayan abbanta da anty Sa'adah

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login